Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
haka idan dubagari basu
kama mutum ba Ammah ke fadan hakan .
Nace su waye kuma duba gari Ammah tace kaji ba kaji yaran nan duk basu san duba gari ba a yanzu ba
dole kazanta yaiwa mutane yawa ayi ta cututukan da ba magani ba ?
Ke ina yarinyar nan Asmau yana tambayan Ammah din tace tana ciki yace gobe in Allah ya kaimu ita da
yar uwarta su hada hannu su gyara ko ina na gidan ban dan bamu sani bako har ciki zasu shigo.
Mikewa nayi tsam na koma daki naji yace yaki nan zo karbi wanan nasan kwanan nan bakya son cin
abin yasa na riko maki kije kici daki ke kadai kinji.
Ikon Allah kana son koya mata rowa ke nan Ammah ta fada bai bada amsa ba ya fuske kawai yana miko
min ledan na karba da dan rusunni tare da fadin nagode Abbu.
Gurasace mai zafi yaji kayan hadi sai kamshi yakeyi na nufi dakina dashi bayan na mikawa Ammah ta
diba na wuce da sauran tunda ba kowa a wajen.
Naji dadin hakan sosai don ko na zauna naci saida na koshi nabarwa su Asmau saura na hada da
maltina mai sayi daya hada min nasha sai gyatsa.
Allah yayi ni da son gurasa sosai anythings filowa da za a gyara nafi son gurasa da komai don zaman cin
tuwo nakewa gurasan balle wanan da Abbu ya sayo min yana da dadi sosai don wanan hadin na kuli kuli
da ganyen kabej da yaji idan yaji magi yafi dadin ci ga mutum.
Washegari koda nafito zan tafi school don kasancewa thurday duk inda nabi mutanene keta gyaran
gidajesu yara da manya kowa na aiki tsabtace gidansa da waje a unguwar.
Daga school na wuce sallon na wanke kaina aka gyara minjiki wai don kada Man yai min girshi ya
sameni gajal ba gyara a jikina yasa naje aka gyara min jikina din.
A gajiye na dawo gida misalin biyar har ya dan gwauta nashiga na watsa ruwa a jikina sai naji dadin
hakan sosai sai lokacin na samu daman kallon kaina a mirron wardrobe dina dake dakin.
Ni kaina ba sai wani ya fadaba nasan na canza sosai a yanzu tsayawa fada wasane na saka wani dogon
riga a jikina nafito na samesu a waje suna shan iska don babu wuta.
Anty safiya ke fadin wai har gidan nan sun shigone mama naji ammah tace sun shigo mana ai har
bandaki dako ina sun duba suka bamu dubu biyar duk gidan da suka samu anyi gyara haka sukayi.
Ai gobema su dawo Asmau malam yaba kudin ita da sama,ila da suka wahala tare sai lokacin nayi
magana nace suko dai don Allah ?.
Dubu biyar yace masu me su dai kawai ka gyara gidanka ina laifi dubu biyar keko Aisha ta tareni da
fadan hakan sai nayi shiru.
Shiru yayi yana saurarenta har tagama fadan abinda ya kawota kan yarta da tun safe take cikin tashin
hankali a cewanta.
Dan tsohon dake kishingide ya kallota yace kingama idan baki gama ba sai ki karasa ammafa kada ki
manta shima dane kamar kowa don naji kamar kin manta matsayin sayadi a wajena.
Kallonsa tayi kafin ta tausa murya tana fadin shi ai don na sanin ne nazo gareka ba don hakan ba sai in
dauki matakin hakan da kaina.
Madalla ko yanzu bai baci ba hakan yayi kina iya daukan matakin hakan ai tunda dukkan su biyun
yayankine.
Saidai kafin nan ki koma ga yarki ki tambayeta mai ta aikata har ya juya mata baya a yanzu din ?
Kallon mijin nata tayi kagin tace rankai dade na fahinci kamar kana bayan sayadi me zata aikata masa
kuwa banda dai yayi aure ya juya mata baya ko ince ya manta yana da wasu iyali a nan.
Kinyi kuskure idan tunanenki ke nan kan aurene zai bar uwar yayansa ya kama wata matsalanku ke nan
ku mata dama ?
Na fada maki ki koma ki zauna da yarki ta fada maki idan taki fada kuma zata tabbata maki a hakan cikin
daki kuwa .
Daga hakan ya juya yaci gaba da jan tasbahan dake hannunsa tare da kurawa tv ido yana kallon malam
Abubakar gumi dake wa,azi akan zakkah.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[10/7, 9:02 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
6️⃣6️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Don Allah masoyana ina cigiyar novel dina kanin ajali complet wace kedashi a wajenta ta taimaka min
dashi don Allah nogode fatan alheri gare ku ko yaushe Allahuma Amin.
Tsofine su hudu a zaune suna sauraren wanda ke bayanin game da dan nasu da yanzu sun rasa gane
kanshi yau ciwo gobe lafiya.
Gashi shine haziki a cikin diyan nasu shi kuma Allah ya jeraba da laluran nan da suke fargaba akansa
yanzu.
Shiru sukayi yana koro masu bayanin abinda ya sani game da dan uwan nasa yayin da tsohon dake
tsakiya yake faman kada kafa ya jijiga sandan dake hannunshi daga zaune.
Ya dai tabbata abinda matarsa ta fada gaskiyane yayi aure har da haihuwa bada sanin iyayyen nasa
yanzu kuma gashi Allah bai basu haihuwa ba da yar uwar nasa da yake aure a yanzu .
Hakan ya jawo mashi damuwa don laluran da yake fama dashi akan hawan jini da sauran matsalolina
zamani da ba,a rasa ba dai.
Lah,lalala wanan zancen ba mai karbuwa bane AbdulRashid tsonhon dake faman kada kafa yake fadan
hakan wanda shine mahaifi ga matar umar faruq din da suke magana a kansa yanzu.
Dukkansu sun fito cikin gida dayane gidan sarautan kudancin dubai din garin da ake kira da Oman
wanda suna cikin kasan dake kawo cigaban kasan ta hanyar yawan hako ma,adaine da suke dashi a
karkashin duwatsunsu don can suke wajen fita daga kasan suna kusan makwabta da wata kasan.
Amma yanzu zama da wayewan kai da harkokin business dinsu ya jawo wasunsu sun dawo cikin Dubai
din da zama tare da iyalinsu.
Wanan zaman an hadune don dansu Umar faruq da dattijon basaraken ya kira meeting din a kansa don
suji ainihin gaskiyar zancen daga bakin dan uwansa.
Sun kuma ji amma dattijon ya tuma ya kafe akan hakan ba abinda zai yuyu bane inma har ya yuyu din
to ya zama dole umar din ya watsar da zancen wanan yar da basu da masaniya akanta ?
Hakkun hakane zancen sultan don kuwa kawo wanan yar a cikin mu zai zubar muna da kima da
martaban gidan mu a idon mutanen mu.
Shima dayan ya dan jinjina sanda kafin ya soma magana yace to shi dai ba abinda zaice sai abinda su
manya suka zarta akan zancen.
Har lokacin shi mahaifin umar din baiyi magana ba yana dai zaune yayi shiru yana saurarensu saida yaji
sun gama yace.
Amma a nasa shawaran tunda har mustapha ya tabbatar da hakan idan suka kyale yarinyar nan sun
aika wani babban zunubi a rayuwansu.
A yanzu ilimi da wayewa yana saka mutum ya auro duk macen da yake so a cikin duniya ai ba wai sai
dole yar kabilanka ba.
Yarinyar nan jinin muce tunda dan mu ya samota kuma bata hanyar haramiya ba banga dalilin da
yanzu zamuce ba zamu karbeta ba a matsayin yar mu.
Sai wanda yai maganan na karshe yace nima abinda nake duba ke nan mahaifin nasa yaci gaba da
fadin dakata na karasa yau idan munji kunyan abinda dan mu ya aikata a rayuwansa mun boye wanan
zancen ?
Gobe kiyama idan munje gaban Allah akwai wanda zai cece mu ya dauki nauyin wanan zunubin da
muke son mu aikata a yanzu na wofintar da yar nan da mukayi a cikin duniya a yanzu ?
A takaice dai kana nufin zaku karbi yar nan da kai da dan ka babban nasu ya dakatar dashi da wanan
tambaya a fusace .
Sai da ya dan saki murmushi yace kwarai don bansan amsan da zan jewa ubangiji dashi ba idan na
kyale yar nan ban halasta taba a cikin iyalina tun a duniyan nan.
Dama nasan za ai hakan nasan da zaka goyi bayan dankane kan zunubin da yaje ya aikata ka kawo
akidar sunna ka saka ka yaki mutane dashi nasani ya kara fadi a hasale.
Ba haka bane laifin nan umar ya riga daya aikata ba tare da sanin mu ba dole yanzu muyi hakkuri mu
rungumi kaddara yadda tazo muna.
Kuma abun nan yayisa a bisa ka,ida ai tunda ba zina ya aikata ya samu yar nan ba zaman aure yayi da
uwarta har na shekara biyu don kaucewa zina har rabon yar nan ya gitta tsakaninsu.
Tir tir da wanan akidar taka kai yanzu ka yarda da ba zunubi ya aikata ba ke nan ina dama a nan dan da
yaje yayi aure bada sanin mu ba har da haihuwa ?
Duk abinda zamuyi indai bai kaucewa sharia ba mu tuna da goben mu don ba nan duniya zamu
tabbata.
Wallahi daga kai har yarka baku isa ba baku isa ku kawo muna yar wata kabila a cikin gidan mu .
Kabilar ma ta kabilan bakar fata ku ke son gauraya damu.
Kuje can kuji da abin kunyar ku kaida danka mu bamu yarda da wanan ba wanda aka kira da jafar shi
ya dakatar dashi yace ya dawo ya zauna don Allah ya sauraresu.
Don gaskiya dan uwan nasu yafisu gaskiya ya juyo a fusace ya kallo jafar din jafar din yace kwarai don
ko Allah bai haramta hakan ba don me mu zamu kyamaci abin ?
Wanan diya ta umar ce kuma ya sametane a bisa hanya ma daidaiciya kada muyi gangancin da fushin
ubangijj zaizo ya hau kan mu saboda son zuciya da gudun surutun mutane .
Balle me zasu fada ko banza umar din kowa yasan ba akidan mu na gargajiya yake biba sosai haka kuma
akwai da yawa da suka fara auro bakin kabila a yanzu cikin mutanen mu don haka shawaran Usman
shine abin dubawa .
Mu san yadda zamuyi mu kawo yaeinyar nan nan don duniya tasan da ita a matsayin diyar Umar da ake
kururuwan bai haihuwa dama.
Dayan ya jijiga yar sandashi yace bai haihuwa ya haifi wanan din dole dai akwai matsala ko ina salma
dince bata haihuwa ko kuma alhakin wanan yarinyar yasa bai kara samun wani rabo ba.
Tab baban salma din ya mike a fusace yana fada don me dan uwansa zaiyi kokarin dorawa yarsa sheri
matsalan haihuwa ?
Da kyat dai ya fahincesu karshe suka sulhunta tsakaninsu suka hade kai shawaransu tazo daya badon
mahaifin salman yaso ba .
Din yaiwa yarshi alwashin cewa wanan abin ba me yuyuwa bane sai gashi yanzu a karshe shawaran yan
uwan nasa yafi nasa karfi.
Gidan yar nasa ya nufa ya dade a zaune yana bin gidan da kallo tare da jijiga kai shi yasan abinda yake
tunane a zuciyarshi kafin ta fito cikin shiga ta alfarma tasa a cika masa gaba da kayan abinci kala kala na
taronsa.
Fuskanta akwai yanayin damuwa don haka baiyi mamakin batayi dokin ganinsa ba sosai a lokacin sai
yaji ta kara bashi tausayi.
Zama tayi a hankali tana gaida mahaifin nata da itama take hango tsananin bacin rai a tare dashi
lokacin bayan sun gama gaisawane yake fadin nazo akan zancen mijin kine.
Mun zauna da yan uwana muga wanan abin bai tabbata ba amma kinsan mahaifinsa akwai wayewan
zamani a tare dashi.
Bayan haka kuma mutum neshi mai bin sunna dan tsaurine kin sani baya yarda ya hada addini da al,ada
a rayuwansa don haka a take ya rushe dikan dana kafa akan yarinyar.
Ya nuna tunda addini bai hana hakan garemu ba don me zamu dauki al,da sama ga addinin mu don
haka shi zai karbo yarinyar nan ya kawota nan cikin mu don kowa yasan dansa ya haifi diya ta sunna da
wata a baya can saudiya daya zauna.
Kai ya girgiza cikin takaici kafin yace Usman yana da halin goyon baya akan karya da zai watsar da
kimar mu a idon jama,a .
Yana amfani da sunan al,ada to nasan ta ida zan fito masa zan saka kyamar yarinyar nan cikin zuciyar
mutane in sheganta masu ita in nuna karyane ba da aure ya haifeta ba.
A,a Abbu kada kai hakan don Allah mu dauki wanan kaddaratace abu daya nake son kayi shine ayi abin
nan a zamanace yadda ba zamuyi laifi a wajen wasu ba kan abinda zamuyi din.
Har udan sun yarda sun kawota nan to ayi gwaji a gani a tabbatar da yarsace ko kuwa tunda irin matan
nan basu zama da namiji daya neman kudi da bin maza ke kawosu kasashen mu.
Duk da hakan salma ki barni dasu a,a Abbu ko kayin hakan zumunci zai bacine a banza tsakaninka da
yan uwanka amma a gwada wanan din dole gaskiya zai baiyana ga kowa.
Don zuciyana yana ban cewa ba yar umar bane kawai dai tayi cikintane tana son ta dafe mashi don ya
karba shi kuma yanzu yana neman diya ido rufe zai karba din yar tayi amfani da sunansa.
Kai ya girgiza tare da matse sandansa dake hannunsa ya tokare yana daukan karfi daga sandan yace
baki tunanen idan hakan ya kasance gaskiyane.
Yar ta karbu garesa ke nan dole yar zata tsaya a matsayin yarsa tillo daya ke nan don sun kawo zancen
matsalan haihuwan ku daga garekine ke nan badaga wurinsa ba tunda ga yarda ya haifa da wata yanzu
ta baiyana.
Lah lah azeemun ba laifina bane ko nasa shima likita ya tabbatar muna baida matsala komai akan
haihuwa Allah daine bai kawo muna haihuwan ba tsakanin mu.
Wani huci ya fitar kamar kosasshen doki yai haniniya kafin ya dukar da kansa yana tunane na dan
lokaci kafin yar ta katseshi da fadin.
Ba zan nuna mashi komai ba akwai hanyoyi da dama da zanbi wajen ganin yar bata samu karbuwa ba
ai ko a wajensa don nasan ba lalai bane tayi kama dashi tunda uwarta bakace dama.
To shike nan nima zanyi nawa kokarin a can ya dan taba abinda aka kawo mashi din kafin yai mata
sallama don a ranan zai koma garinsu din.
Damuwata shine exam din mu na karshe da muke kan zanawa wanda kusan yai muna girshi gashi a
cikin kuraren lokaci mukeyinsa saboda yajin aikin da ake sa ran malaman jami,a zasu fara yi yasa suka
matso da jerabawan namu kusa wanda a yanzu hankalina ya koma a kansa banda natsuwa ko kadan
cikin sati biyu mun kammala a wahalce gashu shine na karshe a wajen mu.
Wasu na murnan hakan wasu kuma ire iren mu hankalin mu yana a tashe don munsa hope a wanan
karatun sosai shine muke ganin madogara a wajen mu wata rana.
Abin ya hade min biyu lokaci guda ga Man da bangani ba hakan ya ban haushi ga kuma jidalin exam da
mukai fama dashi.
Hakan ya dan jawo min dan rama nayi dan duhu kadan amma muna gama exam din da sati daya na
fara murmurewa fargaba ya wuce man kuma na tattara zancensa na watsar .
Ko sakonshi na samu a wayana ban tsayawa in duba sai in wuce don nasan ina dubawa yana online
zaiga na duba din sai nake shareshi.
Ina son in dan huta yasa nacewa Abbu zani abuja ingano su inyi sati daya yaso hanawa amma da sukai
waya da ita mama din tace hjynta zanzo gani da ta kwanta asibiti yasa yace ina tafe insha Allah.
Tafiyan bani kadai bace tare da mutumiyata Asmau zamuyi tafiyan muka shirya rigin rigin tsaraba da
komai mun saya da zamu kaiwa mama din.
Sai me sai ga Auwal yazo gidan mu da waya don man din yace koya kira bana dauka yasa yaba Auwal
din ya kawo min dole na karba.
Ina dauka naji yace GF me zakije Abuja yi wanan lokacin kuma bana son yawon nan ki bari na dawo
bani kasan ne idan na dawo sai nayi maki arrangin ki tafi.
Mamaki da takaici ya rufeni lokaci guda nayi shiru na kasa amsashi a raina kuma ina mamakin wani
munafukine yake addaban rayuwata hakane wai ?
Banda shakat ko wani irin motsi nayi yana a kunnen man yanzune zan ji yayi magana akanshi.
Shirun da nayi yasa yace ko ba zaki iya jira in dawo bane idan ba zaki jira ba ku bari ayi maki booking
din jirgi ki tafi dashi inya kanki kuma kwana ukku don jibi insha Allahu zan dawo.
Ji min mutum kamar wani mijina ko ubana ko wani shakiki nawa yadda yake ban comand haka har da
ban iya lokacin da zanyi a can irin ga miji din nan ko ubana.
Ban tsaya bashi amsa ba na mikawa Auwal wayanshi ina fadin nagode ya zama dole in gano waye yake
min wanan zagon kasan a gidan nan amma bari zan gane koma waye ai ?
Auwal sai anjima ko yayi min hannu dana dakata yana mashi bayani a lokacin sai wani faman daga kai
yake masa ina gefe ina dakonshi har ya gama cikin abinda baifi mintuna biyu ba.
Rankishi dade yallabai yace in yi maki booking din jirgi a yau din nan na kallosa cikin mamaki ina fadin
nifa bani kadai bane tafiyan nan tare dasu Asmau zamu tafi mu dawo.
Wai ashe wayan a kunne take naji yace dashi hello yana masa bayani ko me yace oho na daiji yace
gobe zan zo in daukeku zamuyi waya don sayen ticket din.
Wani iri naji lokaci guda sai kuma na tsaya bayan na kula ya kashe wayan a lokacin nace Auwal meyasa
Man yake wahala a kainane wai ?
Nifa na kasa fahintar matsayina a wajen mutumin nan har yanzu ka duba yadda yake min magana
yanzu kamar wani da nake karkashinsa ?
Har kin ban dariya da kikai wanan magana a karkashinsa kike mana kowa ya sani da sauri nace wanan
ba gaskiya bane Auwal .
Naji nasani yana ban duk wani kula daya dace abawa kanwa ko yaya ko dai mijin ka din nan