Chapter 103 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   103 / 109

306K to 309K   out of 326.5K words

8:52 Safiya] Seenabu Makawa:




JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Shiga muje na fada don karta tsaya bata muna lokaci a wajen don yadda naga tana murnan ganinshi kar
tazo ta sake layi a gabanshi ta fadi abinda ba daidai ba a gabanshi.

Ashe ban tsira ba don ko tana zama naji tana fadin daddy naji dadin zuwanka wallahi bakaga dadin da
naji ba dana ganka ?

Murmushi naji ya dan sauke ita ko sai fadi take na dade ina son yiwa mummy zance a kanka sai nake
jin shakkun hakan sai gaka Allah ya kawo muna kai har gida daddy.

Kun dace da juna halin ku da ra,ayinku kusan dayane dama na fadawa su farida duk inda mummy taje
zaka nemota zaka zo ka dauki abinka gashi kuma hakan ya tabbata.

ASMA,U na kira sunanta da dan karfi tare da dan juyowa ina fadin kina cikin hankalinki kuwa kokin fara
halin banzane ban sani ba ?

Halin banza kuma mummy wallahi dadin ganin daddy ya biyoki yasa na kasa boye farn cikina a raina
dole in nuna murnata a fili wallahi.

Saida ya danyi gyaran murya ya dan juyo yana kallonta ya soma fadin daughter na gode kwarai saidai
ganina da kikayi yau nazo in bawa mummyn nakine hakkuri saboda laifin da akai mata.

Subbahanallah laifi kuma ta fada a dan razane tana bin kowam mu da kallon mamaki yace munyi mata
laifi ko ince na mata laifi ni kadai ban fada mata zancen aurena da wuri ba saida taji a bakin wani.

Bangane ba daddy har an saka ranan auren ku da mommy mu bamu sani ba ko mai da sauri nace
enough Asmau meyasa kika faye maganane ke ?
Why please ban daukoki don ki dinga zuba haka ba control ba na daukekine ki rakamu yaje ya gaida
dadina yana company sa na karafa yau a can zamu samesa.

Kin zauna sai zuba shirme kikeyi haka don Allah ki kama min bakinki haka surutun yai yawa don Allah a
hasale nake wanan maganan dake nuna zalla bacin raina a fili.

Kada kikaga laifinta abinda take zato ta fada a fili wanda ba hakan bane a yanzu just be cool rashim
sanine yasa take fadan hakan ai.

Tana baya zaune sai raba ido takeyi a tsakanin mu ta rasa wanda zata tsayar da kallonsa a kansa daga
cikin mu don kanta daya daure lokaci guda.

Yaushe kika san garin nan haka Ayshaa yake fada cikin sallon kawar da bacin ran daya hango zaune
saman fuskana a lokacin .

Saida na dan juyo garesa na kawar da kaina da sauri don idonsa dake a kaina yana min wani irin kallo a
lokacin.

Murmushin dole na kakaro mai kama da yake a fuskana kamar dole kuma na bude baki ina fadin haba
dai yau da gobe bai bar komai ba ai yaya Man .

Bin wajen danake kokaein shiga yakeyi da kallo tare da dinbin mamaki kasan zuciyasa sai fadi yake
Ayshaa bazanbi taki ba tun farko abinda nayiwa gudu ke nan nasan halinku na larabawa.

Nasan dama zaki hadu da iyayyen ki irin hakan ya faru tsakanin ku sam ba zasu taba amincewa kiyi nisa
dasu ba kuma a yanzu.

Haka suke kamar zazzagawa ba kasafai suke yarda yayansu suje nisa da gida ba sunfi da son suga da a
kusa dasu ko yau yaushe.

Sai faman gaidamu akeyi a wajen inda hankalina a lokacin in yayj dubu ya daga sosai don a cikin wani
irin yanayi nake jin kaina.

Asmau dai tun lokacin bata kara wani magana ba haka muka karasa ciki da mota a lokacin naji tana
fadin wai dama da gaske abin nan da nake gani a cikin film akwai shi a fili haka motama saita hau lifter
zuwa sama.

Dagani har shi duk da zancenta yabamu dariya hakan baisa mun yi magana ba sai shinema yayi kokarin
fadin Asmau baki fita garin ke nan tunda kikazo ?

Ina zani daddy iyakata wajajen unguwar da muke zaune din nan nan kan nasan wurare da dama
gaskiya mummy bata faye fita ba kuma kowan mu yana gun aikinsa sai dare muke dawowa gida.

Tsayar da motar da nayi a hawa na shidda yasa tayi shiru tana bin wajen da kallon mamaki fita mukayi
muka muka nufi wajen lifter din da zai sadamu da inda mahaifina din yake.
Dan murmushi na sake kakarowa a fuskana ina fadin yau zakaga mahaifina bayan Abbu ba zakace shine
ya haifaniba idan ka gansa zalla rabone kawai ya gitta a tsakanin shi da ummu aka sameni na karasa fada
a daidai lokacin da kofan ya bude wurine mai tarin ma,aikata a wajen .

Yana kuma kula da yadda suke ban girma dukda dai gaisuwan na sallamu alaikum ne a wajen suna dan
buga goshinsu mai nuna Alaman amincin Allah ya tabbata a garesu.

Gaahi har lkacin basu bar gulma da mamakin kasancewana diya ga mahaifina ba wanda suke ganin
abin kamar a mafalki a wajensu.

Mun sameshi suna meeting duk da haka sanar mashi da zuwan mu baisa ya zauna har ya karasa
meeting din ba don yana matukar mutunta sha,anina a zuciyansa hakan yasa ya samu gurbi a wajena ba
tare da matsalaba nima ina matukar kaunansa a zuciyata kamar yadda shima yake nuna min kauna da
damuwa da kulawa irin ta mahaifi.

Wanan yasa na dauko man din zuwa garesa a yau don ban boye masa komai game da man ba tun
zuwana da yakan jani da son hiran yadda rayuwana ta kasance a Nageria a baya.

Ban san meyasa Abbina ke son wanan hiran ba don ko da yaushe ina kula yana jin dadin in dinga bashi
labaran rayuwata a Africa ko yaga nayi irin dressing din su sai na dinga ganin farin ciki a tare dashi a fili.

Yana fitowa yai muna sallama muka amsa a cikin irin yanayin maganansu da dan sauri,sauri kafin ya
mika min hannunsa na sumbata don neman albarkanshi a gareni kamar yadda al,adansu yake dai .

Hannu ya daga ya gaida Asmau don ita din ba muharraminsa bace ai yasa ya gaida ita da hanka ya tako
tako biyu ya mikawa man din hannu sukai mubayi,a irin ta musullunci a tsakaninsu.

Daga Nageria ko ya fada na amsa da larabci da fadin Abbi shine mam bashir da nake fada maka wanda
ya taimakawa rayuwata har nakai haka a yau wanda kuma har yanzu a cikin taimakona yake din.

A yau yazone ya sanar min da zancen aurensa daya taso Abbi wanda abin yazo min a bazata bada
tsamani ba.

Duban man din yayi kafin ya mika masa hannu zuwa juya harshe a cikin turanci yake masa murna da
samun karuwan da zaiyi din ya dora da masa godiya kan irin taimakon da yai min a baya har lokacin yana
rike da hannunsa don girmamashi a wajensa yadda sukeyi.

Abbi kana masa godiya haka yarka yaki aure zai auri wata abinda ke yawo a kasan zuciyana kenan a
lokacin yasa na kurawa hannayen nasu idanu.

Man namijin duniya kamar ya karanta zuciyana sai naji shi yana bawa Abbina hakkuri akan rashin sanar
damu da baiyi a cikin lokaci haka kuma Abbi ya ban hakkuri kan yadda abin ya faru shima bai san da
hakan zai faru ba yake fada.

Nan Abbi din da baisan kaiba ya dafashi yana fasin wanan ba komai bane ya zama strong ya dubi
iyalinsa yanzu wani girma da nauyine zai hau kansa.
Har gobe yana bakin ciki da shiga damuwa da rabuwa da ummu da kurciya yadebeshi yayi a lokacin
yana jin bai muna adalci ba a rayuwansa yana tunanen ta ina zai sakawa Ayshaa a rayuwanta da zata iya
fahintar bai watsar da ita a cikin duniya ba ko ya wofintar dani.

Duk da Allah ya tsaya min yakawosu a rayuwana basu barni na wullakanta don banda uba ba.

Ya karawa man din godiya tare da fatan alheri sosai na kuma ji dadin hakan da yaiwa man din inda yake
fada mai zaiga sako daga wajena ya kuma gode sosai da irin kulawan da taimakon da yai min din lokacin
da ban kusa dashi.

Saida mukasha ruwan shayin mai sanadarin ingantattun diyan icce kafin mu bar wajen mahaifin nawa
direct airport muka kaishi kai tsaye.

Mun jima acikin mota ba abinda yakeyi sai ban hakkuri a fakaice wanda hakan kamar yana kara zubawa
zuciyana fetur nake ji a lokacin.

Duk da nasan halin mutanen mu masu kudi da masu mulki kwarya tabi kwarya sukeyiwa diyan su a
yanzu sai kalilan ne sukan tsallaka su auri na kasa dasu .

Koshi sai ankai ruwa rana idan yaro ya hinjire macen ko namiji shine zasu yarda amma ba don sunso ba
da hakan anfi son dai ace dan wani da wani ko yar wance da wancene ai kowa ya nuna karyan arziki a
gaban duniya.

Abin takaici kuma yayan tallaka sun kasa hakkura da hakan yarinya tasan ba aurenta zakayi ba bata
mata kurciya kawai ya kawoka wajenta sai ka cika mata kudi ka rudeta dasu ido rufe zata yarda da
bukatanka kayi abinda zakayi ka tafi ka barta.

Ya Allah ka shiryemu a baki dayan mu Allahuma Amin inawa kowa fatan alheri irin hakan kamar yadda
nakewa kaina addua a kullum.

Tunda ya fita daga motar ba zance na iya daga kai na dubi inda yake ba don yadda nake jin kamar ba
zamu sake haduwa dashi ba daga wanan ganin da nake masa a yanzu.

Kamar ya san ina kallonsa har yayi tako zuwa uku sai kuma naga ya tsaya ya juyo zuwa inda nake ya
zagaya zuwa gefena hakan yasa yasa na sauke glass din dake rufe ina kokarin controling kaina daga jin
abinda zai fada min.

Ayshaa naji ya ambaci sunana cikin wani kasalalen murya da ban taba jin ya kirani dashi ba sai kuma
yakai hannunsa saman fuskansa ya dan shafo kafin ya maryar da hannayesa waje daya ya hardesu saman
kirjinsa yaci gaba da fadin.

Nasan banyi maki daidai ba don Allah ki gafarceni ba zaki gane dalilin hakan ba a yanzu sai nan gaba.

A zamana dake nasan ban taba furta maki kalman so ba a fili haka har Allah ya baiyana maki mahaifinki
kika dawo garesa a yanzu.
Enough yaya man Allah ya baku zaman lafiya na kuma gode Allah ya saukeka lafiya na fada da dan
karfi ina tada mota sai kuma na kasa barin wajen kaina kife wani kuka nazo min dake saka zuciyana wani
daci a lokacin.

Hannusa naji ya dora a saman nawa ya fara dan murzawa a hankali alaman bani hakkuri da kyat na
dago kai ina fadin fadin ba komai ya man kaje kada ka makara time din dagawanku yayi.

Bai iya yin magana ba sai kallon yadda nake faman jan maji saboda kukan da nayi a lokacin zamuyi
magana a waya indan Allah ya saukeka lafiya na fada ina tayar da mota.

Saida muka hau titi da kyau naji Asmau daga bayan mota inda take zaune har lokacin tana fadin kiyi
hakkuri mummy na fahinci abinda ke nan yanzu.

Ba komai Asmau abinda Allah ya rubuto muna ke nan a tsakanin mu muyi sabon da ba zamu kasance
da junan mu ba na hakkura da man daga ranan itayau saidai zumunci a tsakanin mu kuma insha Allah.

Gudu nayi sosai ba tare data farga da hakan ba saida taganmu a kofan wajen aikinsu na tsaya a nan
ma din kifa kai nayi sosai ina kuka sosai don ba zan iya controling din kaina ba a lokacin.

Yanzu ina zaki mummy muryan Asmauce naji tana min wanan tambayan da kyat na iya budan bakina
nace da ita ban sani ba Asmau sai naji tace dani muje gida kawai mummy .

Banki nata ba gidan na nufa dakina na nufa kai tsaye itace ta biyoni ciki da jakkunana zuwa dakin waje
ta samu ta zauna a bakin gado ta zuba min idanu kawai tana kallona.

Don ta rasa kalman da zatayi amfani dashi wajen ban hakkuri akan dan abinda ta fahinta a zuciyarta
game dani din da man a lokacin .

Don idan ba karya tunanenta ya bata ba hakan na nufin shike nan mun rabu fa rabuwa ta har abada
kuma dashi.

To ina matsalan hakan ya samo mafari take tambayan kanta da kanta matsalan abin dai ba magana
nakeyi ba balle in fada mata matsalan da muka samu.

Abune da idan da ba a gabanta abin ya faru ba zata iya fadawa maishi karya yakeyi don a iya sanina da
ita tazo kano ta samemu tare da man ne sai kuma a ce wai haka kawai yau mun rabu ?

Irin tunanen da take faman yi ke nan a zuciyarta har lokacin sallah la,asar yayi lokacin ne take fadin
mummy ki tashi kiyi sallah har la,asar yayi bamuyi azahar ba.

Na dan kai mintu biyu a wajen kafin in daga ba tare da nayi mata magana ba na shiga bayi don in
gabatar da sallah kodana idar na jima a wajen zaune.

Itace dai ta dawo dakin ta sameni saida ta zauna ta soma magana tana fadin mummy ki daure muje kici
abinci koda kadan ne.
Asmau bana jin cin komai a yanzu na bata amsa tace da dai kin daure mummy kada ki saka wanan
zancen a zuciyar ki don dai ke macece mummy.

Idan har da gangan sunka hana ya aureki da insha Allahu gaba dayansu sai sunj kunya tunda dai kina da
gatanki ai ya kwana gidan sauki don da ba yanzu bane balle suce don suna fadan baki da asalin da zaki
iya aurensa ne yasa hakan.

Murmushin dole na kakaro a saman fuskana na dan dago ina fadin ki manta da zancen kawai Asmau
wanan bashine na farko dana rasa masoyina ba don haka nasaba da irin wanan tun farko.

Amma ai yanzu ba da bane da suke fadan wai ke din baki da asalin da zasu bari yayansu su aureki don
yanzu kaf dinsu ba wanda yakai ki nasaban kwarai a cikinsu.

Kuma insha Allah idan kika tashi aure sai duk sun girgiza da mijin da Allah zai kawo maki mummy ni
yanzuma na gama tunane nake ganin mijin daine baizo ba kawai mummy .

Hakane wani lokaci munawa Allah shishigi a cikin lamarinsa sai muga kamar ya hanamu abinda muke so
a rayuwan mu wanda hakan kuma ba alheri bane a wajen karshe in mun nace sai munyi sai Allah ya
barmu da iyawansa.

Balle ba zan taba zama a innuwa daya da anty hindu ba a matsayin kishiyata muna auren miji daya
kawai dai sabo nakewa kukan hakan ba wani abu ba.

Don ko a gaskiya man bai taba furta min kalman so ba duk zamana dashi wanda bansan dalilinsa nayin
hakan ba alhalin nasan muna son da kaunan juna a tsakanin mu.

Wai wace hinduce kike magana ba dai wanan ta gidan su ummu din nan ba nace itace zai aura da wata
nake gani ban dai san ya zancen yake bane dai.

Wanan bakar matar dai da akace yar mijin ummu ce ita me daddyna zaiyi da wanan mace mai muni
sunan kawai tace ita amma bata kama da masu asalin sunan ba ai.

Murmushi nayi ina mikewa tsaye kafin nace su gidan sarauta ai nasaba suke jawa a lamarinsu bawai
kyau ba ko wani tsari .

Kaya na sauya muka fito falo ganin mu a gida dasu yaya Nazir sukayine ya basu mamaki suke fadin wai
dama kuna gidan nan ashe ?

Muna nan mun dawo tun dazun Asmau ta fada a kujerun falon inda muka samesu a na muka zauna
muna gaisawa dasu .

Ganin hankalina ya dan dauku a garesu yasa Asmau kara fadin mummy abincin fa bakifaci komai ba tun
da safe bayan shayin da mukasha wurin Abbi da mukaje dazun .

Ai kinsan shayin nan nasu yana da kama ciki sam banjin yunwa ko kadan yadda kike tsamani ai narasa
da wani irin sanadari ake hadawa Abbi shayinsa don daban yake da wanda nake sha a nan.
Wai yau kuje wajen Abbine kafin na bada amsa Asmau tace kallo ya wuce ku ai yaya Najib yau naga
duniya a sama abinda ban taba mafalkin ganin sa ba .

Nan tashiga basu labarin abinda ta gani wajen ina zaune sai murmushi nakeyi dadin naka a kusa dakai
ke nan yau ba don Allah ya ban hikiman kawosu a kusa dani ba yaya zanyi da zuciyana da wanan famin
da nake cikinsa a yanzu ?

Har jirgi ya sauka yana zaune kamar an dashi a wajen bai taba tunane ko zaton zaiga hakan daga wajen
Ayshaa ba yarinyar da a yanzu har shakkunta yake a idonsa duk mulkinsa da muka min sai gashi tayi
masa ba zata itace take kuka akansa.

Ma,aikatan jirginne ke sanar masu da saukansu inda kowa na cikin jirgin yake haraman bin umurnin fita
daga jirgin amma shi ko motsawa baiyi ba balle yayi niyar fita.

Muryan dan chainan dake kusa dashi zaune ne yake rokonsa daya dan daga zai fita sai lokacin
hankalinsa ya dawo gareshi.

Inda ya dan sauke ajiyan zuciya yana murmusawa tare da fadin yayi hakkuri hankalinsa baya tare
dashine a lokacin.

Da,kyar yaga ya isa gidansa don kansa dake wani irin sara masa a lokacin dama kukan ya samu yadda
yaga Ayshaa ta samu da zaifi mai sauki da wanan ciwon kan daya addabe tun bayan rabuwan mu din.

Saman kujera ya zube a nan falon tare da dafe kansa da hannunsa daya yana cigaba da tunanen da
yakeyi ya dauki dogon lokaci zaune a wajen hakana .

Wayansa yaji kira na shigo masa a dadafe ya samu ya daga kiran daddy ne ya kirashi da tun safe yake
kokarin kamashi da layinsa bai samu ba.

Yana dagawa muryan daddy din yaji yana furta Alhamdullahi ya dauka yanzu yaci gaba da fadi yau ina
ka shiga haka tun safe muna kiran layin ka baya shiga.

Kai tsaye yaba mahaifin nasa amsa da Dubai na tafi wajen Ayshaa daddyn yace Aisha kuma

103 / 109