Chapter 46 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   46 / 109

135K to 138K   out of 326.5K words

din ya fada mata har take son daukan
wanan mataki a yanzu duk da yasan bai wuce ya goranta mata kan mahaifi ba dai.

Shi daine abinda zai fada wanda yasan zai bakanta mata rai fiye da komai a rayuwanta yaushe zasu
daina irin akidan nan ne ?

Duk da nasu case din ya gane ba akida bace illa zallah son kai da isa da izza da mummy kura ke son
nunawa kawai akansa amma bai dace kuma tayi amfani da salman ba a nan ?

Sanin yadda suke da salman din tun suna yara duk da shima ya saka son rai a cikin lamarin koda yake
fadan haka a gaban mami ya ci arzikin hakan ne a lokacin.

Yasa ya daga mai kafa daya gane baida wayau har nawa zata bashi ko me zata fada mai yaje ya aikata
hakan thank god bai fada mai komai daya danganxci yarinyar nan dama don hakan ba dabi,ansa bane.

Har wani na kusa dashi yasan abinda zaiwa mutum na alheri saidai idan mutum yaji daga baya bakin
wanda yaiwa din amma ba a bakinsa ba.

Ko Auwal da yake aike don sanin halinsane da yayi yasa ya yarda ya dorashi a wanan fagen tsakaninshi
da ita tunda shi ba halin a gansa wajen yanzu zancen zai bi gari da wani fassara na daban.
Ido ya bude ya kallon irin halinda akaso jefa sayadi a ciki ba don Allah ya kareshi ba daga abinda akai
nufi dashi duk akan dukiyan da yanzu gashi ya kare a banza su basu barshi da yan uwansa ba kuma basu
amfana da dukiyan nasa ba a karshe.

Yau da zasu san yana da rasa wani hali zasu kasance bayan irin abinda suka so aikawatawa a gareshi
din Allah ya kareshi.

Akance mace shu,umace sai a kan wanan matar yasan da hakan babu yadda zaiyi ya fito fili ya fadawa
maimartaba abinda aka aikata din din gudun shiga wani hali ga tsufa yasa suka rufa zancen har zuwa
lokacin da zai dawo garesu a bazata.

Shi kadaine mutumin da ya yarda dashi har ya aminta ya sanar dashi yana raye dashi da mahaifinsa
wanda suka san mazauninsa har yakai suna ziyaran juna a tsakaninsu.

Ba shakka a yanzu ma plan dinta ne ta aiwatar da hakan karshe a kansa wanda bata san shi nasa shirin
akanta yafi karfin wanda take masa ba kan yarta din.

Komai ya gama hadawa a yanzu kamar yadda suka tsara din lokaci kawai suke jira a yanzu shine su yi
masu girshi cikin bazata a garin.

Saidai kafin nan yana son ya kara dulmiyar da ita ta kara rubtawa ramin da yake haka matan tunda taki
fadin gaskiya a tsanake ta yadda kowa zai fahinci gaskiyar su nan gaba.

Can kuma kano zaune ta tasa abunci a gaba tun safe takasa cin komai har wanan lokacin hakan yasa
jakkadiya bugwa hjy Nasare waya ta taso tazo ko mahaifiyar nasu zata rage damuwa tunda tafi dama a
cikin su.

Yadda ta fada matan hakan tazo ta sameta zaune suka gaisa take fadin jakkadiya ya ba a fita da kayan
abincin nan ba tun safe ?

Uwar dakina ai rakishidade bata taba abincin ba ma tunda aka shigo dashi dakinan hjy lafiya bakici
abinci ba yau ?

Saida ta dan bata fuska cikin jan aji tace bakin ne nawa Nasare ba dadi kwanan nan hjy ko dai zancen
likitan nan ne da yace kina tunane ?

Tinane kan Nasare ai dole mairai yayisa balle a yadda nakai din nan ga mara kunyar nan magiji wai ace
har magaji ya shigo gidan saidai ya tsaya wajen maimartaba nan yaki zuwa mu gaisa yaya za,ace mairai
ba zaiyi tunane ?

Wanan aiko da akidar Nasara da iskanci yau idan abokan zamana sukaji wani ido yake son na kallesu
dashi don ?

Amma hjy sai naga ba laifinsa bane nafi ganin laifin hjyn mujahid ita data lake kan sai kin saka baki ya
auri yarta duk itace ke jawo wanan abubuwan.
Amma Nasare idan ban matsa ya auri yar uwarsa ba kina ganin sai mu zuba ido ya dauko yar kwara din
nan cikin family din mu tazo ta bata muna zuria ?

Haba hjy kada ai fatan hakan don Allah nakanso in lurar dake wani lokacin amma gudun halin hjyn
mujahid yake sa in kyaleku watarana.

Amma maganan gaskiya fisabillahi magaji ya wuce wanan a yanzu ko wa yanda basu waye irinsa ba su
Nura wacan karon yaya aka kwashe dasu hjy balleshi ?

Komai na yanzu da zamani yake tafiya iyaka in ita wanan yar ce bakwaso ya dauko tunda da ita aka
sanshi sai a bashi zabi ya kawo wata amma ba wanan din ba.

Bayan hakan nifa sai ina ganin kamar akwai wata kullaliyar harka tsakanin hjyn mujahid da magaji
yadda yake mata din nan.

A yadda nasan halin magaji hjy ba zaiyi abu haka kiri kiri ba nauyin komai a idonshi ba yadda yakeyi
mata yanzun din nan.

Saida ta dan murmusa tace babu komai banda rashin kunyar da yake ji kawai a yanzu Nasare yana
ganin kafanshi ya kama kasa a zatonshi.

Ina dai da dukiyar ubansa yake kuri ko to dukiyan uban nasa asalinsa na waye nawane lokacin da yake
can yana karatu na hada na basa yaja jari dasu wanda har hakan ya jawo fitina tsakaninshi da dan
uwarsa imamu a lokacin.

Yanzu ko zan bukaci Ahmad ya ban dukiyan a lissafa a gani riban da aka samu zuwa yanzu sai,,, amma
hjy shima ai yaya imamu din an basa a lokacin idan ban manta ba haka itama mama mujahid din.

Amma ai bata tuna na hannun ta sai wanan take damuwana akansa yanzu da in karba abawa kowa
kason sa don tana ganin Ahmad din ya sakarwa dan nasa kudinne a yanzu yasa yake iskancin nan.

Umm,humm dama nasani hjy wallahi nasani don dajin zancen nan ba zancan ki bane hjy shirintane
taga ta musgunawa yaya Ahmad din da iyalansa don abinda ya faru din nan.

Hjy ki natsu hjyn mujahid wani lokaci bata abin gaskiya wallahi tasan wanan abin yana iya kawo rikici
dakin nan amma ta kawo wanan shawaran da zai tayar da hankulan mutane a karshe.

Basu kai karshe ba sai gata ta shigo tana ganin yar uwar fuskanta ya sauya a wajen don bata son yar
uwar na zama da uwar sai gashi yau ta girshesu.

Kanwar nata ta gaida ita da kwana ta amsa fuska daure kayan abincin dake wajen rufe tafara budewa
tana fadin wanan na rana ne kona safe ?

Haba kura wanan wani irin dabi,ane kuma ai sai kijawa mutane zagi sai kace wace bata girka ba a
gidanta zakizo kina faman bude buden kwanoni haka yanzu idan wani ya shigo ya sameki kina haka fa ?

Ta juyo tana fadin hjy a dakin uwata nake fa ko kuma wani zai mun shamakine da abinki gidan nan ?
Kallon yar uwar tayi kafin ta koma ta zauna tana fadin na zata kincine ai naso na karya don ban dafa
komai ba yau nafito da zuman nazo nan na karya din.

Shiru suka danyi kafin ta kallon kanwar nata tana fadin lafiya na ganki haka gida da safe ?

Lfy kalau ta bata amsa nazo ganin hjy ne da jiki tace O,wooo ashe ko hjy yaron nan yazo da gaske gidan
nan ba sako yayi ba shine yazo dai din wajen baba ?

Aina fada maki zai aika indai magajine bar yaron kawai zan sameshi ai naci masa mutunci har iyayyen
nasa nasai ai bai tafi ba yana garin nan.

Hjy Nasare data mayar da hankalinta ga waya ta dago tana fadin magaji kan baya kasan nan ya koma
tun ranan kwana daya yayi ya tafi .

Nan ta fara fada tana bakaken maganganu har da cewa ai karya ta kusa karewa muga ta zaman turai
din a yanzu tunda abin ya zama rashin mutunci.

Haba dai hjyn mujahid ki sasauta don Allah yaron nan jininkine fa balle banga abinda yayi maki ba hjy
Nasare ta fada tako dago ta shiga rigan arzikinta itama .

Tsam ta mike tana fadin hjy zan koma don Allah ki dinga cin abinci kada wani ciwo kuma yazo ya shige
ki a koma kuma damuwa.

Tayi masu sallama ta fice abinta sai bayan fitan nata ta dubi uwar nasu tace Nasare ta canza a yanzun
hjy na gane bata bayan mu kwata kwata bata son zancen abinda zai soki magaji.

Ba canzawa tayi ba kema kinsan halintane haka fadan gaskiya ko za a kasheta kuwa kamar hjy Yanti ta
haifota sak ita wanan yar taku dake gana ai ta kwasa.

Wai ummi yar wajen umma yo aini hjy tunda naga yarinyar na daukan kanta wata tsiya na watsar da ita
sai tazo garin nan amma bata san kofana ba.

Wai kinyiwa yaya imamu magana azo a zauna din hjy gara kowa yasan abinda yake ciki kudin nan in
sunanan a raba abawa kowa nasa idan kuma sun shige ya sayar da kaddararonsa a biya dashi tunda
dama dasu ya saya.

Ke naga kamar ba abinda ya dameki sai zancen kudi ko anbayar da kudin nan kwana nawa zasuyi a
hannunki kura ?

Ni dai zeey nace watau ko wani babban gida sai an fitar da zakka a gidan ita wanan da alama itace
zakkan wanan zauren ke nan ?




ZAINAB IDRIS MAKAWA
[9/18, 9:14 PM] Zainab Idris Makawa Writer: ELSUTRA HOME OF FASHION & BEAUTY ACCESSORIES AND
BEYOND

MAMAN BIBO KAYAN MATA

08068871330 KOKO ROAD SOKOTO




JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

5️⃣2️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Da Yamma Yazid yazo ya daukeni zuwa gida zuwa lokacin nayi waya da Abbuna da Asmau yakai sau biyar
ina tambaya yaci abinci yasha magani ta bashi abu kaza haka na wuni waya dasu agida .

Tunda na shiga daki ba fito ba don na gaji sosai rana ina so hutawa ina nan lafe kamar ina barci muryan
mama naji a bayana tana fadin Allah sarki barci kikayi ashe tun yanzu zan juyo nace a,a sai naga ta juya
zuwa falo hakan yasa na fasa magana a lokacin.
Suna falon zaune can na mike da zuman zuwa inci abinci mukan rufo kofa hakan kesa ka gane wanda
ya fito daga dakinsa don motsin kofan sai ban rufe ba da zan kwanta na barshi a bude.

Hakan yasa ko yanzu dana taso ba wanda zaiji motsin fitowana daga dakin kuma murya mama dince ke
magana da Addah a hankali falon tana fadin.

Ai Addah abu daine na gidan sarauta da wani bin didigin tsiya a yanzu waya saura wanan tunda yar nan
ta samu tarbiyan da duk akeso a tare da ita.

Tun zuwa yar nan gidan nan banga wani abin asha a tare da ita ba wallahi na fadawa shi yallabai Ahmad
kuma yar nan bata da matsalan komai tun farko yanzu gashi ku kuje kuma kungani irin tarbiyansu a
gidan .

Tun lokacin da suka ban pictures dinta na fara bata lift na hango natsuwa a tare da ita ita dai mamice
dince da wani ra,ayin rikau nata in bashi ba yaran nan suna son juna su fa ki dubu duk da akace kada ya
biyota amma da yaron nan yazo kasan nan ya kasa hakkuri ya biyo yarinyar nan har gidan nan ?

A hankali na juya na koma dakin maganganun mama din sun daure main kai sosai a ranan na shiga
tambayan kaina wai dama ana nufin zuwana gidan mama duk shirine hakan ashe ba taimakon girma da
arziki bane dama ?

Haba haba ni kan dai nayi mamaki a wanan garin da ko makwanta ba ruwan wani da wani amma za ace
wai haka kawai ta gani taji tana son ta taimaka main amma gaskiya ta iya tako indai hakane kuwa.

Koma meye da Yazid zan fara naji takamaimain yadda zancen yake a wajenshi nasan koma meye show
ba zai boye min komai ba a yanzu har in ya sani.

Kafin na koma godewa Allah daya sa ba wani abin asha a kaina da zasuce sun gani ga wanan kwanton
bauna da sukai min na zama dasu su karanci characters dina a fakaice god so kind na samu ingantattacen
tarbiya da ake bukata gun ya mace dashi.

Daba haka ba wanan guy din nasan dole in fadi a jerabawashi don't inma gwajine wanan gwajin yai
main yawa gaskiya .

A lokacin kuma na fara kwankwanton da zargin dalilin kawoni nan yin IT da zanyi duk fading kano ace
sai nan akai accepting din sunana.

Duk da nasan karatun mu yana da wuyan sha,ani sosai don ba ko ina ake karban mu ba dama amma
dai gaskiya yanzu na gane da walakin zuwana wanan headquarters din yin training.

Kai ni Aeesha wanan bawan Allah me yake nufa danine haka wait wanan dai ba iya abota bane ko
kaunace haka zan iya cewa abin yayi yawa ai ?

Ko dai haka dams su yan sarauta sukene wai inma hakan suke da karamci nidai sai ince nasa yayi yawa
gaskiya ko wanan manyan na,Iran sanyin dana samu an sakawa dakunan gidan mu aiba karamin kudi aka
kashe a nan ba ?
Ina ma wanan zancen motar nan fa sai yanzu nasan babbace nake shiga ashe mai tsadace sosai kai
abubuwa dai na daukaka rayuwa haka yayi minsu arayuwata.

Wanda hakan yasa nagane ba karamin daga min darajata hakan yayi ba a idon mutane yana da wuya
yanzu gaskiya wani ya kalleni yai main cin fuskan da ake min a baya na kirana da yar kwara ko tsaraban
saudiya.

Yanzu kan idan naji hakan sai daga bakin masu ido da kwali irin ahalin shi Man din da wa yanda kafansu
kuma ya data kasa haka dai.

Hafsat ce ta shigo dakin take fadin wai ina da ci gaban film din data fara kallo a kano cikin laptop dina
na nan hakan yasa na dago na dan kallota ina fadin gaskiya wanan ba wasu film a cikinsa ko wancan
Aimanace lokacin ta loda fina finan a ciki take kallo.

Saidai idan zamu daukone ta kalla sunan film din ta fada muna hiran Aimana ina neman film din har
nayi loading dinsa a wanan system din na mika mata ta fara kallo tun a dakin namu.

Lokacin mama din ta leko mu tana fadin yau yata bakya con abincine haka zaki kwanta ko had yanzu
kewan gidane a ranki ?

Addah ta fada min bakiso ki dawo ba saboda Abbukin da kafa ke damunsa amma ai akwai mutane a
gidan mana Aisha kuma yadda tayi bayani ana bashi kulawa sosai yadda ya dace ai.

Saidai Abu dayane naso inga maganin da mai kula dashi din yake bashi don rage zogin kafan nasa sam
saina shafa da ince ku dauko min sunan maganin ingani ai.

Amma bai baci ba ai mama zansa Asmau ko samira su dauko su turo min da sunayen kwalayen maganin
gaba days zuwa safe.

Hakan ma yayi kwarai don Allah sa su dauko min din nagani akwai wani magani da nake son mu nema a
nan a saya ya dinga sha yana amfani sosai wallahi.

Ku fitafa Ku ci abinci dare yayi sosai don naga a yawo din nan ya dawo gashi can yana shigowa gida
naji mai gadi yana bude masa get zai shigo.

No kan ruwan zafi nasha son cikina ya kulle bakina kuma ba dadi a lokacin tun a kano nake jin hakan a
tare dani .

Ina sha naje na kwanta duk lokacin hjy inna na falo tana abinda data saba sallah ko wani lokaci ranan
ina jin yazid na mata Sheri sai cewa tayi ai dole tana yine don sallah kurciya da batayi ba a baya take
ramawa.

Haka ko cikin dare ka falko zaka sameta zaune tana sallah a binta yasa duk yawancin abinda akeyi
gidan bata faye saka baki cikin zancen ba ita ko yaushe a cikin ibada take ko lazumi ko sallah dai.

Wanan rayuwan nata yana tuna min da rayuwan Abbu don shima kusan haka yake raba dare yana
ibandansa kamar yadda yanzu naga inna nayi din.
Abinda yasa na sako zancen cikin labarin kuwa falkawa nayi a lokacin nasamu ta dawo dakin tana tsaye
tana sallah duk daga tsufa amma wani lokacin a tsayen take sallah ta har yanzu sabanin wasu da karfinsu
zaki samu suna sallah yanzu a zaune.

Saida ta sallame ta juyo tana fadin yar nan kwanan kin rage tashi kiyi sallah dare daure ki tashi ki mika
kukanki ga ubangijinki sarki buwayi gagara misali kikai masa zabi akan lamuranki.

Don na fahinci akwai cakwakiya a cikin lamarinki ki kara hakkuri insha Allahu ubangiji zai kawo sauki da
yardan Allah gareki.

Zubur na sake bude ido tana tsaye tana sallah ta hankali kwance har lokacin wai ashe mafalki nakeyi da
inna din lokacin ba magana mukeyi ba a zahiri.

Ganin hakan yasa na tashi tsam na nufi ban daki na dauro alwala sallah nazo na tayar nabi bayan inna
din saidai ba zan iya jurewa irin nata ba nayi iyawata nima na raba dare na koma na kwanta barcina da
fatan Allah ya karba muna baki daya.

Washe gari kodana tashi wasai najini ba wani kuncin komai a zuciyana saida nayi wanka na shirya na
fito mama na gida sai gamma zata fita asibitin ranan.

Don haka nida yazid kadai zamu fita a yau zai saukeni nasan bata tashi ba tana hutu ko inna har
nagama shirina tana kwance a inda take sallah a dakin nan tayi barci.

Muka gaisa da Addah tayi min saina dawo na fita zuwa wake inda na samu har ya tayar da motan yana
ciki zaune yana jiran fitowana.

Sai bayan na zauna mun fara tafiya nace ina jin kamar in koma kano in zauna da Abbu wallahi tun jiya
dana dawo sai tunanensa nakeyi wallahi.

Ko mu wuce kano daga nan anjjma da yamma mu dawo ?

Kai kana da hankali kuwa na fada a dan razane yace hankalina ras kuwa ranki shi dade kinsan aike
babbace yanzu.

Babba kuma Bros ya akayi na zamo babba ya danyi murmushi kafin yace wallahi babba kike Aisha da
uba da

46 / 109