Chapter 96 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   96 / 109

285K to 288K   out of 326.5K words

mota yanzu a hanyan mu ta zuwa company.

Duk dashi a wajensa hira yake min yana kallona mai nasara inda ni kuma nake fassara zancen da wata
manufa a raina.

Badon na kasance mai ilimi ba a rayuwata a nawa fahintar ba zan shiga harkan kasuwancin Abbi ba ke
nan duk da ina ya daya tillo a garesa ?

A yau ya zama dole in dage in nuna masu ya mace ma diyace kamar kowa naji dadin yadda faisal ya
fada min abinda ya wakana a wajen zaman nasu ranan kan maganata.

Zan kuma dage in nunawa duniya diya mace ma yace kamar kowa ba duk muke da rauni ba duk da
nasan komai dagewana yana da wuya nakai namiji hazaka a wani fannin .

Amma duk da hakan zanyi iya kokarina naga nayi bakin iyawata a nan sai har nake jin dama ban karbi
wanan tayin nasu ba na bore na koma Nageria inda nafi wayau.

Saidai kuma komawata Nageria ai baida wani amfani tunda har gobe bakin fentin da suka yaba min
yana nan a kaina don wasu kallon mara uba suke min a idanunsu.

Tafiya nake amma bansan inda nake takawa ba son ire iren irin tunanen nan daya baibaye min zuciya
ko a yanzu nasan sun yardane don su gwada a kaina su gani yaya zanyi zan iya ko zan gazane ?
Wani guntun murmushi na sauke don jin amsan da zuciyana ta bani a lokacin da nida ke da Man ba
zan taba gazawa ba matukar ina amfani da shawarasa kuwa.

Lura nayi da iein kallon da suke bina dashi sai nayi zaton suna kallona ne a matsayin bakuwae fuska a
cikinsu yasa suke min wanan kallo haka.

Wai kinsan me suke kallone ?

Muryan Faisal ce ta daki kunnuwana na sauke ajiyan zuciya ina dan girgiza masa kai yake fadin suna
kallon ke mace ce ba zaki iya wanan harkan ba.

Dan murmushi na sauke a fuskana kawai ina cigaba da amsa gaisuwan da suke min tare da bin duk
wani umurni da Man ya dorani a kai na tsare gida.

Ba sai an fada ba wajen sabon wajene da ganinsa don komai neat a wajen haka ma aikatan wajen suma
matasan larabawa masu jin sun kai.

Da bissimillah na shiga office din wanda tsayawa fadan girmansa da irin kayan rayuwan dake ciki bata
lokacine ga computer irin da sai a film nake ganinsu new morden din nan.

Addu,a nayi na zauna yayin da suka fara gabatar min da kansu nayi fatan Allah ya bamu hakkuri da
juna tare da fatan samun hadin kai a tsakanin mu.

Faisal baiyi kasa a gwiwa ba dan ya tsaya kamar yadda aka umurcesa da yai min ya nuna min wasu
abubuwa da zasu iya shige min duhu.

Amma kuma saiya fahinci na wuce hakan na barsa da mamakina a kasan zuciyarshi har yana dan
waigena wani lokacin.

Nageria kasan mu ta gado ko dame kazo an fika kana muna kallon birai muna maka kallon ayaba duk
inda dan nageria ya shiga saiya fito daban.

Saidai idan mashiririce za a barsa a baya wajen komai sai kuma idan mutum ya saka duniya a gaba
dama ita zaune take tana jira a kullum badai kaga karshenta ba saidai taga naka duniya ke nan.

Sunso su afkani ni kuma na samu training na kwana biyu tsab daga wajen man daya koyar dani dabaru
a kansu sai gashi koda zan dawo gida na samu kakana har da dinner na mussanman ya hada min a ranan
shi da matansa suna zama jirana.

Donshi kakana kyalewa yayi kawai su gwada din don yasan ba za akai ko,ina da wanan dabaran nasu ba
duk da yana da yakinin zan dan turza irin nawa fasahan daya hango a gareni.

Saidai abin mamaki koda ya kira Faisal yaji me ake ciki sai labari yasha bamban don abinda Faisal din ke
fada masa .

A wani tafkeken gida da wasu mutane suke zaune suna tautaunawa kan wani bussiness dayan da
hankalinsa ke a waya ya dago yana fadin.
Imposible wanan ko yana da hankali karamar yarinya kamar wanan zai mikawa company irin wanan
mai kyau da tsada da muhinmanci ?

Hankalin sauran ne ya dawo gareshi suke tambaya yake fadin Omar sultan ne ya dankawa bakuwar
yarsa wanan company daya bude wancan watan.

Dariya suka kwashe dashi kafin wanda yafi manyata yace ai hakan yayi kyau faduwarsane yazo yanzu
don ba karamin kudi ya kashe a wajen aikin nan ba amma kuma don batar basira ya dauka yaba yarsa
jagoranci yar ma rainon Nageria ba wani kasa mai muhinmanci ba.

Dadai ya kaita club ta dinga rawa da waka irin nasu na can watakila da ta dan sama masa wasu kudin
ya kara a bussines dinsa zaifi masa wanan gurguwan dabaran da yayi din.

Dariya sosai suka kece dashi lokaci guda don abinda mutumin ya fada sai mutum dayane baiko kallosu
ba balle ya dara din.

Ganin hakan yasa suka kalloshi yana a yadda yake kamar mai tunane kafin na kusa dashi yace wai bakaji
me muke hira bane a kai ?

A dakile yake fadin naji mana gani nayi hakan bai shafemu bane matsalan gaban mu shine abin yi
yanzu a garemu.

Omar Sultan mutum ne mai matukar kaifin basira hakan da yayi yana nufin yasan yar nasa yaya take ya
dora ta a wanan harkan bawai haka kawai zai dauko yarinya daga Nageria ya dorata a cikin bussiness
dinsa ba.

Kukewa yan Nageria wanan kallon na dakikai basu iya komai ba sai rawa da waka ku duba ko wajen
musabika yadda suke da baiwa da basira mana.

Me kake fada hakane Nasirdeeen kana zance kamar kana da wani masaniya akan yarinyar nan ita din
fa macece fa Nasirdeen ba namiji ba ?

Ban sani ba amma zansa a binciko min baiyanai a kanta don sanin gaskiyar zancen bayan haka kai da
kake wanan magana haka ?

Mata nawa suke da kwazo ya sake fada a dakile yana kokarin mikewa suka kara binshi da kallo yace shi
zai tafi tunda sun gama abinda ya kawosu .

Suma mikewa sukayi ba tare da sun tsaya kara wani zance don kan a lokacin ya barsu da kwankwanto a
zukatan su tunda sukaji ya fadi hakan .

Saidai dukkan su babu halin tambayansa dalili duk da ya nuna masu baisan komai a kaiba amma kuma
suna da tarin tambaya saidai ba fuskan hakan a wajensa.

Wata mota ya nufa da tun kan ya isa gaban motar ya matsa remote ya hankade motar dake bada wani
dan sauti wanda hakan kan jawo hankalin mutane a gareshi.
Arziki da martaba Allah yayiwa balaraben mutum shi a duniya tankar yadda dan arewa yake a zamanin
daya wuce wajen sauran kabilim Nageria .

Ba a yanzu da yan arewa din suka zubar da kimarsu da mutumci a idon sauran kabilun Nageria din don
kwadayi da son abin duniya ada dan arewa ko almajiri yan kudu suna bala,in tsoronsa ba don komai ba
sai hasken musulumci da zallah imani dake tare dashi.

Amma a yanzu a wullakance dan kudu yake kallon dan arewa saboda halin yaudara akan abin duniya da
rashin amana da yai yawa a yanzu cikin zukatan al,umman bahaushe .

Odan kana neman tantiri daya waye yake iya shege ka samu dan larabawa a yanzu ka gama gani wanda
a yanzu suma surke suke da jimsi daban daban daban nacikin duniya.

Musanman a nan dubai da yazamo kasan kazo nazo a yanzu don tushen harkan kasuwanci na duniya
daya zama a yanzu.

Wanan yasa kowa zaka gani a Dubai din da tashi kalan shigar kasansa wanda yan kasan wani lokaci suke
yawan koyi da hakan a al,adunsu sai da kyat zaka iya bambata su da sauran al,umma .

Karfe tara daidai nashigo gidan inda umma halimat ta tareni tare da gaidani ta kuma isarin da sakon
kakana dake gaiyatana cin abincin dare.

Saida na shiga na dan watsa ruwa a jikina tare da sallolina na fito na samesu a zatona sun kare har sun
bar wajen a lokacin saidai ga mamakina suna zaune suna jiran karasowana.

Gaidasu nayi a cikin mutunci kamar yadda na fahinci suna jin dadin hakan da nake masu haka din nema
har a cikin ransu don naga yadda masu shigowa suke gaisawa dasu .

Saida mukai nisa ga cin abincin naji muryan kakana yana fadin amma kin taba irin harkan bussiness din
nan a baya ko don nayi mamakin yadda yau din nan da farawanki komai ya tafi daidai a bangarenki haka.

Don ko wanda ya taba irin hakan ba kowa bane zaiyi saurin yin yadda kikayi din nan abinda mamaki
gaskiya ?

Saida nakai cibi a bakina nake fadin banta ba kaka indai wanan harkance haka saidai nayi aiki da wani
ma,aikata dake headquater din mu na can a can nasan wasu abin.

Amsan dana bashi ke nan a takaice don irin tambayan da yayi min din ke nan a gurin Faisal yaji komai
dalilin hadamun da yayi dashi ke nan don ya saka min ido ga abinda nakeyi din.

Katse min tunanena yayi da fadin dole dai nasan kina da ilimin hakan a gaskiya da alama zaki bamu
mamaki cikin harkanki nan gaba idan kinci gaba da hakan.

Murmushi nayi ina fadin ban kai a fara yaba min ba sai anga abinda zai faru nan gaba zaifi shima Faisal
daya guntsurama labarin ai shawaran yan marketing na nema da hakan.
Gara mu fara da talla don duniya ta san mu tasan irin kayan mu kuma zaifi da mu dinga yin abu a
dukele ba kowane zai san mu ba a nan illa iyaka a cikin fadin kasan kawai zamu dan haska.

Kai ya jinjina yana murmushi muka kare cikin hira dashi yayin dana mike yake fadin zan kwanta ke dole
ai don akwai gajiya sosai ga aiki.

Zan dan taba karatune na bashi amsa ina shigewa tare da yi masu saida safe na bar wajen zuwa part
dina dake cikin katafaren gidan nasa da baida iyaka.

Babu abinda ake haskawa a tashoshi nahiyar da dama sai tallan kamfanin mu din da irin abubuwan da
muke saidawa har ta online muna bussines da mutane.

Wanan ya kara haska mu don bayanin dana fito inayi a karshen tallan a nan mutane da yawa suka
sanni da kuma koni wacece .

Da yawa suna mamaki zamana ruwa biyu da hakan bai sauyani ba haka a bangaren iyayyena su zallan
mamakine ya rufesu yadda nake abu a cikin hikima da basirata.

Don sam ba wanda yai zaton haka din sai gashi masana,anta namu ya samu karbuwa ta wajajen
mutane Allah ya buda muna kasuwa ta ko ina.

Wanda har hakan ya fara shagal dani da gida da iyayyena saidai ban yarda da hakan ba illa a yanzu dai
baifi mu gaisa dasu ba da nakeyi a online sau biyu ko sau daya a sati.

Haka kuma haka kawai zanyi shiga irin tamu ta hausawa a ranan nakansha kallo sosai a wajensu zasuyi
ta min tambaya akan yadda na iya wanan shigar ta atamfa din.

Da mamana na Abbuja ce ke dinko min tana aiko min dashi a yadda zan iya shiga babu takura a nan
don ban yarda na yarda duk wani wanda yai min mutunci ba a baya.

Haka kawai kwana biyu naji ina son ganin kaina a Nageria don yawan tunanensu dake addaban
zuciyana wani lokaci.

Sam banson na zamo butulu a rayuwata don haka na yanke shawaran fadawa kakana niyata nason
zuwa gida da nakeyi bayan ga aiki tukuru da yanzu ya taso muna a company mu.

Lokacin dana sameshi da zancen sai naga a take fuskansa ya matse bai boye min ya nuna min baya son
nayi nisa dashi a yanzu donshine ma ko kasansu bai yarda inje don ina da amfani sosai a wajensu.

Mamakine nima ya baiyana karara a fuskana don ban zaci jin hakan ba a garesa sai gashi yana jero min
dabara da fadin.

Kiyi hakkuri ki zauna ki fuskaci abinda ke gabanki idan ma don tsofin nan biyune zan sa a turosu suzo
nan ki gansu su kwana biyu tare dake.

Don naga kun shaku sosai dasu ban iya magana ba saida na dan jima zaune a wajen kafin na mike zuwa
part dina da son samune aini banki ace kowa na kusa dani muna tare dashi ba yanzu a nan.
Amma kaddara kaddaran da zankirashi da rataya nauyin kaddaran wasu daya dawo kaina ya rabani da
ainihin mutanen dana saba dasu suka ban tarbiyan da yanzu nake amfani dashi.

Gashi a kullum muke vedio call dasu Ammah saita tambayeni cikin damuwa da yaushe zaki dawo
gidane Aeesha ?

Na kanji anty safiya na kwabonta da fadin haba mama yakamata fa ki hakkura ko ita ai zamanta a can
yafi mata nan yanzu.

Mutum yana cikin daulan duniya haka yaushe zai tsaya tuna wanan akulkin namu don Allah mama kima
debe rai ga dawowan Aisha nan kuma Allah ya kaita gaba.

Wanan maganan ta fadeshi kusan saubiyu nasanta nasan halinta don hakane zancen ya tsaya min a rai
ina yawan tuna wanan zamce idan sun fado min a raina.

Yana daya daga cikin abinda ke takuran zuciyana a yanzu don magana take zubawa Ammah a fakaice
da nasan zata baiyana nufinta a bayana.

Mahaifina yakawo muna ziyar kamfanin mu mun jima dashi muna tataunawa da bamu taba yi dashi ba
hakan yasa na fahinci nauyi da alkunya yakewa yan uwansa da mahaifisa hakan yasa yake nunawa a
gaban mutane kamar babu ruwanshi dani.

Don ko wanan zuwan korafi yazo min dashi yana fada min ana yawan masa sata ta account dinsa ya
rasa daga ina wanan abin yake fitowa haka.

Yayi iya bincike ya kasa gano wanda ke yawan tatsansa a boye dan shiru nayi kafin nace zan iya ganin
details din komai na accout din nasa sai yaban zuwa kwana biyu mu gani.

Ga mamakina baiki ba sai gashi ya karanto min komai na rubuta a cikin wayata da zai tafine nake fada
mai yadda mukayi da kakana na son zuwa na dubo iyayyena don da haka nake kiransu ko a gaban kowa .

Dan jin yayi kafin yace dani nasan mai Abbi ke nufi da hakan yana ganin idan kin tafi ba zasu barki ki
dawo nan kusa ba zasu iya rikeki a can din ko dai wani abu makamancin hakan ya biyo baya.

Murmushi nayi ina fadin har da kaima ka yarda da zan iya barinka a cikin wanan matsalalon dake gaban
ka yanzu ?

Ban taba tunanen hakan ba amma shi Abbi a nasa tunanen zaki iya canza ra,ayi ki koma hannun
mutanen Nageria kuma gashi na kula kin shiga ransa sosai a yanzu don ban taba zaton hakan ba.

Har dai mukai sallama dashi banji wani abinda zai bani kwarin gwiwa tafiyana ba saidai nuna min da
yayi na bari nan gaba kadan ai zanje din tunda yai min alkawarin hakan dama.

Hakan dai muka rabu ya barni da dinbin tunane a raina kafin na soma laluben man da zancen da
Abbina yazo min dashi din.
Ki ban nan zuwa gobe zan turo maki da komai akan account din sai ki duba ki masa bayani yadda zai
fahinta nayi masa godiya muka taba dan hira aka bussines dina kafin muyi sallama dashi din.

Shigowan wasu masu son kulla halakan kasuwanci damune a bazata ya katse min dogon tunanen
dana shiga a lokacin.

Don Jiki na rawa faisal ya shigo yana min albishir da zuwan bazata din da sukai muna tare da kara
jaddamin cewa idan muyi nasaran hada wanan bussiness din dasu akwai karuwa sosai a ciki da daukaka.

Hakan yasa muka shiryawa zuwan nasu ba afi yan mintuna ba suka karaso taro na musanman nasa
akai masu wanda basu taba samun irinsa ba .

Kafin mu shigo inda zamu gana dasu din mu tatauna yadda farashin mu yake da kalan kayan da muke
bayarwa din a company.

Saidai nayi mamaki kwarai ganin matasan dake zaune a gabana don a zatona na dauka wasu manyan
hamshakaine zan gani a idona sai gashi naga sabanin hakan.

Da farko godiya suka fara yi min kan karamasu da akayi sai lokacin na dan murmusa ina fadin Annabin
tsira Alaihim sallam ya muna koyi mu mutunta bakon mu har inda hali mu mayar da bakon kamar wani
sarki a wajen har ya tafi.

Sai dayan ke fadin sai gashi kinyi dace daya daga cikin diyan sarkine yau a gaban ki kuma mun yaba da
irin tallan da muka gani na kayan ku shine muke tunanen masarauta tana bukatan kalan kayan nan da
dan lokaci.

Wace ta fito kano ana nuna mata izzan mulki dai gwagwado muna ji muna gani anayi a gari saidai
al,ada daya dan bambata danasu a nan kadan.

Don zan iya cewa komai na malam bahaushe sak na baraben mutum ne dan bambamcin kadan ne a
tsakaninsu gaskiya.

Don ko wani kabila yana surkawa da al,adan garinsu shine kawai bambancin dake tsakanin mu dasu
din.

Cikin yadda na iya na ban girma ba tare da na yarda na bada kaina ba nake mika godiyan kamfani a
garesu na bamu wanan daman da sukayi ta hada hurdan bussiness damu din.

Larabcina ba nisa yayi sosai ba don haka nake surka masu da turanci don naga suma yan zamanine ba
wasu tsofi ba da alaman hakan da nayi masun yai masu daddy inda na fara masu bayani a jikin allon
bangon mu mai na,ura akan kayan da muke dasu din.

Sosai suka yaba da kayan suka saka hannu akan jarjejeniyar mu dasu sai da zasu tafine wanan dayan
yai magana a karo na farko yana fadin .

Munji dadi kwarai da irin taron da muka samu a wajen ki ba tare da an samu wani matsala ba ko wani
dan tangarda saidai matsala daya shine.
Jin hakan yasa na kasheshi da idanuwana nima kamar yadda yake kallona a lokacin don a zatona zasu
fasa wanan harkallan damune ko kuma wani abu.

Ssi naji yace ko da yake barshi ban sani bako don karon farkone akai muna sauki haka don gobe mu
dawo amma ina fatan kayan qualities ne kamar yadda kuka nuna.

Gyara zaman dan tabarau dake fuskana nayi kafin nace basai mun tura kudi da yawa a kayan mu zaisa
mu asan qualities bane sayan nagari maida kudi gida akace.

Haka kuma dan abinda zamu samu kadan yafi albarka a garemu da yawan riban da zamu saka a kai ya
mike yana fadan masha Allah tare da

96 / 109