Chapter 22 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   22 / 109

63K to 66K   out of 326.5K words

yanzu.

Ai kuma hjy naga koda ta kasance ba yar kowa bace indai tana da hali walillahi,hamdu inji daddy tunda
shiya ganta yace yana son abinsa ko.

Matsalan ku ke nan maza da kuma iyayyen yanzu son diyanku sai ya rufe maku idanu kan halaka baku
damuwa .

Haka kuma da zaran kuna son mace idon ku sai ya makance ku kasa tunanen abinda kaje ya dawowa
rayuwanku gaba sai idan kukai kwadan ku ya fada kuke komawa da kun sani wani lokaci hjy mai babban
daki ta fadi hakan ga mahaifinshi da yai magana yana kokarin kare yarinyar da take zance a lokacin.

Hjy naga in ma abinda kuke tunanene inhar hakan gaskiya ne meye laifin yarinyar a cikin zacen nan
tunda ba itace ta aikata wani sabo ba balle a kyamace ta ?

Kaiyya naka tunanen ke nan Ahmad na zata a shekarunka zaka san illan wanan abin a yanzu ba sai anje
ba wata rana me zaku fadawa yayanta idan ta gauraya daku ta haihu da danka ?

Hjy ai duk wanan abin baikai can ba ayi tunanen mafita a yanzu a gano ita din yaya take kafin a fara
tuna zurian da zasuzo gaba.

In ma har bata da gata aishi magaji sai yai mata gata Allah yai masu baki daya ina dama ko wani namiji
shine gatan iyalinsa dai.

Rufa min baki Ahmad da zancen kana banza na fahinci son dan ka yasa kana kokarin abinda zai zubar
muna da mutuncin mu da kimar gidan mu nan gaba .

Na fahinci Idon ka ya gama rufewa a yanzu kan son kai irin na nasara da ka koyo zamanka cikin su ni
zaka jawa abin gori cikin zuria ta don kawai kada ran dan ka ya baci ?

Ga yar asali jikan asali wace asali ya haifa ka tsaya kana son yiwa mutane wasa da hankali Hindu ce na
zabar masa ita kuma zai aura nagama maganata ta fada tana wani kaiwa kishingide saman tintin din
gefenta.
Mikewa man bash yayi don ya fice daga falon saboda bai iya jure jin zancen tsohuwar nan na shirme a
kunnuwansa donshi a shirme ya dauki duk zancen ta.

Har ya kusa kai kofa zai fita din yaji tana fadin kaje duk inda zaka magaji sai ka dawo nan ka sameni
indai nice.

Aure da hindu ba fashi tsakaninku don na riga dana yanke wanan hukuncin babu kuma mahalukin da ya
isa ya tayar da wanan zancen a cikin iyayyenka.

Har yakai kafa zai fita din ya juyo ya tsaya don jin abinda ta fada ya kalleta yayi murmushi kafin ya kara
tako biyu zuwa gareta ya nunata yana fadin .

Gara dai da kika gyara zancen ki hajjaju don su kika haifa ba niba ya nuna iyayyen nasa dake zaune a
gefe tsit kamar ruwa yaci su wajen.

Don sunsan kwanan zancen duk wanda ya motsa cikinsu zata hada dashine tayiwa mashi rashin
mutunci don haka kowa ya kama bakinsa yana kallon draman da sukeyi tsakaninsu ranan.

Akidan nasara kuma da kikace munayi ni da ubana yanzune zan nuna maki an haifeni cikinsu da nasan
akan wanan shirmen naki kika taramu don ki yi hakan wallahi da ban zan zo ba.

Haka kuma indai Bashir ne ki sani ba zan kara zuwa nan don ke ba bance gidan ba a,a nan dai matukar
kina raye a doron kasan nan mubar haduwa dake har abada tunda nagane son kai yayi maki yawa.

Don ko a cikin yayanki dukkansu diyan kine amma kina zabe a kina nuna masu son kai balle wani.

Tau ba zan dauki wanan ba zan kuma fadawa mijinki ya tsawata maki karo na biyu a kaina ko na dauki
mataki da kaina.

Ahmad's kana jin yankan kaunar da danka ke kallona yana min kuma a gabanku kuna kallonsa .

Ai basu sukace ki kirani ba kuma ban yake maki kauna da kikace na yanke maki a gabansu

ba, sai nan gaba .

In har kikai gigin daura min bakar yarinyar can da sunan aure zaku rainawa kanku wallahi.

Kai waye dan iska yaro me kake daukan kankane cikin mu Bashir hjy kura ta mike tana fadan hakan
gareshi.

Ta nunashi tace kana dauka kafi wanine a cikin mu nan kome hjy zata fadi magana ka ketare a gaban
mu ?

Har kana kokarin fadin maganan banza ko ita hindun ka fitane data yarda, saima ince taimakonka za ayi
har hindu ta zauna dakai ai

Ooh soryy aunts zancena da tsohuwar nan ne a yanzu ya shafeki ko don Allah kiyi shiru ba daku nakeyi
ba a yanzu ina zance da kakatace wanan da tayi zamaninta take son ta shigo na wasu nake magana ban
kawo gareku ba tukun ya hada hanayesa waje daya lokaci guda alaman ban hakkuri a gareta ya juya zai
fita.

Hakan yasa hjy kura fadin tabbas ya tabbata kana shaye shaye bashir wanan iskancin har ina kai kuma
yaya ka zuba masa ido yana ciwa hjy mutunci haka a gabanka ?

Babu mai kallon bashir ya kira sa dan shaye shaye yarki daice yar shaye shaye kowa kuma ya sani
wajen nan mami ta fada.

Shima saida ya kallo uwar balle su da suke ganin abin mamaki a yau don sunbar zancen bashir sun
koma mamakin mami da ko hannu kasa mata a ido bata taba cewa don me ?

Yau sai gashi a gaban kowa tana fada akan danta da akai wanan zaman donshi ba tsoro ko shayin idon
kowa ta tarewa danta fada karo na farko a rayuwanta.

Af hajiya yau dai kinji kin gani da idonki kuma hjy maryam tana kokarin kare danta ta aibanta min tawa
yar a gaban kowa.

A,a Kura inza a fadi gaskiya kowa yaji sanda kika fara aibanta mata da kafin ita dan galadima ya fada
don shima yana zaune tunda taron na dakinsune iya su kadai aka kira a lokacin.

Au kun yarda ke nan zaku hade min kai su aibanta mi ya anan a,a fa ya kara fada zaici gaba da magana
hjy mai babban daki tace kuyi min shiru don Allah da wanan abin kunya da kukeson jawo min a yanzu.

Duk wanan abin ke kura ke kika jawoshi bayan nagama magana meya kaiki tofa wani zance kuma a
baya koma meye yanzu ai yarki taja komai ta dauka duk tabar gazan da tayi a can wajen karatunta kafin
su korota ba a sani bane ?

Yanzu anbar kiwon dabbobi an koma kiwon mutane yan adam duk abinda kakeyi da masaniyar mutane
akanka don haka ku kama min baki anan.

A haka suka watse saidai ba a san a inda zancen hadin ya tsaya ba a yanzu don hjy kura ba kyalewa tayi
ba asalima tana ta faman shiri a bangareta yadda hjy Nasare ta kyankyasawa su umma labari.

Dad ya fada mai komai hakan yasa ya murmusa don tuno da rabuwan nasu da tsohuwar kakansa
fitinana tare da fadin trouble woman ya furzo da iska.

Kafin ya koma tunane anya hukuncin daya daukarwa rayuwansa yayiwa kansa adalci kuwa bafa Allah
bane ya haramta tsakaninsu camfi ne kawai na yan adam hakan.

Duk lokacin da irin tunanen nan yazo masa abinda yake tambayan kansa shine meye laifin irin yayan da
aka haifa ta wanan tsigar da sune ke ganin ukuban hakan a karshe.

Don gashi kai tsaye yarinyar nan take fada mashi bata da asali wani irin rayuwane wanan itama
mahaifiyar nata ina ta shiga ta gudu ta barta kamar uban.
Photon yayi zooming ya kura mai ido na dan lokaci kafin ya sauke wani irin zuciya acan kasan zuciyarsa
ya furta Allah ya zamo gata a gareku baki daya masu irin laluran nan shikan a nasa irin tunanen baiga
aibun kulla wani halakan arziki da irin yayan nan ba gaskiya.

Kamar yadda hjy mai babban daki da hjy kura suke kokarin kushe yar mutane akan asalinta duk da
basu san halakan dake tsakaninshi da ita ba amma su suna daukan hakan da wata manufa wanda bashi
ba.

Karshe dai haka kawai yaji kasala na sauka masa sai faman tunane yakeyi shi kadai a gida ya kasa fita.

Ranan sai ya ji gaba daya kasa fita ko ina abu daya ya tsaya mai azuciya shine zai taimakawa rayuwan
yarinyar nan kota halin kaka.

Kada ta nakasa tazo ta wullakanta a banza duk yadda zaiyi alkawari ya daukarwa kansa kan hakan tun
farko tun daga ranan da hjy umman su salman tayi masu sharhi akan irin yadda rayuwan hakan sukan
kasance a karshe.

Balle wanan din da yaga tana da kyakyawan niya zama abin kwarai a rayuwanta don haka yayi alkwari
zai taimaka mata tun daga wanan ranan sai daddy shine yasan wanan niyar nasa tun lokacin.

Bayan haka yana son ya taimaka masu ako wani bangaren rayuwa yadda iyayyen rikon nata ba zasu
taba jin sun gaza da ita ba irin tunanen da yayini yanayi ke nan shi kadai a gidanshi.

Aike kan muzo gidan Rabakaya tun aika Asmau da nayi da kudinsu na amarcin su ita kuma iyayi yakai
ta ga fada masu ba zan sake zuwa ba Abbu yace har dani don yawan takuran da saratu take min.

Shine hjy su Anty fati take ta min aike har wurin Ammah ayi hakkuri abarni inzo dan Allah amma naki
fita saida akai sallah azahar na shirya na shiga gidan a lokacin yana dam da yan buki .

Ko kwaliyana ma abin kallone ga mutane don haka na zamo masu abin kallo dakin hjy umma muka fara
shiga muka gaisheta nan take min fada da nan gidan mune saboda da saratu ba zan daina shigowa ba.

Karshe dai muka mike da wanan yar ta yaya habib data leke min tun shigowana dama suna falo ne ita
da uwarta dake kwance tana ganina tazo ta rikeni muka danyi hira da ita tana fada min sunan ta da
sunan makarantanta irin dai hiran yara.

Da zamu fita zuwa dakin amare kuma ta lake saita bini uwar tana riketa umma tace ki barta mana
yarinya nason bin yan uwa kin riketa ?

Idan ta zauna a nan wani abu zatayi maki ai gara dai tabisu taga gari tunda Aeesha ba bakuwa bace yar
gidace sam banso zuwa da ita ba yadda uwar ta kankame abinda cikin daki.

Amma maganan umma yasa na kama hannun yarinyar muka fita tare zuwa dakin amaren samira na
fadin walle da bakizo da yar shigiya ba ta rike kayan ta mana waddamu da ita ?

Ni dai dariya take ban haka muka shiga dakin yana dam da yan mata sun baje suna cin taliya group
group mukai sallama muka shigo.
Yauwa ga Aeesh din ina zubaida da tace bata gane Aeesha ba wai ita bata sanki ba saudat ta fada anty
fati tace da ita aiba kowa yasan Aeesha ko unguwar nan saboda basu wani dade da dawowa nan ba.

Ai yar gidan yaya Habib ce ashe saudat din ta kara fada wai ya akayi uwarta ta yarda ta biyo ku wanan
yar da ake rowanta kamar tafi kowa.

Sunga wace tafisu class mana wata ta fada kafin su fara min bissimillah muzo muci abinci ana faman
kus kus kus a kaina duk da gamu a cikin dakin lokacin.

Yauwa Aeesha zance dinner nefa akeyi kinsan wurin special ne ba kowane zai tafi ba ga yan gida sun
nace kowa na fadin shi zai tafi.

Zaune nakai ina fadin ai sunsan wanan ba tsarin mu bane gidan ango keda wanan tsarin don haka ku
kyale kowa kawai idan sunje an hanasu aisa dawo kawai.

Yau akwai butar kashi saratu ta fada daga inda take zaune tana fama loda taliyan a cikinta kai kanawa
akwaisu da son filawa Asmau ta fada.

Kuko dawo ko wata ta fada tace aigara dawo hatsina yana kara lafiya a jiki shiko filawa fa ko can dinner
kuka tai shi za a zuba kuyi ta kwasa daga nan in kunga taliya kun rude barauniya ta shiga harka ta hade
sarkokinku dana amarya duka ta nade tayi tahiyar ta kuna can kun rude kan hilawa.

Dan hausa ba haushene rabu da bassakwacen mutum duk abinda ka fada yasan mai kake nufi amsan
tabawa saratu a take da take fadin akwai kaza yau.

Nan sukaita cacan baki nikan surutunsu yana hawa min kai hakan yasa na riko hannun yarinyar nan
muka fito da maryam wajen gidan.

Wai bakizo da motarki bane maryam ta tambaya nake fadin haba dai nan da nan zan wani dauko mota
kuma ?

Wai me Asmau nan naku ke fadane naga saratu tayi shiru nace koma me take nufi Asmau ta fita
dabanci wallahi nima nan tsoronsu nake ji dukkansu biyun.

Suka kwashe min da dariya Aimana ke fadi nima nayi mamakin ganin yadda kuka shirya dasu yanzu
wallahi ?

Haba dai yau da gobe basai Allah ba ana waje guda kuma yan uwa sai tayi shiru bata kara tofawa don
ba zan bada kafan da zatayi tsegumin yan gidan mu dani ba.

Photo suka farayi da waya kafin nima in shiga muyi tare harma da wasu suna shigowa nayi da yarinyar
nan sosai don tana lake dani ko ina sau biyu uwar na turowa ana fada mata muna tare

Can naji wanan yar na kokarin fisge hannunta daga rikon da nayi mata don kada ta bace min a cikin taro
nawa ya sameni ashe babanta ta gani saida na waiga naganshi ya faka mota gidan massalaci yana zaune
a ciki abinka da naka wai har yarsa ta gashi ita.
Asmau nayiwa magana ta mikata wajen uban ta rikewa yarinyar hannu ta nufi inda yake tsaye takai
masa yarinyar nan yarinyar ke fada mai cewa tayi photo da sabuwar anty din can.

Nan ta dinga masa hira wai zatayi photo da uban dole yasa azo a kira mu sam ban dauka mu duka yake
kira ba saina tura Asmau taje.

Sai gata ta dawo tana fadin yace muzo na nuna kaina irin na mamaki kafin nace muje din a zatona zaice
wani abu ya faru da yarsu ne.

Saidai muna zuwa yake fadin tace kunyi mata photo take son nuna min sannu wazan baka so a jikinka
kaga murde muna kunnuwa yanzu zaka nuna muna son yar cikinka a fili na fada a zuciyana

Yar bakin nan Asmau ke fadin da wayan mummy Aeeshace akai mata photon kawo mu gani mummy
tana karba wayan a hannuna cikin zumudi.

Ba mus,su na mika mata wayan juyawa nayi na dan gusa nisa dasu kadan ina kallonsu don irin kallon da
yake min na fara tsaguwa da hakan tun farin ganina dashi.




ZAINAB IDRIS MAKAWA[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: M/C COLLECTION MAKAWA COLLELECTION
ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES, BAG, COTONO KAMFALA
COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER KIDS,FASHIONS etc

LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,



JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

3️⃣2️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1ftp




Wani gida babba mai kyau duk da ginan dane amma gidan ya tsaru iya tsaruwa don da gani ba sai ka
tambaya ba a zaman baya gidan na ciki jerin gidanjen da sukai tashe a garin.

Don yanayin ginan ya nuna hakan har yanzu kuma ko yanzu din ba,a canza fasalin ginan ba gidan yana
da dadin kallo don komai a tsare yake amma yasha gyara da kayan alatu na zamani ginan daine yan gayu
a yanzu zasu daukeshi a old mordel saidai ko yanzu din dubban mutane suna kwadayin ace nasune
wanan gidan.

Sannu a hankali wani babban mota ya tsaya a kofan gidan kafin a bude mutanen cikin motar su fara
fitowa a hankali.

Anty Ummi ce da yan uwanta ta kawowa kakanin nata ziyara kada ta koma ghana bata samu zuwa
wajensu ba shine dalilin fitowanta ta fara zuwa wajen kanwar mahaifiyarta mami suka gaisa daga nan
tace zata wuto gidan kakar tasu shine yaran mami din sukace suma zasuzo suka hade su hudu da yaranta
zuwa gaida kakanin nasu sai ince wanan ahalin sunyi dace da gadon tsawon rai don uwa raye uba raye
harda kakani tako wani bangare irin hakan dace ne da baiwa daga Allah.

Don ba kowa Allah keba wanan falalan haka ba wani ya taso ba uwan ba uba wani uwace kawai a raye
wani ko ubane kadai a raye wani kuma rabuwan aure yashiga tsakani haka zai taso koda suna a raye ya
koma kamar maraye haka dai abubuwan tsarin rayuwan sukan zo wa bawa wani lokaci.

Tosu wa yan nan ahalin har wace ta haifi iyayyensu din mata bata jima da rasuwa ba don a lokacin baifi
shekara ukku data rasu ba.

Tana tsaye cikin kulawa saida kannen nata kaf suka gama sauka a motan kafin su nufi cikin gidan kai
tsaye kharat ce tace ga sabbinani a zaure fa mu fara shiga.

Hakan yasa suka shigo ta kofan zauren gidan mai kama da falon mutanen da zauren babbane ga kujeru
ga fankan sama data kasa agefe daya.
Ga tarin littafai na addini gefe daya duk da kujerun dake akwai a falon ga shimfida irinta alfarma mai
nuna jin dadin rayuwa ga mutum inda tsohon ke kishingida ya huta ko yayi karatu saboda zama dake
masa wuya a yanzu don tsufa.

Sallama sukai masa cikin girmamawa kafin ya dago yana fadin su waye yana mai kura masu ido kafin
yace au yau kuce in shirya ina da baki tafe ai.

Suka kwashe da dariya kafin anty ummi din tace wai tsohon nan kana gani haka har yanzu yace ko zaki
ban aron idonki in kara da nawa nina fiki gani a wajen nan suka kwashe da dariya .

Kafin sukai kasa cikin ladabi suna gaidashi yayinda suka mike kuma suka dane kujerun aka fara jero
ba,a a tsakaninsu.

Mai karatu kada in kaiki nisa wa yan nan tsofin sune mahaifan iiyayyen su Man Bashir da Salma dasu
khairat su Ummi.

Na fada maki a baya ds uwarsu kharat da uwar Man bashir mami ya da kanwace suma asalinsu dai yan
bauchine mahaifansu amma zama ya mayar dasu yan asalin kano don kowa nasu na kano amma ruwan
fulanin nan yana yawo a jinin ahalinsu har

22 / 109