Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
masu.
Ance samun wasu faduwan wasu saidai a wajensu ba haka bane don zance tashi wasune son kayan
nasu da aka fitar akabawa mabukata kusan zakice sabbine suma amma haka akayi yan sauye sauye
saboda azumin dake gabatowa don yadda suke mutunta zuwan wanan watan mai albarka.
Godewa Allah nayi da komai ya kammalu a daidai lokacin dana so hakan donshi na shirya zuwa odan
wasu kayan akan lokaci don a yanzune kasuwan mu yake budewa ga masu kudin kasan dake ta shirin
azumi din .
Cin hukuncin Allah kuma haka abubuwan ke zuwa muna kamar yadda muka tsarawa komai cikas
dayane sai wasu kayan ba zasu iso cikin lokaci ba.
Don shine na zama busy ban da lokacin kaina balle na wani don shinema ban samun ko lokaci zama da
kakana dake daure min a yan kwanaki.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[12/2, 12:43 AM] Zainab Idris Makawa Writer: Q[9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,
9️⃣9️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6
Tunda na shigo airport din na sauke ajiyan zuciya yau tsohon nan zan barshi da mamakina don nasan ba
karamin tashin hankali zai shiga ba a rashin sanin ina na shiga ?
Already naga settle din kayana da zamu iso a tare dasu kwana biyu kafin tafiyana muryan yan aikin
wajen dake kiran passenger,s dinsu su shirya yasa na dago kai a hankali.
A cikin dadi nake a yau ko banyi tozali da Abbu ba zanyi da mamata ta Abuja da zan gani tsawon lokaci
bamuga juna dasu ba a rayuwa .
A hanyata ta shiga jirgine wayata tayi kara na ciro mahaifinane a kan layi yake tambaya ina inane kaka
ya bugo mashi waya ban dawo gida ba.
Ba zan dawo gida ba yau Abbi gani hanya zuwa Nageria zan je wajen iyayyena na gansu na fada kai
tsaye ina jin irin sautin mamakin daya sake a cikin wayar lokaci guda.
Mayar da wayar nayi cikin jakkata ina sauke ajiyan zuciya na fadi hakannewa Abbi don kada su dauka
kona batane ko wani abu ya sameni kuma yasa na fada mashi inda nake kai tsaye.
Abbuja muka sauka sai saukan yai min dadi don akwai jirgin da zan bi zuwa kano kai tsaye a lokacin
dan kudade na kashe sai gashi cikin ikon Allah jirgi ya sauka a kano .
Saidai goma na darene wa zan kira a lokacin daga gidan mu yazo airport daukana da uban kayana
ummu ce ta fado min a rai don haka na daga wauyata na kirata ina sheda mata ina airport yanzu ga dare
yayi.
Ummu dataga numberta na Nageria hankalinta ne ya tashi tana salati ta daga wayan don ta dauka
wanine ke amfani da layin nawa sai kuma taji muryana ina fadin gani airport azo a daukeni.
Hankali tashe ta juyo tana kallon Abba da tun da yaji tace Aisha kuma waye kekirana da layinta kuma
yau din nan?
Ya kafeta da ido don jin ko waye saiga muryana sunji da sauri suka fito hankali tashe suka tayar da
driver da zasu tafi airport din a cikin dare.
Koda suka iso sha daya har ya gwauta a lokacin cikin mamaki gaba dayan su suke bina da kallon
mamaki na lafiya kuwa saidai Abba yai karfin halin fadin diyata tafiya haka babu sanarwa ?
Abba mun sameku lafiya na fada ba tare da bashi amsa ba ina shigewa kai tsaye na duka na dauki
jakkata ina masu alaman mu tafi.
Ummu tsaye tayi sororo tana kare min kallo ko wani abu ya samenine na zo haka da alama kuma taga
ba wani tashin hankali a tare dani saidai hankalinta bai kwanta ba yadda ta ganni ni daya ba haka ?
Mota daya muka shiga dasu yayin da aka loda kayan dana odo a bayan hilux din da suka zo dashi muka
dauki hanya barin airport din kai tsaye.
Muryan Abba na kara ji yana fadin yata daga ina haka kin barmu da tarin mamaki a tare damu har
yanzu ganin ki haka ke kadai ba tare da kowa ba Aisha ?
Abba daga Dubai nake yau na sauka Nageria nazo inga iyayyena da yan uwa na fada ina duban hanya
ban kara jin yai magana ba kuma.
Ganin mun shiga gari da kyau yasa nace cikin yar murya Abba gida za a kaini wajen su Ammah da Abbu
na fada yadda Abba din zai iya jina a lokacin.
Wai kanki daya kuwa Aisha kinsan karfe nawa yanzu da zamuje mu daga masu hankali a cikin daren
nan idan mukai kaiki dajin mu kada ki kwana a can.
Ta karasa fadi a hasale sai yanzu ta kara nadaman kuskuren da tayi a baya tayiwa rayuwanta illa dana
yar ta ta data kiyayya da rashin kauna a tsakaninta da yarta daya da take matsayin mace a wajenta.
Da tasan haka abin zai juya mata a yanzu data tafi da yarta duk inda ta nufa da bata barta ba a hannun
yar,uwarta da take ganin babu mai rike mata yar ta sai yar,uwarta nata shine mafita gareta a lokacin.
Ashe hakan wani babban kuskure ta aikata a rayuwanta wanda a yanzu take girban abinta a zuciyanta
ita kadai tasan yadda take ji a yanzu.
Yadda yar nata take nuna kamar tana gudunta ba wani kauna ko shakuwa a tsakaninsu ba wani sabo
irin na uwa da ya dake wakana tsakanita da yarta mace guda data mallaka a duniya.
Muryan Abba taji yana fadin kiyi hakkuri muje gida Aisha da safe sai a kaiki gida wajen iyayyenki nasan
sabodasu kika dawo garin nan yanzu.
Nagode Abba Allah ya kai mu hong,kong zamu shiga gobe sai na wuto zuwa Nageria ina son ganin
Abbune don ina yawan mafalki a kansa duk kwanakin nan.
Kallon juna sukayi shida matar nasa kafin yace Abbun ki nan lafiya Aisha kwanan nan daine ya danji jiki
amma da sauki don yanzuma gida yake kuma ya soma fita ma.
Shigowan mu haraban gidan nasu da haskensa ya gama gauraye rabin unguwar nasu yasa ban samu
magana ba amma a zuciyata ina fadin nikan nasani nasan wani abu ya samu Abbuna.
Ban yarda na kara magana ba don yadda na kula ummu tana hake dani lokacin don haka naja bakina
nayi shiru dakin nan nawa nan na sauka yana gyare don zakice dama ina cikinsane lokacin.
Abinci tasa aka kawo min na danci na watsa ruwa sai barci don akwai gajiya sosai a tare dani lokacin
ban falka ba sai asuba na mike donyin sallah.
Tunda na idar ban koma barci ba ina zaune ina lazumi a wajen har gari ya waye wanan dama yana
cikin dabi,ata tun ina karama Abbu ya koya min hakan har Ammah.
Wanka na mike nayi na fito na samu ummu a dakin shigowanta ke nan dakin itama take fadin ashe kin
tashi nace eh ummu ina kwana acikin ladabi ta amsa tare da fadin bari na barki ki shirya sai in dawo.
Ba wani shiri zanyi ba ai ummu mun sameku lafiya yaya su Hamza suke tace suna lafiya ai basu san
kinzo ba da yanzu suna nan ai.
Rigana dake saman gado na jawo ina kokarin zurawa a jikina take fadin bari taje ta dawo ta juya ta fita
sai bayan kamar one hour sai gata tare da Abba da suka shigo har cikin dakin tare gaidasu nayi a ciki
ladabi Abba din ya kai zaune saman dogon kujeran dake dakin yana amsawa.
Ganin hakan yasa na dan natsu tare da saukowa saman gadon da nake zaune da farko na tsuguna Abba
din ya ambaci sunana yana fadin .
Aisha ina dai lafiya wanan tafiyan naki kwatsam haka ke kadai karshen watan nan nake zancen muje
mu diboki acan din sai gaki kuma kinzo ?
Ba komai Abba nazone naga iyayyena don hankalina ya dawo garesu yanzune tareni yayi da tambayan
amma iyayyenki sunsan zakizo nan din ?
Kaina girgiza a hankali kafin na bashi amsa da baki nace a,a daga gurin aiki na taho nan din nayiwa
kakana magana ya nuna ba zanzo Nageria ba kuma.
Najeriya ai dole kizo tunda kin hada dasu bayan haka kuma anan kikafi wayau damu don hakane kikai
bugun gaban kanki kikazo nan din kai tsaye ?
Shiru nayi na dukar da kaina kasa ba tare danace komai ba naji yacigaba da fadin baki tunanen zuwan
naki nan zai iya jefasu a wani hali su dauka wani abune ya sameki ?
Nan ma dai shirun nayi ban iya magana ba a lokacin dolene mu nemi iyayyenki a yau din nan su san
kina nan wajen mu.
Sai lokacin na dago ina fadin Abbina ya sani don ya kirani nace gani airport zanzo Nageria in gane ,,,,,
Katseni naji yayi da fadan sai lokacin yasan da tafiyan naki nace ehh Abba ba tare da jin nauyin komai
ba baki kyauta ba Aisha sam baki kyauta ba ya sake fada cikin bacin rain mai nuna sanyin hali.
Sayadi aina fada maka na fadama wanan tafiyan yin gaban kanta tayi bata sanar dasu ba tazo don
kawai ta dagawa mutane hankali.
Lokacin da kike nan kin daga hankalinki ke ubanki kike nema yanzu kuma Allah ya kaddara saduwan ku
kin gudo daga can din kuma ki dawo nan .
Da kika dawo nan uban me kika dawo muyi maki a nan ko wani irin gatane basu nuna maki ba a can
don Allah ya isa haka tunda bata boye ba ta fada muna dalilinta na zuwa.
Kadaici da damuwa da rashin ganin kowa ya sakata yin hakan tunda bata taba barinsu haka da tsayi ba
zuwa wani waje ita kadai don haka ki bari ai mata uzuri don Allah.
Allah banga amfanin riketa a nan ba kawai ta koma can tunda hankali zata rabawa mutane idan taji
dadin hakan kallon ummu nakeyi a cikin mamakin jin kalamanta a lokacin.
Wanan matar ko bata sona a kusa dasune na tambayi kaina don yadda take faman fada dani don kawai
nazo gida a lokacin.
Jinake kamar nace ba ita nazo gani ba wajen su Abbu nazo amma Allah ya gyara ban bude bakina nayi
magana ba sai nayi shiru.
Yanzu ki karya kafin a kaiki can gida din ki gansu zanci gaba da nemam layin shi Abbin ki muyi magana
dashi yaji daga bakin mu cewa kina nan tare damu don kada su damu.
Nagode Abba na sake fada ummu ta dago tace godiya kamar wata data san ciwon kanta wanan abin
kunya da kika aikata fa har ina don Allah ?
Yanzu da wani ido zaki kallesu ta sake fada naji Abban yace da ita Asiya ki bar dakin nan indai ba zaki
kwantar mata da hankali ba don Allah .
Jin hakan yasa ta watso min harara tana fita daga dakin kai na dago ina sauke a jiyan zuciya tare da
nazarin zancen kowansu a kasan zuciyata.
Sunkai kamar minti talatin da dita dakin saiga yaran ummu sun shigo cikin murna da jin dadin gani daya
bayan daya muke gaisawa dasu wanda sai kallon mamaki suke min jin harshena ya zaunu da larabci
sosai.
Mun jim dasu muna hira a dakin kafin su anty barakah su shigo da yaranta don duk basu san nazo ba
sai ummuce ke fada masu zuwana.
Naji dadin ganin su anty baraka sosai don wurinta na dan samu labarin halin da gida yake tunda ita
ummu bata tsaya taji damuwana ba.
Bayan fitan fitan Anty barakane muna nan dakin da kanne na har na kunna data massage din Abbina
nane ya shigo min yana tambaya ko na sauka lafiya ?
Na amsa da lafiya kalau saigashi ya hau online ya danyi min fada da nayi irin tafiyan nan ban sanar dasu
zanzo gida ba.
Na bashi hakkuri ya juya da tambayana yaushe zan dawo nan ne na tsaya nayi masa bayanin makasudin
zuwana Nageri tunda siri ne a tsakani mu yakuma ji dadin yadda na tsara abin yace kuma zai fahintar da
kakana a cikin hikima .
Ua fahinceni sosai don har ya gama bincikensa ba wanda zai zargeni akan matsalanshi da dan uwar
matarshi balle mu samu baraza a wajenta.
Sai wajajen karfe tara Abba da kansa shi da ummu suka kaini gida tare da rakiyan yan uwana da anty
baraka bin ko ina nake da kallo ina lumshe idanuna don yadda garin ya canza min dan tafiyan da nayi din
.
Kodon na fito kasa irin Dubaine nakewa garin namu kallon ya canza min a idanuna a idanuna oho
bayan dan tafiya sai gamu a kofan gidan mu.
Hamdallah nayi ina sauke ajiyan zuciya kafin na bude kofa na fito Allah Allah nakeyi in shiga gifa a
lokacin inga yan gidan mu da kowa dana bari.
Da sallama muka shiga ciki ina rike da hannun autan ummu daya lake min don yaron bai manta dani
ba kamar yadda yake lake min hakama a yanzu din yana lake dani duk inda nasa kafata.
Asmau ce ta fito daga falo da roba a hannunta jin sallama yasa ta dago kai mukai arba ta jefar da roban
dake hannunta cikin wani ihu tana fadin lah mummy.
Hakan yasa suka firfito da sauri daga dakunan su har Ammah duk wanda mukai arba dashi sai kiji ya
sake ihu yana fadin mummy a cikin ihu zuwa gareni cikin jin dadi muna makale juna.
Ammah data fito muna arba da ita saita sake kuka tana hamdallah ga Ubangiji daya kaddara saduwan
mu tare da fadin kai ku sheka ku kira min malam don Allah ysnzun nan ya fita gidan nan tana share
hawayen fuskanta.
A,a to shiyasa yarinyar nam take abinda taga dama yanzu don ta dawo yaya zaki zauna kina wanan
kuka saboda Allah irin wanan shagwabatan da kukeyi yasa taki zama a can din.
Abba da Abbu suka shigo gidan da sauri Abbu yana raraba ido ya hangoni ya karaso yana gyaran
babban rigansa yana fadin ikon Allah nanata kece yau a kasan namu.
Kuka na sake yana fadin subbahanallahi yaya kuma da kuka haka nana ki godewa Allah daya sake
kaddara haduwan mu cikin koshin lafiya.
Shimfida akai masu daga waje suka kebe suna magana nan hamza dake kusa ya tsoma baki ga
zancensu cikin katse mahaifinsa da fadin Abba mun gaisa da mahaifin ukuthy dazun ta video call .
Ya dubi yaron yace kwarai mun gaisa dashi dukkan mu ta fada mashi cewa zaka nemesa a waya ka
sheda mashi zuwan ta ai.
Mamakine ya kashe Abban ya saka yaron ya kirani sai bayan nazone na zauna a gefensu muka kara
gaisawa da Abbuna da sai ido ya zuba min yana min kallon mamaki.
Abban ke tambayana abinda dansa ya fada nan nake fadin ehh mun gaisa dashi sai a lokacin nayiwa
Abban bayanin komai a tsanake yadda zai fahince ni dashi da Abbu.
Na kara da fadin ban fada bane gaban ummu kada taji wani iri a game da maganan na fada masu yadda
ake son a kama wanda kewa Abba datsan kudi ba tare da angano nice na bincikoshi ba.
Ya gamsu sosai da bayanin da nayi mashi din kan dalilin zuwana wanda kuma hakan duk da plan ne
koshi Abbi din nayi masa da hakan don nasan bama zasu zargeni ba kila amma barin kasan a lokaci zai fi
min sauki .
Kayan dana loda na tsaraba aka fara shigowa dashi cikin gida kamar yadda Abba yaba drivers umurni
ayi din shigowan su maryam yasa na mike muka tari juna dasu cikin dadin rai.
Zaune suke cikin damu kan abinda na aikata din bayan mahaifina ya sanar dasu ina nageria naje ganin
su a can.
Hakan yasa ran tsohon ya baci sai da abinda na aikata din suma kansu bakin tsoron tsohon sukeji don
hakane suka zauna zugun zugu suna jiran isowar Abbina .
Sallama yayi yana mai bin tsohon dake zaune yan dasa taba a irin lohe din nan na mutanen baya a
hannunsa sai zukan taba lohe din da yake hannunsa kallo daya yayiwa dan nasa ya kawar da kansa
wajen.
Har ya karaso ya gaidashi tare da yan uwasa ba wani darrr ko damuwa a fuskansa sai waje daya samu
ya zauna yai shiru kamar yadda kowansu yayi hakan.
Sai bin hayakin da tsohon ke fesarwa da sukeyi lokaci lokaci can ya gara katakom lohe din dake
hannunsa ta hanyar dan bubugashi yana bada dan sauti kafin yaja ya fesar yana kallon dan nasa watau
Abbina yace dashi.
Umar kana takama da yarka a yanzu shiyasa ka hada baki da ita tagudu daga nan ta koma hannun wa
yancan iyayyen nata don bata son zama damu ?
Abbi ba komai yasa tagudu ba sai don auren da taji zakai mata da faisal yasa tabar kasan nan ba tare da
sanin kowa ba.
A Abbi idan don aure zata gudu ai sai abarshi tunda bata so kada ta bata muna sunan a halin mu dama
akanta akwai ayar tambaya din da mutane ke kallon mu dashi.
Saukin abin dai Aisha yatace don haka su kalleni su daina kallon ka don ba gudu tayi ba Abbi ya dago
yana kallon tsohon da kansa ya daure.
Gida ta tafi wajen iyayyenta nima saida takai airport ta sanar dani ta kuma fada min tafiyan ne ya
kamata dole tayisa ya fada with full confidence a fuskan.
Har lokacin da mamaki tsohon ke kallon dan nasa kasan abinda barinta kasan nan zai jawo muna
kuwa kasan irin hasaran dake kwararo muna ?
Dakatama in tambayeka abinda nake son ji shine yasa kuma na taraku a yanzu don ina tsoron ace
yarinyar nan ta gudu mana da dukiyane tunda ita din ba tarbiyan mu bace nan.
Innalillahi ya ambata kafin yace haba Abbi kai da kanka kasan Aisha ba zata aikata haka ba don dukiyan
mu baya gabanta.
Kwandala daga cikin dukiyar company Aisha bata taba muna ba don ita din jinina ce bata halin banza
kamar yadda wasu diyan keyi .
Yasan dalilil soma sakewa juna bakar maganan da suka soma a tsakaninsu hakan yasa ya tsawata masu
da sauri sukai shiru.
Inda ya kara da fadin zan bada wata biyu