Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
Allah ya isa tsakanina dake Aginatu yau din nan zaki bar min gidana keda yarki da sauri Abbu yace taje
ina bayan wanan shekaru da kukayi a tare ga iyali an zuba ?
Iyali indon wa yan nan dakata abi abin nan sanni Abbu ya kara katse dan uwasa din idan rai ya baci
hankali yake nemosa ai .
Katsaya a bincika idan tana da hannu cikin wanan abin sai muji dalilinta nayin hakan ke Nana tashi kijeki
ina kun gama da ita duk wani yaro a nan ya bamu waje saikai habibu da yarinyar nan saratu muke son ku
tsaya.
Su yaya salis basu so haka ba a lokacin sunso ayi komai a gabansu sai gashi Abbu ya nuna masu halinsa
ya kauda idon mu akan abinda zai faru a lokacin.
Karshe dai yadda mukaji ba hannun hjy su saratu a cikin satan sarkan saratune da kawar maman nata
da wata hjy kudidi akai wana deal din suka ba saratu a karshe ta sayar masu amma sunce hjyn tasan
suna hakan a wajen buki .
Hannun da muka gani hannun hjy kudidine bana hjy Aginatu ba wanan ya wanke ta amma yarta kam
tana ciki tsundum a harkan .
Allah ya saukewa mutane girman kanta da rashin kunya da cin mutuncin ko waye da hurawa mutane
hancinta a cikin unguwa.
Don duk yadda ake son a rufe zancen ba zai rufo ba tunda gaban mutanen da sukafi biyu uku harma
ankai goma sha akai case din .
Ranan idan nace nayi barcin kirki a idanuna karyane don sai auna zancen salman dana Asmau nakeyi a
zuciyana ingane gaskiya da mafita ko wani daga cikinsu.
Saboda kaina da salman ya barmi akulle kan zantukanshi gareni ido rufe da Asmaun ta kira da kurman
kishine kawai yakeyi a kaina.
Na aje a raina zan nuna masa ni yar halak ce zan nuna mai mata suna suka tara ba yadda yake nufin
kwadayi ko son kai ya kaini ga cutuwa ba.
Da banyi niyar shiga school ba amma daga baya naji ina son shiga kawai don haka na shirya nashiga
late minits don na samu mun fara lectures a lokacin.
Ba laifi an dan dawo fiye da jiyan da muka fara attending inda malamin bai fita ba saida ya tsuremu
mukai test test ukku mukayi a ranan hakan ya hanamu fitowa da wuri.
Ga yunwa da nake ji ban samu cin abincin kirki ba tun a jiya saboda bacin rai kindarmo na sayo mai
kyau na zuka naji cikina ya dan tasa.
Hakan ya ban daman dauko waya ina dubawa inda na samu miscalled ratata a wayan daga matar yaya
habin sai wasu layuka da sukai ta kirana da ba suna.
Na fara kiran matan yaya din aka ce min not reachable at the moment ashe suna hanya lokacin sai
kuma wa yan nan sauran lamban dana kurawa ido na gano na sojan nan a ciki shima yayi min kira biyu
lokacin ban daga ba ina class.
Lumshe idona nayi ina mai sauke ajiyan zuciya lokaci guda kafin na bude idon nawa kuma ina kokarin
mikewa inda nayi sallah azahar naso na tsaya nayi la,asar don lokaci ya kusa.
Amma hankalina yana aji don haka na mike na nade abin sallah na koma class na samu classrep din mu
yana nemana ina shigowa yake fadin yauwa zo ki muna solving din wanan don Allah muna ganin zai fito
muna a exam.
Kallon aikin nayi tun muna one hundrent level aikai muna shi kuma man bash ya koya min shi sosai ta
waya a lokacin.
A take nayi masu solving din yadda wayan ke tafiya zuwa wani na,ura ta daban yayin daukan
information na gagawa.
Tafi suka fara min suna fadin lalai wanan da namijine da anyi zakakon dan na,ura saimu hada dake tun
a yanzu mu dinga zakulo manyan kasan nan .
Aka fada maku ita mace bata da daraja ko kimar irin hakan ne bandai yi niya ba banyi kuma na fada na
mike nabar wajen kujerana na koma na zauna ina nazari aiyukan da Man Bash ya koya min a lokacinsa
damu.
Don ba karamin karuwa nayi da sanin saba da yanzu nake ji a zuciya daga shi har salman duk na tsanesu
a lokaci guda don ban fahinci amfanin da salman yake nufi yayi dani ba har zuwa yanzu din.
Ban kara marmarin ko a hanya in hadu da wanan salman din ba ko tunawa da wani abu daya
dangancesu karatuna na mayar da hankali akai.
Saboda hakan kuma banje gidan yar uwarsu da nayi niyar zuwa ba illa iyaka a bakin anty safiya nake jin
sun koma ghana ai ita da mijinta da yaransu.
Khairat kuma duk da muna school daya ban damu nasan komai daga gareta ba a yanzu don haka nima
ban nemeta ba koda sunan gaisawa yadda itama bata nemeni din ba.
Yar tallakawa nake amma ina da zuciya da kuma gudun wullakanci kan abin mutum yau da man bash
ne yayi min wanan gorin haka tsike nasa ba zai kwana a hannuna ba zan maida mashi da abinsa.
Shima din yanzu yaci albarkacin shawaran Asmaune data bani inda ba don hakan ba zaiga aiki da
cikawa gareni duk da ya kasance.
Yanzu yan gidan mu sun saba da dadin daulan daya zube muna muna sha,anin mu dashi a gidan mu duk
da sunan biyanane na aikin fakaice da nayi wanda ban sani ba kamar yadda shi salman ya fada.
Acan kuma masarauta a lokacin hankali yakai kololowan tashi sosai don sun samu bashi din ya nuna
baisan komai ba akan batan su hjy kura da yarta da iya din.
Murmushi kawai maimartaba yayi ya kyalesa ga abu a zahiri yana son sai sun gama sanin waye bashir
zaisa ya sakosu .
Kwana uku a tsare ba wanda ya waiwayesu hakan yasa mai babban daki kara shiga cikin damuwa ta
saka tako ina a nemo mata wa yan nan iyalan nata amma shiru .
Gashi kowa na fadin shi baiga fitansu a gida ba balle wanda ya daukesu din wanan wani abin kunyane
ke shirin faruwa a gareta.
Daren da zasu cika kwana ta ukkune kakansa ya kirashi yana fadin wasan ya isa haka magaji kasako iya
iyalamsa suna cikin wani hali a yanzu.
Kafin safiya sai labari aka samu na dawowan shi gida saidai yayi kyau ya kara murjewa gashi in an
tabayesa waya daukeshi amsa dayane shima bai sani ba.
Amma ya gana da maimartaba sunyi magana dashi na siri wanda baiyi da wani ba ko a cikon iyalansa.
Dawowan iya ya tayar da hankalin dattijuwa hjy hauwa mai babban daki uwargidan sarki inda a yanzu
ta debe rai ga zargin jikanta da wasu da takeyi.
Wasa wasa satin su biyu a wanan gidan aka sakosu a cikin dare suka dawo gida babu ta yadda zasu
zargi cewa bashir ne yayi masu wanan aikin .
Don mutanen basu danganta kansu dashi ba illa iyaka sun masu barazana da tambayan ta dukiyan
mijinta inda takai ne ?
Da wanan kan kowa ya daure ana mamaren ko suwaye suka kamasu din sai akafi dangantasu da
wasune dai da ba,asan ko suwaye ba kuma ?
Sai shige da fice akeyi gidan hjy kura abinda ya dameta ya dameta a lokacin kan ko waye ogan masu
aikin nan yasan sirinta ciki da wajenta irin tambayoyin da sukai mata din masu tsauri.
Gashi kuma sunce zasu fallasata duniya tajita asan aikin data aikata ga tsohon mijin nata marigayi da
tayi sanadin barinshi duniya.
Ga yan uwan marigayin dama suna zarginta kan hakan gashi wani da yasan komai yana shirin mata
kutse a cikin lamarinta.
Abinda ya daure mata kai shine yadda akayi wani mahaluki yasan zancen su na karshe da mijin nata
dake zargin tana son halakashi din.
Ga Hindu da bata san komai ba tun acan ta fara tambayanta da mama dama kinsan Abban mu zai mutu
ashe ?
Mama kece kika kashe mahaifin mu dama don kawai ki mallaki abin hannunsa don kawai Abba zai kara
aure me kike nema kika rasa mama a gun Abba da kika yanke masa wanan huluncin haka ?
Saida kyat ta samu dabara ya fado mata na cewa hindu ki natsu mana ki dawo cikin hankalinki don
Allah wanan zance da sukeyi ni bansan dashi ba ?
Mama idan baki sani ba yaya zasu fito da zancen su bayan kafin daddy ya tafi kuna kan wanan fitinan
dashi dama ?
Tsawa ta dakawa hindu din tace ki barni inji da zancen dake damun zuciyana hindu ba wanan shirmen
naki ba don Allah.
Cikin dare bayan kowa ya watse daga wajensune ta ciga tantama a zuciyarta anya kuwa batayi
kuskuren saurin yarda da zancenTajjudeni ba na ya gama da Usman a lokacin.
In bashi ba shiba ba wani mahalukin da yasan da zancen nan sai iyan zangina da suka hada plan din
tare dashi kuma ta sallameshi tun wanan lokacin.
Ta ina wanan zancen ya fito mata haka bayan kusan shekara goma sha yanzu ke nan har tayi dumu
dumu da dukiyan usman ta sayar dana sayarwa tayi facaka da kudinta ita da yaranta.
Yanzu ga kuma wani zance daga baya yana son tasowa a kan hakan dolene ma tagano ta ina wanan
lamarin ke shirin faruwane ta tosheshi ga ga sagir yadda ya mayar da kanshi yanzu balle ta nemi
shawaran dan nata.
Munyi exam lafiya mun kuma gama lafiya an bani zabi waje biyu kaduna ko Abuja dole a can zanyi IT
din nawa gashi duka garuwan banda kowa a can da zance zan zauna a gidansa.
In bashi ba kaduna dai yafi min kusa da gida gaskiya ko weekend ne zan dinga zuwa gida inayin abina
inyi kwanakina in dawo bisa ga abuja to amma matsalan gidan wa zan zauna acan din yanzu ?
Da wanan tunanen na dawo gida ranan saida nayi sallah na huta a dakina nafito na mikawa Ammah
kindarmo data ban sako in sayo mata.
Wuri na samu na zauna ina fadin yau ina anty safiya Ammah kece min ta kwashi yarta sunkai kaya
wani gida da aka kirata.
Shiru nayi kafin can ince amma bai dace ace tana fita wanan harkan dasu ba gaskiya idan can su basu
dauki hakan komai ba nan zasu fassara hakan da wani abu.
Ai kinsan halin yar naki Aeesha nayi mata nuni da hakan tace suba komai bane a can to wakace kuma
yanzu yadda take ganin tauraron nan nata ya haska a yanzu .
Asmau ma so nake ta karasa karatun ta ita kuma samira tunda ta gama in gaba zata taje gaban idan
kuma tana da tsayayyen ta fito dashi tayi aure.
Murmushi Ammah tayi min kafin tace ai diyankune amma kinsan auren su yanzu wani fitinane kuma
tunda daga uban har danginshi kaf sunyi watsi dasu a yanzu ko labarinsa ma bance sun sani ba a yanzu
gaskiya.
To Ammah su zauna hakane tunda sun isa aure dukkansu a yanzu ko mu in badon karatu ba aida yanzu
an fara saka muna ido .
Ke kin fi yar naki tunane don ita neman kudi kawai tasa gaba dasu bata tunanen hakan garesu bata ko
san ba haka za a tabbata ana kallonsu ba dole dai ko anki ko anso akai ga hakan watarana.
Zanyi magana dasu idan sun dawo tace ai ita samira din dazun nan ta fita zuwa gidan Akwai farida ta
aiko nemanta nasan fita zasuyi.
Ammah farida tasan abinda ta taka a yanzu yawon nan ba zai fitar dasu ba wallahi ato ke ka fada a
zauna lafiya kila nikan idan nai magana suce min yar sa ido.
Muna wajen muna hiran duniya har suka dawo Asmauce ta fara shigowa tana ganina ta washe baki na
daure mata fuskana .
Ganin hakan yasa tace mummy nayi laifi halan kinyi mana na bata amsa tana sauke kayan nace ina
kikaje Asmau ?
Kallon Ammah tayi tace aina fadi idan kika dawo kikaji nabi mama fada zakiyi wallahi gashi kuwa
yanzu ke yadace ace kina wanan harkan ba aure gareki ba don Allah yarinya karama dake ma,u ?
Tayi shiru nace kafin na bar garin nan saina tabbatar da kin fara karatu insha Allahu tace don Allah
mummy nace insha Allahu bari Abbu ya dawo muyi shawaran inda zaki shiga daga ke har samira din.
Tafiya zakiyine mummy nace insha Allah saidai bansan inda zani ba nima kaduna ko Abuja suka
turamu gani duk garuruwan bansan kowa a cikinsa ba.
A,a wallah abuja kan baga anty Basira da mijinta ba fuska na tabe alaman kai kafin na furta kinsan halin
mutane Asmau ba kowane yake yarda da hakan ba ai ?
Kuma ni yaya habib namu baizo daya ba wallahi dashi dama ita matar nasa dai muna dan dasawa da ita
yanzu.
Ina ruwanki dashi tunda ba a kansa zaki zauna ba da matarsa zaku zauna meya shafeki dashi kiyi abinda
ya kaiki ki gama ki dawo ki barsu iyaka ke nan ko ?
Nidai da ana samun haya ko a turamu wani waje da irin muke zama zaifi min Ammah kinsan fa surutun
mutanen gidan nan namu ?
Surutu kan ai cikinsa suke suyi sugama dadin abindai har yau basu ga wani daga gidan nan yaje kofansu
roko ba yanzu dai saiki bari baban naku ya dawo kiji ai.
Daki na shiga don in gyara kafin magariba yayi Asmau tazo muna gyara tare da ita wayana yai kara na
dauka wanan sojan ne da yanzu ya zamo min chewing gun yakirani .
Yana tambayana yaya exam na amsa da alhamdullahi yake fadin yana son yazo yai min weekend nace
sai kace wata mai zaman kanta ?
Why zakice min hakan baby don kawai nace zanzo in maki weekend aiba a gidan ku nace zan sauka idan
nazo haka yake da saurin jin zafi matsala na dashi ke nan rashin fahinta da saurin fushi.
Amma yana da kula sosai ko yaushe yana kan kirani yaji halinda nake yana kuma turo min da alheri
akai akai jin nayi shiru sai kuma ya koma ban hakkuri yana fadin ranki ya baci da amsa nako ?
Umm,umm don me raina zai baci kuma naga dai daga magana ka mayar dashi bakar magana Ok keba
baka kikai min ba ko ?
Iam sorry na fada naji ya saki dan murmushi yana fadin zanzo kaduna wajen hjy in dubasu daga nan sai
in gangaro kano in ganeki .
Ai da ka fada min tun farko amma kace zakazo min weekend aisai naji zancen wani iri a raina dariya
naji yanzu ya kwashe dashi yana fadin tare da sister dina zamu zo ta matsa zatazo ta ganki.
Don zanzo da sune zan sauka a kaduna da kano naso sauka direct idan na ganki sai in wuce zuwa
wajensu yanzu kuma ta canza min lissafina a yanzu.
Kace ina da baki kenan wanan weekend din yace insha Allah saidai ba kwana zamuyi ba don sunday
zan dawo lagos na karasa mashi da insha Allah.
Mun dan jima muna hira kafin muyi sallama dashi ina aje wayan Asmau tana fadin shikan dai da gaske
yakeyi har zaizo da kanwarshi.
Asmau su dai zo din kika sani ko zata zo bincike ne a kaina ta koma kuma wani magana ya biyo baya .
Koma dai meye ai tazo ta fada nace ban ma dauka da gaskiya yake zancen ba yana da wuya din suzo
kila dai ya fadane kawai .
Yadda na fahinta kamar fa S matazun yana da mata ma,u don kinga ko two weeks ago yazo gida ya
dubasu idan baida mata yana zaman bin hanya haka ?
In mai kulane sai yazo kuwa ko don mahaidiyarsa mummy kinsan wasu sun san darajan kula da incense
sosai balle koma meye ai dole aji komai nasa dai idan komai ya kankama tsakanin ku .
Abbu ya dawo da dare saida na bari ya gama komai na fito nayi mashi bayani abinda zamuyi din shiru
yayi kafin yace ikon Allah yanzu ba ayi a kano sai can kaduna ko Abujan Nanata ?
Wallahi Abbi muma haka muka roka amma suka nuna muna a can ake da kayan aikin da zamu koya
dasu .
Babban magana ke nan kuma saukin abindai muna da yaron nan Habibu zaune a Abuja sai kuma ita fati
dake aure can yanzu amma ba zance kije can ba tunda sabbin ma,auratane su.
Gidan habibu din dai dole a can zaki zauna dasu zan kirasa in masa bayani muji ta bakinsa tukun na.
Na amsa da to Abbu badon naso ba amma dole a nan din zan zauna dasu saidai kuma idan ya kirasu din
amsan da suka bayar akan zuwan nawa zama dasu din.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[8/31, 9:06 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [8/15, 07:30] Seenabu Makawa: M/C COLLECTION
MAKAWA COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES,
BAG, COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER
KIDS,FASHIONS etc
LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
3️⃣7️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1ftp
Tashina ke nan daga barci na gyara daki na fito in zubar da shara na samu yaran anty zaune kananun
suna kallo suna marming din wakan harda rawa uwar na zaune gefe tana kulla taliyanta a leda.
Tsawa na daka masu tare da fadin ke jamila yaya akayi baku je islamiya ba yau sai ta kalli uwar naji
uwar tace dasu ai saida na fada maku tun dazun ku tashi kuje makaranta yau mummy Aeesha na gida
kukaki.
Indai baku zuwa islamiya saboda kallo zansa Abbu ya cire kayan kallon nan gaba daya me zaku gane a
cikin kallon gara dasu wayan nan da kuke gani sun karbi kudinsu ko.
Suna shagalar da mutane ku baku fatan ku samu naku rabon a wajen Allah kun tsaya kuna biyewa
wanan shiriritan nasu haka ?
Kema anty wallahi da laifinki kina ganin lokaci karatu yayi baki turasu ba don Allah ku bar yin wanan
dabi,an hakana mana cutarwane ga yaran nan kikeyi wallahi.
Ina tsaye saida naga fitansu gidan uwar harda