Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
sani ko mai ko wani abu akanku tunda bakya son mu sani to amma ina son ki
sank shi namiji ba ai mass haka tunda har yataso yazo inda kike balle iron wanan ma.
Don ba karami daraja da kima yake dashi ba a duk inda ya je cikin kasan nan balls har ya iya sauke duo
wanan girman kan nasa yau ya yazo gareki.
Quite sure koma meye matsalan nasan babbane amma bai kamata kiyi masa yadda kikayi din nan
agaban mu da gaban abokinsa daya dauko ya rakoshi nan.
MD dinku kanshi ba karamin mutum bane a garin nan ke kin sani balle shi mam din koda yake a yanzu
soyayya baisa ki gane hakan garesa.
Mama ba soyayya mukeyi da man ba mutuncine a tsakanin mu amma said mutanensa suka dauka
soyayya har yakai sunzo gidan mu sun samu iyayyena sun masu kashedin hakan a kaina.
Haka baisa na barshi dan wanan zancen ba suna kuma kan bibiyata mama suna aibantani tare da fadan
mugun kalamai a kaina.
Murmushi naji ta danyi da yasa na dan dakata ina dan kallonta da idanuwana da sukai ja a lokacin don
yanayin da nake ciki kuma nakejin zuciyana yana min suya.
Ina jin ki ta fada bayan haka mama ranan naga dan uwansa ina murnan ganinsa sai kawai ya dakatar
dani da fada main maganganu masu zafi na kwashe yadda mukayi na fada mata kaf.
Dan murmushi tayi tana fadin kaiya shiyasa wani lokaci dan adam kanyi sabo yace dama hannun agogo
zai dawo baya garesa ya gyara kuskurensa na baya.
To irin wanan kuskuren kike son aikatawa a yanzu son damane Allah ya baki nan Kansas ke kuma kina
son kiyi watsi da daman naki Aisha.
Kinsan meyasa na fadi hakan na girgiza kai tace yau ba iyayyensa ko wani Dan uwasa bane yazo nema
mass ke shine da kansa yazo gareki .
Duk da kince ba soyayya bane tsakanin ehh na yarda aje a hakan ba soyayya sai mutuncin din sai ki jira
kiji furcinsa ko wani halin da zai nuna akanki din kan hakan .
Sauda yawa mu mata muna tabka kuskure don karamin kwalkwalwan mu sai har damar mu ya kubce
muna wajen jan ajinmu na mata din.
Don haka shawara dake bada danginsa like taraiya ba dashi shi kadai kikeyi a yanzu koda ma ya
kasance Allah ya kaddara kin shiga gidansa da sunan aure ne inda zaki hade da dangin nasa sai ki shanye
komai a ranki aje a hakan.
Basuso shigan ki hurda dashi Allah yayi ba yadda zasuyi din dake kuma don haka nake rokonki da maza
kiyi saurin gyara kuskuren ki run dare bai maki ba tun yanzu.
Tafada main maganganu da dama kafin ta five daga dakin ranan ko abinci banci ba haka nakwanta da
zulumi biyu a rains washe gari tunda safe muka tashi da shirin mu Yazid ya kaimu airport din inda karfe
takwas saura akayi muna yan bincike irin na airport muka dungumo zuwa kanon.
Tafiyan jirgine kafin kice me mun iso kano din acikin kaguwa nake ina son inga halin da mahaifina yake
ciki hakan and kawai burina ba dokin gida ba a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[9/15, 7:53 AM] Zainab Idris Makawa Writer: ELSUTRA HOME OF FASHION & BEAUTY ACCESSORIES AND
BEYOND
MAMAN BIBO KAYAN MATA
08068871330 KOKO ROAD SOKOTO
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
5️⃣0️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Karon farko dai a tarihina da wayau na kuma ke nan yanzu dana shiga jirgin sama duk da hakan banyi
wani bada kai ba ko razana.
Dan mamakina shine a zatona sit guda zamu zauna dasu tunda tare tafiyan namu yake dasu Addah da
hafsat ashe abin ba hakana bane acconding to numbers ake zama ba wai duk inda ka samu ka zauna ba
irin na zaman mota ba da kowa zai nuna yadda yake son zama.
Hakan yasa na zauna daban dasu sukuma ma din suna dai kusa da junane a gefena wani mutum ne da
banda gaisuwa ban kara kallonsa ba don ya rigani zama a jirgin.
Jirgin na shirin tashi naji yace min dawo nan ki zauna a cikin harshen turanci sai lokacin na dan dago kai
na kalleshi nace nagode nan zaifi maki wajen taga ku mata tashi ki dawo nan ya kara fada hakan yasa na
mike mukai musayan wajen dashi.
Naji dadin zama wajen sosai don yafi min inda na zauna da farko yanzu ta karshe nake zaune shiko
kallo ga maza na saba da wanan din tun ina kankanuwata.
Nakan rasa meyasa ga kowa amma ni dai idonsu ke kaina sai yanzu na fahinci ba komai bane ashe illa
banbancin wasu halintu nawa dake saurin nuna nasabata da larabawa suke mamaki kila !
?
Hutu zakijene ya tambaya zakice bashi yai maganan ba nace a,a kafin na kara da No au ko kina jin
hausane ma jin hakan yasa na dan kalloshi ina murmushi matashi ne da bai kaima Man ba a shekaru .
Saye yake da kayan zamani na maza wanan yasa ma na kara kama kaina dashi a wajen yaci gaba da
fadin.
Wlh na dauka bakya jin hausa ai sam sai dai ina mamaki kuma balarabiya haka da shigarmu ta hausawa
kuma ?
A kano zaki tsayane ya sake jefo min tambaya karo na barkaitai lokaci guda wanda yasa na fara kaguwa
da zama kusa dashi lokacin.
Yanayin fuskana ya gani kila naji yace ohh sorry to interrupt ina damuwan ki ko kiyi hakkuri please
sunana Sulaiman ni haifafen kano zanje gidane induba mahaifiyata datayi rashin lafiiya bayana.
Allah sarki Allah ya bata lafiya yasa kaffarane gareta ya amsa da amin nagode kefa kada kice nadameki
don Allah ?
Ba komai ai na kara fada din a gundure ina gyara zama ya dan kalloni yai murmushi har gefen fuskan
nadan lotsawa ashe don gaskiya kyakyawane shima da gani kuma dan hutune sosai don kamanin ya
nuna kansa.
Bandai hakkura ba naji ya fada haka kuma ban nuna nasan dani yake zancensa ba yace a Abuja kike
zama ko zuwa kikayi.
A yatsune cikin nuna gundura da tambayabshi a kaina nace wai ni ?
Shima abin dariya ya bashi yayi alama dakai irin ehh ke din fa nace kano nake naje IT ne Abuja kince
dalibace ke nayi murmushi yace ni ina aikine Federal ministry of fice nan Abuja duk da dai nan muke
zama har iyayyena mahaifin mune ke zaune da dayan matarshi a kano shine yazo ciwo ya kamasa a nan
din zanzo in ganshi ?
Amma ainihi mu yan kanone gaskiya Allah sarki haka yaita jana da hira har dai nake dan bashi amsa
wani lokaci bamu rabu ba saida mukai musayan number dashi.
Koda muka saukama bai barni haka ba saida yayi muna tayin mota god so kind saiga Auwal kwatsam
yazo taron mu da motar Man dake nan aje da ita mukaje gidan mu.
Muna tafe Auwal na min sheri wallahi na sauya gabaki daya sai kaje turai naje hutu ba Abuja ba
kewonki zaman ki dai Abuja yafi dacewa dake Aeesha.
Tun a nan suka fara jin sunan Aeesha a bakin Auwal da yake ta faman yi min sheri ni dai a cikin damuwa
nake don ina zullumin halinda zan samu Abbu a cikinsa lokacin.
A dan wata biyun da nayi bangarin sai gaba daya gidan naga ya sauya min ba kowa a kofan gida koda
muka sauka .
Na tsaya magana da Auwal daya dan fara ban labarin ogansa na katseshi da fadin Auwal bari zan kiraka
barin shiga inga halin da Abbuna ke ciki don Allah.
Ba matsala amma ai baba jikin nasa da sauki don Man ya turo an masa dori har ya samu sauki an
sallamoshi daga asibiti.
Gabana ya fadi don jin abinda ya fada ban tsaya sallama dashi ba na juya da sauri ina fadin mushogan
ku ciki Addah suka biyoni a baya.
Nasan weekend ne dole kowa nagida wanan lokacin kai tsaye nayi sallama suna falo zaune suna kallo
sai jin sallamana sukayi Asmauce ta dan leko ganin waye ke sallama ?
Ta yanka ihu da fadin Lah mummy oyoyo tayo kaina da gudu sauran ma suka taso a cikin murna ina dan
yake ban gamsu ba don sai raba ido nakeyi neman Abbuna da bangani .
Ina Abbu yake na fada cikin dakatar da ruguman da Samira tayi min mummy muna rugumar ki kina
tambayan Abbu kuma yana daki nade yazamo gawa kaki rami da kafa daya.
Suka juya wajen su Addah suna masu sannu da zuwa suna karbawa suma cikin dan murmushi dakin
Abbu na nufa da sauri.
Da sallama muka hade da Ammah dake fitowa rike da kayan dayaci abinci lokacin tau dada fa ai dama
nace idan kin sani akwai tashin hankali ranan.
Gurfane nakai kasa gefen kafan da akai mai dauri ina fadin innalillahi Abbuna garin yaya haka ya faru
dakai kuma ba wanda ya fada min na shiga ukuni ?
Haba dai Aeesha ai jikin baba yai sauki da wanan bawan Allah ya turo aka kaishi babban asibiti gashi
har muga fuskan baba garau yanzu.
Ai da lokacin da abin ya farune ashe ba,a san ya zakiyi ba don ma matsa ya gankine ai yasa har akace
kizo din amma jiki da sauki gaskiya.
Wai da baki kike ashe kika barsu waje Ammah tashigo tana fadin hakan gareni tare dasu Addah da
hafsat.
Ayyah am ashe kariyace ga kuma jikin girma sannu baba ta fada Ammah na nuna masu wajen zama da
zasu zauna din a dakin.
Mummy gara da kikazo kiwa babanki fada ya damu mutane da murkusan yan shilan kaji da tantabaru
kada ya cinyewa mutane kajinsu.
Ehh yana da kyau yacisu sune daidai dashi yanzu baru don suna taimakawa mai kariya sosai musanman
ma irinsa da shekarunsa yaja Addah ta fada.
Har lokacin ina zaune ina hawaye a gaban Abbu din kafin can na dago nace Anty safiya garin ya haka ya
faru da Abbu ne wai ?
Kaddara mana Aeesha kaddara ance musulmi takaci Ammah ta fada banda kaddara ai tafiya shi yakeyi
yaron yazo ya kideshi saman babur dinsa.
Kuma ya gudu ba anty safiya ta fada Allah yasa akwai wa yanda suka sheda shi awajen su suka fadawa
yan sanda komai nace amma yakai azzalumi ka kade mutum kuma ka gudu ?
Ai haka kowa ke fada dai irinsu ko kashewa sukayi ai gudu zasuyi don rashin imani na juyo ina fadin
yaushe abin ya farune wai ?
Tafiyanki baikai sati daya bafa ina ji na juyo na kallo Abbu ina fadin yanzu duk wayan da mukeyi Abbu
ashe kana cikin wanan halin haka ban sani ba ?
Murmushin karfin hali yayi kafin yace aida sauki Nana ta saidai tsamin jiki yanzu dake damuna kawai
amma yanzu da sauki gaskiya sosai.
Sannu Abbu Allah ya baka lafiya na fada a dan maraice cikin damuwa nan Addah ke fadin yo aida an
fada mata yafi yanzu an daina wanan balle ai ba karatu take ba wajen aiki take zaifi isan anfada din ko
karin addua mutum saiya samu.
Sai jiyan nan da yamma muke jin ba lafiya hankali ya tashi tun jiyan take wanan damuwan Allah yasa
dai yazo da shirin sa don saida ya biya kudin jirginta yazo sanar mata.
Jinyan Aida safe sun shigo nan duban baba din nan ya rokesa yana son ganin yarsa don Allah suna ta
mashi sheri wai ya zata zai mutu ne bai sake ganina ba.
Ni dai murmushi nayi saiga Asmau tashigo tana fadin nagama gyara kayancan da akashigo dasune
mummy ce suzo ga ruwa can da abinci na aje masu a falo.
Asmauna har yanzu halin kirkin naki ashe yana nan saima abinda ya karu ko tayi murmushi ta juya ta
fita nacewa su anty hafsat ku tashi muje kuci abinci .
Bamu da yunwa ai Aisha kema kin sani saidai zuwa anjima Ammah tace haba ku biyo irin wana hanya
haka kuce baku da yunwa kuma ai abin bana yunwa bane kuje don Allah ke Aeesha tashi ku tafi su biki.
Muka taso zuwa falo danbun shikaface sai kayan sanyinsu na sayarwa muka zauna kowa na min sheri
wai haskena ya fito nayi wani irin kyau kamar bani bace .
Nace rabace na samu gida sanyi office sanyi kinga dole jiki ya canza samira mikewa nayi na juyo ina
fasin Asmau dakina gyararene Anty hafsat taje ta kwanta ta huta ?
Gyare yake mummy ta fada ta mike tana fadin bari na dauko key a bude na kara gyarowa haka ko
akayi tazo tace ta bude na kalli Anty hafsat dake shigide saman kujera nace anty muje dakina ki kwanta
ki huta ?
Ta yunkura ta tashi muka shiga daga ciki tun akan bedsheet din dakin idona ya kara tabbatar da sauyin
da kaman nake gani gidan yayi min don an kara ingatashi a yanzu dakin harda dan AC dinshi can makale
naga Asmau ta kunna.
Dakin ya fara daukan sanyi saidai na dake banyi magana ba Addah ma ta shigo tace tana son ta kwanta
ta huta tana danjin kanta na ciwo.
Saida suka kwanta na samu fitowa zuwa falo ke Aeesha jirgin naku har da irin kayan nan yake daukowa
ashe na zata mutane kawai da dan jakkarsu yake dauka ai anty safiya take tambayana ?
Wasu kaya ke nan anty gasu can mana tsaraban da kukazo dashi nake nufi doya haka manya manja mai
kyau wallahi ni ai kajin nan sunfi daukan hankalina.
Nakai idona kan kayan da suke magana sin da Asmau ta tara kofan shiga daga falon mu din kaya nagani
zakice mudin mukazo dashi daga can din abinda suka lissfo din ne na ban mamaki su kwai kayan tea da
sauran tarkacen cima ciki dai.
Man Bash na fada a raina don nasan aikinsane wanan bakin baturen mai baudaden hali bai fada saidai
ka gani a aikace kawai yayima girshi da abin mamaki.
Dan murmushi nayi na kawar da zancen da fadin maryam da farida fa sukace ko jiya suna gidan nan
sunzo gaida baba kano nan muke muna hiran bukin Aimana.
Wai bukin ya kusa ke nan tace ehh ina ganin karshen watan kirimetine fa bukin amma dai bamu
tabbatar ba haka dai ta fada muna ita.
Lokacin insha Allahu ai ina gida tunda da sauran lokaci ma bukin yaushe zaki dawo gidane mummy nace
baifi sati ukku ba in kammala baidai kai wata daya ba gaskiya.
Basu barni na huta ba don ko dakin Abbu dana koma samira saida tabini can tana min hiran kayan
Aimana da aka kawo din yadda akayi wajen.
Asmau kuma sai faman hada girkin rana takeyi don bakin dake garemu ita samira din girkin dare takeyi
sun raba aikin a tsakaninsu yanzu.
Bansan waya fadawa su maryam zuwana ba sai gasu agidan sunzo nan muka zauna falo dasu muna
hira duk rabin hiran akan Amainace.
I dont no why suka damu haka da zancen illa maryam da ra,ayin mu yake kusan daya na halin ko in kula
donni banga wanin abin zakewa yadda sukeyi .
Taga zata iyane yasa take faman tsarawa kanta karya har Asmau ta kare girki ta zubawa kowa takai na
bakin mu dakina suna barcin gajiya sosai har lokacin.
Karshe tashi nayi na koma gun Abbu muna hira dashi da Ammah kan wurin aikina kafin Amma ta jefo
min tambaya da.
Su wa yan nan fa Aeesha daga ina kika samusu kuma gasu dai da mutunci nagani ko wurin aikin ku
dayane dasu ?
A,a Ammah ita dayan karamar yar mamace itako babban kanwartace don ban tsaya mata dogon
bayani ba watace mama din ta tambaya ?
Saina kalli inda Abbu yake zaune nace matar da nake gidanta zaune dasu yartace da yar uwata tace su
rakoni su duba jikin Abbu .
Wai kina nufin kin bar gidan Habibune ko me nace eeh Ammah ai tunda naje banfi sati daya ba a
gidansa na canza wajen zama don gidan bai zaunuwa a gareni gaskiya.
Abisa wani dalili naki zakice gidan dan uwanki bai zaunuwa a gareki kin raina da arzikinsa ke nan kin
samu masu wadata ko ?
Ko daya Ammah tsarin gidansane kawai be min bane yasa na koma gidan wa yan nan din yanzu ke yar
nan kibi duniya sannu wallahi ?
Yanzu ke don baki da kunya har kinyi wayau da zakice arzikin wani bai maki ba ki gudu gidan dan
uwanki kibi daulan zuwa gidan wasu dama don kin gansu da arzikin da yafi nasa kome ?
Dama ina karatun take taken ki Aeesha salon kawai kijawa mutane magana don kina ganin yanzu kamar
kinfi kowa a gari ko ?
To bari kiji in fada maki gaskiya su din dai dan uwansu ya zauna dake har haka ya rufa muna asiri damu
dake har kika kai hakan da yanzu zaki guji jininsu.
Wani kallo nayiwa Ammah din saina dukar da kaina kasa cikin mamaki daidai lokacin Abbu dake sallah
zaune a gefen mu ya idar baiko tsaya addu a ba yace.
Ammah matan wani irin magana kike fadawa yarinyar nan haka wai a tunane ke dake zama da yar nan
ko yaushe a gida zaki fini fahintar wacece Nana a yanzu.
Haba malam yanzu fisabillilah ya kyautu yau ace tabar gidan habibu ta koma gidan wasu don sun fishi
maski ?
Tace dake hakan ko ta fadawa wani hakan kikaji yarinyar nan batayi bugun gaban kanta ta koma
wanan gida ba saida sanina .
Haka kuma su din da suka rike muna ita a can ga zahiri yanzu kin gani mutanen kirkine don saida
matar ta kirani idan na yarda zata dawo gidata da zama kuma zata rike min ita bisa amana insha Allahu.
Amma sai naga idan ba takura a ciki naga gaskiyane da yarmu ta shiga wani hali gara ta koma gidan
musulunci da zama da arnaku a takure.
Shi bai zama gida sai wanan matar nasa kuma ta cika gida da yan uwanta arna maza da mata bayan
daki biyu ne ashe gidan nasa ras suna rayuwa haka cude da gardawa da mata.
Naji tace jam asha haka gidan nasu yake yaya za a iya rayuwa irin