Chapter 64 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   64 / 109

189K to 192K   out of 326.5K words

banda
dogon motsi man ya sani yanzu zanceb abujan nan banda yan gidan mu ba wanda yasan da zancen
tafiyan nan amma wai man yaji zancen nan saboda Allah fa ?

Dole akwai wanda yasa ya saka maki ido either a cikin gidan nan ko kuma nan wajen gidan ku amma
akwai dai man ya wuce yadda kike tsamani din nan Aisha.

Shi mutumne mai ba abinda ya dosa muhinmancu sosai kina a ransane dole akwai abinda yake so a
rayuwan ki yasa kike ganin hakan daga gareshi.

Me yake nema a wajena Auwal don Allah ka taimakeni ka tayani fahintar hakan na kasa gane wanan
abin duk wanda yaga yadda muke da man an dauka soyayya muke dashi wanda ba haka bane kuma a
zahiri.

Kinsan takon manya basu dogon motsi fa hjy Aisha komai a cikin tako sukeyinsa da yana zuwa nan da
kansa da yanzu gari ya gama dauka akan zancen ku.

Haka kuma da wallahi tsawon dadewan nan da kukayi a tare ina mai tabbatar maki da yanzu baku tare
dashi saboda tsegumi zaiyi yawa akan ku har ku rabu.

Amma hakan yafi kema kin iya rike sirine da watace da yanzu tana faman yadawa a gari ko don a sani
amma kin iya kinja bakinki kinyi shiru kin kyale kowa.

Abinda ke cin wasu matan ke nan a yanzu yawan surutu ko dan uwankane yanzu kana fada masa
magana zaka jishi a waje.

Gaskiya ni bansan komai ba amma abinda na sani kuma na kula dashi shine ke din ta musanmance a
wajensa gaskiya.
Dan kallon harara nayi masa yace wallahi hakane kina da muhunmanci sosai a wajensa shine abinda ni
nafi yarda dashi kawai .

Nashigo nake fadawa Asmau labarin abindake faruwa itama din mamaki tayi a ina yaji zancen nan kafin
tace.

Baban kano ya fada mashi ke nan ko don inba baban kano ba banga inda zaiji wanan maganan ba
gaskiya koda kuwa shi aljannine.

A lokacin sai ban yarda ba saima naji haushin Asmau din nace mau banson tsiya fa Abbuna ne marainin
ku ko shi kika mayar dan gulma ?

Tana dariya tace Allah mummy kada kiyi mamakin hakan idan bashi ba a ina zaiji cewa zakiyi wanan
tafiya don Allah ?

Shiru nayi ina tunane me zai hada Abbu da man haka har ya dinga fada mai duk wani abu daya
danganceni yanzu kuma ?

Amma kuma biri yai kama da mutum fa zancen Asmau akwai kamshin gaskiya don ko lokacin da nayi
ciwo inba Abbu ba waya sani ko su maryam da muke tare basu sani ba.

Amma sai gashi kamar aljanni yana tambayana yaya jikjn nawa yanzu kuma jiyane fa mukai wanan
magana amma wai ace man yasan da zancen to a ina in ko ba wajen Abbuna din zaiji ba ?

Innalillahi na fada kafin nace meya hada Abbu da man kuma Allah ya ceceni da wanan zargin inko
Abbune dole gaskiya in san dalilin halakarsu din.

Sai banji dadin hakan ba har kasan raina son a gaskiya ba dadi me zai kai Abbu yin wanan katobaran a
yadda nasan sa nasan halin Abbu kuma ?

Zuciyana taban amsa da kudi ni kuma na karyatata nace kai ina kudin me can Abbu ba zaiyi haka don
kudi ba kan saidai don wani abu dai.

Tunda suka zauna gaban abincin yake satan kallonta ya kula bata taba ko cokalin abincin ba balle taci
zaune dai take tayi tagumi da hannayenta biyu.

Maman umar lafiya kike kuwa a yan kwanakin nan bakya son cin abinci meya sa hakan ne wai ko garin
ne bai karbeki ba mu koma ?

Mu koma fa kace dani shek yace ehh mana idan gidan bai maki ba ko ?

Umm,humm kana da gaskiyar ka tunda munzo kaga iyalinka da yan uwanka da kowa naka dole zakace
mu koma ni nagaji wallahi nagaji da wanan abin yau gun yan uwana nake son zuwa kaji.

Ke da kanki kike fada min hakan maman umar dole in fada ban gane me kuke shiryawa ba haka yau
kwanan mu nawa a garin nan wai ?
Tun ina saka rai har na kula kuna shashantar danine kai da yaron nan Bashir abin ya isa haka ina son
ganin yan uwana nima hakana ?

Yan uwanki ko yarki kike son gani ya fada yana mai kasheta da idanuwanshi itama dagowa tayi ta dan
zuba mai ido kafin ta dake tace dashi.

Ko itace nake son gani a yanzu hakan laifine don Allah nayi masu adalci ke nan daga ita har marikanta
wanan shine adalcin da zan masu saboda Allah ?

Ina gari tsawon mako biyu ke nan Amma ban nemesu ba su san da na shigo garin nan ko su san inda
nake ?

Na tabbatar su da sun san ina garin nan da malam mijin yaya ya nemeni a yanzu duk inda nake ko ?

Yar tawa ce ke exam da farko yanzu kuma tagama zata tafi abuja a goben nan tafiyan yana cikin tsarina
don Allah sai kiyi hakuri zuwa jibi idan ta dawo.

Kallon ashe kai kasan komai game da ita nice kuka mayar shasha ke nan sai kawai ta mike ba tare
datayi magana ba zuwa dakinta .

Nan suka hade da hindu data shigo gidan cikin wani shigan banza a ganinta wai hakan wayewane sama
sama suka gaisa da matar uban ta shigewanta ta barshi tare da yaransa a falon.

Tana tafe tana waigen matar mahaifin nata wanan matar akwai dan banzan kyau da diri ta fada dama
ace yar hannune mu jona da ita kafin tayi sabbin kamu a nan.

Muryan uban ne daya bita da wani irin kallon takaici yake fadin ke kina da hankali kuwa ina kika fito
haka kika ratso mutane ko kunya bakya ji ?

Wanan shiga naki dake da wanda take tsirara duka dayane a wajen mutane karna koma ganin wanan
shigar banzan a jikinki ya fada a fusace saida sauran yaran suka kalloshi.

Fuska ta bata kafin tace dashi ina kwana don tana son kudine kayan mayenta sun kare ta buga ta buga
bata san inda zata samu ba.

Da me zai kawota wajen shima mutumin dayasa uwarta kwanci ciwo kuma ko a jikinsa har yau din nan
bai tambayi jikinta ba ko ina take me zatayi dashi yanzu.

Indai badon dollars din da take hango kwancinsu a wajensa saidai na hanane kamar yadda uwarsu ke
shan fada masu baida ungo saida dalili kuma har yanzu da alama halin nasa yana nan masa.

Don duk zuwan da takeyi har yau bai taba dauko ko kwandala ya mika mata ba duk tana ganin yadda
abubuwa ke tafiya dama ita ko zuwan mummy Nasarece ta matsa mata har ta kawota inda take suka
gaisa dashi.

Bai nuna wani jin dadin ganin ta ba saima hiransa da mutanen da suka sama a tare dashi lokacin daya
cigana da yi ya fita batunta.
Dan dama matar nasa lokacin da suka shiga ciki mummy Nasare tayi mata bayanin ko ita wacece ta dan
nuna kulawanta a gareta a lokacin.

Itako sai binta take da kallon mamaki yadda balarabiya ta samu waje ta murje haka ga gwal a hannu da
wuya da kunne kamar zasuyi magana.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[10/9, 9:31 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:




JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

6️⃣8️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Sunji dadi sosai da zuwan mu Abujan ranan wuni da kwana mukayi ana hira dani da anty hafsat da
Addah yazid ne ban samu a gida ba wai yaje yobe tare da mahaifinsu.

Adda ke min hiran daddy su tun wancan zuwan mu dasu wajansa ya sauko yanzu sosai hankalinsa ya
dawo ga italinsa kuma.

Har suna saka ran zasu koma da aurensu da mama ita mama dince bata yarda ba amma shi daddy ya
turo Addah ke fada min hakan.

Allah sarki mama data yarda ko ba abinda yafi dadi ga mace tana zaune da iyalinta a wuri daya ga kowa
nata amma wacan mai diya biyun ai shanmantaku takeyi a yanzu.

Allah dai ya barki yar nan nima abinda na fadawa maman taku ke nan taki yarda kin santa da dan
banzan taurin kai yaya zaiyi ya rabu da wacan a yanzu bayan sun kai ga iyali da ita.

Ko itama tana son alhaki hakan ya kamatane yadda waccan tayi da ita yau gashi duk abinta dai mijin ya
dawo yana dodofa a gareta kuma ba mamaki anjima kadan ki gashi gidan nan hjy inna take fadan hakan
cikin takaicon yarta watau hjy mama din ta Abuja kamar yadda nake kiranta dashi a bakina.

Mama tayi hakkuri a yanzu meya rage kuma banda hakkuri ta sake tareni da fadan hakan akan
maganan dana dauko.

Asmau dai tana gefe ta zamo bakuwa a cikin mu babu abinda zata iya tsoma bakinta acikin zancen da
akeyi don ya girmewa shekarunta zancen.

Anan mama ta dawo ta samemu don bamu sameta gida ba a lokacin ta riga data fita wajen aiki lokacin
da muka iso din.

A,a a,a wai yata ce nan ban ganeta ba ko idonane yake min gizo nayi murmushi tare da mikewa zuwa
gareta ina jin shaukin uwa a jikinta .

Don ina jin dadin yadda matar ke min wani lokaci bilhaki take nuna min cewa itace ta haifeni babu ban
baci tsakanina da yayata.

Kinyi kyau my daughter anya anya kuwa sai kuma ta kara dagoni tana faman murmushi kunya naji na
kara fadawa a jikinta ina fadin.

Mama exam fa na kare last two weeks aiko na fada jan hannuna tayi muna zama take fadin Allah kin
sauya sosai daughter .

A,a ta canza mana inna ta fada na juya nace inna ke kina ganine ni ina can hankalina ya tashi naji inna
ba lafiya uwar dakina zata tafi.

Ina zata tafi kuma hafsat tace wuein zuwan kowa mana tunda lokaci zuwanta yayi sai inna din take
fadin ko zan tafi saina dauki abokin rakiya ai.
Aka kwashe da dariya ina mai matukar jin dadin ahalin nan sosai wallahi ayi wasa da dariya aso juna
tankar ba za a rabu ba.

Mama ta kalli Adda tana fadin Adda har kin dora girkine yau fa kinsan diyata tana gari dole abin dadi
zaki girka masu .

Kafin kuma ta juya gun Asmau da tunda suka gaisa bata kara wani magana ba tace boyar Allah yi
hakkuri kinji na shagala naga diyata na barki.

Kece wa ke nan kinsan ba sanin ku nayi ba saidai mu gaisa a waya nace Asmau ke nan mama au Allah
sarki ta mika mata dukka hannayenta biyu alama tazo gareta.

Hakan tayi ta taso zuwa ga mama din ta rungumeta tana fadi ma,una Allah sarki yarinyar kirki duk
mukai waya da daughter sai naji kina fadin mama ina wuni sannu kinji injin an kare karatun ko ?.

Take fadin da saura mama yanzu na jona health ina karatu can mummy ta zaba min tace amma mamaki
tayi maki zaben kwarai kuwa fanin lafiya ai yana da kyau sosai wallahi.

Gafa uwar nata a kusa dake mama kinsan Aeesha kanawar mamansu ce ita take nufi da mummy ba
wata ba.

Au wai kece take nufi dama to Allah yai maku albarka baki daya don ko kin taimaka sosai wallahi gara
da kika jona ta da health deparmenta.

Ankai wani lokaci ana dan fira kafin mu shiga kitchen muna taya Adda aiki wanda karshe muka barsu
da Asmau don kaina dake min ciwo.

Magani anty hafsat ta karbo min wajen mama nasha na dan zauna falo muna hira da ita don magariba
ya kawo jiki a lokacin.

Sai bayan sallah isha,i mama din ta sake fitowa aka dasa wani hira nan hafsat ke fadin ato dakina dai
zasu sauka nasan inna da rigima haka wancan karon tasa Aisha sauka dakinta.

Ai kin makara don Aisha har ta gyara muna daki tun zuwanta saidai kija wanan yar taku ku karata da ita
can amma ba uwata ba.

Sai sha biyu da wani abu muka kwanta ranan washegari kuma mummy sai sha biyu mama zata fita
hakan yasa ta aiko aka kirani na sameta a dakinta.

Waje ta nuna min in zauna take fadin an dai karasa karatu ko nace wallahi mama tace to maddala Allah
yasa anyi mai amfani na amsa da amin.

Yanzu kuma sai jiran sakamako da fatan aiki me kyau sai nayi murmushi kawai ban bata amsa ba kafin
ta dan kawar da takardan dake gabanta tana fadin .

Wajen iyayyenki dai shiru ko a take dan fara an da nake a fuskana ya bace na hade raina taji shiru ta
dago tana fadin ko angasune sunzo.
Na dan yi murmushin yake ina fadin mama ni na debe rai da ganin su don ban sa zasu taba tuno dani ba
a cikin duniyan nan balle suzo inda nake.

Subbanallahi haba dai haba daughter kin taba ganin inda ka haifi da ka koma kinsa wallahip duk inda
suke kina ransu sosai ma kina ransu lokacin haduwan kune kawai bayi ba inji Allah.

Ki sawa ranki hakan dole wata rana zasuzo gareki indai muna raye zakice nace haka kuma ki kyautata
kyakyawan zato a garesu kinji daughter.

Iyayyenkine fa duk ranan da Allah ya kawosu gareki ina mai rokon ki da kada ki yarda ki nuna wani
abinda bai dace ba a zuwan nasu.

Kutt na hade wani malolon bakin ciki daya tokare min zuciya lokaci guda kan dauko wanan zancen da
tayi a gareni..

Aisha kina jina ko din Allah duk ranan da zasu baiya a gareki ki zamo mai da,a da biyayya ga iyayyenki .

Kada ki yarda fushi da zafin zuciya su jaki ki aikata wani abin asha a garesu ko yayane iyayyenkine su
sanan baki san uzurinsu ba Aisha ?

Baki san me ya tsayar dasu tsawon wanan lokacin ba basuzo gareki ba har wanan lokacin kuka na fashe
dashi tace a,a daga magana sai kuka haka ?

Ai sai a dauka nayi maki wani abin ne anan ki zamo me juriya da biyayya don hakkin iyayye nauyi garesa
a minzani.

Bar ganin sun barki sun share na tsawon lokaci ki dauka basu kaunarki ne yasa hakan a,a na tabbatar
da kina zuciyarsu sosaima kina ransu.

Kawai ki dauka kaddaran kune kawai a hakan haka ubangiji ya tsara maku daga ke harsu din da cewa
zakuyi rayuwa a mabanbanta wajene.

Idan kinyi hakkuri kin dauki hakan sai kiga Allah yai maki sakaya da mafificin alherinsa ki daina kuka
addua ya kamata ace kinyi a yanzu.

Allah ya baiyana maki su a cikin sallama su ganki suyi alfahari yau da abunda suka haifa din su godewa
Abbu da Ammah da rikon da sukai maki na amana.

Duk da basu da abinda zasu saka masu dashi wallahi dayafi addua a yau koda kuwa sun basu rabin
duniyan nan rike dan mutum akwai nauyi da wahala ba kowane zai iya zama da dan wani haka ba tsakani
da Allah.

To amma ta yaya zasu gane hakan dole ta wajenkine zasu gane kedin kin taso a cikin tarbiya da da,a da
mutunci ga irin halaiyan da zaki nuna masu yanzu.

Na dago kai na dan kalleta tace wai ina nufin duk ranan da Allah ya kawosu gareki don dole suzo din
dole su nemeki Aisha dolene.
Ta kare da fadin ina Asmau bata tashi ba har yanzune nace ta tashi mama tana waje tana gyaran wajen
gida tun dazun.

Kin gani ba wallahi dattijan nan sun baku tarbiya maikyau da akeaon diya mace ta taso a cikinsa ko yaya
gidansu yake kuwa ana son ya mace ta saba da yan aiyuka irin haka ?

Don ba,a san inda rayuwa zata kai mutum ba wata rana in ba rai akwai mutuwa haka kuma ko ana tare
din akwai jerabawa rayuwa.

Amma ka sabawa danka dadi da wahala yasa ba ko yaushe jin dadi yake ba saidai uwayen yanzu bamu
gane hakan akan yayan mu.

Muna ganin kamar koyawa yaro jin dadi gatane bamu san muke halaka kan mu da kan mu a nan .

Tazo don Allah ta karya kada ta biyewa aikin gidan nan don ba karewa zaiyi ba jeki ki kirata tazo ta
watsa ruwa ta karya ta kara fada min.

Nace to mama a sanyaye na mike har nakai kofa tace yau zaku komane nace banda gobe da safe take
fadin a,a a da sauri haka ?

Na dauka zaku kai irin wata biyu ko daya din na ai a nan nace a,a jibi zamu koma a raina nace nida
keda uban gaiya ina naga kai wanan kwanakin ?

Amma a fili dan murmushi nayi ina fadin kwana biyu abu ya bamu muyi mu koma tace aiko hakan mun
gode zaki leko gidan yayan ki ko wanan karon ?

Da sauri na gyada kai alaman a,a na fice tana min dariya na samu Asmaun ma tagama ta shigo suna
magana da Addah a falo nayi mata sannu da aiki nake fada mata mama tace taje tayi wanka tazo a karya
ta amsa da to tashige.

Munyi wanka aka fito aka karya kafin yazid ya kira waya yana rokona in bari ya dawo don Allah kada
mu tafi don mum ta fada mai wai kwana biyu zanyi kawai a abujan.

Na dai ce mai naji muka danyi hira kafin muyi sallama mun fita ranan mun kumayi sayayya sosai da
zamu gida dashi ina mai jin haushin takura min da man yayi na tafiya da jirgi babu halin yin wani tsaraba
sosai ke nan a gareni.

Washe gari kuma tare da mama din muka fita acewanta zata saya min abune aikuwa kaya na alfarma
masu tsada na samu har asmau ma aka labata ta samu nata rabon a aciki sai murna takeyi.

Bata barni hakan ba sai hannuka mai sanda da take min tana kara lurar dani hanya kada in yarda inyi
wani batanci akan kowa balle iyayye ta nusar damu darajan da iyayye suke dashi ga yayayensu.

Duk da kusan komai data fada nariga da nasani a baya amma dai nasihar nata yayi tasiri a zuciyana
lokacin har nake jin wani iri a raina.
Mun dawo mun samu su yazid sun dawo daga tafiyan suna sauke tsaraba daga

64 / 109