Chapter 65 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   65 / 109

192K to 195K   out of 326.5K words

cikin mota a lokacin
muka shigo gidan .

Mun masu sannu da zuwa mama kan tunda tace sannuku da hanya ta kada kai zuwa ciki bata tsaya ba
mune muka tsaya muna gaisawa da Abba din.

Abba din yake fadin a,a diyata yaushe kuka zo garin nace shekaran jiya Abba yaya su anty hauwa da
kannen mu yace lafiya kalau suke wallahi.

Zaki kwana muna biyu ke nan garin na dago cikin kunya ina fadin a,a Abba gobe zamu koma insha
Allahu kwana biyu aka bamu daga gida.

Munzo duban jikin hajiya inna ce dama yace kunyi kokari amma gobe goben nan aiko kamar basuyi
muna adalci ba tunda muma nan muna son ganin ki.

Dan murmushi nayi ina fadin ai zan dawo Abba idan an kwana biyu tunda mun kare school masha Allah
ya fada har lokacin yana jingine da motarsa da yazid ya gama fitar da kaya.

Addah ce ta fito tana gaidashi da hanya hakan yasa na sulale na shige ciki na samu mama da yazid tana
fada tana fadin yana can ya tsareta da shegen tambayan nan nasa na lauya yaji komai ?

Sai gamu mun shigo kin samu kin gudo ba ai shiyasa na tura maku adda wurinsa ku samu ku shigo ku
huta.

Sai mutum yagama cima fuska ya dawo daga baya yana wani kame kame can kamar bashi ba ni wanan
mutumin ba zan taba mantawa dashi ba ai yaje can su karata da yar duniyar matarsa dai.

Mama don Allah kiwa Abba hakkuri tunda ya dawo yanzu hakkurin nan fa kuke koya muna a kullum
mama ?

Ke dai bari daughter kinji su dai je can su karata nina gaji kinji bani iya fita da girmana yanzu kuma da
Allah yabar min yayana na farko su ukku dana rasa aida yanzu nakai ga aje jikoki a gidan nan.

Sai naji ta ban tausayi kuma na kara fadi a sanyayye hakkuri dai za,ayi mama abar tuna abinda ya wuce
din.

Ance hakkuri baya faduwa akasa banza sai kaga ribansa insha Allahu ita kuma taje tayi tayi ai ubangiji
ya gwada mata ya fita ko yanzu.

Barshi kinji daughter yanzune da idonsa ya bude yasan muna da amfani garesa ai ya manta da irin cin
fuskan daya dinga muna a baya dagani har yaran nan.

Me zaki fadawa Aisha mama wanan da suka buga da Abba a ranan saima ince zuwanta ya sauya komai
ga Abba ai har muke ganin hakan ?

Son face to face ta fada mai gaskiya a kan mu har matarsa nina dawo da mamakin yar nan naki nace
dama soja kuka kaita tayi zaifi ai.
Ban samu bashi amsa ba din shigowan mahaifin nasa shida Adda falon mama din ta kara hade rai ya
zauna yana tambayan inna sukace ta shiga ciki bari a kirata.

Madam yaya gida ya fadawa mama din ta wani basarwa kafin tace gida lafiya namike inawa Asmau
signal da mushiga daga ciki mu barsu.

Sai naji yace diyata mamaku taki ta yafe min kuskurena akansu duk da tasan hakan bayin kaina bane a
lokacin.

Kunya naji na dan sada kai ina fadin Abba insha Allahu zatayi hakkuri ko don mu ai tunda muna son ku
a tare ke tafi kyaleshi kinji ta fada nashige ina dariya.

Dakin hjy inna muka shiga dan mun hadu da ita zata fita wajensa lokacin muna shiga dakin Asmau ke
fadin sannu dai mummy kin zama alkali ga mutanen nan ke nan.

Nan na zauna ina ba Asmau labarin dan abinda na sani nasu sai can hafsat ta shigo da kudi take fadin
Abba yace a kawo min mukara muyi tsaraba.

Nace lah anty da baki karba ba wallahi banda uban kayan nan da mama ta saya muna kuma kika karbo
kudin Abba ?

Ke kayan nan fa ba mamaki bace ta saya maki su haka ba kamar sata akayi ta saya maki su ki karbi
kudin nan zan maki bayani letter.

Na karba ina godiya tare da mikewa tsaye don inje inwa Abban godiya take fadin aiya tafi tun dazun ina
zai tsaya tunda baiga fuska a wajen mummy ba.

Mama nada gaskiya gara ta danja ajinta na mata kinji maza haka suke dama don fa wata yaiwa mama
abinda yai mata yanzu kuma ya dawo yanayi kamar bashi ba ?

Asmau kanki daya kuwa na fada cikin bacin rai to mummy daga dawowansa kuke son tace ta amince
tun ba aga kamun ludayinsa ba ko ya sauya ?

Ai ba a sanin sauyawansa kuma sai kun kula da yadda yake rawan kafa kan wacan din idan ya sauya
zaku gane hakan amma yana da wuyane sauyawanshi baki daya.

Kada mama ta dubi hakan idan ana duban wani abu ba a iya hakkuri duniyan nan tayi hakkuri kawai
don yaranta da Allah kuma.

Saidai hakan kam amma ko me mummy tayiwa Abba ban ganin laifita a yanzu don abinda yai muna a
baya kiris ya rage a lokacin mu rasa mummy din.

Saboda har saida ta kwanta ciwo sosai kamar ba zatayi rai ba ke tuna zancen ma yana sa mutum yaji
gara hakan kawai su zauna nisa da nisa dai tunda ba rabuwa yayi da wacan din ba ?

Anty hafsat anyi hakkuri a mayar da auren nan ki dinga tausan mama din keda kike mace don Allah
bari nuna ko in kula akan rabuwansu din.
Mun zauna zaman gyaran kaya tare da hafsat din a daki muna tatauna maganan mahaifanta din kafin
mu fita zuwa falo kuma inda nan ma muka zauna zaman shan hira da yazid.

Saidai zancen da hafsar din ta dauko min na batun kaya kuma yana raina abubuwa dai gasu nan na
daure kai ga mutum suna faruwa.

Lokacin ba don kuriciya ba da mutum na iya kamuwa da hawan jini a lokacin kan damuwan da yake
ciki.

Ga zancen Abbu da nake hango kamshin gaskiyan zancen Asmau kan Abbu din ya tsaya min a rai na bari
sai mun koma zayi maganan da Abbu din.

Duk da na rasa ta yaya zan fito masa da wanan maganan cewa ina zargin shi ke fadawa Man wani abu
game dani tambayansa zanyi koko zarginsa zance ina yi ?

Abinda ke tsaya min a raina ke nan duk tsawon lokacin nan har na mike naje na kwanta ina faman sake
sake ga kuma zancen ita hafsat din data dan gutsura min .

Haba dole kayane na alfarma da fitan arziki kaya dako bansan kudunsu ba zasu tasan ma duban kudi
daruruwa wallahi nikan nayi mamaki hakan dana gani din.

Saidai abu ba dama ka tambayi dalili gun wanda yake kamar mahaifi a wajen ka son yayi ma alheri irin
haka abinda kamar wuya gaskiya na tsaya tambayan ta.

A gurguje muke faman shiri don jirgin karfe goman safe zai tashi zuwa kano ga mama tsaye a kanmu
tana azazzalan mu mushiriya kada mu rasa jirgi.

Itace da kanta kuma zata kaimu har inna na fadin ko za a bari har gobene mu tafi take fadin haba inna
ina laifi mutanen nan sun bari sunzo muna dubiya mu kuma saba masu yanzu ga kwanakin da suka
basu ?

Dole haka muka shirya muka fito din ta daukemu a mota har hafsat da muke jin kamar kada mu rabu a
ranan don yanzu kam munyi wani mugun shakuwane da ita sosai.

Ko a filin jitgin saida mukai tsayin kamar na mintuna ashirin kafin aka sanar passenger masu zuwa kano
su shirya muka fara sallama da juna tana wani kara sakani a hanya a fakaice da kuma godiya gun
iyayyena.

Muka shiga jirgi munyi sa,a mun samu seat daya Asmau ta karbi wayana tana zuba muna hotuna a
jirgin da zata ba samira takaici idan mun koma.

Zuwa karfe daya har motan dan kadafi Auwal ya tsaya damu kofan gidan mu yana fito muna da kayan
mu don kayan ya dan bata muna lokaci har muka kai wanan lokacin.

Shi da kansa yayi dakon shiga muna da kayan cikin gida sukazo taron mu a cikin murna bakin Abuja an
dawo asmau sai yauki take masu da iyayi.
Wai idonane haka unguwar nan ya sauya sosai wallahi ko don yan gyare gyaren daya shane wai naga
wajen ya sauya min ?

Gyara duk garine gurare da yawa anyi wanan gyaran gwaunati tabada kudi akai yan gyare gyare don
cutan cizon sauro da yai yawa yanzu Auwal ya bamu amsa.

Mukai sallama dashi ya tafi muka shiga ciki Ammah na zaune tana tsifan kai tana muna sannu da zuwa
muka amsa nan aka zube asmau ta hau basu labarin da jirgi muka tafi muka dawo ba a mota ba.

Sun karyata,tane da farko saida na saka baki ina fadin ba karya bane hakane dama naki fada matane
sai da muka isa wajen .

Wayan mamane ya shigo tana tambayan mun isa lafiya ya mutanen gida nace duk suna lafiya ga
Ammah su gaisa ma?

Bayan mungama na kashe waya na mike ina fadin yau kan nan zai samu kitso ke nan Ammah tace ke
dai bari wai wata sabuwa jiya in kinji yadda mahaifin ku ya matsa min kan na tsefe kan nan kuwa shine
yau dai na tsefe ban iya jidalinsa nan ?

Dariya nayi ina fadin ai Abbu nada gaskiya kanki fa ya kai wata biyu ko ukku wani wata uku shekara dai
samira ta fada.

Na harareta ina fadin lokacin datayi kitso kina ina ke maman Aimanace ke mata kitso duk sati kuma ga
suma ba irin kanki ba.

Dariya ta somayi tana fadin ai abunda na gani zanyi amfani dashi wari ne ya ishi baban kano yace ta
banye kan kowa yaji iska ta nunani tana fadin ko kan uwarki baikai nawa samun gyara ba

Itace bata son kitso gata nan nayi dariya na nufi daki na shiga da yake da Asmau mukai wanan tafiyan
sai ban samu dskin a gyare ba yadda take min duk da baida wani gyara ko a hakan ?

Kewayawa nayi na fito na dan kai kwance ina faman tunanen yan abuja dana baro tare da kewansu
ban tashi ba dan barcine ya daukeni sai karfe uku da wani abu.

Gani dai kwance nake amma ban tashi ba hayaniya na soma ji kamar muryan Ammah saidai abinda take
fadane ya daure min kai don sunan da take kira din da Nana wai ko ba nace nake gani ba a nan ?




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[10/12, 9:47 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

6️⃣9️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




A hankali na sauko saman gadon na nufo falo ina kara jin sautin muryan Ammah din na fadin Nana ta fa
wai ko idona dai ke min gizo dakene wai ?

Itace mana dai gata kuwa kina gani tare da yayan ta kuwa ki natsu mana kina Abbu kamar wace ta tabu
kuma ?

Muryan Abbuna ne ke fadan hakan yasa na karasa fitowa daga falon saidai ban sauka a kofan ba don
mutanen dana gani din a tare da ita ?

Nana ina kika shiga haka tsawon lokacin nan munyi kuka har mungaji kin tafi kin barmu a cikin zullumi
a kanki nana sai kuma naji Ammah din ta fashe da kuka.

Tsab na kalle hamshakiyar matar dake rugume da Ammah tare da yaran da nake saka ran yayantane a
lokacin sai kawai na juya zuwa cikin falon da niyar shiga.
Nanata bakiga baki garemu ba gidan zaki koma ciki baku gaisa ba muryan Abbune yake fadan hakana
yasa na dan tsaya saida na hade abinda naji ya tokare min zuciya lokaci guda na dan juyo ina fadin
nagansu Abbu tare da dan waigawa ina fadin sannu ku na fada a cikin wani kasalalen murya mai kama sa
kuka ko dole akasani fada a lokacin.

Wanan mutumin da nagansu tare baiyi kama dana jikin photon dana taba gani akace mahaifinane ba
amma sai faman mutmushi yake a fuskanshi.

Gashi gaba daya wajen anzubo min idanu dani dasu sai kawai na juya zuwa cikin dakin kai tsaye abina
don ban gama tabatar da ita din bace ko watace.

Ko kuma mafalkine yazo min nakeyi nake ganin kamar a gaskene dai abubuwan ke faruwa haka
komawa nayi na kwanta rigingine idanuwana sun kada lokaci guda sunyi jawuri dasu.

Ga wani kukan tashin hankali da sukeyi harda anty safiya dake nata kukan munafunci wai na zuwan
nana din sai kace anyi masu mutuwa a lokacin.

Niko sai naji zuciyana yana kara bushewa da kangarewa banda idanuwana da suka kada sukai ja jajir
dasu ina kallon siling din dakin .

Motsin mutum ya shigo dakin naji amma ban motsa a yadda nake ba muryan Asmau naji dake fadin
mummy ashe mahaifiyarki ce tazo tare da kannen ki ?

Dan Allah dai na fada ba tare dana ko motsa a yadda naken ba sai ta kalleni cikin mamaki yadda na
basar da zancen.

Allah mummy wace ta haifekine akace da yaranta tare da mijinta yanzu mama ke fada muna muma
muna mamaki taji banyi magana ba ta kai zaune tare da zuba min ido na dan lokaci.

Can naji tace mummy tashi mana kije ki taresu da zuwa kada ace kin kyalesu hakan ba kyau aiba zataji
dadi ba itama idan kin sharesu ?

Amma Asmau a gabanku na gaidasu da zuwa ko wani irin gaisuwa akeson mutun yaiwa bako kuma
bayan wanan ?

Bakuwa kuma mummy wallahi ba zataji dadin hakan ba idan kin sharesu fa ta sake fada a dan mairace
tana bina da kallo ko zan daga.

Asmau kada taji dadi mana matar data tafi ko ta guduma zance ta barni nan dasu abbu don tana kunyar
haihuwana so kike inje in rugumeta don ta gaji da duniya ta dawo ?

Haba mummy kada ki dubi wanan ki dubi gir,,,, ke daga daga nan ki fice ki bamu waje Abbune naji yana
fadan hakan a kan mu yasa na yunkura na dan juya shima baya na bashi ban kalloshi ba.

Ina jin fitan Asmau daga dakin tsawon dan lokaci banji motsin kowa ba sai muryan da ban zatabane
naji a kaina sai lokacin kuma nake jin ashe ba karya hancina ke min ba a lokacin.
GF why doing this to your mum !

why are you showing her a hate rest like this is she not your realy mum ?

Ko motsawa banyi ba duk abinda yake fada baya sauke numfashi kince zaki karbi gift din da nazo maki
dashi da hannu biyu kince zaki ban kyautan akan gift din kyautar da zaki ban ke nan dama ?

Kut na hade wani malolon bakin ciki da zumar budan baki nace ya dauki kyautarsa indai natane na yafe
don harshi takaicinsa naji a lokacin.

Nanata wani irin shegantakane wanan zaki nunawa mutane ga uwarki irin tarbiyan da muka koyar dake
ke nan akan amanan data bar muna naki a hannun mu ?

Sakaiyan da zaki min ke nan a yanzu ki nuna baki kaunar ganin uwarki ko me wanan ai saikisa a
zargemu akan hakan da kika nuna din a gaban kowa.

Abinda naji Abbu yana fada yasa na dan dago a daidai lokacin suka karaso take fadin Abbu ba zan taba
zargin kaba kan yarka don bakai kayi mata hudu ban hakan ba ?

Ku kyaleta tayi mai isarta na san dama hakan zai faru a duk ranan da nazo tana fada a cikin kuka ya
kara fadin dole mana a dauka mune ke zugata tayi hakan.

Ina mindin,kis naki ko kara motswa a yadda nake sai kifewa da nayi ina kuka wiwi bakuwar muryan
mutumin nan na sake ji yana fadin .

Ku barta tayi kukan nan shine saukinta a yanzu daba somewa tayi ba a yanzu din don irin hakan yana
jefa mutum a wani hali wani lokaci.

Amma Alh ai ban dauka yarinyar nan zatayi haka ba a irin ranan nan daya zamo na farin ciki a garemu
baki daya ranan da muka dade muna jira yau Allah ya dawo muna da yar uwarmu gida haka ?

Dan magana nake ji sunayi kasa kasa kukan da nakeyi bai bari naji me suke fada daga bayane naji dakin
yayi tsit a lokacin a zatona kuwa ya fitane sai kamshin su da suka bar min a dakin na dan motsa kadan ina
gyara kaina nake fadin a cikin kuka .

Na tsani kaina a yau matar da tayi silan zuwana duniya ta kawoni nan ta watsar dani badon Allah ya
hadani da Abbu da Ammah ba waya san inda rayuwana zai tsaya.

Duk da hakan ban tsira wajen zagi da cin fuskan mutane kamar nice abin kyama ta farko kosu iyayyena
irin bakin cikin da suka gani a kaina suka hadiye aiba kadan bane yanzu tagama cin duniya sai yanzune ta
tuna dani.

Innalillahi naji muryanta a bayana tana fadan hakan yayin da lokaci guda naji yace dani

GF stop it please ? Ya fada da dan tsawa .

Can yaci gaba da fadin don,t ever repeat this again .
No ka kyaleta bashir komai tana iya fada a kaina yanzu tunda bata san komai ba game da niba ba zata
daukeni matsayin uwa ba a yanzu.

No ta daina in ba haka ba na zare hannuna ga komai naki ya fada tare da ficewa dakin har yakai kofa
yaji nace inba raina zaka zare ba aida sauki.

Matsalan ka ko nawa wani irin juyowa yayi tare da zuba min idanu na wani dan lokaci kafin naga ya
juya ya fice daga dakin.

Kaina naji ta dafa tana shafa take fadin kiyi hakkuri banso hakan ba nima amma kuma haka tamu
kaddaran tazo muna ta mike ta fice daga dakin.

Ina jin fadan Ammah a kofana sai kuma ta juya bata shigo ba bandai daga ba ina kwance a yadda nake
har lokacin.

Babu kuma wanda ya kara leko dakin nawa hakan yasa na samu lokacin kaina ina tunane wai yau wace
akace itace mahaifiyata wai itace a gidan mu.

Zuwanta bashine gatana ba ai ingata tare da mahaifina ko inga mahaifina yazo da sunan shine
mahaifina don akanshine ake min gori.

65 / 109