Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
PLEASE,,,,,,,,,,,,,
https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6
Jaridan dana samu saman gadona da na fito bandaki ya dauke min hankali mai taken baiyanar boyaryar
yar Omar bin Sultan Abdulrasheed.
Ga photo na baro baro a shafin bangon cikin wanan Assh din jallabiyan da ummu ta saya min sai kuma
wanan shigar attamfar da nayi a saudiya da har kakana ke tambaya da nayi kyau a cikinsa.
Meyasa na debesa da zamu fita sai kuma wasu bakake shiga da nayi iya fuskana round kai ingajarce
maki mai karatu kusan shigan da nayi tare da mutaneb nan an yaddashi a cikin mujallan nan da labarai
daban daban.
Bude shafin farko ya tsaya min a zuciya inda aka nuno wani katon photona da ake fadin yar Omar bin
sultan ta bayana bayan tsawon lokacin data dauka da bacewa .
Wanda aka ganota a saudiya bayan uwarta ta gudu da ita ta boyeta a Nageria boyewa kuma na
tambayi kaina ?
Zaune nakai don karanta labarin kanzon kuregen da naka anfara wallafawa a jikin mujallar .
Ina shirin somawa na jin karan budan kofan yasa nasan ummu Halimat ce don babu mai shigowa inda
nake sai ita kadai .
Duk da ta fada min akwai matan kaka din zaune a gidan suma amma ban taba gigin tambayarta ko ina
suke ba?
Juyawa nayi tare da mujjalan a hannuna ina fadin wanan ai ,,,,,,,,,,,,
Zancen nawane ya makale a baki don ganin wata bakuwar fuskan wata mace da zata kai sa,an ummu a
gabana tana sakarmin murmushi a fuskanta wace ban taba ganinta ba a cikin ahalin sai wanan lokaci .
A cikin dan ladabi nagaida da ita cikin kulawa nima sai naga tana karasowa gareni tana fadin kiyi
hakkuri tunda kikazo bamu hadu ba.
Nayi tafiyane zuwa kasarmu ganin mahaifina Allah sarki ya mai jikin an kuma dawo lafiya ta murmusa
tana fadin Alhamdullahi nagode sosai.
Dama sultan ya fada min indan na ganki zan soki sosai don kina da saukin kai nasan baki sani ba nice
matar sultan ta hudu ma,ana nice last wife dinsa dai.
Nayi murmushi don abinda ta fada din a lokacin sultan ya fada min kina zaman kadaici kiyi hakkuri fa ta
fada tana dafa kafadata.
Kallon inda ta dafa min din nayi ina gwauce nace kawai dai rashin sabone ki saki jikinki zaki saba damu
a hankali ai zaki fito muyi dinner a yanzu muna jiranki a dinning area ta fada tana juyawa tabar dakin.
Wanan mace fadi ba a tambayeki bane tunda gashi cikin dan kankanin lokaci ta jero min magana da bai
shafeni bama a ganina.
A gagauce nayi sallah na fito ta samesu bisa jagorancin ummu halimat a zaune na samesu saidana
zauna aka bude abincin aka soma ci a natse nake komai nawa har saida muka gama.
Kakana ya soma magana yana fadi cikin harshen turanci da Aisha wanan itace matana Nafisa itace ta
hudu a cikin matana bayan rasuwan kakanku na aureta.
Yanzu muna da yara biyu a tsakanin mu da fatan zakiji dadin kasancewa da ita a gidan nan dan kallonta
nayi ina sakin murmushi a fuskana.
Ganin an kammala yasa na mike ina masu saida safe nan kakan nawa ke tambayana ko naga mujjalar
da aka buga game dani ?
Nagani na bashi amsa kai tsaye ba tare da nuna ko naji dadin hakan ba daga haka na juya na tafi ina
masu saida safe.
Sai bayan na tafine matar nasa ta kalleshi tana fadin a sannu zata saba damu yanzun bakunta takeyi
damu tukun.
Yaya kukayi da iyayyen Saratu din don nasan ba zata bar yar nan ta zauna lafiya ba a gidan ubanta
matukar tana tare dashi.
Yayi namijin kokari sosai wanan karon don ya fito fili ya nuna mata yarsa yake kauna bata kuma isa ta
rabashi da ita ba tun a makka suka kwasa har dawowa nan.
Nasan za ai hakan da ita matar ta fada tana kallon mijin nata koma mai zatayi ai sai tayi wanan dalilin
yasa na dauko yarinyar gaba daya zuwa nan .
Don nasan takura mata zasuyi a can tunda shi ba zama yakeyi sosai hakan ma yayi sosai a barta nan
tare damu ta kara fada.
Mujjalam nake bi ina dubawa ina mamakin irin bayanin karyan da wani ya wallafa a kaina wanda
bansan dalilin yin hakan ba a lokacin.
Haka rayuwa ya dinga tafiya sau daya mahaifina ya shigo muka gaisa inda yake fada min cewa baya
kasan ne yayi tafiya zuwa kasan Spain .
Mun dan jima tare dashi kafin ya samu kira mukayi sallama ya tafi tun wanan ranan ban sake ganinsa
har wanan lokacin da sukasaka na waliman ya gabato.
Ina kallo sai shirye shirye sukeyi a tsanake duk da ba ganewa akeyi sai idan wani zance ya tashi nidai
nawa idone kawai.
Ina nuna masu hakan ko a jikina don ban yadda na zake ba ko banza kuma bidi,a bai dameni ba
donshine ban wani damu ba.
Ashe abin ya zarta yadda nake tunane don saida ranan yazo tun karfe goman safe muke karban baki
zakice wani gagarumin bukine akeyi ake wanan kashin kudin haka .
Wai amma duk a kaina ake wanan abin din taron sunan da basuyi min sai gashi suna min shi da
girmana kiri,kiri wasu kan don gulmane suka halarto a wajen.
Daki nake kwance nagaji da jin ga baki ga baki nazo mu gaisa don yan uwa na nesa da suke zuwa idan
sun iso a gidan tsohon suke nufowa inda nan suke sauka.
Ummu Zainab ce ta shigo da wata mace fuskan nan nata da murmushi tana fadin ki tashi a shiryaki don
lokacin tafiya yai kusa kada a makara.
Mamaki ya kamani wani shiri kuma za a ai min saidai na dago ina bin wanan matar da kallo wace aka
kira da mai gyarani din.
Wani yaren nasu ba ji nakeyi ba saukin abin nan dubai gaskiya suna hadawa da englishi amma dai ana
taba yaren harshen Arab sosai fiye da english din.
Bawani abu bane fa gyara ka tsaya ka yiwa kanka kwaliya yadda ranka yake so ba sai ka fito kamar
siffan baby dol ba.
Wanan yasa ban yarda ta bata min fuska da wani fenti mai yawa ba ligt make up na zauna tayi min don
dashi na saba amma duk da haka na zuba kyau sosai dana duba madubi.
Wasu kaya ummu zainab din ta shigo dasu a matsayin wanda zan saka sai abin nake ganinsa kamar
shirmen mafalki a wajena.
Yauni Aisha ce zan saka kayan da sai a magazin dinsu na larabawa kake ganin matan manyansu cikin irin
shiga.
Sai gashi a gabana a matsayin nice zansaka na tsab na fito ga gwala gwalai kamar suyi ihu ana ta daza
min a cikin jikina tun daga kunne wuya hannu zuwa yasu duk sun sha kwaliyan kamar wata hamshakiyar
ba,indiya dani.
Watau dama dai haka al,adansu yake ko a fili dai da muke gani a cikin film na fito tsab dani zakice ba
Aeeshan da kika sani bace mara asali din na abin zunde a Nageria.
Gaskiya asali gatane ga bawa haka a hali ko wasu iri aka halittoka cikinsu shima rahamane ga mutum
ya Allah ka kare yayayen mu da fadawa tarkon zinah a rayuwansu.
Kyama da hattaran da zina kedashi yasa duk wani baiwa da Allah yai min da farko ashe ya bace a jikina
wanda harni kaina bani ganin hakan a tare dani.
Sai wanan lokacin dana zamo yar baiwa yar asali kamar kowa nake jin kaina wani iri ina ganin a yanzu
daidai nake da kowa a duniya.
Zuwan hjy mahaifiyar Matazun gidan mu shiya fado min a rai da har yasa na runtse idona a hankali
hawaye na batun fito min don naso matazun a rayuwa ta a lokacin.
Sai aka samu akasi saboda rashin asali a lokacin ashe duk hakan yana cikin hikimar da Allah yai min na
baiwa da bansani ba a rayuwata rashin uba yasa muka rabu don dole.
Naji cewa ya auri diyar wani babban mutum a katsina son kanin nan nasa da sukazo tare nazir muna
waya dashi sosai yakan kirani mu gaisa shike ban labarin hakan ga dan uwasa din.
Cin fuskan hjy kura data kirani da yar kwara a gaban idona da irin wullakanci dana fuskanta duk cikin
second abin ya dinga fado min a rai sai gashi yau iyayyena sun wanke ni a duniya sun fitar dani daga
tarkon fitowa ta tsigar zinah ashe ni din yar halak ce kamar kowa.
Ban kara gaskanta hakan ba sai da muka isa wajen taron mai kama da taron shugaban kasa yadda akai
decoration din wajen kowa yana muradin ganin wanan yar mai sa,a data kasance ya daya tilo ga Omar
bin sultan babban dan kasuwa da sunan shi yai fice a cikin duniya.
Gaskiya man yayi yayi kwarai a halarci don man yai min taimakon da ba zan taba mantawa dasu ba a
rayuwata yadda ya tsaya ya dage a yau na zamo wata abu a cikin rayuwata haka.
Ilimi wani matakalane ne da bawa ke takawa zuwa hawan wani tsauni na rayuwa har yakai inda bai
taba zayon kaiwa ba akan ilimin idan ya dage.
Irin hakan da suka tsaya min dasu Abbu a yau nake alfaharin sanin su a rayuwata don da ace dip nake
banda ilimi a rayuwata nasan da a wanan wajen iyayyen nawa danazo danasha wahala da kunya a
rayuwana harma da iyayyen nawa.
Don ko madam Nafisan kaka taso ta gyara min wasu abubuwa sai ta tafi nayi yadda naga shine daidai
dole ta saka min ido sun dauka tunda a Nageria nafito banda wayewan kai a tare dani.
Basu san iya tsara rayuwa yana ga dan Nageria ba saidai wanda ya maida kanshi abin banzane suke
ganin kamar kowa haka yake .
Banga ta inda za a rainawa macen arewan data kama kanta ba wajen iya fitowa fage saiko wace ta aro
wani al,ada ta saka cikin lamarin da wasu mata sukafi yi a yanzu.
Riga dai da sukace in saka na saka haka kuma gwalagwalansu duk na saka din amma gyara na tsaya nayi
yadda nake ganin zai dauku a zuciyana.
An zuba ido an kagu da fitowa yar da akace donta ake taron duk da ga photuna nan ansaka dana
mahaifina a mayan baner a wajen suna haskawa.
Amma mutane sunfi son su ganeni a zahiri suga yaya nake wanan yasa kowa zuba ido duk da an fara
program din.
Tare da mahaifina muka fito kayan dana aka dark blue suka kara min kyau sai walkiya sukeyi suna
daukan ido nan kowa ya zubo ido yana karemin kallo a lokacin.
Shiko mahaifina ya rike dani sai dagawa mutane hannu yakeyi mukaje bakin cake din da aka aje din
muka tsaya .
Nan dai kowa ya nasu kafin a fara bude taron da addua da dan bayanai wasu da larbci donshi yafi yawa
masu turanci a wajen kadanne.
Yayan mahaifina shine ya dan bada tarihin auren mahaifina da mahaifiyata da shekaran da abin yafaru
inda da yawa sunsan wanan lokacin daya tafi aikin gina company su a saudiya .
Har dai wayau a gabana sun fada cewa mahaifiyatace ta gudu dani don kada ya kwaceni a lokacin zuwa
Nageria bayan rabuwan aurensu wanda a yanzu na fahinci gyaran zancen sukeyi a kunnuwan mutane .
Don yadda naji mahaifina ya dan matsa hannuna adaidai lokacin da yake wanan bayanin ga mutane
har dai zuwa haduwan mu a wanan umur da suka tafi anan ya tsaya shima kakana yayi bayani a wajen.
Ya nuna matukar jin dadinsa don ganoni da sukayi bayan shekarun da aka dauka suna zaton kona mutu
ashe ina raye.
Ya kara da godewa Allah daya kaddara na dawo gida a yanzu cikinsu lafiya haka kuma yana godewa wa
yanda suka rikeni a can din don sun ban tarbiya yadda ya dace a bisa tafarkin addinin musulunci.
Nayi mamaki da suka ban speaker sa zuman nayi magana a wajen taron a hankali na dago kai na kalli
mahaifina daya gyada min kai alaman in karba din inyi.
Na mika hannu na karba kafin na farasa masu da sallama irin na addinin musulunci sai kiji wajen yayi
tsit nace gulma ko ina akwaishi dai ke nan .
Na fara jero addua godiya ga ubangiji wanda na illimantu da hakan sosai tun ina kankanuwata kafin na
fara da watsa turancina na yan arewan Nageria ina watsasu.
Na kare da mika godiya na nuna muna kaunan da sukayi tare da fatan alheri garesu da masu fatan
komawa gidajensu lafiya.
Iya nan na tsaya saboda kukan farin ciki daya rufeni don sun nuna min a ranan ni din yar gatace kamar
kowa duk da ba,a barni cikin maraucin uba ba saidai gori da ke jifana ko wani lokaci na gilma.
Nan aka karbi loud speaker a hannuna mahaifina yana dan lalashi tare da nuna min mutane yana fadin
farin ciki ya kamata nayi a lokacin da Allah ya kaddara mu duka muna raye ba kuka.
Bayan an yanka cake ne wanda na diba nabawa kakana a cikin ladabi son ban saba irin hakan ba gun
Abbuna aka shiga tafawa don tsohon yayi min komai gaskiya.
Yau badon yana a raye ba da bansan karshen makomana ba a duniya koda mahaifin nawa ya karbeni
saidai abin ya tsaya a iyani mu dinga zumuncin mu tsakanina dashi kawai.
Amma kasancewar Allah yabar min su gaba dayansu a raye sai hakan ya jawo min daukaka sosai don
wanan taron kamar da gaiya suka hadashi.
Matane suka shiga zuwa suna ruguma nahar da mazan muna dan gaisa duk abin nan ina rugume a jikin
mahaifina.
Bai yarda ya sake mun hannu ba a wajen duk wanda yazo zai tsaya yai min bayani yadda suke da
maishi gashi duk nagaji amma haka na daure ina biye masu ga al,adansu.
Lura da hakan da yayine ya kira wani Samir yace ya kaini gida in huta don nagaji saima lokacin na kula
da matarsa dake wajen suna magana da wasu gungun mata da gani gulman irin na mata sukeyi.
To me zasu fada Allah ya raba garda nida mahaifina kanar an tsagashine aka debeni a jikinsa saboda
mugun kamar da mukayi dashi bana wasa ba.
Sun nuna ranan ana buki gidan dealer gwal donko ko wace mace ka gani tasha kwaliyan zinare ko wani
dutse mai tsada a jikinta.
Wasu da kalan shigarsu ta larabawa wasu kuma sun waye zama dubai cikin mutane daban daban ya
wayar dasu sunyi adone da wasu nau,ikan tufafi na fita kunya.
Ban tsaya kallon wani abu ba nabi bayan wanan Samir din zuwa inda naga ya nufa dagwas dagwas dani
muka fice a wajen suko suka bini da idanu ba maza ba ba matan ba kowa da irin abinda yake fada a
zuciyarsa game dani.
Ina zama a motan na juya na kalli wajen wasu hawayene na farin ciki suka zubo min lokaci guda
yayinda shiko samir din ke fadin gaskiya abin yayi kyau sosai wallahi.
Har da wani shine kaza a masarautan waje kaza har wani duk sunzo da iyalinsu ba a taba taro a gidamu
suzo irin haka ba kamar yau din nan.
Duk da dai wasu sunzone suga yaya yarinyar da aka tayar a Nageria take sai gashi sunga abinda basu
taba zata ba gashi kinyi mugun kama da Abbi sosai wallahi.
Shi kadai keta zuba surutunshi saida yaji ban amsa mashine ya dan juyo ya kalleni kuka yaga inayi
hakan .
Naji yana fadin subbanallah kuka kuma kukan me kikeyi haka Ukuty yau fa ranan farin cikine a garemu
gaba daya yau Allah ya wanke Abbi daga zargin da ake masa na bai haihuwa.
Jin abinda ya fadane yasa na kalloshi ina dakatar da kukan nawa ina fadin kana nufin abbi baida wasu
diya bayan ni ke nan ?
Yace kwarai ma kuwa ai shiyasa akai gwajin jinin ku dashi din a tantace kinsan matarshi tace bata
yarda ba ke ba yarsa bace ?
Yaushe akai gwajin jinin mu na tambayeshi yace tun zuwanki kasan nan mana ina ganin kowa yaga
result din ai saidai in kece basu nunawa ba .
Nan dai ya shiga yi min bayanin irin tashin hankalin da Abbi yayi da matarsa tare da mahaifinta wanda
kusan saida akai gwaji a kaina dashi wajen sau ukku.
Zancen ya ban mamaki yadda yake min bayani na fahinci sun debe gashin kainane da kuma cum dina
da bangani ba na fadawa ummu halimat tace zata dibo min ashe dauka akayi har dashi akai gwajin
yatsuna dashi din.
Sai kuma kofin dana sha tea shima an dauka anyi aune aune a kansa an gano ni jinin Abbince yasa dole
suka yarda ba don sunsoni ba a cikinsu.
Ni dai har muka kai gida bani fahintar zancen da yake fada lokacin don na lula duniyan tunane mai zurfi
game da yadda kaddaran rayuwa ya zo min.
Allah dai ya nufane sai na fito tsakanin mutum biyun nan godiya ga Allah bayan wanan shine na fito
yar halak ba yar nune yadda akaita nuna ni a matsayin shegiya ba a Nageria.
Har mutane suna gudun diyansu dani don kada azo wata rana tarihi ya maimaita kansa na bata masu
zuria shi din dai yasa ake kyamatar diyan da aka haifa bata sunnan ma,aiki ba.
Ina shiga daki kayan na fara sabulewa don nikan a gaskiya sun min nauyi na tara gwal din a waje daya
ina jiran ummu halimat ta shigo ta mayar masu da abin su.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[11/23, 10:03 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
9️⃣5️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6
Zaune yake ya kurawa laptop dinsa ido yana bin shirin da kallo komai daki daki yake binsa har jama,an
da suka hadu a wajen tsab ya ke nazarin kowa cikin dan lokaci ya mike yana rufe System din.
Gyara zama yayi ya fada tunane ta hanyar hade hannayesa biyu a waje daya ya tokare habashi dasu
idonsa daya kurawa waje daya ido zaisa ka gane