Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
fada ta nufi hanyan fita daga dakin na zauna ina kallonsu a inda na tashi kayan dake
gabansu na dan kalla kafin na mayar da kallona ga khairat ina fadin.
Anty khairat yaya aiki ya kwana biyu ta zauna cikin gajiya tana fadin aiki lafiya lau ke dai Aeesha kinyi
wuyan gani ko dan wayan nan kwana biyu ?
Anty khairat kiyi hakkuri kwana biyu munyi exam mun gama kuma na danyi zazzabi kafin kuma na
wuce Abuja wallahi.
Mun dan taba hira anty ummi ke tambayan anty safiya muke bata labarin yadda mukayi da ita ta
kwashe da dariya tana fadin ai barin tura a dauko min ita ai ina son ganin mutumiyar sosai.
Nan mukai sallah azahar kafin mu bar gidan muna fitowa muka shiga mota sai da na dan busar da iska
nake fadin Asmau zaki gane gidan ummu ?
Wai wai wai ta fada gaskiya ni kinsan mummy ba fita nakeyi garin nan ba samira fa muje in munje kila
zan iya ganewa ta fada.
Da bacewa da komai muka karaso koda ta nuna gidan saida nace anya samira gidan nan ne kuwa don
wani irin katon gida mai dogon katanga da shuke shuke dana gani.
Tace Allah gidan ne mummy naji Asmau tace gidanne ga unguwae ai yanzu na gane gidan sosai nan
muka tsaya yin horn wani mai gadi ya leko sai kuma ya rufe ya fito daga waje yana tambaya su waye ku ?
Don masu gidan suna hutawane yanzu basu ganin kowa ikon Allah to shike nan ku sai mu koma tunda
ba,a ganinsu yanzu.
A kasan raina kuma fada nake ina fadin eeh lalai dole ummu ta manta dani dolene ta manta ta haifi
wata shegiya kada in bata mata tsari maigadin ne ya katseni da suke magana da samira dake fada mashi.
Kai mufa wajen uwarmu mukazo ba wani abu ya kawo mu ba kada ka dauka maula mukazo don Allah
inzaka bude ka bude muna ko shekaran jiya ai kaga driversu ya shigo damu ko ?
Shine yace hjy kada kiga laifina haka dokan mu yake kada in rasa aikina ai bance maku yan maula bani
kunyi hakkuri don Allah da sauri kuma ya juya yana kokarin bude kofan don wata bakar mota da zata
shigo gidan.
Sai kuma ya dinga muna hannu ina kokarin ribas da motar yake muna alaman da mu shigo ni banko
kula ba saida suke fada min yace mu shiga.
Maryam tace inaga mai motancan ne yayi masa magana ya barmu mu shiga sai lokacin na juyo ina bin
motan da kallo babu ko tantama man ne duk yadda akayi.
Na fasa shiga kawai mu juya nace da sauri naji samira tace haba mummy gamu ga gidan zakice kin fasa
shiga don wanan maigadin ?
Kawai dai banjin shigane na fada sai naji farida daga bayan motan tana fadin sauke mu mukan mu
shiga wa zaki kula wa sheri ki hana mu shiga ?
Ku shigo mana aka fada daga kofan shiga gidan Nasir ne dan uwan man din suna da dan son kama
amma ba sosai ba yana tsaye ya rike weast dinshi da hannunsa biyu.
Saida naja tsuki na danna motar zuwa cikin gidan har zuwa wajen parking din su dake da girma kamar
wani company na tsaya.
Sai surutu sukeyi kan gidan wanda hakan ke kara min haushi da takaici a zuciyana da ace ta mayar dani
abin kwarai da wane maigadi da ya tsayar dani yace ba zan shiga ba.
Jifa wai kuma laifin ummu da bata masan da zuwan mu ba na koma gani koshi maigadin da yasan
alakata da ita aiba zai min abinda yai muna din ba amma ina zuciyata ta rufe a lokacin .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[10/25, 7:54 AM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
7️⃣7️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6
https://sitrix.africa/signup.php?ref=foleesco
Kaina danna nashiga da hancin motana gidan kai tsaye saida mukai parking ne sun fara bude kofa farida
ke fadin dankari.
Ashe mu kauye muke zaune bamu sani ba yanzun a garin nan wanan irin gidan yake naji samira na
fadin me kika gani kuwa aisai kin shiga daga cikima zakiyi kallon duniya.
Dole kan don Allah ki duba suma yan gidan aikosu abin kallone tana fadan hakan naji Asmau tace
wanan can fa daddy na man ne banjin mai gidan nan ne ya haifesa .
Ai shine Man din mummy na mana ashe baki taba ganinsa ba kema duk suka juya suna satan kallonsa
Allah yasa a cikin mota muke bai gansu ba lokacin.
Wai dama shi dan gidan nan ne ta sake tambaya cikin mamaki kwarai kuwa yayan mahaifinsane mai
gidan a dole tasan komai ta shiga dan masu bayani a gurguje.
Idan ba zaku fita ba in juya mu tafi ai kwa bari mu fito ku fara gulman ku ko na fada ina kokarin tayar
da motana .
Ihu suka saka min kafin suka fara fita daga motar sau daya na daga kai na kalli gidan na dukar da kai
ban sake dago kaina ba har muka karasa a daidai inda nake jin suna gaidasu .
Banyi magana ba muka shige kai tsaye cikin gidan innalillahi na fada a raina don sanyi da kamshi dayayi
min sannu da zuwa tun farkon sa kai a cikin gidan.
Aljannan duniya inji farida naji kawarta tace me kika gani bari dai mu karasa ciki kisha kallon duniya ai
iyakace gidan nan ke dai.
Asmauce gaba itace ta rangada sallama suna zaune suna kallo suka dan dago suna amsawa kafin su
mayar da kansu ga kallon da sukeyi sun zauna sun saka laptop a gaba ga katon tv mai kama da bango
yana aiki amma sun rage karan tv suna kallon laptop din.
Shi babban ya fara ganina don shine yayi karshen dago kansa kallon waye ya shigo a lokacin yayin da
yan aikinsu suke zaune gefe suna kallon tv hakana duk da bai magana.
Acikin larbaci yake mikewa tsaye yake fadin gani nan duk suka zabura sukayo kaina lokaci guda suna
min sannu da zuwa duk wanda yazo zai riko hannuna ya sumbanta ya gaidani.
Umar din nasu ya shiga kiran maman nasu tazo gamu munzo nan yan aikin suka fara gaidamu muna
amsawa ba,a jima ba mukaji fitowanta don karan da kofan yayi a lokacin.
Masha Allah lalai marhabin take fada cikin nuna jin dadin zuwan namu tana kaiwa zaune yaran duk sun
zuba muna ido suna kallon mu.
Saida ta gama gaisawa dasu ta juyo gareni take fadin Aliyu yayi fushi Aeesha har yaji sauki bakizo kin
dubashi ba da baban kine Umar da tuni kin zo gaidashi ai.
Nima banda lafiyane saida Abbu yaje chemist ya sayo min magani nasha aiko basu fada min ba inace
dai kin zuwa kikayi dubashi ai ?
Shigowan su man falon tare da dattijun da lokaci guda muka zube muna gaidashi a cikin fara,a yake
amsawa tare da fadin yanzun nake jin bakine damu gidan.
Wai baki Aeeshace bakuwa kuma Alh gata nan dai wai tazo gaida Aliyu nace baya son gaisuwan baya
don yaji saukin jikinsa ko.
Ina tazo ta kwana muna biyune nan har a gama walima ya fada yana kallona da sauri nace a,a Abba
mun dai zone mu gaidaku na koma gida.
Kaima kasan wanan ba zata yarda ta zauna nan ba ai a raina nace ban ma taba wanan ba indon nice
amma a fili cewa nayi Abbu ba zai barni ba.
Ai komai Abbu dai Abbu wanan Abbun naki ya sagartaki da yawa nikan ni dai nayi murmushi a daidai
lokacin umar din yazo ya watso min larabcun da nakasa ganewa sai karshe cikin fahinta na fahinci me
yake nufi.
Haka nima na dage na hada dan larabcin dake bakina wanda wa yanda ke falin suka dauka larabcin
kwarai nakeyi niko ina ganin shirme ciki ko har da Man.
Don bai taba zato ko tsamanin ina dan jin ko bihin ba kamane dai kawai dasu da nakeyi wanan abin ya
tsaya masa sosai a zuciya da har ya kasa daure hakan a ransa yace.
How comes ta iya larabci haka baffa saida baffan nasa yace shine abunda nakewa mamaki nima
yarunyar nan tana da kaifin basira sosai.
Suna gefe suna dan maganan su ni kuma muna gefe ummu na kokarin jan mu da fira gaba dayan mu
dan takan dan sako sunana tana tambayana wani abin.
Ummu bari na nunawa su maryam gidan mafi kuna iya ku tafi tayiwa dayan matan larabci ta mike don
ta kaisu ko ina na gidan a lokacin.
Na gyara zama tare da maida hankalina ga yaron mummy muje ku gani mana wani bacin rai naji da
dana sanin zuwa da Asmau saboda zakewanta.
No kuje kawai nagaji wata rana zan gani ai insha Allahu suka tafi suka barni zaune ina mai jin haushin
Asmau din a raina.
Ai kema kinsan ba zata ba wanan bata rage mahaifinta da komai ba naji ummu na fada daga inda take
Umar bin sultan Rashid kan akwai izza da isa ga wanda bai fahinci halinsa ba.
Wanan yasa kaga halin yarinyar nan bai zamo bako a gareni ba don kome tayi sai ta tuno min da
yanayin ubanta sak wallahi.
Nayi dan murmushin gefen fuska a bakina duk abinda suke fada ina zaune tare da yaron da yanzu
babban ma ya taso ya dawo inda muke zaune kusa dani wajen da maryam ta tashi yana tambayana
season two din fim din throw daya kalla.
Sun jima a ciki har na fara matsuwa da su fito mu tafi kwatsam akai sallama aka shigo hindatuce ta
shigo gidam a lokacin.
Ta sanni na santa farin sani kowa yayiwa juna a cikin mu duk kuma akan man da shima yake zaune falon
a lokacin.
Saida ta kadu da har ta kasa boye hakan saida ta nuna kaduwanta da ganina gidan a fili.
Saidai ganin iyayyen ta a zaune bai bari ta sake layi ba lokacin saboda taka tsatsan da aka ce tayi da
uban kada ya wofintar da ita a zuciyarsa.
Yayin da nake mamaki koda yake ba abin mamaki bane don naganta gidan tunda su din yan family
dayane dama dole dai wani halaka zai kawota gidan a lokacin.
Suna gaisawa da mahaifin nata yayin da taiwa ummu wani gaisuwan da yaci min rai kasan zuciyata
don babu tarbiya cikin gaisuwan kamar na dole.
Banda harara ba abinda ya hadani da ita a falon sai kuma naji tana masu sai anjima ta fita nidai ina
zaune ina kallon ikon Allah a wajen.
Saiga su Asmaun sun dawo suke fadin sallah zasuyi su maryam nacan suna alwala ashe shiyasa mazan
fita bayan fitan hindu data shigo falon.
Hakan yasa na mike da zumar bin Asmau din sai naji tace dani barin zo kije dakina kiyi alwala a can ?
No barshi naje gunsu inyi ummu au dakin nawa ma ba zaki shiga ba ke nan gara kije gun yan aiki kiyi
Aysha ?
Sai nayi kasa da kaina don banda tacewa kuma ga abinda ta fada ta mike dole na bita zuwa dakin data
kira da sunan nata.
Wa iyazzu billah na fada a raina don wasu irin set din kayan daki na waje da nayi arba dasu a dakin
lokacin kayan white & brown colour masu masifan kyau dasu.
Kamshine ko sanyi da laushi wani zan tsaya tambaba a cikin dakin wai a nan ummu ke rayuwa hakan
yazo min a zuciya na bakinsu sukace khalas.
Don Banga wanin abinda rayuwa yake nema ba yanzu na jin dadi a wajen nan bandakin ta nuna min da
hannu tana fadin ga bayin can.
Ki shiga kiyi idan kin fito sai in shiga nayi barin dawo ta fada tana fita daga dakin na sabule gyalen kaina
ina aje jakata saman gado naji wayata tayi kara sakon ya shigo a lokacin.
Ban tsaya duba ba na nufi bandakin da nan ma saida na shagala don kayan wankan wanke jikina da kai
da baki gasu nan kala kala a bandakin.
Ni dai fadin rai bai barni nayi kauyanci ba inda Allah ya taimakeni kuma zuwana Abuja na dansan yadda
ake kunna ruwan irin famfon gidan a can.
Ina fitowa itama take shigowa bata tsaya ba tunda ta nuna min abin sallah dake dakin ta shiga tayi
alwala na tayar da sallah.
Har ta fito ta zo itama ta tayar da sallah kafinta sallame na idar na nade abin sallah zan fita tayi min
inkiya da na dakata kada in fita din hakan yasa nakai zaune kasa gefena.
Tajima tana addua ta shafa ta mike tana nade sallayan tare da kallona tana fadin naga hankalinki yana
kan kawayen ki na kula da kina sonsu sai da alama ?
Ba kawayena bane yan uwanane da Allah ya ban don suma suna kaunata kamar yadda kika fada ina
masu don bamu taba samun matsala dasu ba gaskiya.
Saidai uwayensu ko don nasan sune masu yadda zancen da kike fushi dani akansa har kike dauka
gaskiyane ?
Na dago na kalleta da sauri kafin na mayar da fuskana kasa in sada tace bansan ko sai yaushe fushin
naki zai kare dani ba ?
Duk da nasan fushi wanan gada kikayi don hakan ban damuwa da fushin ki na rashin sani kikeyi dani
din ?
Ummu fushi akan me ni bani fushi dake wallahi na fada a sanyaye sai naji tayi dan murmushi tana fadin
haka dai kikace duk da dama ance haka kike miskilanki tun kina karama .
Saidai ina son ki sani yau wallahi kin gani nan ki rubuta kuma ki aje a cikin ranki cewa tunda nake a
rayuwana ni Nana Asiya kamar yadda iyayyena suka rada min suna dashi.
Wallahi Allah ban taba zina ko kwatanta yinsa a rayuwana ba tunda nake da kurciyana kuwa har girman
nan nawa inma dashi kike kallona yasa banda daraja a idanunki.
Wani irin kallon mamaki na dago ina mata tace yes kin dauka abinda mutane suke yadawa shu din ne
gaskiya a zuciyar ki a wajen yawon banza na samo cikin ki da wani balarabe can cikin duniya ?
Umm,umm wallahi ni Asiya ban taba kwatanta aika zina ba duk da ukuban rikon da nasha a rayuwata
bance masu zuwa wanan harkan basuyin hakan ba don ba duka aka taru aka zamo daya ba dama ?
Saidai ni kaina na sani wallahi ban taba gigin aikata hakan ba balle na zubar da mutuncina har in
sameki ?
Kaddarace wace ta riga fata da rabon ayi yasa na fada hannun rikon matar data yaudari iyayyena har ta
sayar min da mutuncina da sunan mutu,a.
Sam banda kurciya a lokacin daya hana ingane nufunsu a kaina da hakan bai faru ba inma laifine shi
wanda kike muradin ganin a rayuwanki bani ba shine sanadin wanan abin.
Don ya aureni da yaudara ba tare da sanina ba da hadin bakin yar uwar mahaifina daya bata amanan
rikona a hannunta duk da irin ukkuban data gana min a lokacin.
Hakan bai isheta ba kuma saida ta sayar da mutuncina data iyayyena da suka yarda da ita taba dani
akan auren mutu,a wanda nan ba a faye yinsa ba.
Don haka ba kowane yasan sa ba sai can nahiyar laraba dake da yawan yan shi,a suke wanan dabi,an .
Saidai a lokacin yadda nake ganin na samu yancin kaina tare da sa,an samun balarabe dan usuli mai
ilimin boko dana addini haukan kurciya ya hana in fahinci hakan a lokacin.
Aurene kamar na kwangila da zakayi da mutum na zuwa dan lokaci bayan wa,adi ya cika ka rabu da
mutum ba tare da kun haihu ba ko kaci gadonsa.
Sam ban zata hakan bane don da yawa manya a can suna yinsa mukanji ana fada wance tayi auren
mutua na lokaci kaza .
Saidai a boye suke wanan dabian don hukuma data hana yinsa gashi sam ban fahinta ba saboda
kurciya iya wasu yan tsirun gagan matane suka halarci taron bukin.
Wanda inda a yanzune dole ingane suna da manufa a kaina amma ina lokacin wayau bai kai ba balle
hankali da zangane haka.
Don basufi su bakwai ba a wajen mazansu da matansu gagan takarin mu nacan kuma haka suka
dunkulani suka kaini har binin Riyadh gidan mijin.
Ashe sun karbi makudan kudine a wajensa lokacin suke wanan rawan jikin haka suyi sukaini kada
zancen ya fito fili komai na hakkin aure ya danka masu har da niki a kai.
Hakan yasa suka rude sukai abin a dukulkule ba tare da sun bari kowa yasan da hakan ba suka kaini
gidamsa.
Saidai na samu miji mai mutunci wayayye mai ilimi daya kara shagal da kurciyana na har nake dauka
zaman Allah da Annabi yakeyi dani a lokacin.
Don bai rage min duk wani hakkin aure na rayuwan miji da mata ba a duniyan nan babune kawai
bandashi a lokacin saiko kewan yan uwa da kanzo min a zuciyana.
Ga daula amma ina nida da yan uwa da abokan arzikin da zasu tayani cinsa saini kadai ke facaka da
abina a cikin kurciya don iyakata inci inyi wanka in kwanta don akwai mai aiki har biyu a gidan dana
sama.
Faruwan komai ya somane a lokacin dana baiyanar masa da samun cikinki wanda bai sani ba bai kuma
fargaba saida ciki ya tasa ya zama dan mutum a jikina nima na gane shine dalilin sanar masa din .
Na tsanmacin farin ciki a gurin shi sai gashi naga sabanin hakan a gareshi don kwance yake nake fada
mai ina ganin cikine dani yasa saida ya mike tsaye don kaduna yana tambayan wata nawa nace inaga zai
kai hudu ko biyar .
Iya rudewa da tashin hankali na gansa garesa a kwana biyu bayan wasu yan kwanaki kuma sai naga ya
watsake kamar bashi ba saidai duk da ya watsake din lokacin ba don kurciya ba da rashin abokin
shawara a kusa ya kamata in fahinci wani abu a garesa.
Don dai bamu koma kamar da sosai dashi ba amma komai yana min yana kuma halakan aure dani har
zuwa lokacin