Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
No ga hanya kibi mana ya fada kuma don haka a ranan ta kofan manya na shiga haraban ma,aikatan
zuwa office din mu.
Na samu senior staff din mu bai shigo ba tukun sai mutum biyu a office din namu na gaisa dasu na
wuce wurin zamana don kowa yasan inda wajen zamansa yake.
Banyi sanyi a gwiwa ba na fara jona system din aikina don binciken da nakeson yi kafin ogan mu ya iso
sam bansan zan iya ba sai gashi da gwaji ina bin yadda mam bash ya taba fada min har na shiga wani
na,uran wata kasa ina bincike akai.
Inda na shagala sosai da abinda nakeyi har ogan namu ya shigo office din ba tare dana sani ba hakan
yasa dayaga na shagala ya kewayo zuwa inda nake din a duke.
Sai ji nayi an duka a bayana ya duko yana duba binken da nakeyi din a computer yabi da kallo kafin ya
zaro ido yana kiran yan uwanna da sauri suka karaso wajen sit din nawa.
How do you do these yake tambayana a cikin mamaki na dan tsorace na fara inda inda ina masa bayani
sai kuma nayi nayi shiru ya tsurawa seching din nawa ido na dan lokaci kafin ya furzo iska daga bakinsa.
Juyawa yayi ba tare da ya furta komai ba akaina yace kowa ya koma wajen zamansa kuma yanayin
yadda ya zauna yasa na shiga tsarguwan kaina har na tashi naje gunshi ina fadin sir nayi wani abinda ba
daidai bane ?
Yake fadin yayi mamakin da yar traning ta iya kai hakan a bincike ba tare da jin komai ba wanan
matakine da wasu manyansu suke amfani dashi na nuna don kosu basu san yadda zasu zakulo wanan
hanyan ba a yanzu don,,,,,,,,,
Shiru yayi yana fadin quit sure you are braved as you know these method now don sai wanda suka
samu training din hakan a turaine suka san yadda ake wanan abin.
Have you been there before ?
No nace da sauri yace a,a abin yana da mamaki fa ace ke tun a yanzu kinsan wanan din ba matsala ki
koma ki zauna ya fada tare da nuna mun wajen zaman nawa.
Nabar computer yana loding dama karan da yakeyi kafin inkai na nuna bukata ya shiga yasa ya taso da
sauri zuwaga computer nawa har ya rigani isa wajen .
Saida ya gama dubawa ya juyo yana fadin miss how do you manage to do this serching please ya
tsureni da idanuwan shi cikin dan daburcewa na bashi amsa da i just try it now.
Yadda ya kalloni naga alaman kamar bai yarda ba nidai na share kawai nayi tsuru tsuru da idanuna
kafin ya gama binciken shi ya mike da sauri ya fice daga office din.
Zama nayi cikin karfin hali inda abokan aikina suka taru a kaina da tambaya na share kowa a wajen ba
kawai saiga ogan mu ya shigo da manyan officers din mu ba.
Sun taru suna ta magana kafin a dauki computer nawa gaba daya su fice dashi dama na ma,aikatane
abinda na sani kawai shine yau najawa kaina sabuwar matsala kuma Allah kadai zai fitar dani wanan
kuma .
Shiru shiru ina jiran inji anzo an fitar dani sai naji shiru wanan yasa na dan samu sauki a zuciyana har
time din zuwa mosque yayi musulmai suka fice zuwa ibada ya rage wa yanda basa sallah a wajen sai mu
mata sai kuma wa yanda basu damu da ibada ba sosai tsirarunsu a ma,aikatan .
Ogan office din mune ya tsure ni da tambaya ban yarda na fadi komai ba duk tsoratanin da yakeyi
bance kala ba na kafe da gwadawa nayi kawai.
A haka har muka tashi daga wajen aikin lokacin ina ji kamar na gudu in koma kano in fasa karatun ga
baki daya don halin dana shiga ciki.
Ashe bai kare min ba don ko zan samu wani a gidan yaya kuma dan kayan makulashe na soyowa Amira
dake murna idan ta ganni.
Ina jin nauyi da kunyan komawa ban rika mata komai ba don yanayin dana shiga a office yasa nake jin
kasala na sauka min a lokacin.
Da sallama na shigo gidan da muryana dake nuna gajiya a tare dani lokacin na hawowa samansu kuma
da nayi a falonsu na samesu da kannenta .
Kamar kullum ina sallama Amira tasheko tana tarona na rugumeta nima ina nuna mata jin dadin
ganinta a lokacin yayin da uwarta ke faman waya a cikin yare.
Tsaraban na mika mata sauran na mikawa dayan budurwa don yayiwa amira din nauyi hankalinta
kuma ya koma ga chis ball din dana mika mata.
Anty Basira sannu da gida na kara furtawa a kasalance ban tsaya jin amsanta ba na nufi daki don in
rage kayan jikina .
Ina shiga idona ya sauka akan kayana dana aje da alaman an taba kayan a lokacin ban damu ba tunda
gidan yawane nake zaune a gwamatse dama haka na cire abayan na kai hannu in dauki zanina na samu
an balla min hannun jakka gashi anyi kokarin bude wajen key din ankasa hakan.
Cikin mamaki nakai tsugunne ina dubawa saidai ban fahinci komai ba hakan na dauko zani da riga na
sauya na fito falo inda suke zaune a lokacin tagama wayan ko.
Na kara gaida ita ta amsa da Aisha kin dawo nace eh nashigo kina waya tace wallayi zama nayi a saman
kujera kafin nace anty na samu wani yayi kokarin balla min jakara a daki yanzu da nashiga don har an
balla hannunsa ma.
Cikin mamaki tace sani jakarki kuma sai ta kalli kannen nata tana masu yare ko da banjin yarensu na
gane amsan da suke bayarwa na a,a a lokacin.
Ina jin tana fada a cikin yare nace ki barshi anty amma mashi ya daina don Allah hakan ba kyau tace
shine ai nake tambayansu ?
Don mu dai gidan nan ba,a taba yin irin hakan ba akan me yau zai faru dake kuma mafarin akaimu kano
ana fadan nida yan uwana barayine .
Na kallota cikin mamaki kamar zance nice zan kaiku kano kowa sai kuma nayi shiru don tuno da abinda
ya faru zuwan su kano buki karta dauka halinane dafawa mutane sata kuma.
Har na daure sai kuma naga ban iyawa nace idan da ba aimin ba ba zan wa wani sheri ba anty kuma na
fada makine don ni bakuwarkuce kada a maimaita hakan .
Zancen wai inje kano in fada bai taso ba ki daiyiwa yan uwan naki fada kar akoma min hakan don Allah.
Da alaman taji mamakin amsan dana batane a lokacin yadda ta kalloni sai naji tace inba hakama Aisha
suwa ke gidan nan iba muba da zakice wai kin samu kayanki ba daidai ba ?
Sam banji tsoronta ko shayi ba tsoro ya dade da fita raina ga duk wanda ya kawo min rainin wayau a
yanzu nace idan ba lalura ba baki ganina nan ai.
Ko a kano kin sani ba gidan kowa nake shiga ba an min ba daidai ba ba zanyi magana ba ko me anty ai
kamata yayi ki bincika ki kuma tsawata amma ba kice za a kaiki kano dake da yan uwanki ba kuma.
Sai naji mai karamin cikin mazan yana mata yare hakan yasa tayi shiru na kai second biyu a zaune falon
saina mike na koma dakin na fara gyara.
Na gama na wanko bayi don shi nafi tsana kaf zaman gidan nasu gareni Allah ma yasa suna da ruwa ko
yaushe sai hakan bai mun wuyan gyara.
Nagama na fito na gyara har falon tsab lokacin mazan sun fita sai matan dake aikin girki bayan na
gamane nayi wanka tare da alwala na koma daki.
Miss Called na samu a wayana maryam ce ta kirani na dauka muna waya hakan ya shagalal dani har na
manta da komai ban dai sake fitowa ba har washe gari.
Da safema na sake maimaita gyaran gidan dama waje gyara yake so don gaskiya gidan ya fara komawa
daidai a yanzu.
Abinda na lura dashi ta dauki zafi dani kan zancen don koda ta fito da safe ta sameni ina wanke wanke
na gaida ita da kyat ta amsa min gaisuwan.
Bayan nagama nayi wanka ina zaune daki naji muryan yaya dake gida ranan yana kirana daga falonsu
na amsa na fito.
Gaidashi na fara yi ya nuna min waje in zauna na zauna ke nan sai gata ta fito ta zauna itama yace
kwana biyu bamu hadu ba kina rigani fita da safe nace hakane.
Yace Aisha yaya akayi kuma keda mutumiyar taki daga zuwanki za ace har kun fara samun matsala
haka meyasa jiya na dawo take fada min maganan da banji dadinsa ba why ?
Zaki dafa masu sata da ita da yan uwanta kai na dago na kalleshi cikin mamaki nace banyi zaton jin
hakan ba son kamar ka dauki abinda ta fada ma shine gaskiya.
Na mayar mai da yadda mukayi sai ta tare da fadin dole ince hakan mana wake gidan nan idan ban dan
da yan uwana .
Ai ko fati da tayi zama a nan tare damu gidan nan har mukai ta samu matsala bata dafa muna sata ba
duk iskancita kuwa na dago kai na sake kallonta cikin mamaki taci gaba da fadin.
Haka kikazo muna da sallo iri iri gidan nan na kawo ido nasa maki Aishy tunda nasan bariki nima sai
mijin ya daka mata tsawa da fadin Basira ki san abinda kike fadi kada ki manta she is my sister.
Yaci gaba da fadin wai me yasa hakane why duk wani dan uwa nawa yazo garin nan ya sauka gida sai
kun samu matsala dashine Basira ?
Wanan ai ita taja mu samu matsala da ita akan me zata dafa muna sata nida yan uwana yace amma
yanzu ta mayar da yadda kukayi a gabanki .
Kuma kokece kikazo kika samu abinki ba daidai ba dole zakiyi magana kamar yadda tayi yarinyar nan
tana da kokarinta akan,,,,
Oh oh oh oh haka zakace min ke nan dama na gane take taken ka akan Aishy dama neaboughs sun
fada min na saka ido a kanku da ira.
Tunda sun sanka da bakin son mata tunda ba uba daya ko uwa dayace ta haifeku ba zakayi halin dan
akuya kaga mace haka dole fa inyi magana habib.
Munafuki nagane ka ai tunda tazo kake rawan kafa da zuwanta din wallayi kasani sarai ka gwada ka
gani kaga yadda zamu kwasa dakai gidan nan har ita .
Sai naji yace basira kina da hankali kuwa da kanwar tawa zaki zargeni yau kuma ke wace irin dabbace
mara hankali wai ?
Kanwar ka for where idan ka samu sister in bed ko ai nasan irin halinku idan kunga mace haka nan suka
fara yiwa juna tonon asiri a tsakaninsu ba dadi .
Daga yarinyar dake jikina nayi yana kiranta da karuwan banza mara mutunci zaiyi magani ta ai bada
dadewa ba.
Amira na lafe a jikina ta kankameni cikin tsoron abinda iyayyen nata keyi har sukaci suka sude ba
makwabcin daya shigo gidan da sunan rabonsu fadan.
Tsam na mike tare da yarinyar zuwa dakin mu don ba zan iya ji ko ganin wanan abin ba saboda sunyi
nisa gashi ban saba ganin hakan nayi ba garin mu f.
Fada da tonon asiri haka tsakanin mata da miji na tujara tana wani bugun bango fafafa da karfi kamar
zata fasa bangon ginan gidan wai duk a kaina haka ke faruwa.
Wai sara akan gaba ina shiga dakin na samu waya nata ringing na dauka faridace ta kirani tana
tambayana ya Abuja.
Na amsa da Abuja kalau dama kiran karafin haline tayi min naji wayan ya dauke kuma banda hankalin
kiranta a lokacin don haka na aje wayan.
Ina gyarawa yarinyar kwanciya don sai faman ajiyan zuciya takeyi a jikina yadda tayi barci a kife gashi ko
karyawa banyi ba ranan .
Ga wanan abin kuma da yanzu ya faru sai kuma wayan ya kara ringing da bakuwar layi nagani haka na
daga don banda wanan layin ina dagawa tana jin hayaniyarsu tace wai Aishace ?
Na amsa da ehh wake magana ?
Ke Anty Fati ce fatin kuce ashe kinzo abuja shine baki nemi ba nace anty fati cikin farin ciki muka gaisa
Hello nace ta amsa da fadin Aeesha meya kaiki sauka wanan gidan ke baki san halin wanan matar bace
ga muryanta ina ji dawa take fada hakane wai ?
Nace bari anty nan na kwashe komai na fada mata tace ai wallahi tunda umma ta fada min kina nan
Abuja kuma gidan yaya sai ankwasa da wanan matar.
Tun shekaran jiya naso na kiraki ban samu time ba sai yau nasan kuna gida shine nakira wallahi har
yanzu bamu dawo ba sai next month ina ganin zamu dawo.
Muka dan taba hira kafin mu kashe wayan nikan damuwa yayi min yawa a ranan ga amira lake dani har
tayi barci a hakan cikin tsoro.
Da alama sun saba da hakan dama don su suka gaji suka raba kansu bayan ya daki banza matar bariki
ke nan ko gezau ta gaji ta daina ihun don ba maceci.
Sai ince ya gadane ke nen gun mahaifinshi ko don haka akace mahaifinshi yake da uwarsu saratu daya
auro shima a bariki.
Ganin Amira ta tashi yasa na shirya na fice da ita koda muka fito babu kowa a falon lokacin taxi na tare
ya kaimu wani restaurant na hado muka take away din abinci har wanda zai kaini dare muka dawo a falo
muka samu uwar bakinta ya kumbura saboda bugun da yai mata din.
Yarinyar na ganin uwar kuma ta nufe da sauri ta danje kuma sai gata wajena ina shiga daki muka shiga
tare abincin na mika mata nata ta juya zuwa wajen uwar.
Na zauna naci nawa na kwanta daga tunanen rayuwar duniya barci ya daukeni a wajen mai nauyi da
mamakin basira a raina don kalamanta sun tsaya min a rai sosai lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA[9/4, 10:04 PM] Zainab Idris Makawa Writer: JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
4️⃣1️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ONLINE TRAINING!*
*ONLINE TRAINING!!*
*ONLINE TRAINING!!!*
*Are you looking to level up your game with traditional spa?*
Whether you are married woman, bride to be or some one who loves to master the art of *traditional
spa*, *natural aphrodisiac* and *Traditional incense* asalin kamshin shuwa look no further in this
article *@sady_aromamist_and_spa* have got you covered
Imagine you know all the ingredients used on your skin to moisturise, nurture and revitalise it, *intimate
confidence* and a good long-lasting Traditional scent.
Transform your space
Transform your skin and have that intimacy confidence. Join our online training
Wa.me/9048763046
learn the connection between *skin care,* *Traditional incense* irin kamshin nan mai kama jiki and
*natural aphrodisiac* masu matukar kyau with zero side effects 😍
Sign up now to join the waitlist(https://chat.whatsapp.com/EDJan6LcDjGDrh6geC0Bk5)
Early birds 7500
Actual price 15k
Follow our IG handle for free recipes @sady_aromamist_and_spa
Start Transforming your body
Zance gaba dayane yayanta a kanta lokacin don daga yayan cikinta sai na yar uwarta hjy yanti a dakin sai
faman yi mata sannu da sukeyi tare fifita haka duk motsinta idonta na kansu.
Likitan ya gama dubata ya dago yana mata sannu shima tare da kokarin tattara kayansa da yayi amfani
dasu wajen gwaje gwaje a kanta.
Alh muhammad da Ahamd kaninsa mahaifinsu bash ne suka motso suna masa tambaya akan jikin
mahaifiyarsu din daya duba ?
Ya gyara zaman glass din dake idon nasa yana fadin insha Allah zata samu lafiya idan ta farka
damuwace kawai yayi mata yawa a yanzu sai maleria daya dan shigeta kuma ya haifar mata da hakan.
Amma sai kin rage daga nan din don ta samu barci isashe a idanunta jin hakan yasa farkon fita sune
yayan kanwar nata su umma da mami sai su yayan nata aka bari a cikin dakin kafin hjy Nasare ta fara
yunkurawa don fita tana fadin Allah ya karo lafiya hjy.
Shima Alh Ahmad ya yunkura lokacin guda da yar uwar nasa hakan yasa Alh mohammad kallon ta yana
fadin ina ganin duk mu fice abar tambaya ta zauna da ita tunda itace ke jiyanta dama ?
Jin hakan yasa hjy kura dago kai ta kalleshi a tsiwace akan me zaice su fice insu basu zama ita zata
zauna don tasan zafin mahaifiyarta ita.
Ya gane me take mufi da kallon da tayi masa din yace nace kowa ya fita abarta da tambaya su zauna mu
koma can falo mu jira falkawanta.
Amma tambaya bata kaimu mu tsaya a tare da mahaifiyar muba ai a yanzu ko ta fada cikin gadaranta
gareshi shima lokacin a shirye yake yasa yace.
Ai don nasan bata kai ba din kuma tsayawanta ba zai bamu matsala ba yasa nace kowa ya fice mu koma
falo mu jira ko aje a dawo anjima idan ta falka.
Kallon fuskanshi tayi ta hango fitina a kwance lokaci guda don haka ta yunkura ba don taso ba zuwa
falo inda ta samu sauran yan uwa a zaune cikin damuwa da yanayin jikin mahaifiyar nasu daya firgitasu a
yau din.
Zama tayi tana fadin haka kawai za asa mutum yin abinda bai dace ba akan me kai in baka zama zakasa
mu mufita daga wajenta din.
Duk suka bita da kallo cikin a cikin damuwa da suke inka debe daddy su bash dake waya da danshi a
lokacin yana sanar dashi abinda ke faruwa.
Nace din ki fito duk waya haddasa mata hakan a yanzu ko waya san hjy da wani damuwa a baya inba
daliliki dake baki bari a zauna lafiya ba ?
Dama nasan abinda kake nufi ke nan ai kila nice nasa a sace mu din don inji dadi kawai ko ta fada ga
dan uwan nata kai tsaye yace.
Waya sani kuma don komai me yuyuwane ga mutum mara imani ai ba abinda ba zai iya ba jin amsan
shi gareta yasa tasha jinjn jikinta ga zancen shi tana tambaya nice mara imanin yaya Imamu ?
Jinda sukayi yace ba zakazo