Chapter 91 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   91 / 109

270K to 273K   out of 326.5K words

saba ita da wace suka shigo dakin .
Idonta data zuba min da farko tadan lumshe kafi ta iya buda baki tana tambayana da mun wuni lafiya ?

Kafin ma nabata amsa naga tayi wani juya da karfi ta fice daga dakin wai ashe har dan murmushina
data ganin irin ta mahaifinane sak nakeyi.

Ban dai fahince taba son a zato kishi sai matan Nageria suka san kishi har suke bin bokaye da malamai
akan mazajesu.

Ashe abin ba haka yake ba don ko wani kabila da nasa kalan kishin daya iya na hausawan ma yana da
sauki bisa ga kishin matan wani kasan.

Oho dai na fada a raina ba yadda zatayi dani Allah ya riga daya hada yanzun kuma sai hakkuri da juna a
tsakanin mu.

Sai dare mahaifina ya leko dakin da nake da kansa muka gaisa a nan yake fada min sun tafi jidda wani
aiki tun safe sai yamman nan suka dawo.

Na kara masa ya hanya Alhamdullahi ya fada yana lumshe udanuwan shi kafin naji yayi ajiyan zuciya
yana fadin kin ci abinci ?

Na bashi amsa da ehh masha Allah naso mu dawo da wuri muje dawafi amma hakan bai samu ba yana
son zuwa safe na zauna da shiri zamu tafi din na,amsa masa da Allah ya kaimu.

Kamar yadda yace din mun tafi yin dawafin kuma da kafa muka taka har zuwa masallacin bamu shiga
mota ba duk da ga motoci nan birjit a haraban gidan anan na kula ko a saudiyan kamar suna da motocin
dake jigila a nan kasan.

Amma saina fahinci yafi son mu taka a kasa don bautan Allah zamu tafi.

A gaskiya a yadda na fahince su mutanene su masu riko sosai da addininsu komai da zai kawo lada
suna kokarin ganin sun yinsa .

Haka a dan tafiyan da mukeyi dashi sai adduan La,illah ha,illah wa,adahu la,shari kal lahul,mulkul
wallahul Ahamdu wahuwa Allah kulli,she inkadir yake ambata da dan karafi kusan har muka gama
dawafin mu abinda bakinsa ke ambata ke nan bamu dawo masaukin ba sai bayan sallah isha,i na ranan
acan muka hade wajen wani katon cin abinci da ake ta haba haba damu a wajen nan ma na fahinci suna
da alaka da wajen kila.

Ranan da mukai dawafin bankwana kusan gaba dayan mu gidan muka tafi akai dawafin muka dawo sai
haraman tafiya jidda don shiga jirgi .

Ance na zaune baiga gari ba gaskiyane wana zancen don kurin nasan Abujan Nageria da fadin kano
kawai nakeyi amma a wanan tafiyan saida na raina kaina.

Sauki abin ina kusa da kakana zaune mukai wanan tafiyan shi ke dan min bayanin akan wasu abubuwa
ina gamsuwa da hakan dayake min kuma.
Kai tsaye daga airport gida aka nufo da su Abbu da ake murnan isowansu lafiya Asmau data gama
murnan binsu tana ruguma sai budan ido take faman yi a wajen donta hango mummy Aeesha saidai
bata ga kowa ba har driver ya gama sauke masu kaya ya juya ya tafi .

Sai lokacin take fadin wai ita mummy gidan ummu ta sauka muna nan muna saka ido muga dawowan
ta kuma sai ta nufi can ?

Wace Aeesha ?

Aeesha kan na gurin mahaifinta ya rike abinsa anty safiya ta juyo tana fadan hakan garesu .

Mummy Aeeshafa mama da cewan Samira data wani jiyo da karfi tana kallon uwar da mamakin jin
zancen data fada game dani.

Ita mana tana can babanta zasu wuce da ita kasan su a saudiya muka barsu sai gobe zasu bar saudiya
din ta fada tana kara rugume su Nusaiba.

Daga Asmau har Samira jikinsu ne yaya sanyi murnan da sukeyi ya rage a fuskansu da kyar Asmau tace
mahaifinta daya haifeta mama ?

Shi mana can muka hadu dasu sunzo umura suma da yan uwansa Aeesha kan sai wani ikon Allah kuma
dawowanta nan gaskiya don yadda suka nuna suna son abinsu.

Don Allah safiya bar zuban nan ki bari yaran nan su kwashe muna kaya zuwa cikin gida kafin ki fara fesa
masu labari kin tsaya kuna zuba an bar muna kaya a kofar gida haka zube.

Mama ai ban hanasu ba sune suka tareni da tambayan ina Aeesha nake fada masu inda take sai
Ammah din ta wani watso masu ido da kallo mai kamar harara tana juyawa zuwa cikin gidan kai tsaye.

Tun a lokacin murnan sune ya rage sai jikinsu yai sanyi don sun fahinci ya tabbata dai da gaskene dai
ba a dawo dani kasan nan ba ke nan.

Duk wanda yazo gaidasu da dawowa zai tambaya ina Aeesha amsan dayane shine Aeesha tana wajen
mahaifinta a saudiya zasu wuce kasansu da ita.

Dan Adam mai wuyan gane hali sai gashi kuma sannu a hankali an fara juya zancen cewa sunyi
dubarace kawai sukayi na zuwa umurah sukaje can suka aurar dani .

Don nan an rasa mai nemana da sunan aure Allah sarki hjy Agenatu ke sakin wanan zancen a tsakar
gidansu ga kuma tsaraban data rike a hannunta wanda Ammah ta sayowa matan saurenta gaba dayan
su.

Keke ke Agenah halinki baida kyau wallahi ina aure sukai mata dai babu ruwanki cikin zancen nan yarsu
ce dai koma me zasuyi mata babu ruwanki da wanan .
Meyasa baku gudun yadda sheri akan dan uwanku ne wai yar nan ga photuna da tayi da mahaifinta da
yayyusa da kowa nata mungani Adamu ya nuna muna da irin karama ganinta da sukayi amma kin fito
kina yadda sheri akan zancen da baki da hurumin akansa ?

Yanzu meye a hannuki don Allah ina tsaraba matar nan ta aiko maki dashi bayan haka sau nawa kikaci
arzikin yar nan a duniyan nan saboda Allah ?

Ni Alh saboda Allah yanzu me nace kilafa na fada yayi mata wani irin kallo yana fadin ke yar taki dake
auruwa ina manemin nata yake yanzu ?

Ina horonki lokaci da dama kan wanan halin duk wani halin sheri Agenatu a bakinki ake fara jinshi gidan
nan ke baki san sheri yana komawa bawan daya aikashi bane ?

Gara ita kince ga dalilin dake hana a aureta keko naki diyan wani daliline yake hana a sosu kije ki
tambayi kanki hakan Agenatu.

Dan kame kame ta fara saiga umma ta fito tana fadin Allah dai yasa kana gida Alh kajima kunnuwanka.

Matan nan alherinta bai taba wucemu ba gidan nan haka kuma sha,ani ya tashi tana tsaye har akareshi
da ita ko wanan bai ishi bawa hankali ba don Allah.

Agenatuce baki san halinta ba wajen sheri kuma ai ita bata dauki hakan komai ba gashi nan kuma yana
bibiyanta din bata sani.

Ai dai kuyi hakkuri kada kowa ya dora min baki ta fada tana kallon ummu data saka baki ta juya zuwa
dakinta.

DUBAI DUBAI

Tafiyan dare mukayi haka kuma mun shigo dubai din ana faman kiran sallah asallatu asubahi.

Idan kaji ana fadan dubai ko saudiya saidai kaje din zaka kiyasta abin son akwai tsaurararan matakai
sosai amma haka mutanen mu bakake ke kutse sai sun shiga kota karfin tsiya har kuma su shiga din.

An gama duk wani bincike da za,ayi muna fita airport duk da asubane amma mun samu masu zuwa
taron ahalin a waje suna jiran mu.

Duk a gajiye nake gajiya bata wahala ba saidai kasalan daya sauko min don gajiya da zama airport din
jidda da muka dan bata lokaci a wajen.

Har wani zazzabi na dinga ji tun a airport din nasan munshigo wata nahiyar ta daban don bambamcin
al,ada dana fara gani a wajen.

Larabawane kam amma kuma a gauraye ake kusan ko wani kabila zaki gani a airport din nan na dubai
wanda zai sanar dakai kashigo mahada na duniya.
Matar nan da take kawo min abinci itace take ban kulawan uwa daya dace in samu kusa dani
matsiyana na bakuwa da bata da kowa a cikinsu.

Motocine na alfarma sukazo daukan mu saidai tun a airport din kowa ya kama gabansa inda nikan kai
tsaye tare da kakana muka nufi gidansa su kuma Abbi suka nufi nasu gidajen da iyalan su.

Tafiyane mai dan tazara daga airport zuwa gidan nasu wanda kafin mukai gari ya gama washewa zakice
ba safiya bace saboda yawan cinkoson abin hawa dake shawagi ako ina.

Habullahu wani,imal yakeem na ambata don ganin get din wani dirkeken gidan da mukashiga kai tsaye
mai kama da gidan shugaban wani kasan .

Ido na lumshe a hankali ina kara ambatan sunnan Allah tare da tasbihi a garesa don abin mamakin da
idona ke ganan min .

Biye kawai nake dasu har muka kai idon motar mu zai dakata a gaban wani gida mai wani kofa kamar
na sarauta kan motar naga an danna har zuwa cikin wajen kafin motar ta tsaya a waje daya.

Marhabin naji kakan nawa ya fada yana kallona yana fadin maraba da zuwa daulan Omawa yake
Ayshaa ?

Jin hakan yasa na dan kalloshi yana min murmushi aka bude kofan daga waje duk bangaren biyu masha
Allah na furta a fili saboda sanyin wajen daya dan dokeni.

Mun shiga ciki tsaya fada bata lokaci don idona ya gano min abinda bansan akwai ko anayi ba a wanan
gidan.

Sai gidan miji ummu Abba da ake santinsa a can gida ya koma min gidan gidan kauye dana wanan
gidan na kakana.

Zallah rayuwar duniyace mai shagalar da bawa kawai aka tsara a gidan saidai ina mamaki yadda hakan
bai shagal dasu daga ibadansu ba.

Gaskiya musulunci yayi a rayuwa yan uwa muce Allahu akbar ubangiji Allah ya kara muna imani a
rayuwa Allahuma Amin .

Nidai banga fadin gidan ba cancan don muna fita muna shiga lifter sai gamu gaban tsararun dakunan
kwana ba wani falo saidai kayan alatu.

Matan nan halimat itace dai take min jagora zuwa dakin da akai min masauki a gidan inda ban tsaya ba
na nemi bandaki na fada don yin alwala.

Saidai naso kauyanci amma kuma nagane daga baya wanka nayi na dauro alwala na fito na samu
ankawo min jakkan kayana a dakin .

Donshi na bude nafito da zanin atamfana da wankkaken hijab dina na tayar da sallah na gagauta nayi
don lokaci ya shige sosai na sallah safen .
Ina idarwa sai lokacin nake karewa dakin kallo dakin babbane sosai mai girma da fadi haka akwai closet
maiganga to gangan dakin babba sai mirrow da aka cika da kayan kwaliyan mata.

Sai cway mai wani irin kyau dashi haka can a gefe dayan dakin da wani dogon sofa mai kyau dashi haka
kwara daya a dakin.

Windows din dakin yakai girman get din wani gida a ganina nidai ban karasa kallo ba na lumshe idona
dake min nauyin barci na mike tsaye ina ninke sallayan dana samu an shimfida min kafin nafito bayi .

Kwanciya nayi haka yadda naken sai barci mai nauyi daya daukeni ba tare danayi sana,ata ba watau
tunane.

Barci na samu sosai har da mafalkaiyana a lokacin saida karan wayana dake gefena ya tayar dani na
falka ina mika hannu in dauko wayan da kyar .

Mahaifinane don tun a makka ya saka min layin kasan dubai din gaidashi na soma yi ya amsa min tare
da tambayan ya muka isa gida na amsa da lafiya kalau.

Yake fadin kakana ya damu ance tun dazun nake barci ana ta shigowa dubani ana samu ina barci shine
yake zaton ko banjin dadin jikinane wai ?

Nace lafiyata kalau Abbi saidai gajiya dake dan damuna yace na tashi naci abinci sai na kwanta godiya
nayi mashi kafin munyi sallama ina sauke ajiyan zuciya.

Iyayyenane suka fado min a rai lokaci guda tare da yan gidan mu irin yadda muke rayuwan mu da
al,adun mu acan gida Nageria nan gani tsit kamar babu kowa a gidan sai ni kadai a daki kamar wata
manya.

Rayuwama ga bawa a duk yadda Allah ya halittoka ka tsunci kanka rahamace gareka zama shiru haka
ina yaga dadi cikin mawai banda yawan surutu ke nan amma nake ganin hakan.

Rashin yawan maganata kuma a yanzu zance gado nayi gun iyayyena maza don kusan duk haka suke
basu da hayani sai dai yawan aikin daya shafi rayuwan business din su kawai shine a gaban su.

Mikewa nayi na nufi wajen jakar kayata ina dauko tufafina wani sky color din dogon riga na ciro wanda
ummu ta kawo min tsarabanshi da suka dawo na saka naje bakin mirrow ina gyara fuskata .

Mirrow din na dan kurawa ido ina tunane kafin a turo kofan dakin halimatuce wace nake cewa ummu
halimat don girmamawa .

Ta fadada murmushinta tana sako min larabci da fadin kin falka ashe yallabai yace na zo na duba ko kin
falka ki fito ki karya duk ya damu tun dazun.

Murmushi nayi ina fadin barci nayi sai yanzu na tashi naso ace wanan matar tana jin turanci da nasan
wasu abubuwa daga gareta sosai don naga tana da matukar saukin kai sosai.
Bari na fito nace da ita don ko banza ina son naga jan gidan a lokacin don da wanan na kwanta a
zuciyana dama.

Tare muka fito tana nuna min gidan a bakinta nake jin ashe kakana matanshi hudu biyu na kasan su
zaune biyu suna nan dubai tare dashi.

Amma mahaifiyar mahaifina ta rasu kusan shekara ashirin a lokacin saidai suma wa yan nan matan
suna da yara mata daya daya a tare da tsohon .

Tace duk diyanshi maza kakan mu macece ta haifa mashi su su hudu kuma mahaifinane karami a
cikinsu shine kuma da ake fadin baida da ashe yana dani ba,a sani ba.

Sai daga baya ya shedawa mahaifinsa zancena tace kowa yayi mamaki hakan da duk dadewan nan
amma ba,a san hakan ba amma ashe su yan uwansa sun sani sun dai boyewa tsohon ne sune basu
saniba.

Anyi sa,a kuma tsohon yayi murna sosai da jin hakan take fada min yan uwasa sunso kada a karbeni
amma yayi tsaye yace dole a karbeni tunda ni jininsane.

Don yace ba zai barni na wullakanta a cikin duniya ba ina jininsa tace ki godewa Allah daya kakanku mai
ilimi ne na addini da boko .

Shiyasa ya fita daban a cikin yan uwansa don halinsu sam ba daya ba su sauran har yanzu suna riko da
gargajiya da kuma mugun halinsu.

Tun a makka tayi min wanan bayanin shine yasa naso ace ta iya turanci yadda zan fahinci me take fada
min don insan yadda zan zauna da kowa a cikinsu.

Wani waje ta bude sai ga katon dinning table nagani take fada min kakana yace ta tabbatar da naci
abinci sosai kafin na bar kasan nan.

Jin hakan yasani dan murmushi ina zama saman daya daga kujerun dining din mai kama da kujeran
sarakuna.

Ba laifi naci iya cina kafin na daga saidai ba daki na koma ba na shiga zagaya gidan a tare da ita tana min
bayani lokacin sallah ya dakatar damu muka koma ciki.

Ban shiga bandakin kai tsaye ba rudin shedan saina dan zauna a bakin gado wayata dana bari saman
gadon na jawo ina dubawa.

Man ne ya fado min a rai yau badon shi daya haska min rayuwa ba a cikin hikima ta yaya zan iya da wa
yan nan mutane haka a rayuwata.

Sunanshi na lalubo a wayan ina gwada kiransa ko zai shiga sai ga kiran naji ya shiga waya tana ringin
abin ya ban mamaki sosai don a saudiya na gwada kiransa amma wayan nasa bai shiga ba .
Can naji muryansa ya dauka yana fadin hello cikin muryan nan nasa dakan rikita min lissafi sai na tsunci
kaina da kasa mashi magana nayi shiru ina saurarenshi sai faman hello hello yake yi kafin naji yace.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[11/20, 9:56 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:




JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

9️⃣3️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6
Mutanen Dubai ne naji ya fada hakan yasa nayi murmushi mai sauti da har yake iya jina a lokacin ta
bangareshi.

Kafin naji yace an tuno damu ke nan yau aka kiramu na zata kin shiga yan uwanki kinga dangi ki manta
damu ai ?

Tayaya kake zaton zan iya mantawa da mutanen da sukai min tsaye da rayuwata har muradina ya cika
a yau gani a gidan mahaifina hankali kwance ?

Idan na manta daku a rayuwata na zamo daga cikin butullan mutane ke na kuma dama dai banda layin
kasam nan ne kawai kajini shiru.

Kin kyauta da kikayi wanan tunanen gaskiya ya dubai da yan uwa da iyayyen ki na dan murmushi na
sakeyi ina fadin kowa lafiya kalau wallahi.

Allah yasa dai baki fara haduwa da mutanen ku yan kunan bakin wake ba kinsan yan yanki ku sune
masu ra,ayin rakau din nan.

Masu fadawa wata akida suna zama yan kunan bakin wanke su kashe kansu da kansu sai abin ya ban
dariya kawai don haka na murmusa.

Yake fadin ko cikin larabawa ku din na daban ne kuna can wani yanki na duwatsunane a zaune nasan
zasu kaiki wajen ai kafin ki dawo.

Suna da iyaka da kabilan indiyawa shiya zakiga wasu al,adunsu idan suna abu harma da shigen
tufafinsu irin na indiyawane haka.

Hirace mukayi mai kama da tambaya da sharawa kuma a lokacin kafin mu kashe wayan ina tunanen irin
rayuwan man bash din.

Zuwa yanzu yaci ace na fahinceshi don sam ba zancen soyayya ko wani abu a tsakanin mu saidai nuna
yan uwan taka da yake min .

Haka na fassarashi a zuciyana lokacin ko wasan sa akaina kamar zolayace da nuna hanya ga mutum
amma ba wani zance na soyayya da zakiji ya fito a bankinsa.

Dolene na yaki zuciyana kan bawan Allah nan duk da dama tunda na fara fahintar hakan na yaki
zuciyana akansa a yanzun ma banjin wani felling akansa dake nuna soyayya face da yan uwantaka kadai
a tsakanin mu.



Ranan dana cika kwana ukku a garin Dubai ina daki kwance ina charting da yanzu shine ke dan rage min
kewan gida da nakeyi.

91 / 109