Chapter 97 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   97 / 109

288K to 291K   out of 326.5K words

dogon larabcinsa.

Godiya nayi masu sukai muna sallama zasu tafi zamuji daga jakadansu daga baya nan da wani dan
lokaci ya fada.

Saidana karbi takardan yarjejeniyar ne naga sunansa a rubuce cin wani irin rubuta da zaki rantse
computer ya rubashi an rubuta Nasurdeen bin Sulaiman .

Sunan na maimaita sau adadi ina son nagano shi din waye muryan Faisal naji a baya yana fadin shi din
ya kasance cikin diyan sarkin garin nan kusan shine yafi kowa gogewa a cikinsu.

Kingansa nan ba karamin nasara muka samu ba yau din nan Abbafnan yayi iya kokari suyi hurda damu
a baya sunki hakan.

Kasancewa shima sun san basarakene kamar su duk da kuma akwai fahinta sosai a tsakanin lardin biyu
amma babu cinikaiya haka a tsakanin mu.

Yau Abbfanan zaisa mamakin kasancewar hakan ta daliliki duk da nasan sunzo gwada mune suga irin
abindake wakana a nan din.

Baki na tabe tare da dan ware hannuna ina fadan ba matsala ai duniya da yawa take muka rufe wanan
babin nasu.

Duk abinda nakeyi hankalina yana kan aikin Abbina don naga damuwa karara a fuskanshi lokacin da
muke zancen sai bayan na idar da sallah azahar ne ina zaune na kunna datana don inga sako nan na
samu sakon man dayayo min cewa na duba email dina ya turo min da bayanam komai da nake so.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[11/30, 9:55 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,

9️⃣8️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6




A hankali ya juyo yana dan kallonsu kafin yaja iska yana fadin mena fada maku ranan da kuke mamakin
ya dorata akan harkan bussiness dinsa ?

Kwarai kuwa ni mamakin abin ne ya daure min baki a yanzu na kasa magana a shekarun yarinyar nan
tayi kankanta bude ido irin haka .

Sai zuciyana yake bani kamar mutumin nan yakai yarinyar nan tun farko don ta koyo wani abune
anyama a Nageria tayi wayau haka komai nata a cikin wayewa da da,a takeyinsa.

Meka dauki yan Nageria din nan kai ya juyo yana tambayanshi cikin kuresa da idanu kafin yace
mutanene da Allah yai masu wani baiwa ta basira da iya gogewa gako wani harka fa.
Haka kuma akwai hasken musulunci da suna amfani dashi wajen gabatar da komai nasu basu yarda su
yar da addinin su a gefe saboda wani abu .

Haka others religion dinsu suke suma suna da riko ga orin addinin da suke bautawa tare da koyi da
wasu akidun musulunci na kasan.

Mutane da kusan kansu a hade yake ga komai nayi bincike a kansu sosai ka duba yadda suke shigowa
kasan nan wajen harkan kasuwancin su a kullum.

Dolene yarinyar ta kasance yar baiwace ita don iya matakin karatun da take dashi a yanzu baici ace
idonta ya bude haka da harkan bussiness ba amma sai gashi tana abu a cikin kwarewa kamar ta saba da
hakan tun farko.

Yanzu dai ya zama dole mu cika masu alkawarin yarjejeniyar mu dasu tunda mun saka hannu dasu .

Amma saidai saukin kayan da farashinsu yasa ina kwankwanto akai da anya kayansu masu ingancine
kuwa ?

Bana son aga laifinta wajen fitar da wanan kayan a masarauta nan kayan su kasance ba qualities bane
azo,,,,,

Hakan nake fata a bangarena don mu samu hanyar dakatar dasu ga komai a cikin kasan nan tunda
mun gane suna algus dayan ya fada cikin murmusawa.

Bana fatan hakan ya kasance burina ayi nasara akawo karshen gaba dake tsakanin iyayyen mu dasu
hakana don El Sultan suna bada gudumawa sosai a cigaban kasan nan kowan ku nan yasan da hakan .

Saida ya murmusa ya kalli dan uwan nasa yace kai kana ganin hakan zai yuyu kuwa don nasan dole a
samu matsala sultan ba zai lamunci hakan ba .

Idan har akai korafi akan kayan nan duk dana zargi wani abu a zuciyana game dakai da a yanzu kan
yarinyar nan abinda kasan kuma bamai yuyuwa bane ?

Kome kai tunane akai haka dinne kwarai hakan ne zan kuma tabbatar makan da hakan yana yuyuwa a
bamgarena shima ya fada rai bace.

Naji yanzu yaya zakayi da company el,hayyat da suke jiran tsamanin mu a ko wani lokaci ya kalli dan
uwan yana mikewa tsaye saida yayi nisa yake fadin ka fada mai prince Nasir ya kauda wanan zancen .

Yasa kai ya shige wani kofa nan ya bar yan uwan nasa suna kallon juna a tsakaninsu don sun kasa furta
komai a lokacin sanin akwai yar tsama a tsakanin wa yan nan ahalin.

Zaune nakai ina bin bayanan daki daki a inda na gano wani Saifullah ke datsan wanan account din ako
wani lokaci a cikin hikima yayi dabaransa.

Yake diban makudan kudi daga asusun mahaifina din ta yadda ba za a taba gano cewa shine ba ni kaina
nayi mamakin yadda suka zakuloshi da komai nasa har photonsa da lokacin daya dibi wanan kudin.
Yakai karo na ukku a yanzu yana datsan mahaifin nawa amma bai taba furtawa kowa wanan matsalan
ba saida yaga abin yana ci gaba a yanzu yazo min da zancen.

Inda kuma akai nasaran ganoshi ranan da wuri na dawo gida nayi mamakin samun mahaifina a gidan
tare da yan uwansa da mahaifisu da alama wani magana mai muhinmanci sukeyi a tsakanin su.

Larabawa mutanene masu matukar hadin kai gasu kuma da hatsarin zama duk yadda dan baraka ya
samu a tsakaninsu, kaina dake tare dasu a wajen baka taba fahintar hakan a tsakani hakan yasa suke da
nuna wariya da sauran al,umma.

Kai tsaye wajensu na nufa ina mai mika sallamata a garesu suka amsa min a cikin sakin fuska tare da
tambayana yaya aiki na amsa da Alhamdullahi.

Kakana yashiga jero min larabcinsu mai tsaurin fahinta yana min kirari tare da nuna min waje kusa
dashi in zauna.

Saida na zauna din yake fadin yata ns yarda ke haskece agaremu tabbas ke din kina da wata baiwa da
Allah yayi a jikin ki .

Yau a sanadin ki mutanen da mukai shekaru sama da talatin muna zaman yar tsama dasu sune sukazo
har ma,aikatan mu da sunan son abu a wajen mu.

Magana yake ba fahintar abinda yake fada nakeyi ba lokacin don haka na dan zuba mai ido kafin kuma
na mayar da kaina na sada ina kallon kasa cikin fassara zancen da yakeyi a lokacin.

A nawa fahintar yana min kirarine da nice haske data buda masu hanyar da suka rasa a tsawon wani
lokaci yau a sanadina wanan hanyar tana kokarin bude masu.

A yau ance Royal family sunzo har office dina da bukatan son hada harkallan kasuwanci damu na
kumayi duk yadda ya dace ayi duk da bansan meke nan ba sunji nayi abinda ya dace dasu din .

Ya riko hannuna yana fadin ya godewa Allah da ya hallitoni ta tsatsonsa ko wanan banjinta danayi a
yau ya bar masu tarihi a kasan nan.

Mutanen dake jin kansu a duniyan tankar wasu da suka halicce kansu da kansu basu ganin girman kowa
dake cikin garin nan kansu kadai suka sani a duniyan nan sune za ace yau sunzo neman abu a wajen
mu ?

Dole in jinjina maki a yau don a wajenki suka zo neman wanan abin da bamu dashi da suke ganin
matsayi ko kimar mamu baikai ba agaresu sai gashi yau Allah ya nuna min suna bukatan wani abu a
wajena.

Dagowa nayi da murmushi ina fadin wanan ba nice na jawo hakan ba ai Abbnaf Allah ne yayi nasa ikon
akan mu ya kawo lokaci itn hakan a gareku ta sanadin company nan namu.

Kinyi gaskiya da kika tunatar dani hakan kwarai kuwa Allah shi keyin ikonsa lokacin dayaso ba tare da
dabaran mutum ba na yarda da hakan sosai kin fadi gaskiya.
Kaka bari na danje na rage kayan jikina na dan watsa ruwa in huta na fada ina mikewa tsaye don barin
wajen saboda na gajarce zancen daya dauko din abinda baiko wakana ba shi kakan nawa yake kokarin
bashi wani fassara a yanzu.

Saida nayi wanka na fito na sauya tufafin jikina na dauki waya na kira Abbi ina gaidashi ya amsa nake
tambaya ko sun bar gidan kakan nawa yace gasu a hanya zai koma gida shi da driversa.

Amma meyasa kikewa kakan ki haka Aisha yayi korafi akan baki son zama dashi kina fada mashi
matsalanshi why Aisha kakankine fa kuma yana kaunanki.

Yanzun ma shi ya kiramu muzo kan nasaran daya hango kin fara kawo muna a industry din mu amma
kinki tsaya kiyi bayani yadda zai fahinceki.

Dan murmushi mai sauti na sake lokaci guda ina fadin ban saba dashine nafi sabawa da babana na
Nageria donshi na bude idona dashi shi kuma ya tayar dani har na girma haka.

Korafi na fara mashi akan ya kamata a dakatar da Faisal hakana tunda na fahinci komai da akeson in
sani a yanzu.

Shima murmushin naji yayi don yasan abinda nake nufi da fadin hakan da nayi sai nayi saurin kawar da
zancen da fadin Abbi waye saifullah n ?

Saifullah naji ya maimaita sunan nace eh Abbi sai yai dan shiru kamar yana tunane akai kafin ya kara
fadan Saifullah dai dana sani biyune dayan yaron Ahmad ne dan uwana sai dayan kanin matatace shi.

Kaina ya daure don ba zance ga wanda nake nufi ba a yanzu don shi nace ya bari zan kara kiransa na
kashe wayan ban kara bi ta kan zancen ba sai cikin dare dana gama abinda nakeyi na shiga nemo wani
saifullahi ne wanan maiwa Abbina kutse ?

Nasha wahala sosai ga neman bayanin sa don maishi ya iya tako sosai na kutse saboda baya barin wani
kafa da za agane .

Sai kusan karshe nagano maishi na gama bincikena na kwanta cikin gajiya don wanan karon ban kira
man ba saboda a gaskiya ko ciki daya muka fito iya kokarin da zai min ke nan a lokacin.

Balle ba kowane zai so da alheri irin haka ba kamar yadda Man din ya tsaya min a rayuwa har nakai
wanan matakin a yanzu.

Ga lissafina wasa wasa zancen wata bakwai nakeyi ba tare dasu Abbuna ba ina Dubai ina rayuwa tare
da mahaifina wanda ban taba zaton ganinsa ba a rayuwana.

Sai gashi kwatsam Allah ya hadamu har yau ina karkashin inuwarsu ina cin arzikinsu saidai matsala
guda shine wanan matar mahaifina din da saboda ita banda kusanci sosai da mahaifin nawa a yanzu.

Saidai har in yana son ganina yazo gidan mahaifinshi ko ya same a company muyi magana kan abinda
ya dameshi .
Inda a yanzu na fahinci tsakanin mahaufin nawa da matarsa wacce yar uwarsa ce ta jini babu zaman
lafiya bawai kuma saboda zuwana ba kamar dai akwai wata a kasa tsakaninsu.

Washegari na shirya a gurguje zuwa wurin aiki inda na riga nasa a raina daga ranan zamuyi ban
hannun makafi da Faisal don na kula muddin muna tare tafiyan mu ba zai tafi yadda nake so ba.

Hakan ne ya faru don tun kan yazo nayi magana da mahaifina akan nagaji da aiki dashi don leken asirin
da yakewa kakana a asirce don komai kamar kaka yana tare damune idan yana min bayani wani lokaci
kan abinda ke tafiya a bangaren aikin mu din.

Don haka nasan yana da wuya ace ya komawa zuwa din koma yazo din ba lalai bane ya kwana biyu
damu a wajen.

Tunda na iso ban gashi ba nasan Abbi ya isar da sakona garesu ke nan amma saida missalin sha biyun
rana sai gashi a office dina.

Ba wani daurin fuska a tare dashi saidai ba yadda ya saba ba yazo min nima dai din haka sai bayan
mun gaisa yake fadin meyasa baki fada min kin gaji da aiki dani ba yar uwa ?

Kinko san ma,anan wanan hadamun da akayi iyayyen mu suna da wata manufa na hadamu din dake
sunyi hakan ne don mu fahinci juna dani dake.

Faisal na kirasa da karfi ina daga mai hannu saboda fahintar abinda yake shirin fadakar dani mikewa
nayi tsaye ina fadin .

Faisal get out in my office kasan abinda kake fada kuwa ko kasan ni wacece da har zaka tunkareni da
wanan zance ?

Wacece ke banda yar uwata da mahaifan ke son hadamu aure a tsakanin mu kuma na yarda da hakan
tunda Abbafnan ya yarda ya amince.

Asalima zancen daga gurinshi ya fito don haka ko kin koreni a nan baki isa kisa su koremu a gidan mu da
zamu zauna ba nan gaba ai.

Murmushin takaici mai daci da ciwo na sake ina kaiwa zaune nake fadin Faisal na dauka kana da ilimi
da wayenwan kai ashe ba haka ba kaima wani kalane na daban.

Ka fice min daga office kafin na saka yanzu security su fitar min dakai a nan tunkan na kasa controling
din kaina yanzun nan.

Kallona yake cikin mamami yadda nake kallon idonsa ina fada mashi magana har ina barazanan zansa a
fita min dashi a matsayina na ya mace har ina da power hakan a yanzu ?

Bin bayansa nayi da kallo daya fice a cikin fushi ina gyara zama tare da dan jawo takardun dake saman
table din zuwa gabana na fara zancen zuci a fili ina fadin.
Iya maihaifina dana sani shine Abbu dake Nageria yake da ikon yanke wanan hukuncin akaina amma
bayan shi banga wanda zai iya min hakan ba .

Tsuki naja ina bude takardan a daidai lokacin wayana yai kara kasa dubawa nayi don bacin rai da nake
ciki a lokacin .

Jin kiran ya matsa na mika hannu na dauki wayan sunan Abbina nagani a rubuce a zatona ko har labari
yakai masane a lokacin don naso na shareshi kiran nasa saidai na daga da sallamata murya a dakushe
dake nuna ina cikin wani yanayi a lokacin.

Naji yana fadin yata lafiya muryanki a cikin rauni hakan ajiyan zuciya na dan sauke ina fadin lafiya Abbi
aikine dai nan na fara gaidashi da kwana.

Kafin ya gama amsawa ya jefo min tambaya akan tashi matsalan data dameshi wanda ina ganin dagani
saishine saiko man bash muka san da zancen .

Saifullah biyune nayi iya tunane wane a cikinsu jiya kike tambayana nace bin yunus waye wanan Abbi ?

Dan uwam matanace dakinsu daya kuma nima dan uwanane na jini shine autan su nine kuma na dauki
nauyin karatunsa sai dai yanzu bamu tare sosai dashi don ya fada harkallan da bani so.

Saida na dan ja rai kafin nace shine mutumin dake datsar maka kudi Abbi na shiga lissafa mai ranakun
da hakan ya faru da time din yace kwarai kuwa hakane .

Ko last week muna tare dashi yanzo garin nan mun dan jima dashi shiru da nayi ina sauraresane yasa
shi fadan kinaji na yata ?

Abbi ina jinka yace innalillahi wa,inna alaihim raji,un yanzu yaron nan yake son yi min haka menayi
masa da zai min hakan a yanzu ?

Katseshi nayi da fadin Abbi ka kwantar da hankalinka mu hadu yanzu dakai gani nan zuwa wajen ka na
fada duk da layin daya kirani ya fada min ba wanda yasan yana amfani da layin amma ban yarda da
hakan ba a zuciyana.

Nafison gani gashi a gabana muyi maganan inda zamu hadu ya turo min don haka ban tsaya ba na fita
tare da driver zuwa bakin ruwa.

A zaune na sameshi cikin damuwa nake sanar dashi komai dana sani tare da nuna mai baiyanan da
muka tara nashi .

Zabi biyu na bashi ko mu kwamaso dukka kudaden sa muma zuwa wani asusun na daban ko kuma ayi
karansa kan abinda ya aikata din ga hukuman kasan da yake.

Ai a cikin kasan nan yake zaune ba wani dogon nisa yayi damu ba saidai bamu ganinsa a yanzu sai
lokaci lokaci.

Gashi kuma bai faye zama garin nan sosai ba a yanzu yana yawan shiga kasashen turawa naji ance .
Nan dai muka zauna dashi din mun dan tatauna kafin na jefo mashi tambaya akan zancen da mukayi da
Faisal yana saurarena har nagama

Kai ya girgiza yana murmushi a fuskansa yace kyalesu na fada masu wanan ba abinda zai yuyu bane su
barki ki har lokacin da kika shirya hakan muji daga bakin ki duba da yanayin kasan da kika taso a cikinsa.

Indan anyi maki yadda akewa yaran mu na nan zakiga ba a kyauta maki ba don haka ban goyi bayan suyi
wanan shirin ba akanki

Nageria nake son zuwa Abbi nayi kewan iyayyena ina son ganin su a yanzu na fadawa kakana amma
baiso hakan ba ba zan kara masa magana ba iya abinda na fada ke nan ga Abbi din na mike tsaye ina
mashi sallama.

Abune mai wahala a yanzu su barki ki tafi Nageria kamar yadda sukai masu alkawari amma zan duba
zancen naga yadda za ayi.

Ka barshi kawai har zuwa lokacin da suka shirya zuwan nawa na bashi amsa ba tare dana nuna bacin
rai ba ko wani damuwa.

Tunda na dawo gida naga sauyi a fuskan kakana don haka ban wani tsaya wajen shi ba na juya zuwa
ciki har lokacin kuma bai ce dani komai ba har na shiga.

Ummu halimat ce ta tare da dawowa bayan ta aje min kayana data karba take tambayana meya hadani
da Faisal yau.

Cikin mamaki na kallota ina fadin Faisal kuma komai bai hadani dashi ba ai sai ta sauke ajiyan zuciya
tana kokarin fita daga dakin nake tambayanta ko anyi wani abin ne ?

Tace ba komai tasa kai ta fita zama nayib saman gadon ina debe safan kafana saida na cire na jawo
jakata dake gefe takardan visa na naciro ina dubawa a hankali kafin na sauke ajiyan zuciya ina dan kaiwa
kwance a wajen.

Na jima akwace ina ta tunanen abinda ya dace min kafin nagama yanke shawaran abinda zanyi a
karshe na mike zuwa ban daki.

Nayi mamaki yadda yan Royan family din nan suka turo da kudin su cikin sa,a kuma kaya su ya
kammalu daidai ana jigilan kwasa zuwa inda za a kai

97 / 109