Kurman Allo Sakamakon Kin Karɓar Gaskiya by EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU

Author :  EEDAH ALIYU & ASMY B ALIYU Category :  KDP NOVELS

Chapter   24 / 80

69K to 72K   out of 237.2K words

a wannan lokacin
Da gaske tana son ta je ta gansa sai dai tana tsoron mami, kasa daurewa ta yi daga ƙarshe sai da ta tabbatar baccin Siyama ya yi nisa sosai ta fice daga ɗakin da sauri take saukowa kan stairs banda faduwa babu abunda gabanta ke yi ko takalma babu a ƙafarta saboda kar ta saka ƙararsu ya fito da Mami ta kitchen tabi zuwa bangaren yaya Abba, tana addu'a Allah yasa ƙofar parlorn sa abude take. Ta kama handling ɗin tana murdawa ta ji ya buɗe wata ajiyar zuciya ta sauke ta shige cikin parlor ta mayar da kofar ta rufe a hankali babu wadataccen haske a parlor duk da haka idanunta basu kasa hasko mata yayan nata dake tsakiyar rug ya tattare jikinsa wuri ɗaya. Sai da gabanta ya fadi ganin irin kalar kwanciyar da ya yi tasan idan ya yi irin wannan kwanciyar to baya da lafiya a haka ta nufesa da sauri ta kai hannunta saman fuskarsa jin wani irin zafi yasa ta janye hannunta da sauri hannu tasa tana bubbugasa tana kiran sunansa.
Sama -sama ya rika jin muryar Aydah akansa da sauri ya buɗe idonsa saboda ciwon kan da ya kwana dashi
yasa idanunsa suka yi masa wani irin nauyi sai ƙoƙarin miƙewa zaune yake yana kallonta da mamaki, yana tashi zaune da kyar ta faɗa cikin jikinsa ta fashe masa da wani irin kuka mai taɓa zuciya da ruhi, cikin kuka take faɗin."Yayanmu baka da lafiya mu je asibiti kar wani abu ya sameka wai meyasa kake son zama da ciwo dan Allah."Runtse idonsa ya yi zuciyarsa na wani irin bugawa yana jin yadda hawayen Aydah ke sauka cikin ƙirjinsa shiru ya yi yana jin yadda take shesshekar kuka. "Babyn yaya Abba?'"ya faɗa cike da ƙarfin hali dagowa ta yi tana kallonsa ya ware mata manyan idonsa yasa ɗayan hannunsa yana tare hawayen idanunta "wai waya faɗa maki budurwa tana kuka?"yasan kalmar data tsana kenan a kirata da budurwa ai kuwa ta haɗe rai sosai ta turo masa bakinta ganin haka sai da ya saki murmushi, to na ji har yanzu ke baby ce kije ki yi shirin zuwa school zan fito na kaiki idan na saukeki sai na karasa clinic a dubani."a hankali ta saki murmushi ta miƙe tsaye tana faɗin."na kawo breakfast muyi anan yayanmu?"dan shiru yayi yasan da yace a'ah itama tana iya cewa bazata ci ba, gyada mata kai kurum ya yi da farin ciki Aydah ta juya ta koma part ɗinsu kai tsaye ɗakinta ta koma wanka tayi ta saka uniform ɗinta tana ta addu'a kar su haɗu da Mami har ta wuce makaranta sosai take jin haushin Mami, a kitchen ta samu huwaila mai aiki tana soya doya, Aydah ta tambayeta ta soya wata bayan wannan ta nuna mata cooler ta wanko plate ta saka masu ita da yayan nata anan ta haɗa masu tea cup biyu sai da taje ta fara kai tea lokacin bai parlor ta koma ta dauko plate ɗin soyayyar doyar, zama ta yi a parlor tana jiran yaya Abba har na kusan minti goma tana ta kallon tea ɗin kar ya huce.
Master bedroom ɗinsa ta nufa tsayawa tayi a bakin ƙofar tana knocking sai da aka bata izinin shiga ta shiga tsaye yake a bakin mirror dressing shima yana shiryawa ya yi wanka cikin ruwan tokan japaness suit da suka yi masa kyau suka fito da kwarjininsa sosai sai dai duk wanda ya kalli fuskarsa yasan baya cikin natsuwarsa a bakin ƙofa ta tsaya tana ganin yadda gadonsa ya yi wani irin suqeezing ƙarasawa ta yi tana gyara masa gadon a ɗakin ya barta ya koma parlor ita ma bata jima ba ta fito tare suka yi breakfast ƙarfin hali kawai yake dan wani irin zazzaɓi yake ji da ciwon kai ko yawan magana baya son yi suna gamawa za ta koma ta mayar da kayan tana ƙoƙarin shiga ɗakinta suka ci karo da Mami, kallonta Mami take tun daga sama har kasa saukar da kanta ta yi tana gaishe da Mami."batare da Mami ta amsa ba take tamabayarta daga ina take dan ta ji kamar ƙamshin turaren Abba tare da Aydah, daga kitchen da haka ta juya ta shige ɗakinta tsaye tayi cikin ɗakin kamar zata yi kuka duk bata ji daɗin fitowar Mami ba kar ta hanata shiga motar yayan nasu. Kamar Mami ta san abunda take shiryawa zamanta tayi cikin parlor dan har kitchen ta samu Huwaila tana tambayar yaushe Aydah ta tashi?"nan ta faɗa mata tun ɗazu har tayi break fast ita da Yaya Abba, sosai ran Mami ya ɓaci daman tayi mamakin da taga Aydah da uniform karfe bakwai na safe ita da bata shiryawa da wuri zama ta ci-gaba dayi a parlor tana so taga ta inda Aydah za ta fito.
*KIM'S AUTOMOBILE INDUSTRY LAGOS*
"Good morning Abbu!
"Morning my princess ya zance ganawar mu da CEO na Kamfanin moonlight tun kafin na yi tafiya zuwa Cotonou ya dace ace mun haɗu dashi anya kuwa kamfaninsu yana so kula wannan yarjejeniya ɗin?"
Sai da Anaal ta sauke numfashi kafin ta ja kujerar dake gaban desk ɗin Alhaji Aliyu na uku ta zauna tukun kafin ta ɗora da faɗin "Daddy ko jiya na kira shi sai kawo min uzurinsa har ya yi insisting da a dage zaman har zuwa na wani ɗan lokaci, saboda ɗaurin aurensa da za a yi ranar juma'a ɗinan ta jibi.
Har Alhaji Aliyu na Uku ya buɗe baki da zimmar magana kira ya shigo cikin ɗaya daga cikin wayoyinsa da yake wayar ya kebe ta ne saboda family and friends ya ɗauki wayar tare da duba sunan mai kira nasa magaji ƙarami ya gani sai kawai ya maida wayar batare da ya dauka ba ya ƙara gyara zamansa ya kalli Anaal ya ce "To shikenan babu damuwa tun da shine ya bukaci hakan. Sai dangane da Hamdallah motors dake garin Kaduna jiya na amsa kira Chairman na kamfani yana buƙatar manyan motoci sababbin samfur ki yiwa Zeeyad magana ya tura masa waɗanda muke da shi kuma Zaheed ki faɗa masa ya kira mr obina ya faɗa masa wa'adin da ya nema mu yi masa lamuni ya cika ya tura mana da kuɗaɗen mu ko kuma na haɗa shi da lawyer mu.
Wayarsa ce ta sake ringing a wannan karon daga Gimbiya Zainaba ce ta kira shi wacce daga sarki Mahmood sai ita da sauri ya yi picking call ɗinta saboda yasan ita bata kiransa sai da kwakkwara dalili "Aminci Allah ya tabbata a gare ki yaya Gimbiyar Kudu lafiya!
"Wa'alaikum salaam! Tare da kai sarkin sabon birnin!
"Yaya Gimbiya ya na ji muryarki wani irin Allah yasa dai lafiya?"
"Babu lafiya Aliyu yau da safe muka tashi da wani mummunan al'amari mai martaba Mahmood ne ya tashi da wani mummunan rashin lafiya ko ɗan yatsansa baya iya ɗagawa gashi nan kwance magashim!
"Innalillahi wa'inna illahim raji'um! in-sha-Allahu gani nan zuwa sannan yaya Gimbiya ku kwantar wa mai babban ɗaki da hankali kinsan tana da hawan jini dole sai ku yi ƙoƙari wajen kwantar da hankali.
"Uhm! Kamar ka manta da jaruntar mahaifiyarka, duk yadda ta shiga tashin hankali ba zai taɓa nunawa akan fuskarta ba. A halin yanzu ita ce ma ke kwantar wa da iyalinsa da hankali musamman Fulani ƙarama, sumanta biyu a lokaci guda ta dawo abar tausayi.
"Subhanalillah! Lallai al'amarin ba mai daɗi bane in-sha-Allahu nan da five hours za mu iso.
"To shikenan Allah ya tsare ya kawo ku lafiya Aliyu.
Daga haka ya kashe wayar yana mai dafe goshinsa yana sauki numfashi da sauri Anaal ta taso ta zagaya wurinsa ga baki ɗaya jikinta ya yi sanyi cikin mutuwar jiki ta ce "Abbu me ya faru ne a masaurata?"
Sai da ya ƙara sauke numfashi kafin ya ciro kai ya kalli fuskarta muryarsa a sanyayye ya furta "Mai martaba ne.
"Subhanalillah!
"Ki je maza ki faɗawa Zaheed ya siya mana ticket ta online su shirya gaba dayanku za mu wuce tare. Amma kada ki faɗawa musu mahaifin su ne bashi da lafiya ki ce dasu mai babban ɗaki ce banaso su tashi hankalinsu.
"To Abbu!
Ta faɗa da sanyi murya kana ta nufi kofar fita da sauri ta isa office ɗin Zaheed, cikin sa'a ta tarar dasu duka suna wani aiki a laptop ɗin Zaheed sai da ta tattara natsuwarta wuri ɗaya kafin ta isar musu da sakon Abbu. Dukansu jikinsu ya yi sanyi nan take Zaheed ya siya musu ticket ɗin Jirginsu zai tashi ƙarfe biyun rana, saboda haka dukansu suka tashi daga office gida suka wuce suna jira time ɗin tafiyarsu ya yi ƙarfe 1:40pm suka isa airport.
*ALH BASHIR MANSION*
A hankali Aydah ta sake leƙo da kanta ta jikin ƙofar ɗakinta taga still Mami ta nan zaune wannan shine karo na hudu kenan da Aydah tana leƙowa. Wani irin abu ta ji ya tokare mata maƙoshi har ga Allah tana bukatar yaya Abba ya kaita school she wants to bws with him this morning tana so ta sake bashi haƙuri akan abunda jiya Mami ta yi mishi, Mami da ta gaji da zama ta miƙe ta nufi ɗakin Aydah ta jikin ƙofar Aydah ta hango ta tai sauri maida ƙofar ɗakinta, ta murza key, tana ji Mami tana knocking tare da kiran sunanta amma ta yi biris da Mami ta gaji da dukan ƙofar ta yi ƙwafa tare da nufar ɗakinta dake upstairs. Aydah tana ji sawun tafiyar Mami ta buɗe ƙofa a hankali cikin sanɗa ta fito tana fita ta buɗe ƙofar fita daga main parlor ta kwasa da gudu ta nufi bangaren AB daidai ya fito suka ci karo sai da kanta ya bugi jikinsa ta yi baya ta yi tangal-tangal za ta faɗi daman can ba wani jikin kirki ne da ita ba ya yi sauri taro ta, ta hanyar kamo hannunta fisga ɗaya yai mata sai gata kwance cikin jikinsa. Sai kawai ta ƙanƙame shi tana shaƙar ƙamshin daddaɗan turarensa wanda yake saukar mata da wani kalan natsuwa. A hankali ya ciro ta daga jikinsa amma sai ta ƙara komawa jikin nasa "yaya Abba barni na ci-gaba da shaƙar ƙamshinka har a busa ƙaho.
Duk da yana cikin damuwa hakan bai hana masa dariyar shirmenta ba, da yake ya saba da wannan halin nata na shaƙar ƙamshinsa ciki ma yanzu ta rage yi masa haka ada yana tsakiyar baccinsa zai ji hancinta tana shinshinar sa kamar magge, shiyasa a wasu lokuta yake kiranta da maggen yaya Abba.
"Kin ga Babyn yaya Abba bana so shirme school fa za ki tafi ko so kike ki makara garin wannan childishness ɗin naki yi latti a yi miki duka?"
Yana magana ne tare da sake ciro ta daga jikinsa ya kama hannunta suka nufi parking lot "Yaya Abba ka ga yadda yau ɗinan ka yi wani irin nau'in kyau na musamman?"
Bai bata amsa ba sai da ya shiga mota ya yi warming ɗinta kana ya fita daga parking lot ɗin, Balmo maigadi ya buɗe masa gate.
"Yaya Abba ko ba ka yarda da ka yi kyau bane sai magana nake yi ka yi shiru?
Ta yi magana cikin shagwaɓaɓbiyar murya tana wani turo baki.
"Baby me kike so nace?"
"Ka yi haƙuri yaya Abba about yesterday night daga ni har yaya Siyam ba mu ji daɗi abinda Mami ta yi maka ba ka ɗauki shi a matsayin kuskure da sharrin zuciya saboda Mami tana ƙaunar ka sosai wannan so-called daughter ɗinta ne ke so haddasa fitina a tsakanin ku. Amma kowa zai iya bada shaida akan kyawawan halaye Mami.
Ɗan ƙaramin murmushi ya yi wanda ya tsaya iya laɓɓansa, sai da ya kalli innocent face ɗinta kana ya yi concentrate tukinsa.


#Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo.








Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only




ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A. Gtb
Or
8098456130
Fatima Ishaq
Opay digital services
Shaidar biya
08098456130


KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya ta 07065283730


Ko a tuntubi
08086207764
0816 114 6563
+234 704 040 2435
‪+234 903 056 9336






*ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU.


*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar


*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu


*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce


*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari


*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan


Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500


VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k


NORMAL GROUP 500
VIP 1000
[12/20/2023, 11:03 PM] Asmy B Aliyu: *KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)


NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU




*AREWABOOK*:Jeddah3256


Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye


033.


Ganin yanayinsa wannan karon sai suka zauna zaman shiru daman kuma ita ce mai masa surutun yau bata dame sa da surutu ba ta kwantar da kanta cikin seat ɗin motar ta kurawa titi kawai ido, dan kallon gefenta ya yi ta taimaka masa ma a haka da tayi shiru dan yana son ya ji shiru acikin kan nasa na ɗan wani lokaci har suka karasa bakin gate ɗin makarantarsu. Yana gama parking motar ya dauko wallet ɗinsa ya ciri 2k aciki ya miƙa mata girgiza kai ta dan yi tana faɗin."Akwai kuɗi a tare dani. Harararta ya yi ya buɗe hannunta ya saka mata kuɗin, murmushi ta yi sosai ta karaso gafda fuskarsa har suna jin numfashin juna ta sumbaci gefen fuskarsa a hankali ta furta "i love you Yayana."murmushi ya yi mata da haka ta balle marfin motar ta rufe masa tana daga masa hannu.
Shima hannun ya daga mata har lokacin murmushin cikin fuskarta bai bace ba baya son wannan murmushin ya ɓace daga fuskarta har lokacin da numfashinta zai tsaya yana son kannen nasa da dukkan zuciya da ruhinsa ta yadda baki ba zai iya misalta shi ba, acan ƙasan ransa Aydah tana da wani matsayi mai girma a zuciyarsa wanda ba zai faɗu ba. Haka ya ja motarsa ya ƙarasa office wannan ranar ma cikin tunani da damuwa yayi ta kusan ƙarfe goma sha biyu na rana aka tura kofar office ɗin nasa yana kwance cikin couch ɗin dake cikin office ɗin nasa da mamaki yake kallon mutumin da ya shigo office din nasa. Kallonsa kawai Daddy yake yana ganin yadda yaron nasa ya yi wani irin zuru-zuru gaba ɗaya jiya bai saka shi a idanunsa ba da gaske yaga yaron nasa ya yi wata irin rama wacce za ka ganta kwance cikin idanunsa. Idan ka yi masa farin sani kuwa za ka tabbatar akwai damuwa sosai a tattare dashi. miƙewa tsaye AB ya yi kai tsaye ya nufi Daddy, yana ƙoƙarin wadata fuskarsa da murmushi yake faɗin."Daddy meyasa baka kirani a waya ba na sameka a office ɗinka ai ba ma sai ka zo ba.
"Menene asalin damuwarka Abba?" Daddy ya faɗa yana kafesa da idanun dake kassara duk wani tunanin AB. Cikin rawar murya AB ke faɗin. "Daddy duk meya kawo wannan maganar? Yadda yake magana za ka san baya cikin hayyacinsa kuma a rude yake, Daddy ya nemi wuri ya zauna ya ɗora kafa daya akan ɗaya yana girgizasu a hankali."shi dai AB yana tsaye a wurin tamkar wanda aka dasa banda faduwar gaba babu abunda yake ji a wannan lokacin."Baka rasa ci da sha ba kana da gata kana da iyaye da yan uwa a zagaye dakai kashe kanka kake so ka yi ne?" Wannan karon Daddy ya faɗa da ɗan ɗaga murya, zama Abba ya yi gefen Daddy yana riko duka hannayensa biyu bai san taya zai soma yiwa daddy bayani ba. Idan kuma ya faɗa masa asalin damuwarsa bai san tayaya zai dauki al'amarin ba kenan karar Mami zai kai wurin mahaifinsa kararta zai kai da bai yiwa kansa adalci ba maccen da ta shekara talatin tana hidima dashi bai kamata ya ji haushinta ba koda na minti ɗaya ne, koda kuwa yayyanka naman jikinsa take a kullum."Ko kuma hukuncin da na yanke akanka ne yai maka nauyi!" Daddy ya faɗa da raunin muryar da ta dawo da AB duniyar tunanin da ya faɗa da sauri AB ya shiga girgiza kai yana faɗin."Har abada dadydy baza ka yanke hukunci akaina naki karbarsa ba komai nauyinsa zan karba da hannu bibbiyu nayi maka biyayya Daddy.
"Yanzu ka tashi mu je gida na soke zuwanka zuwa office har na sati biyu ka huta. Wani irin fargaba da tashin hankali zuciyarsa ta kara shiga lokaci ɗaya, komawarsa gida shine babban tashin hankalinsa a yanzu yana gujewa duk wani abu da zai haɗasa da Mami, wannan umurnin da Daddy ya basa ko kaɗan bai masa daɗi ba.
Ga matsalar Sadiya a gefe dake son ta zamar masa matsala cikin rayuwarsa har yau kalamanta basu daina yi masa yawo cikin kunnuwansa ba sun samu wurin zama sosai a ƙasan zuciyarsa. Har yau bai daina mamakin kalaman Sadiya ba. Kananan shekarunta bai ci ace ta san wa'yannan manyan kalaman ba ko Rumaisa da ta girmeta bai taɓa tunanin ita da suka kwashe shekaru biyar a tare irin waya'annan kalaman basu taɓa haɗasu ba. Duk kuwa budewar idon Rumaisa da wayewarta wacce tayi karatunta na degree a abroad. Bai san wanda ya canja duniyar ƙanwarsa ba lokaci ɗaya.
Ya dauki car key ya dauki suite jacket ɗinsa da ya cire ya sargafeta akan hanger ya saka ya kwashi wayoyinsa da car key ɗinsa har lokacin Daddy na tsaye yana jiransa. A tare suka fito suka nufi cikin parking lot da kansa AB ya buɗewa Daddy bayan motar, mai makon haka Daddy ya mayarda kofar ya rufe ya buɗe frontseat ya shiga murmushi kawai AB ya yi ganin baturen Daddyn nasa a gaban mota har lokacin da ya shiga motar murmushi bai bace cikin fuskarsa ba, "Za ku cigaba da zama wancan gidan ne ko kuna bukatar canji? Daddy ya yi maganar batare da ya kalli gefen da AB yake ba hasalima hankalinsa na kan titi, Daddy ina ganin kawai mu zauna acan tunda ko kwana bamu yi ba ranar.
Ya karasa magana da raunin murya, Daddy ya numfasa yana faɗin."naji ra'anyinka sauran Mamana idan tana bukatar a canja kayan daki za a canja. Duk lokacin da Daddy ya dauko masa zancen aurensa da Aydah jin yake duniyarsa na birkicewa wannan karon har cikin gida ya bi Daddy dauke da briefcase ɗinsa bai yi gigin zuwa bangarensa ba dan kauda duk wani zargin da Daddy zai yi masa Sadiya kaɗai ce a parlor har lokacin kayan bacci ne ajikinta cikin sanyin murya take yiwa Daddy sannu da zuwa tana mamakin dawowarsu a irin wannan lokacin haka ta tsayar da fuskarta cikinta AB wanda bai yadda da ya kalli gefenta ba zuciyarta wani irin bugawa take da sauri da sauri

24 / 80