Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
kada ince zan koma Nageria hannun
mahaifiyata wata rana.
Banyi sanyi a gwiwa ba wurin taimakawa rayuwan Asmau kamar yadda nayi alkawari sai gashi cikin yan
watani ta kware sosai tasan abubuwa da dama da zai taimaki rayuwanta wata rana.
Ko yaushe muna waya da iyayyena na Nageria haka kuma suna dan gaisawa da Abbi idan yazo gidan
mu suna kuma jin dadin hakan da mukeyi.
Takanas zan yi recharging din kudi mu zauna muna hira dasu gaba dayan mu idan nace ina damuwa a
yanzu karyane gaskiya damuwata dayane shine man da nake gani dole in rabu dashi da zancen sonsa da
nake dakonsa a zuciyana.
Na farko ga zancen aurensa ya fito fili a yanzu kowa ya sani dan tsaikon da aka samu dayane hjy kura ta
kafe akan hindu ba zatayi kishi da yar sarautan bauchi ba.
Saidai in zata shiga a matsayin uwargida a gidan man din su kuma daddy imamu sunce bata kai masu
can ba ganin fitinan yana son yin yawa yasa daddysa cewa a fasa auren ga baki daya baison abinda zai
kawo masu barka a tsakaninsu.
Donshi ya je gaban mahaifinsu ya dakatar da zancen auren hindu din duk da hakan kuma ba,a tsira ba a
wajen ta don ta koma fadin dama daddy baya son zancen hadin yaran shiyasa yai hakan ga yarta.
Duk a bakin ummu nake jin wasu zance idan muna hira nakan rasa dalilin ummu na zama tana ban
wanan labaran ?
Da farko na dauka saboda in fitar da rai ga Man din take min hakan sai daga baya na fahinci kuncine da
uwa kan zauna da danta su tatauna akan abinda ya shafi rayuwanta take amaye min.
Don a yanzu sun saka ummu a gaba irin na dangin mijin tun bayan da akaso a hada mijin ummu da
wata yar uwarsa bazawara aure shi kuma yaki hakan shine suka tasa a gaba suna nuna mata kiyayya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[12/8, 10:49 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Sannu a hankali cikin hikiman ubangiji haka abubuwa suke tafiya a tsanake kamar yadda nake da burin
hakan da kyakyawan nufi a zuciyana.
Allah da ikonshi angama gina muna katafaren shangon mu a cikin kano da zamu dinga kawo kayan mu
nan nau,i nau,i mu baza kulin mu.
Kamar yadda nace matasan unguwan mu da dama har ma magidanta sun samu aiki a wajen sun rage
zaman banzan gulman majalisa a yanzu saidai da dare idan an dawo a bude daban hira a wajen isa mai
shago wasu kuma sun daina zama ga baki daya don sun wuce hakan a yanzu dama rashin nayi ua jawo
hakan garesu.
Wanan yasa kiyayya da saka idon da sukewa Abbuna ya ragu a idanunsu sai yab kalilan da abin ya
zamo masu kamar jini sune suka saura tsurku a kan mi wani lokacin.
An gyarawa iyayyena gidansu har da yan uwan haihuwansu wanda hakan ya haska unguwar sosai a
yanzu.
Idan nace mun rage hurda da man karyane don har yanzu yana nan a matsayin da yake a zuciyana
shine mutum mafi kusanci dana yarda dashi sai kuma Asmau.
Da kusan komai nawa ma,u tasani saidai sirin ciki da mutum yake barwa cikinsa abinsa zance bayin
Allah nan basu sani ba a game dani.
Wani lokacin Allah kanyi hikimarsa ga bayinsa ta yadda ba zasu taba fahintar hakan ba sai abin ya
tabbata a gane don haka zance Allah ya halittonine nayi rayuwa a nan cikin mutanen daba jinsina ba don
wani hikima nasa.
Ban sheda hakan ko tunanen wanan ba sai dana samu wayan ummu tana tabbatar min da lalai
nashigo bukin man da za,ayi a sabon wata saboda irin muhinmancin da yake dashi a wajena.
Innalillahi na ambata kasan zuciyana da ummu ta sani da bata dinga min irin zancen nan ba a kunnuwa
don duk lokacin da mukayi sa zan dade a cikin kunci da bacin rai gami da tunane hakan ke saukar min a
karshe.
Na dai amsa mata da to amma banyi tsanmanin zan zo bukin man ba nidai kan nazo na zama abin nune
ko dariya irin abinda nake fada ke nan a raina idan na tuna da wayan mu da ummu.
Itako ummu a ganinta zuwan nawa zai sa shi man din farin ciki da yan uwanshi a san nasan yayi min a
baya ina tunanen nata hikiman ke nan da ta tillast min zuwa din.
Damuwa akan hakan yasa na dan shiga wani yanayi har na dan fada gashi shiko gogan ko yaushe muna
waya dashi amma bai fada min komai ba a kanshi.
Haka na barshi mu tafi a hakan saidai bukatan ummu da takan yawan jaddada min shi bai karbu a
kasan zuciyana ba.
Dole idan lokacin yazo insan uzurin da zan kawo in gitta mata akan hakan ya hanani shigowa Nageria
wanda dama nasa idan bada mahaifina ba ba zan kara shigowa nan kusa ba.
Kamar yadda ya yake son ya ban mamaki a tunane nima hakan nake son na bashi mamaki don na
yanke a zuciyana in yarda da yarima Nasirdeen wanda a yanzu ya lake min kamar maye karfe duk wani
takona yasan dashi da motsina saidai inji yana fada min.
Ban ra,ayishi sam a rayuwana don haka ban yarda ko sau daya mun hadu dashi da sunan zance ba don
in har hakan ya faru bada tacewa a kansa idan iyayyena suka samu labarin hakan.
Hakan yasa ban taba kulashi ba duk nacin sakon dayake turo min a wayata bani bashi reply saidai in
karanta in wuce wajen .
Akan hakan zuciyana take izani da in fara kulashi tunda wanda na matowa a yanzu ya samu wasu a
bayana asalima tun farko ba zancen soyayya ko wani abu makamancin hakan banda sabo kawai da
taimako a tsakanin mu.
Muryan Asmauce ya dawo dani hayacina daga dogon tunanen da nake yawan yi a kwanakin nan inda
take fadin mummy nace kanki yana son gyara har da kumshi tunda weekend ne na gyara maki shi
mana ?
Fuskana nadan bata ina fadin Asmau nifa kinsan ban faye son zaman gyaran nan ba sai duk in gaji
wallahi.
Ayshi,yasa zamuyi a nan gida nazo da komai mummy a hankali har mu gama kafin monday ku fita kinga
sai ki fita tsab mummy .
Murmushi nayi tace yauwa kokefa mummy tun satin can nake binki mu gyara kankin nan mummy kina
ki.
Gyara sosai tayi min gaskiya Asmau tana da fasa don har mamaki take ban yadda ta haddace abubuwa
cikin dan lokaci kankani.
Don ni kaina naji dadin gyaran nan da tayi min sosai wallahi siffana ya kara fitowa shar dani yarinyar
tayi kokari matuka.
Tsab na shirya a cikin wasu jajayen kaya masu kyau wando da riga saidai rigan ya sauko kasa sosai sai
dan farin hijab dana saka daga ciki nayi rolling kuma da wani jan kyale ba inda zakice kinga jikina bayan
fuska da yan wasu wajajen jikin nawa .
Cikin tafiyan nan nawa da halittatace hakan yasa nake wanan takon amma ke da zaki ganin zaki dauka
sallo nakeyi ko yanga a irin tafiyan nawa.
A waje muka hade dasu yaya Najib muka gaisa don duk da gida daya muke rayuwa ba lale bane mu
hadu da junan mu a rana.
Don yanzu sun fara gane kan garin sosai har suna dan fita yawo wani lokaci saidai basu nisa da gida
sosai don akwai yan Nageria sosai a dubai sun gane wani mutum a can suke zuwa hira.
Munyiwa juna Allah ya tsare ya kare kowa ya nufi motarshi ya shiga muka bar gida Asmau motansu
daya da Isma,il da zasu sauke a makaranta sai a ajeta wajen aikinta duk basu danisa da gidan mu din da
muke zaune .
Haka kuma kusan duk yan uwane a wajen don su suka sayi fili suka gina gidajen wa kansu ko aure
sukayi a wana gidajen suke zama a cikinsu .
Gidane na gani na fada masu kyau gaske da za,ace a Nageria ne wanan ginan sai wanda yaci kudinta ya
koshi zai mallaki daya daga cikin irin gidajen .
Nan dai na isa office ina kallon yadda abokai aikina suke kallon shigata don suna ganin na bambanta
dasu sosai a wajen shigata da nake dan surkawa dana inda na taso watau Nageria.
Sosai na shiga yin aiki na fara don ina da aiki a gabana lokacin da zan duba a ranan hakan yasa na hana
kowa shigowa wajena.
Office naji an turo saidai duk da hakan ban dago kaina ba ina duke ina bincike a cikin computer na a
lokacin saidai kamshin da hancina ya shako yasani dagowa da sauri ina sauke mashi kallo.
Suit na fari a jikinshi sun karbi kuma jikin nasa sosai son sunyi mashi kyau iya kyau saidai ya fada sosai
a yadda na sanshi nayi mai gani na karshe a turkey da muka hadu.
Dan guntun murmushi na sauke na sauke a fuskana tare da fadin Surprise visting haka yaya ya karaso
yana fadin nazone na bada hakkuri akan laifin da nayi.
Mikewa nayi tsaye a daidai lokacin aka biyoshi akan an hanasa ganina amma yaki ya kusto kai yashigo
shine sukazo kamashi .
Hannu nayi masu da su koma ina fada masu yayanane shi suka gaidashi cikin mutunci ruwa da cup na
kawo mai gabanshi na aje sai ga shi kuma sun kawo mai suka samu na bashi ko don haka ya juya dashi
din a hannu.
Yaya man yaushe kazo garin nan na jefa mai tambaya a daidai lokacin da yake kai ruwan a bakinshi
yana zuka saida ya shanye duk wanda na zubo mai a kofin.
Ya sauke numfashi ya dago yake fadin yanzun nan na sauka saidai na dan jima a waje security dinki sun
hanani shigowa ciki wai banda appointment dake a yau.
Murmushi nayi ina jefo larabci da yanzu ya kama bakina fiye da komai ina bashi hakkuri kafin nace
sorry yaya basu san yaya nake da kai bane.
Nan na sake gaidashi a cikin ladabi tare da rashin nuna wani abu a fuskana yadda ya zata zanyi mashi
idan yazo sai gashi baiga sauyin fuska a wajena ba.
Ido ya kura min yayin daya harde kafafuwanshi ya tokare hannayenshi saman habarshi ya zuba min
idanuwanshi.
Dagowa nayi na dan kalleshi yadda ya zuba min idon yasa gabana faduwa sai dai na dake na dan sake
murmushi nima na dan zuba mai ido na second na kawar da nawa idon da sauri don nakasa jure kallon
nasa kamar yadda yake min a lokacin.
Sam niba zan iya juran hakan ba gareshi a lokacin donshine na sada kaina kasa ina dan wasa da key
board din system din gabana.
Saidai kasan zuciyata ina tunanen irin kallon da yake min din mai kama da na kin min laifi yana tattare
da wasu ma,ana da ban fahinta ba ko ince na kasa gane kallon meye zan daice kamar na tuhuma.
A kusan lokaci guda muka soma magana sai nayi shiru don naji yana ambatan sunana da Aysha akan
me kike rejecting din wayana duk kwanakin nan ?
Kallo ni din nan na aika mashi dashi ga idonsa daya kureni dasu baya ko kiftasu a kaina lokacin nace ni
kuma yaya yaushe da yaushe ka kira ban daga ba ?
Look banzo nan don mu tsaya wasan boya dake ba kinsan halina ban tsayawa wani boye boye strated
forword nake maki magana.
Tabarman kunya ance da hauka ake nadeta shi wanan mutumin yazo min ke nan bari nima na fito masa
Aishana yau ya sani.
Yo ai ko nayi rejecting din wayan ka sai naga ba laifi bane tunda kowan mu a yanzu busy yake
abubuwan gaban mu sun sakomu a gaba ?
Kamar me ke nan fa ya tareni da jefo min tambaya sai kuma ya koma fadan gaskiyane abubuwa sun
maki yawa a yanzu don ke din babbace ko makaho ya lalaba ya sani.
Kai na dago na dan kallesa a raina ina fadin zurfin ciki aikin dana sani kasaita da isan izza ba zai bari ya
dauki laifinsa ba ke nan a wajena.
Saidai a fili furta masa nayi na zata aiba zamu hadu ba sai wajen bukinka sai gashi Allah ya kaddara
saduwan mu kuma a yau ?
Buki wani buki fa ke nan au buki ai na maimartabane da iyalansa idan yace inzo buki ya tashi dole inje
in amsa kiran maimartaba nima a lokacin.
Abinda ya fada yasani dan sakin murmushin gefen fuskana lokaci guda ina fadin haba dai yaya Man ko
don bani cikin yan gaiyata zakace min hakan.
Nima gaiyar ummu ce da Abba don sune suka gaiyaceni zuwa bukin yayan nasu ni kuma zanzo da
Abbina insha Allahu zaiwa Abba kara shima .
Still ido ya kureni dashi a wajen wanda hakan ya saka nakasa sukuni katse hakan nayi da tambayan wai
ya Salman yana inane sam na daina ji daga garesa ?
Saida ya dan yunkura yake fadin ba zancen salman nazo yiba kinsan inda zaki sameshi ai kiban amsan
dalilin dayasa kike rejecting din call dina nace.
Ba komai na bashi amsa a takaice ba komai fa kikace Ayshaa well ya fada tare da yunkura yana fadin ni
zan koma .
Ina yaya na fada da sauri nima mikewan nayi a daidai lokacin ina fadin a iya tunane kasan da sanin ba
wanda yafi balaraben mutum karrama bakonsa.
So kai bakon mune don haka babu inda zaka sai munje kaga Abbina kakuma ci abinci duk da har gidan
kakana naso muje tunda kashigo.
Ba yau ba banzo don ziyaraba a yau tambaya nazo yi na kuma fahinci me ke nan a yanzu don na harbo
amsata a zuciyar ki ?
Meka harbo a zuciyata yaya na tambayeshi har ya juya kamar zai tafine sai kuma ya juyo yana fadin
dani dake duk masu laifine a yanzu .
Abinda kike ji a game dani naji na dauka a yanzu komai laifinane sai dai na tako nan ne da zumar na
baki hakkuri da abin ya kasance muna hakan ni dake.
Nasan nayi kuskure babba a cikin rayuwan mu Ayshaa banso kiji zancen ba a bakina ba naso na zamo
mutum na farko da zan maki bayanin yadda abin nan ya faru.
Saidai kin riga kinji a wani wajen yanzu duk yadda zan fahintar dake ba zaki yarda ba zaki min kallon
mayaudari a gareki don ,,,,,,,,
Yau,dara kuma akan me yaya akan zakayi aure baka sanar dani da bakin kaba alhalin ni ina sanar dakai
komai nawa idan ya taso ?
Na karkada kai nace a,a kada ka manta cewa kai dan uwanane kuma babban yaya kuma kamar uba
kake a wajena don haka ba sai kayi wanan tunanen ba a kaina ba yanzu.
Saidai kuma idan nace nayi mamakin hakan ba laifi bane don a zatona nice mutum na farko da zan
fara jin wanan zance a bakin ka sai gashi sam baji makamancinsa a wajen ka ba.
Me zance dake Ayshaa me zan iya fada maki a yanzu nace dake Ayshaa zan auri wata ba,,,,,,, sai kuma
yayi shiru ya daga da sauri ya fara kokarin fita daga office din .
Cikin daga murya nace dashi ka jirani in fito da sauri na saba jakkata na take masa baya don ganin
yadda idonsa ya sauya lokaci guda sai ya tuna min wani lokaci mai tsawo dana taba ganinsa a hakan .
Ranan da hindu tasaka aikai zanen mu dashi a school irin bacin ran daya shiga a ranan shina hango a
idanunsa a lokacin.
Saurin dana fito inayine tare da dan hadawa da kiran sunansa yasa hankalin sauran ma,aikatan
dawowa garemu.
Wanda ganin hakan yasa na gyara yanayina har na samu na cin masa da kyar ya yarda ya shiga mota
don in saukeshi airport wanda ni da kaina a ranan naja motar saida mukai dan nisa shiru ba mai magana
a cikin mu.
Sai can naji ya danyi gyaran murya tare da fadin Ayshaa Iam so sorry kada ki fahinceni ta baibai don
Allah mu dauka hakan mukaddarine a garemu baki daya.
Don yarinyar nan wallahi kwata kwata har yau din nan bansanta ban kuma taba ganin taba su ke
abinsu can bada sanina ba ki fahinceni don Allah.
Babu zancen tsayawa kuma wani boye boye a yanzu tsakanin mu gaba dayan mu mun tafka kuskure a
zamantakewan mu munsan da muna son junan mu amma muka tsaya munawa juna wasa da hankali.
A yau nayi nadama da dana sani da a yanzu ba zai amfana min komai ba sai bacin rai da nadaman irin
yadda rayuwana yake da bansan yadda zan fito na fadawa mace kalman so ko wani zance daya shafi
soyayya ba.
Idan ma akwai wanda zan iya fadawa hakan Ayshaa na dauka kece ta farko amma bakina ya kasa furta
hakan gareki duk da dakon sonki dake wahalal dani a rayuwata.
Wanda nasan kin dade da fahintar hakan saidai kin jirane kiji daga gareni kamar yadda abin yake tun fil
azal namiji shike fara furta wanan kalman ga mace wanda ni nake ganin hakan kamar kasawane a
wajena.
Sai yanzu na fahinci ba kasawa bane shine kula da damuwan da mace ke son namiji ya nuna mata a
zahiri don mu maza Allah yaba wanan daman na furta .
Banyi wani magana ba sai hawayen dake tsiyayya a idona kawai don a yanzu nasan man yai min nisa
tsakani dashi kuma mutunci dai da muka saba shine ya saura a tsakanin .
Kai tsaye shagon Asmau na tsaya waya nayi mata a cikin hausa da ta fito gani gaban wajensu ina jiranta
yanzu.
Ba a dauki lokaci ba sai gata tafito tana waigen inda zata hangone ta karaso da mamakin ko meya
kawoni glass din motar na zuge da sauri tace daddyna don ita kadai zance ta san man a cikin gidan mu
baya ga Abbu ko ita baifi sau biyu ko uku data ganshi ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[12/15, 10:09 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14,