Chapter 99 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   99 / 109

294K to 297K   out of 326.5K words

zuwa uku tare da bincike idan komau namu bai salwanta ba
daga company mu.

Ko hakan ba a kaiwa zata dawo bakin aikinta don wani dalili ya kaita can din da zaran taga kuma zata
dawo garemu ya fada kai tsaye.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[12/4, 9:56 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:




JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

9️1️⃣
1️⃣
0️⃣0️⃣
0️⃣0️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6




Zaune muke a falon Abbu da kusan kowa yana wajen sai ido suka zuba min suna kare min kallo don su a
ganinsu sunga na sauya ga komai nawa.

Binsu nake a yadda aka saba din don ban yarda sun da koni wacece ba a yanzu wanda naji dadin hakan
ga tambaya da anty safiya tasani gaba dashi saida kyar nake iya bata amsa don akwai gajiyan hakan a
tare dani.

Malam Adamu saika zauna da yarka kun natsu ko zaka fahinci halin da take ciki a can kaji meya kawota
kasan nan kuma don alama ya nuna zuwanta kamar bada shiri bane tazo din nan.

Duk da dai ga har kaya ta shigo dasu amma hakan bai hana ingano akwai dalilin zuwanta dinba uwarta
kuma taki kwantar da hankali ta hango abinda na hango ga zuwan yarinyar.

Abbu da sai kallon mamaki yakewa Abba din dake masa bayani cikin damuwa don hankalin shi ya soma
tashi don bai gama fahintar abinda Abba ke nufi ba a lokacin.

Ya dan gyara zama yana fadin subbahanallah ke nan ba zuwan girma da arziki yar nan tayi ba ke nan a
yanzu ?

Haka nake tunane malam saidai kasan ba zata fada muna bamu kamar yadda zata iya sanar dakai komai
don akwai fahinta da yarda sosai tsakaninka da yarka.

Insha Allahu idan ta huta ta natsu zan bincketa din kamar yadda ka bukacin iya indai nanatace nasan
koma meye da kanta zata sameni ta walwale min komai naji.

Madallah don shine na fada maka kaga gara dai mu sani ba sai mutanen nan sun kai ga nemota ba wai
ina zarginta ba a,a nasan Aisha tana da tarbiya yadda ya kamata.

Amma kasan halin dam yau ga abinda ba ai zamani garesu ba don a yadda mahaifinta ya fada min
company suka bude mata babba a can.

Tana juyawa kuma abin ya samu karbuwa sosai a wajen mutane sai gashi kwatsam kuma ba a ko jima
ba mun ganta a kasan nan.

A cewar ta dai wai tazo ganin kune amma sam sai hankali na bai kwanta ba gaskiya wa iyazu billah Allah
kasa yarinyar nan ba magana ta dauko muna ba a can ?
Duk da dai bansan nana da daukan magana saidai a yanzu canzawan dan adam cikin dan lokaci yake
sauyawa din zan zauna da ita ko zuwa yammane kamar yadda ka bukata din ko meke nan kuma zakaji
daga gareni insha Allahu zan kira na sanar dakai komai duk yadda mukayi din.

Godiya sukaiwa juna kafin Abbu din ya mayar da hankalinsa kofan falo zakice ni din yaga fitowa na
yake kallo muryan Abbane ya dawo dashi daga guntun tunanen dayaje din Abban ke fadin.

Sasai suka karbeta a can ni abin ya ban mamaki matuka duk da dai nasan harda rashin haihuwan da
mahaifinta bai samu bane a baya yasa suka saka kaunarta a zukatansu.

Yarinyar ce tasan kanta kuma bata da rigima sai dinbin basira basiranta koshi zai iya jamata farin jini da
akasin hakan kuma garesu.

Don ba za ace sun taru gaba daya suna kaunarta ba dole a samu yan uban dake adawa da zuwanta din a
yanzu yana daga cikin abinda ke daga min hankali kan zuwan nata.

Jikin Abbune ya kara sanyin dajin zancen Abba yace gashi mu kuma mun saki yarinyar haka baki sake ta
tunkaresu ba ai mata komai na dafa kansa ba irin namu.

Allah dai ya tsare malam Adamu albarkan iyayye shine kan gaba da komai a rayuwa a daita saka mata
albarkan ko yaushe.

Sun jima suna zance kafin sunyi sallama da juna Abba din yace ummu ta fito su koma gida rana yayi
hakan yasa ta fito daga dakin Ammah din inda suka gama tataunawa suma a tsakanin su a kaina.

Mamaki taji na yadda ina ganin ta fito na mike tsaye da sauri ina fadin zasu tafi ke nan taja ta tsaya
tana kallona.

Na taka zuwa gareta ina fadin tsaraban yayanta na nan idan na bude kaya zan kawo masu har gida a
gaida min su ace masu zan dawo muyi hira dasu.

Jin hakan yasa ta sauke murmushi a fuskanta tana fadin sai sun gani din yanzu naga yan uwa ina zan
tuna dasu .

Har waje na rakasu na ina ruguman Ummu yadda nasaba yiwa ummu halimat a cab sai nake gani
tankar itace a lokacin.

Inda na barta da mamaki Abba ya sauke ajiyan zuciya yana murmushi kafin yace Asiya mena fada maki
akan yarinyar nan ?

Babu dan da baison mahaifiyarshi a duniya koda ya kasance uwar a bola take rayuwa kuwa wanan so
da kauna dake tsakanin da da mahaifi wallahi sai ya kada a zukatansu.

Amma kin kasa gane hakan don sauyin a yanzu na hango sauyi sosai ga yarinyar nan kamar an debe
mata wani abune a kasan zuciyarta a yanzu.
Ajiyan zuciya ta sauke tana zakudawa tace ni mamaki ma ya hani magana ai yarinya saikace mai
aljannu wani lokaci.

Yanzu dai na fadawa Abbunta zai zauna da ita yaji muna ainihin meya faru ta dawo kasan nan haka
lokacin da bamuyi tsamaninta ba ?

Allah yasa ta fada mashi gaskiya kansan halinta da taurin kan tsiya koma meye ai kanta zatayiwa tsiyan
ba wani ba.

Ni kaina irin kallon da ake min na fara tsarguwa duk da nima kallon nasu nakeyi a fakaice gashi naga
sun wani canza min ga baki daya kamar basu a cikin walwala.

Ina kunna data mahaifina ya kirani vedio call muka gaisa yake min bayanin abinda ke faruwa cewa
wanan saifullah din yazo a haukace yana fadin anyi masa datsen asusunsa na ajiya.

Kamar yadda man yace in fada mai na fadawa Abbi din ya fada mai ba sacewa bane inda kudin suka fito
suka koma.

Hakan daya fada shine yaso ya tayar da rikici a tsakaninsu har yakai manya sun shigo a cikin zance anji
meya faru.

Abbi bai boye masu ba ya zauna yayi masu bayanin komai da lokacin da suka fitar mai da kudadensa
masu yawa daga account nasa.

Shi kanshi saifullah din yaji mamakin yadda aka zakulunshi haka ba tare daya farga da ana bibiyansa ba
saida komai ya kankama ya gano hakan when it,s too late for him.

Kamar yadda Abban yaso haka ya kasance don ba wanda ya kawo zancena a wajen saboda sunsan a
lokacin bani kasan ana fadin na koma Nageria wurin uwata sai hakan ya dauke masu hankali.

Wanan zance kuma yajawa Abbi din matsala da matansa da yan uwanta sukai rikici sosai har ta wuce
zuwa kasansu shi kuma Abbi din bai damu da hakan ba tunda dama yasan komai da suke mashi da
dukiyansa hadin bakine da ita.

Ko wanan kudin yasan sunyi mashi hakane don arzikinshi yai rauni sosai a dawo ana fadan nice na
rushesa daga zuwana komai nasa a yanzu yaja baya.

Abbune zaune yana shan ruwa don yayi azumin alhamis a ranan ni da Ammah zaune tare dashi ina
gyara mashi fruit da zaisha naji yace dani.

Nikan nanata baki ban labarin komai ba game da iyayyenki tun zuwan ki don Alh mijin Asiya ya nuna
min kamar zuwan naki bada masaniyan iyayyenki na can ba kikazo.

Abbu mahaifina yasan da zuwana kasan nan dan kaucewa nayi daga wajen don wani aiki da za ayi
mashi nan na ba tare da an zargeni ba nan dai na kwashe komai a tsanake naba Abbu labari abinda ya
faru.
Da kasar hongkong zan tafi nayi kusan wata daya sai gab da azumi zan dawo sai kuma daga baya nayi
tunanen cewa inzo kawai nan in ganku tunda ina da niyar zuwa nan din hakan yasa kai tsaye na wuto
zuwa gida don mu batarwa mutane da hankali akan mu.

Saidai ban yarda na fada mai dukka ba kada hankalinsa ya tashi na kare da fadin Abbu mahaifina yana
ban tausayi irin rayuwan da yakeyi da yan uwansa mu sanman ta bangaren matarshi.

Ya kasance shi mutum ne mai hannkuri gashi baison yawan fitina sai dai suyi ta cuta mai baya magana
ga shi yana fama da wani lalura daya fada min daga bayan nan lalurar ta sameshi na mantuwa.

Wanda in abin yai yawa Abbu sai ya koma har yana sakashi suma da fita hayacinsa ya fada min ni kadai
ya yarda dani ya ban labarin matsalolinsa wanan yana daga cikin abinda yasa na zo nan don in samu
sanar daku ko akwai abinda za a taimaka masa dashi.

Kinjiki da wani zance mutanen daba al,adan mu daya ba dasu Aeesha me malam zai iya yi a kansa
kuma nan yanzu ? Ammah ta fada din .

Barta ta gama fadan komai dole ai ba a rasa yadda za ayi suma ai mutanene dole suna da gargajiyansu
da suke wani abubuwa nasu.

Yanzu yaushe kika saka ranan komawa ya bugi ciki don ya kara tabbatar da gaskiyan maganan da nake
fada mashi.

Eeh to Abbu gaskiya ba zanso na wuce sati biyu ba a nan don akwai abubuwa da dama a gabana da in
na koma zan gudanar.

Sosai Abbu ya gamsu da dan gajereb bayanin da nayi masa lokacin washegari ya samu Abba har gida ya
labarta mashi yadda mukayi.

Da kuma abinda ya dace su taimakawa mahaifin nawa dashi sun tatauna sosai akan matsalan nasa har
suka gwada kiransa yana kusa a lokaciln ya dauki kiran nasu din.

Zancene na maza don haka basu yarda da munsan da wanan taimakon da suke shirin masa a
bangaresu.

Ban fita ko ina ba ina gida ko yaushe saidai na rabawa wa yanda suka dace tsaraba hakan yasa suke
faman tururuwan zuwa yi min sannu da zuwa.

Zancan dai gudane shine da mahaifin nawa nazone sai ace ni kadaine nazo zaki ance affa dama mun san
bat da sau akaje muna ai ba wani ubanda take dashi.

Sai kuma a tambayana ko tadawo ke nan akance dasu bama zan yiba zan komane nazo ne kawai inga
iyayyena zasu fita suna tsegumin hakan.

Don wallahi gaba daya kan na sauya kallo daya zakayi min kasan nidin na sauya a yanzu koba a fada ba
duk dabi,una sun canza a lokaci guda.
Wanan bakin tabon nake son na gogeshi a jikina na cireshi na har abada insan nagoge wanan bakin
sunan da ake jafani dashi.

Muyi waya da mahaifina yake sanar dani halin da suke a ciki bayan mun gamane na fada mai kai tsaye
abindake zuciyana ina kuka .

Abbi ina son mutanen nan kamar yadda nake son raina amma abu daya yasa nake tsanan su ba wai
iyayyena da yan uwansu ba abi ?

Mutanen nahiyar da ke jifana da kalman bastard girl ma,ana banda uba da sauri naji yace wa,iyazu
billah ban boye mai komai ba ina kuka na fada mai irin maganganun da suke fada a kaina din.

Yace gashi nan zuwa ya sheda kansa ba yanzu ba Abbi na bashi amsa da mamaki yace sai yaushe nace
sai ka sakawa iyayyena alherin da sukai min ka gyara masu muhalinsu .

Yadda inkazo kana da wajen sauka a wajensu ba sai kaje wani wajen ka sauka ba abi suna rayuwane a
cikin kuncin talauci a nan din kuma haka nake son su don da haka suka tayar dani har na girma.

Yata zan masu duk yadda kike so kafin ki bar kasan ki shirya duk wani project din yadda kikeson komai
ya kasance akansu da duk wani wanda kike bukata.

Sai lokacin nayi murmushi a raina nace azo wajen ke nan don ba karamin dagasu nake sonyi ba yadda
zuti,an Abbu zasuyi alfahari da rikon da sukai min din na tsakani da Allah.

Man na kira na fada mai komai yace za a duba yadda ya dace nace a hada da gidan akwai da kidan
raba kaya duk a gyara unguwan don har kakana ina son ta dalilina sai ya tako Nageria asan ina da gatana
insha Allah.

Ta bangare daya kuma mutum biyar na sa aiwa visa da zasu biyoni zuwa dubai don gudanar da aiyuka
acan tare dani gidan mu akwai Asmau da nake so kusa dani don debe min kewa.

Sai Nusaiba isma,il kaninta da zanje dashi can yai karatu gidan akwai yaya buhari gidan raba kaya yaya
Najib sai yaya sulaiman dina da a sirce mukai magana dashi don ina son ya soma bussiness irin namu a
nan.

Naso na juya da Asmau amma hakan ba zai samu ba don visan ta da ba zai fito cikin lokaci ba dole inyi
gaba su biyoni daga baya.

Su maryam ma nayi shiri mai kyau akansu don su samu madogaron rayuwansu zaman gidan ya isa
hakana a wajensu tunda mijin baizo ba.

Duk abinda zanyi insan na tuna da duk wani wanda ya taimakawa rayuwana a baya nayi na kuma leka a
cikin kwana biyun nan da nayi a kano .

Inda na samu Aimana tazo da yaron ta namiji tana goyo sai wani feleke take muna Faridace take fadin
ke yanzu Aymana har yanzu halin nan naki yana nan ki duba Aisha fa ?
Batazo tanawa mutane daga kai da nuna ita wata bace duk da musan ko wata amma haka baisa tace
zatayi muna wullakanci ba ko wani iyayi irin naki.

Suka dai wasance aka maida abin wasa tsakanin mu kafin na bata kudi masu yawa hakama iyayyenta
mahaifiyar ta har da kuka na zagaya gidajen makwabtan da akai zaman arziki suma na dan basu alheri
muka juyo gida.

Da farko dana kawo wa Abbu driver da zai dinga kaisu ko ina shida Ammah yan unguwa gulma suka
fara wai sallone kawai nazo masu dashi.

Bandamu da abinda ake fada din don yanzu kaina na sani don Allah bai yini da rigima bane yasa ba
zasu gane ko wacece ni din ba a lokacin.

Gidan ummu naje kusan sau uku mun kuma fita da yaranta munje shoping nayi masu sayayya sosai
muka dawo gida anan ma muka kwana ranan .

Ban boye mata komai ba na abinda ya faru tun zuwana gun mahaifina har wanan lokacin da nayo
tataki don in dan huta inga iyayyena kuma.

Shiru tayi kamar tana tunane kafin inji tace dani dama nasan haka zai faru shiyasa da Alh ke zancen zai
nemawa dansa auren ki tunda kun shaku dashi nace ya barki da iyayyenki can yana da wuya su barki kiyi
aure a Nageria gaskiya.

Dansa kuma na tambaya ina kallon ummu din tace wanan dan nasa mana Mam bashir da suka zata
yana neman kine a baya ?

Ba zanso ki aureshi ba don idan anyi hakan wani sabon fitina kuma za a dauko a yanzu tsakanina da
yan uwan Alh don a yadda nake ji sun riga da sunyi mashi irin hadin nan nasu na gidan sarauta har mata
biyu.

Yanzu kuma Alh ya fito masu da zancen ki aisai su dauka ina son na mamaye masu ahalinsu dani da
zuriata ina dai maki addua a kullum Allah ubangiji ya baki miji nagari inda zaki huta har yan uwa su huta
a karkashin innuwanki suma.

Shiru nayi banyi magana ba don zuciyana da nake jin yana min wani irin harbawa a lokacin game da
zancen man din mata biyu at the same time su waye wanan matan kuwa ?

Bata kula da yanayin dana shiga ba a lokacin inda taci gaba da zancen ta tana fadin dama ace bada yar
Alh bace shi kansa a cikin zance ba zance dashi komai ba tunda naga akwai kyakyawan fahinta a tsakanin
ku ?

Gashi ko dazun naji kinawa Alh hiransa cikin zancen ku nasan fitina kawai da tashin hankali za a hada
yasa nace yabar wanan zancen don Allah.

Ni uwarta na kishi dani azo kuma ace kema kishi ya hadaki kuma da yarta ai kinga tsugune bai kare min
ba gara dai kowa ya nemi daidai shi zaifi min kwanciyan hankali hakan.
Ta dai kara zancen ta don ba fahintama nakeyi ba a lokacin don zuciya da nake jin wani abu ya tsaya
min lokaci guda duk da man bai nuna min soyayyanshi a fili ba hakan bakicewa ba soyayya a tsakani mu
a yadda muke nidashi.

Allah ya taimakeni Asmau tazo tana fadin ana kiran layina hakan yasa na mike nabar ummu din da bata
kare fadin abinda zata fada ba a lokacin.

Saida na tabbatar ban bar wani kafa da Abbu ko Ammah zasu zauna a cikin kunci ba na bar garin kano
a cikin kunci na rashin son rabuwa dasu din don dole nake son in koma Dubai akan zancen da mahaifina
ya fada min sunyi da kakana din.

Ina son in koma in nunawa tsohon bai gama sanin yan Nageria ba don ba dukka bane muka zama
mayaudara har gobe akwai nagari don mu musulmai daban muke har gobe.

Bawai yadda suke ganinsu barkatai din nan bane suke dauka kowa baida imani a zuciyar kamar dukka
haka muke gaba dayan mu a nan.

Saidai na yanke cewa wanan karon zan bar gidan tsohon da zama in koma koda gidan mahaifina duk da
nasan ba dadi acan .

Sai don ina ganin ya kamata in nuna masa nima nasan kaina a yanzu son gudun abinda kaje ya dawo
kada wata rana in wayi gari in samu ya daura min wani a kaina.

Kwana daya nayi a Abuja wajen mamana da wuni da dare muka tashi zuwa dubai inda muka sauka
wajajen asuba amma zakice ba dare bane hakan sosai saboda yadda mutane suke zirga zirgansu a garin.

Ko a jirgi haka zancen mu da ummu yake fado min a rai sai faman tunane nake akai abinda ya ban
mamaki kuma ya daure min kai

99 / 109