Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
da duk idanuwansu yana kansu duk wani motsi naki a kasan nan fa sun sani Aisha ?
Umm,humm wanan kuma maganace kawai iron naka wani da da ubansa kake zance wai ni ban gane
zancen kan zancen kaba ai ?
Yallabai mana mai martaba da dansa duk idonsu nakan motsinki ke din ai ta dabance Aisha ni sai yanzu
ma nake tunanen hakan.
Nayi mamaki da farko wallahi sanin wacece mum amma lokaci daya fa wai kin shiga rayuwan mum
abin akwai mamaki gaskiya.
Had in Allah ne fa hakan me kakewa mamaki kuma yanzu kai ya girgiza yace idan da hadin Allah da
wani plan cikin hakan da aka boyewa mutane shi.
Wai me kake nufine Bros Aisha nasan kema baki sani ba gaskiya amma zaman ki wajen mum wani plan
ne hakan ba yadda za ayi shi yallabai Bashir idonsa na kanki hakama mahaifinsa daya ba mum alhakin
kulawa dake dole akwai wani a kasa gaskiya.
Duk da mum taja main kunne sosai amma ni gaskiya kaina ya daure da hakan dole akwai abinda suke
nufi dake Aisha manya basu irin haka banza.
Shiru nayi ina tunane don na kula zance ta gaskiya yake min a lokacin dole kuma gabana ya soma
faduwa nan yake min bayanin yadda yaji zancen suna hanyane aka kira mama din.
Akan me yasa tabari Man bash ya turani kano shine tace ai bata yarda naje ni kadai ba da yarta da
kanwanta ta turamu zuwa kanon don haka babu yadda za ace ban dawo ba.
Kinga ke nan duk wani motsinki a kullum yana a idanuwansu ke nan wanan ya daure min kai har nake
tunanen duk yadda akayi ke din watace a rayuwa amma baki san hakan ba a kanki Aisha ?
Ni kana ban tsoro wallahi son jiya naji mama na wani maganan a kaina wanda gaskiya ban fahinta ba
kuma bata san ma najita ba a lokacin .
Maganan ya danganta da wanan ke nan nace kusan hakan ya yazid don kuwa ashe da sanin mama
akaina run farko har dawowana gidanta kamar wani plan be hakan .
Saidai yanzu da ka ambaci sunan mahaifin man kuma lamarin ya kara daure main kaina gaskiya don
banda wani alaka dashi asalima baifi say daya ko biyu ba dana taba ganinsa a rayuwana don me zai tsaya
bata lokacinsa a kaina kuma ?
Yawan takuran hjy kura kan mahaifiyar yasa hjyn yin shawara gara tun tana da rai ta karbi wanan kudin
da take faman jinini a kansa kada tabar baya da kura akansa bayan bata duniya.
Donko tasan wacece hjy kura sarai tunda ta fara wanan zancen a kullum zata iya aikata komai bayan ta
din yasa ta yanke shawaran bugawa kowa waya yadda ta saba iyasu su hadu tana son ganin su.
Kana kuma ta kira Alh Ahmed ta sheda masa idan zaizo yazo da takardan daya juya kudinta dake
hannunsana tsawon lokaci.
Ba matsala hjy yafada insha Allahu zan zo da komai amsan daya bata ke nan a lokacin ita kanta duk da
tasan halin dan nata amma saida tayi mamakin jin yadda ya amsa mata kai tsaye haka ?
Babu wani damuwa ko darrr ko fargaba a tare dashi lokacin don ta tareshi girshi da zancen da bai zaci
hakan zai task masa ba a yanzu.
Don ba yau bane fa kudin nan an dauki tsawon shekaru da dama data dauki kaddarorinta na gwala
gwalai ta mika masa da sunan ya sayar ya juyasu can kasan lokacin daya fara sana,adin.
Sune a yanzu hjy kura ta dorawa kafa ganin arziki daya taso masa shida dansa take zargin ai duk
sanadin wanan kudine take ganin har yanzu suke juyawa a tsakaninsu shida dansa suke ganin a yanzu
kamar sunfi kowa.
Bawai don sha,anin bukin yarta da takeson yin karyan arziki ba kawai yasa ta matsa sai akawo kudin a
raba a tsakaninsu tunda kowa nada hakki akai .
A,a tuntuni ta kwallafawa wanan kudin na hannun dan uwanta rai kan lalai saj ya mayarwa uwar da
kudin ta yanzu.
Duk da tasan cewa itama da akwai kudaden mahaifiyar nata a wajenta ai data bata da sunan irin
hakan don haka akidar hjy hauwa din yake duk abinda ta tara yayan ta take mikawa shi a karshe.
Ba kunya gaban uwar take fadin nasan dole ya tsaya ja a yanzu tunda yasan dadin rike kudin a hannusa
shi da dansa suna kallon mutane a wullakance.
Uwar dai tana jinta duk da ranta ya soma back da halin yar bata iya furta mata komai ba a lokacin don
bakinta da yar ta rufe da asiri kafin ta tunkari uwar da zancen ance tsafi gaskiyar maishi dama.
Kamar yadda ta fada ranan ta riga kowa shigowa gidan duk a nan suka sameta zaune suka fara bin layin
zama don jin neman da mahaifiyar take masu.
Shine mutum na karshe da yashigo don haka ya dan ba basu hakkuri kan delay dins na rashin zuwa
cikin lokaci kafin imamu ya bude masu taron da addua.
Bayan an shafane imamu ya kalli uwar tace eeh na kirakune nan din yau dan Ahmad gashi nan zaune
kan zancen dukiyan dana bashine a baya nace ya juya lokacin yana zaune da iyalinsa turai.
To yanzu ina bukatan kudaden yasa na bukaci da yakawo nan a gaban kowa agani da fatan ba wani
matsala ta fada tana dago kai ta dubi dan nata dake zaune shima yana saurarenta a cikin ladabi.
Ahmad sai kai muna bayani uwarta fada nan ido yadawo kan shi ya Dan muskuta yana gyara zama have
Alhamdullahi da Allah ya nuna muna wanan ranan a yau.
Ya jawo wani dan jakka duk suka bishi da kallo lokacin imamu daya fahinci me ake shirin yi a wajen ya
dakatar da Ahmad din da fading wai dakata Ahmad hjy meke shirin faruwane wai ?
Wasu kudi kike zace kuma a yanzu bayan kowa nan kin masa kwatankwancin yadda kikaiwa Ahmad din
muma ?
A,a yaya Imamu ka dakata da wanan zancen hjy dai itace keda abinta ta bashi yanzun kuma tace tana
da buka sai ya kawo a gani kuma ina shike nan dai ko ?
Amina wai meke damun kine da Ahmad da iyalinsa ina kula dake duk aka zauna kokari kike ki soki dan
uwanki gaban mahaifiyar mu ?
Dagakata yaya Imamu ni kada ka shirya min sheri agaban kowa son Allah dukiyanta tace tana bukata
yanzu a hannusa nace hakan yayi zaka kuma ce ga kara ga itace don Allah a kaina ?
Yaya ka kyaleta don Allah kada zancen nan yakai yadda ba,a so a tsakanin ku hjy kudi kika ban ko
kaddara a lokacin ya tambayi mahaifiyar nasu ?
Kallon mamaki uwar tayiwa dan da wanan tambayan rainin hankali da yake mata a yanzu bayan yasan
abinda ta bashi kafin tayi magana kuma ya dauko abinda yake kokarin daukowa ya mike ya kawo
gabanta yana fadin
Sune wanan ko hjy sai,ki duba ki gani idan suna daidai ko wani abu ya bata don yadda aka ban su tun
lokacin ban taba komai daga ciki ba ?
Ba hjy ba duk yaranta saida suka dago suna mashi kallon mamaki tare da duban kayan daya aje a
gaban mahaifiyar nasu.
Tabbas gwala gwalantane data bashi shekarun da dama da suka wuce akan zai shigar dasu ya kara a
jarinsa yaci gaba da kasuwanci.
Ya haka ya kasance hjy ta dago tana tambayan dan nasa cikin mamaki da daure fuska yace hjy akan me
zan sayar maki da wa yan nan kayan masu daraja ?
Ganin kayan haka yafi min kudin da zasu kawo min wanda bani kadai ke da hakkin hakan ba na mu
dukane da sauran yan uwa.
Shiru tsohuwar tayi na dan lokaci kafin ta dago tana fadinn yanzu Ahmad baka saida kayan nan ba
dama suna ajiye kana ta juya wajen kura tace.
To kin gani keda kike tuhumarsa ya sayar da kaya ya danne kudinsu shi kadai ba tare da kuba yanzu sai
ki kawo naki kudin dana baki don kudine zunturutunsa na baki a lokacin ko kin tuna haka ?
Kallon ban gane ba taiwa tsohuwar cikin mamaki tace kwarai yadda kika tasani gaba kan Ahmed ya
cinye dukiya kika so hadani da dan cikina naji kunya Allah ya kare .
Yanzu ke kuma ina kudin wajenki suke ki fito dasu a kasafa abawa kowa nasa kamar yadda dan uwanki
gashi ya kawo nasa kowa ya gani a yanzu.
Yau kin sheda cewa dukiyansu suka nema shida dansa ba wai hakki wani bane yadda kike fama mita
akan kudin nan.
Haka aka tashi baram baram yaya imamu yai wa hjy kura tas a ranan don ya fada mata bakaken
maganganu iya son rasa tana mayar masa da amsa kwatankwacin abinda ya fada din gareta.
Aimana kuwa abin duniyane ya dameta kan yadda taga na sauya mata gani abinda takewa kanta fatan
gani da dadewa ke nan sai gashi a kullun yarinyar nan Aeesha tana son darata.
Inda hankalinta kedan kwanci shine idan ta tuna cewa ita turai tayi niko ina Nageria zaune don ta
tabbatar babu yadda za ayi naje canada iyakata dai nan cikin Nageria din.
Allah sarki ashe ba wai sai manya kadai ke hassada ba abin halintane dashi ake haihuwan mutum ke
nan don ranan da Farida ta fada mata tunda safe aka kaimu airport .
Ranan wuni tayi tana bakin ciki da bacin rai cewan wai nashiga jirgi ita bata taba shiga ba saidai ta
ganshi a sama.
Ba kunya da dare ta kira waya akan itafa ta matsu ya turo da komai ayi auren nan kowa ya huta ko
kuma ta koma taci gaba da karatunta tunda bai shirya ba.
Ya dai samu ya lalabata tayi hakkuri zaiyi magana da mahaifiyarshi duk abinda ke nan zasu gun
mahaifiyarshi din daga baya kafin su dawo su shirya acigaba da hiran arziki tsakaninsu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[9/20, 9:59 PM] Zainab Idris Makawa Writer: ELSUTRA HOME OF FASHION & BEAUTY ACCESSORIES AND
BEYOND
MAMAN BIBO KAYAN MATA
08068871330 KOKO ROAD SOKOTO
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
5️⃣3️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Yanzu kan ban wani dogon motsi a gidan hjyn nan dana dawo aiki muna daki da hafsat data lakanci kallo
season film a laptop dina.
Sai kuma idan na fito neman wani abu ko gaida ita amma zama irin da duk da ko a baya ba wani zama
sosai nakeyi dasu ba yanzu kan gaba daya na daina zaman.
Kusan wata ukku ban san mahaifinsu ba duk da inna ta dan min bayani kansu ranan amma dai ban taba
ganinsa a zahiri ba kwatsam muna kwance Hafsat kece min gobe insha Allahu zamu je gidan daddysu
ance yana gari.
Kafin kuma taja tsuki tana fadin wallahi Aisha bana son zuwa gidan matan nan don a dalilinta daddy ya
rabu da mum din mu hakan yasa naki jinin wanan matar a rayuwana sai dole kawai ke kaini wajenta.
Yanzunma don zancen motarce da muke son ya saya muna yasa na yarda muje inba hakan ba ta kada
kai tana alama da sautin baki gaskiya ba zanje ba Aisha.
A raina kafin na bata amsa nace haka duniya tagada dama yau da nice a matsayinki komai ubana zai
mun ba zan kulaba zan masa biyayya kamar yadda Allah yace aiwa iyayye.
Amma a fili katseta nayi da fadin haba dai antyna ba,a fushi da iyayyefa yau komai yayi maku dole dai
ya amsa sunan uba a gareku.
Allah sarki banda sunan fa Aeesha yanzu gaba daya fa Abba ya mayar da hankalinshi kan diyan matar
nan sam baya zancen mu nida yazid saidai wa acan yaran nata kawai.
Allah sarki bakiji manya na fadin diyan baya sonsu akeyi abin basune babu ba ku manyan nan dai kune
aka fara sani a diyansa dai.
Nasan ranta yakai kololuwan baci don ta kasa ban amsa a lokacin sai shiru da tayi nayi ta zubawa tana
zaune ta kurawa film din da take kallo ido.
Shima yazid yazo da nasa gunguni kan maman tace sai suje gidan wajen daddy su shi wallahi inba don
mama ba babu inda zai tafi.
Shima hakkuri na bashi kusan abinda ta fasa shi yake fada na dai taushi zuciyarsa yayi hakkuri washe
gari din zasu tafi kamar yadda aka umurcesu dayi din.
Washegari misalin karfe goma safe sun shirya banda niyar zuwa don ni ina kwance ina shakan barci naji
an bugeni a baya hakan yasa na bude da dan magagin barci.
Hafsat dince tsaye kaina take fadin ga tsiya kesa na dauka kin shirya sai kuma inzo in samu kina barci
haka ?
Koba zakije kiga Abban namu bane kafin ki tafi fuska na dan bata ina fadin wallahi barci nakeji jiya
kinsan mun dade muna kallo.
Ok kina nufin ba zakije bake nan ta fada a dan hasale hakan yasa na daure na mike na shiga shiri badon
raina yaso hakan ba lokacin.
Mun gama shiri muka fito su dai sunyi kwaliya nikan wani light purpple din abaya na dora saman
wando da dan wani armless din riga dana saka nafito suna falo har uwar kowa ransa bace a lokacin duk
daba magana sukeyi ba kamar dama ni suke jira ina fitowa suka mike.
A motan hafsat din muka gungura muka tafi har unguwar da mahaifin nasu yake da zama a kusa da
Jabi .
Gidane mai kyau nagani na fada tun da muka kutsa kai maigadin gidan ya bude masu yazid ya shiga
suka hango wani motan yara a bakin kofan falon naji yazid yace kingani ba sis anan kudin daddy ke
karewa ai.
Ni dai ban gane me suke fada ba lokacin saida naji tace yanzu kar kaso kaji kudin abin banzan nan
wallahi ya tsayar da motar muka fita zuwa kofan shiga gidan.
Hafsat na jininin fadin zaka gani yanzu sai anga dama a bude muna kofan nan kuma fa ansan da zuwan
mu .
Nikan a yanzu nasan ba karamin tsanar mahaifin nasu sukayi ba ko me yayi masu haka oho amma nafi
zaton don rabuwa da mahaifiyarsu da yayine akan wata mace.
Yadda hafsat din ta fada hakan ne ya kasance kuwa don mun kai wani lokaci tsaye a kofan kafin wata
mace mai fari irin na man shafi tazo ta bude muna kofan cikin kasaita.
Tana da dan tsayi da fadin kirji jikinta saye da wani silk din bubuh maron mai dan hannu sai kamshi
take zubawa kanta yasha kitson ghana weaving masu dan girma tace.
Au kune ta fada a wani yatsune suka amsa zuwa ciki nidai naji Yazid yace ina kwana ko ta amsa oho
amma ita hafsat banji sun gaisa ba.
Daddy ko na gida ya tambaya tace ehh yana ciki bai fito ba tukun can ta juyo tace ku zauna in sanar
dashi ta wuce zuwa ciki abinta ga gidan gaba daya ya dauki kamshin soye soye ana breakfast.
Muna zaune zugun a wajen sai tsuki hafsat ke faman zubawa can bayan kamar rabin awa muka fara jin
muryanshi yana fitowa tare da wasu yara yan mata guda biyu.
Duk da ba yaro bane tunda ya haifi hafsat da yazid hakan baisa shekarunsa sun nuna tsufa a jikinsa ba
yana saye da yar riga jessi yelow mai kwala da dan wani wando baki iya wuyan kafansa.
Nikan yana fitowa na gyara natsuwata waje daya muka shiga gaidashi ya amsa kadaran kada ham kafin
ya kai zaune tare da dagwara karamar yarinyar saman kafashi suka zauna tare dayan kuma tana manne
dasu.
Yana ta hira da yaransa ni kaina sai naji ba dadi yadda ya nunawa su manyan ko in kula na dan lokaci
Abba ka dawo lafiya ?
Yazid ya fada ya dago yana fadin lafiya a takaice kafin ya dora da fadin ya kuke can lafiya Abba shima ya
bashi amsa.
Saiga matar ta fito tana fadin D ka dauki sauran azzanab din dana ajene yace ki duba yana bedside na
dora don yaran nan kada su dauka wani abinci ne.
Har ta juya yace kun gaisa da antyn ku kuwa yana tambayan yaran nidai kaina yana kasa kamar wata
munafuska dani.
Yazid na fadin mun gaisheta ita kuma matar na fadin ko basu gaidani ba aiba matsala don basu gabana
ta juya na dauka zaiji zafin abinda ta fada sai naji ya hau yaran nasa da fada.
Yana fadin ke Hafsat na rasa irin hankaliki wallahi yanzu matar nawama kina bakin cikin ki gaida ita don
kina jin girman kai ko me ?
Amma ai Abba da zamu shigo mun gaida ita bata amsa muna ba itama yace dole saita amsa maku ya
kamata ku gaida ita tunda uwarkuce ita.
Cab lalai ba zaman lafiya wajen nan na fada a raina yana tawa yaran fada sai kace an taba uwarshi
harda fadin idan ma uwarsu ke hure masu kunne suzo suyi mai rashin mutunci a gida su daina zuwa in
sunsan abindake kawosu ke nan gidan ?
Jin hakan yasa na dago dara daran idona na kallesa karo na farko ido da ido don jin katobaran da yake
shukawa gatanshi nagobesa a gaban idonsi.
Babba zai iya manta wani abin yaro kuma yana rike dashi a cikin kwakwalwa kamar yanzune abin ya
faru zai dinga gani shiyasa ake kaucewa idon yaro idan za ai wani abin.
Sai bayan ya gama hucinshi ya kalli Yazid din yace ita wanan wacece kuma da cewani yana wani shan
kamshi dashi.
Bakuwar mum ce daga kano take tazo course ne na wata uku garin nan take zaune a gidan mu ya dan
dago ya kalloni karo na barkatai a lokacin.
Kafin yace yanzu meya kawoku kuma nasan dai baku zuwa inda nake sai idan ta turo ku rokon wani
abin a wajena ?
Ni sam bansan amfanin aikin Wuro ba da bata iya tsayawa tayiwa dinya data haifa laluran komai ?
Yara biyu kacal amma ko yaushe tace ba zata iya maku laluraba idan bukatanku ya tashi sai dai ta turo
ku nan ina fama da laluran wa yan nan kannen naku.
A laikuwa idan har haka wanan mutumin yake da katobara dolene yaransa su tsanesa gaskiya ko uwar
na aiki ai