Chapter 2 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   2 / 109

3K to 6K   out of 326.5K words

Ba a sake jin duriyansu ba sai labarai kala kala ke zuwa game dasu inda kowa ke fadan labari daban
daban akan shirunsu a can din .

Sai bayan shekaru masu yawa don har kowa ya fitar da rai ga sake ganin su saiga Nana ta dawo muna
da goyonki kwatsam da rana tsaka.

Wanan babban tashin hankalin ya dagawa mutane hankali tare kawo muna rudani da tashin hankali
sosai a lokacin yan uwa da abokan arziki hankalinsu ya tashi ainun da gani haka .

Nan tsegumi ya fara tashi haka kuma wa yanda sukai Sanadin abata nana ta tafi da ita a lokacin daga
baya duk suka jaye hannunsu suka koma gulma da nune ga iyayyensu.

An tutse nana aka tayi bayanin yadda ta samu ya amma ta kasa bayani ssboda kukan da take aiki yi
hakan yasa mahaifinsu ya kwanta ciwo jinya mai tsanani yayi a lokacin duk sanadiyan hakan daya faru.

A gidan mu kawai nanake samu kwanciyan hankali a duk fadin kauyen nan zatazo ta wuni taci tasha
sai daren kwana zata koma gida.

Haka kuma washe gari zata dawo nan tunda safe haka tayi ta faman yi a lokacin don yadda mutane har
gungu sukeyi do zuwa ganin yar balarabiyan da tazo da ita a goye wace ta zamo abun kallo a wajen mu.

Wanan dai in gajarece maki ciwon mahaifinsu ya kara tsananta sosai har yakai yayi ajalinsa ganin haka
yan uwa suka kara hattaranta akan sanadintane mahaifinsu ya mutu don bakin cikin abun kunya dataja
masa a gari.

Suka kori nana daga gidan ta dawo nan gidan mu da zama a wajen mu ta zauna inda Ammah ke faman
dawai niya da ita da yarta sannu a hankali tafara sakewa tana rage damuwa har yar uwarta Ammah ta
samu jin labarin abinda ya faru zuwansu saudiya da taki ta fadawa kowa da farko.
A yadda tace da suka je can sana,a take sosai kashe rika suna samun kudi amma kudin ba nata bane na
hjy ce.

Don har hjy ta gina gida anan kano da iri kudin da take turowa a nan gida Nageria kuma ashe ita hjy
din takan shigo nageria tayi abinda zatayi ta koma ba tare data je kauyensu ba.

Ana cikin haka da girma ya soma ita nana hankali ya fara zuwa mata ta nemi da ta koma gida amma
hjyn ta hana don takarrdun da komai nata na wajen hjyn .

Dama kuma haka sukeyi da anje can ance sai su karbe takardun tafiyan ka sai kagama masu bauta ka
gama wahala zasu fito maka dashi a lokacin kaima zaka fara neman kudi ka.

Suna hakane har Allah ya hada ita nana din da wani balaraben mutum shi wanan da kike gani a jikin
photon dai da shakuwa yai shakuwa a tsakanun su har ya nemi auren ita nana a wajen mutanen su
nacan.

Wanda ba tunanen komai hjy din da sauran shuga banin su suka taru suka aurawa nana wanan
mutumin acan suka sha bukinsu batare da kowa na ita nana ya sani ba ana gida.

Yadda ta fada muna zama sukayi na so da kauna dashi na fi sabi lilah har Allah ya kawo masu rabonki
aka samu cikinki a lokacin.

Wanan mijin nata tace yayi murna sosai da samun karuwankidon ya gwada mata gata iya gata kamar
yadda Allah ya umurta a nunawa iyali.

Har Allah ya sauketa lafiya suka radawa yarinya sunan nana Aeesha ma,ana Aishatu a nan dai wajen
mu.

Ya kula dasu yadda ya dace sosai ko bayan haihuwanki din kwatsan suna nan ta fara ganin canji a
gurinsa na wasu dabiun da bata sanshi dasu ba daga baya ya fara nuna hattara da tsana daga ita har yar
nata.

Abinda nana bata sani ba shine ashe auren contragi yayi da ita nawani dan lokaci dama sai kuma aka
samu akasin hakan rabo ya shiga tsakani a lokacin.

Shi aiki ya kawoshi saudiya yayi wanan aurene don kaucewa zina kamar yadda sukeyi acan din wanan
yasama ya zabi bakar fata yayi auren hakan da ita.

A nasa shirin idan zai koma gida kasansu saiya sallami ita nana din sai kuma rabonki tsakaninsu ya shiga
ciki wanan ne ya daga masa hankali a lokacin.

Har ya fara nunawa nana da yarta wanan halin gashi kuma kasansu sun fara matsa masa lamba ya
dawo gida hakana son har ya kara lokaci a can.

Kwatsam nana ta wayi gari bashi sai takarda da kudi masu yawa daya barmata wanan ya dagawa nana
hankali sosai a lokacin.
Mutanen su nacan ta fara nema ta sanar masu da abindake faruwa kinsan halin mutane sunga wurin
cin kudi sai suka fara karban kudi a hannun nana da sunan suna taimaka mata a lokacin a gano inda
Abduljalil ya shiga.

Dadewa dasu yasa nana din ta farga da abinda suke mata kudinsu kawai sukeci suna mata karya bayan
haka ba wani taimakon da suke mata a lokacin sai karairayi na yau daban nagobe daban.

Don haka ta daure bakin aljihunta ta tsuke wanan ya kawo sukai mata sheri ganin ga dukiyan da miji ya
bar mata ya gudu ya koma kasansu sai sukai shawaran yi mata cune ga askar dinsu nacen.

Don idan ta baro can din su koma su mallake komai nata wace tayi shekaru mai yawa a cikinsu tasan
hakan zai iya faruwa don hakane ko yaushe tana tafiya da dukiyanta a jikin ta da komai a cikin jikinta
tace.

Kwatsam kuwa rana daya sai gashi Askar din sun sallama mata akan suna tuhumarta ta hauro kasan ta
kazamin hanya tazo nan tana aikata alfasha a kasansu.

Wanan abin yayi sanadin da suka hada da ita da wasu da aka kama suka ingizo keyansu zuwa nan
Najeriya shine ta nufo gida a lokacin kwatsam muka ganta.

Kinji Nana duk abinda mutane ke fada a kanki cewa ke shegiyace baki da uba ba gaskiya bane kedin har
halak ce kamar ko wani da a duniya illa akasin da aka samu naki kaddaran yazo a haka.

Ya dago yana kallona zuwa lokacin hawaye ya gama bata min fuska don kuka nakeyi shafe shafe ya
shiga lalashina a cikin tashin hankali yana fadin.

Na dauka shekarun ki yakai na rugumar kaddara a yanzu yasa na yarda na fada maki asalinki da muke
boye maki a yau ai nana da nasan ba zaki iya jure hakan ba da banyi gangancin baki wanan labarin ba a
yanzu.

Wanan kukan da kikeyi zai iya jawo hankalin makwabata su yi zaton ko wani mugun abin nayi maki
gashi ni kadaine dagani saike a gidan nan yanzu.

Jin hakan yasa ta tsagaita kukanta don gaskiya Abbun ya fada balle tumba ta aiko kan tazo gidan nasu
kamar yadda uwarta Ammah ta fada.

Tace anan zata kwana bata zuwa can din tuno hakan yasa ta mike zuwa dakin kwanta ta kwanta shima
Abbu din bai kara cewa da ita komai ba a lokacin don zuciyarsa da ba dadi.

Saboda tuno da abubuwan da suka faru a baya game da yarinyar yasan dole sai hakan ya faru dasu don
tun suna boye mata dole wata rana zaizo da zasu fada mata gaskiya akan zancen ta.

Haka kowan su ya kwanta da bacin rai ga Aeesha ba zancen barci a ranan haka ta kwana tana tunane
akan mahaifanta dataji labarunsu a yanzu wanda abin ya tsaya mata a zuciya sosai.

Sai tambayan kanta takeyi da meyasa ya rudi mahaifiyar ta har ta yarda da hakan yasan ba auren
fissabillah yayi mata ba a lokacin.
Da irin zancen nan ta kwana a zuciyanta idan tace tayi barci a wanan ranan karya ta fada yadda taga
rana haka taga dare a wajenta dukko da dun,bin gajiyan dake jikinta ta nemeshi ta rasa a rana.

Hakan yasa washegari ta tashi da wuri jin Abbu ya fita zuwa massalaci itama ta tashi tayi sallah bayan ta
idarne ta fito ta hasa wuta don yin dumamen da zasu karya dashi.

Koda ya dawo har kunu takai ga dama masu da dan guntun gumban da Ammah ta rage har ya saura
zuwa wani lokaci Abbu ya dawo daga masallacin da tasbaha a hannunsa yana ja.

Shimfida ta shiga ta dauko masa tayi mai a wajen da yake zama tare da dauko abun karyawan ta jera
masa yadda Ammah dinta ke masa a kullun idan zai karya.

Albarka da fatan alherin daya saba jero mata ya dinga saka mata duk da yasan a ranan hankalinta ba a
kwance yake ba alama ya nuna tana cikin damuwa sosai a lokacin.

Ta juya zata shiga dakinta taji muryanshi yana fadin nana zonan yaki yana nuna mata gefenshi da
alaman tazo ta zauna zaiyi magana da ita lokacin.

Kamar itama yasan da sauran zancen da take son tambayanshi a lokacin kasan zuciyanta ta dawo ta dan
tsuguna a gefenshi don ta kasa zaman daidai yadda ta sabayi dashi a lokacin.

Kafin yakai ga furta mata wani zance yaji ta jefo masa tambaya tana fadin Abbu dama nace yanzu ina
ita wanan Nana din take da kace itace mahaifiyata ?

Ya dan murmusa a fuskanshi yana kada kai tare da kai loman tuwon da ya yanko a bakinsa yace Nana
nan insha Allahu muna sa ran hakan saida tana can kasa mai tsarki don can ta koma.

Duk da dai bada yardan mu tayi hakan ba don data kawo shawaran komawa can din daga baya bamu
yarda mata da hakan ba sai ta shamace mu ta sulale ta koma ba tare da sanin bu don ba zata iya
rayuwan nan ba don acan ta taso tayi rayuwanta da komai.

Hankali ya so ya tashi bayan batanta saida na zaunar da ita Ammah nan na bata magana don tafiyanta
ya nuna tabar muna amananki a hannun mu nida Ammah din don wayiyar gari mukayi muka nemeta
muka rasa a lokacin.

Sai ke kadai a dankin kwanan kwace da yar takardan da wasu tarkace cikin leda data bari a gefen ki na
daukeki Ammah ta bude ledan kudine a cikinsa masu yawa sai sarkan gwal guda biyu a cikin wani leda
daure.

Ganin batarta zai iya jawo magana tun kan mutane su farga da hakan yasa nayi shawara da ita Ammah
washegari nazo nan cikin kano na saya muna wanan gidan nan a wanan unguwar a cikin kudin.

Nakoma can kauye ba wanda yasanda hakan saiji sukayi kawai munce munbar gari zuwa nan cikin kano
da kowa nawa wanan yasa kikaga ko dayan mu zaije gida bamu yarda muje dake har yau din nan don
gujewa abinda zuwan naki zai haifar a kauyen mu din.
Gudu tayi ta barni ke nan a wajen ku itama na fada ina kallon fuskan Abbu din da alokacin shima ransa
a bace yake da tuno da abubuwan da suka faru a baya.

Cikin murmushin yake yace dani ba zance gudun tayi ba kuma zan iya cewa hakan don hankalinta
nacan kan nema maki inda zataji labarin mahaifinki daya tafi ya barku da kuma makomar dukiyanku data
baro a can a lokacin.

Wanan nake zargin ya mayar da ita wacan kasan a lokacin don mun taba samun labarinta wurin wani
mutumin garin mu inda har tabada sako garemu yace taji dadin ganinsa kuma shima din yace bai ganta a
mugun kama ba lokacin.

Kinga ke nan duk inda nana take tana cikin koshin lafiya haka kuma muna a ranta musanman ma ke din
nan da a yanzu tasan kin girma kin kai munzalin hakan a girma.

Ba abinda muke kullum sai adduan Allah ya karkato muna hankalinta zuwa gida ta dawo cikin yan uwa
kamar kowa wanan shine fatan mu a yanzu.

Ki godewa Allah nana da kika taso a cikin mutuncin daba duk ya zata samu hakan duk da muke ba mu
muka haifeki ba Allah ya dora muna kaunarki a zukatan mu fiye da yayan da muka haifama a ciki mu a
yanzu.

Don ke din kin kasance ammace a wurin mu idan munyi maki rikon daba daidai ba ranan gobe kiyama
Allah zai tambaye mu wanan a bainan jama,a.

Na sani Abbu banda kamar ku a fadin duniyan nan koda kuwa yau uwata da ubana zasuce zasu dawo
gareni basu kaiku girma da daukaka ba a idanuna.

Masha Allah tunda har kin san wanan to ina son ki cire duk wata damuwa dake kasan zuciyarki game
da iyayyenki a yanzu haka kuma ki daina kwankwanto koke wacece daga wanan ranan .

Don kema ya ce kamar kowa da aka samu ta hanyar halak banson in kara ganin ki a cikin damuwa
wanan kaddarankice da Allah ya zano maki tun farko.

Abbu yayi min magana da zasu kwantar min da hankali da wanda zaisa kada inga laifin mahaifana da
suka haifoni kuma suka kasa rikona a hannunsu don saba lamba.

Da haka Abbu ya fita zuwa kasuwa bayan ya ban dari yace insai taliyan hausa in sulala da rana inci
komawa nayi daki naci gaba da tunanen duniya don har yanzu zuciyana ya kasa gaskanta labarin da
Abbu ya ban game dani din ashe mutane sunyi gaakiya da suke dangantani da larabawa tabbas ni din yar
balaraben asaline ashe .

Jinin sune a jikina kamaninsune na kwaso nake ruwa dasu jinin su shiyafi karfi a jikina bisa ga na
mahaifiyata wanan tunanen na wuni yi ni kadai a gida da haka har barci ya daukeni ban sani don idona
dake da rankon barcin jiya da banyi ba.
Koda ta falka karfe ukun rana ya gwauta a gagauce ta debo tuwa a randa ta shiga bayi ta watsa ruwa
tafito tayi alwala zuwa sallah bayan ta idar wanan hoton dake gefenta ta kara jawowa ta zubawa matar
jikin photon ido na dan lokaci tana nazarinta.

Tabbas ko a cikin hoton rayuwa ya nuna tana cikin jin dadi da walwala a lokaci saboda yanayin da suka
dauki photon ya nuna gidane hadade ko a dacan baya don akwai abubuwan more rayuwa a gidan da
photon ya nuna.

A fili take fadin don me zaki gudu ki barni cikin bakin ciki da takaici bayan kune sanadin zuwana duniya
a haka ina kika shiga kika watsar dani haka kamar marainiya ?

Idonta ta mayar kan wanan balaraben tun daga rawaninsa daya dan daura ga kai har zuwa fuskansa
dake nuna tsawon dogon hancinsa zuwa dan gashin bakinsa kafinta mayar da idonta kan farar jallabiyan
jikinsa tana runtse idanuwanta.

Cikin jin kuna da wani irin tsanarsa a zuciyanta ba zan yafe maka ba ta furta a fili kayi sanadin zuwana
duniya ta hanyar yaudara kuma ka wofintar dani a cikin duniya duk da kasan da ina raye a doron kasa.

Hakana dinga sakin maganganu ni kadai a gidan kamar sabuwar mahaukaciya in na gaji in fashe da
kuka inyi kuka saina gaji kuma in cigaba da magana.

Har nagaji nayi barci a wurin saida almajiri yazo yana bara na falka sauran tuwon dana zubawa Abbu ya
rage shina raba biyu na kirasa nabashi ya shiga jero min addua.

Nan kofa na zauna bayan na debo ruwa a randa nake zauna na tasa abincin a gabana na kasaci da kyar
nayi loma biyu naji tuwon bai wucewa hakan yasa na mike zuwa alwala nayi sallah.

Haka na wuni ko wanka banyi ba a ranan sai zuwa yamma na dan samu zuciyana ya sake har na samu
na dinga yan aiyukan daya dauke min hankali.

Sauran garin tuwon daya rage na tuka muna don zai isa saboda daga bakina saina Abbu har miya na
hada koda Abbu ya dawo da wasu kayan cefane yasanu ina kwasan tuwo.

Tun daga kofa yake fadin nana ikon Allah a ina kika samo kayan girki na juyo ina fadin Abbu sannu da
dawowa ya amsa da yauwa har lokacin da mamaki a fuskanshi.

Ya sake maimaita min tambayan dayayi min da farko na bashi amsa da fadin Abbu sauran na jiyane
daya rage na tuka muna.

Allah yayi maki albarka nana ya fada nakanji dadi idan Abbu da Ammah suna min wanan adduan don duk
sukai min nakanga fa,idan wanan abin




ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/23, 10:14 PM] Zainab Idris Makawa Writer: JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,



00️⃣33️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Kwanan Ammah uku ta dawo cikin bacin rai hankali tashe na gane hakan ne ga yanayinta duk da hakan
bai hana ta hango yar rama da nayi ba.

Keko Aeesha wanan rama fa ko bakya cin abincin ne bayan tafiyana lokaci daya duk kin zube haka meke
damunki haka ko kinyi ciwone a bayana take tambaya cikin damuwa ?

Lafiyata kalau Ammah kawaidai kila kewanki ne yasani rama nake gani tafi can ja,ira saboda tafiyan
kwana biyu ki zube haka ?

Kodai malam ne baya kawo abinci ki dafa maku ta tambaya cikin nuna kulawanta a gareni nace abinci
kan har sai mun ture ai.
Gefenta na karasa isowa na zauna ina fadin da alama dai a gajiye kike Ammah ko in fita in nemo maki
wani abu kici ta kalloni tana kako murmushin dole a fuskanta tana fadin dadina dake Aeesha tausayin da
jinkai.

Yanzu har kin fahinci damuwa a fuskana to kwantar da hankalinki gajiyace kinsan hanyar namu
bakyaune dashi.

Ina maman gwarzo don naga tare suka tafi ai da ita take fadin tun acan kowa ya shiga motar garinsu
don tafiyan zai zama wahala idan tace sai ta biyo ta nan kuma.

Nidai ban matsa mata ba naci gaba da aiyukana da nasan nice zanyi idan tana gida har lokacin Amma
din tana zaune a inda take .

Har lokacin Ammah na zaune a inda na barta cikin damu saida aikai kiran sallah la,asar na kawo mata
ruwa a cikin buta a nan inda take din don tayi alwala ta samu ta mike ta zagaya ban dakin ta dawo tayi
alwala ta shiga daki.

Nima shinaje nayi bayan na idarne na fito a hankali nake jin sautin kukan Ammah din yana tashi daga
dakinta na dan dade tsaye a cikin damuwa kafin na yunkura na shiga dakin tana ganina tayi saurin share
hawayen dake fuskanta tana saita kanta.

Don kada in gane halin da take ciki a lokacin da wayauna dole in gane ko ace ni karamace yau naga
uwata tana kuka haka dole in shiga halin

2 / 109