Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
na wayance da fadin hakan gareta.
Dakuwa tayi min tana fadin kaiya yaro dai yarone wanan bokon na karanto maku karya a rayuwa kiba
kan idan kin gada ai sai kinyi dama kin sani ki daina wahal da kanki don mu zurian mu bamu da gadon
kiba can din nan bandai sani ba ko can cikin zurian ubanki idan su sun gaji kiba wata kila.
Ai a Nasarawa banga mai kiba ba cikinsu suma duk da ba zubinsu na kwaso ba ban sani ba ko dangin
mahaifin nawa can akwai mai kiba dai .?
Wani kallo Ammah din tayi min lokaci guda kuma na fuske kamar ban san abinda na fada ba a lokacin
sai cin abincin nakeyi a hankali a lokacin cikin daure fuska.
Yayin da Ammah din ta danyi dan shiru na dan lokaci tare da zuba min ido kamar tana tunane sai kuma
naji ta nisa tana fadin.
Kai anya Aeesha sai kuma naji tayi shiru fasa fadin abinda tayi niyar fada a lokacin don dan tunanen da
tayi a wajen a zuciyarta.
Takai wani lokaci kafin naji ta sauke nauyayyen a jiyar zuciya tana fadin Allah ya kyauta ta tashi ta daga
zuwa daki ta barni a wajen har na karasa cin abinci ina gab da tashi ta fito tana fadin.
Ni mutanen nan su dagula min lissa na rasama ko dame zan fara a yanzu ni gani ba sabon dinki ba ko
takalma kirki bandashi a gidan nan balle sabon zani duk yan tufafin nawa sun sani dashi a baya tun
wancan bukin na kwanaki.
Ammah meyasa kike son matsama kanki kan wanan zancene wai kiyi amfani da abindake gareki mana
irin wanan wajen wasan ma ka saka balle yasama ido mutanen da duk yadda ka iya dasu ganinka suke
dan kauye .
Sai naji Amma din ta katseni da fadin aini bani nake jiwa ba Aeesha a yanzu kece tunda kinkai munzalin
budurwa a yanzu dole ki dan bukaci abin da zai dan sauya ai bari malam ya dawo.
Inji ya za ayi da wanan zancen ance da wuri wuri ake fara shiri ba sai tafiya yazo ba inji manya da sauri
na dan kallota ina fadin ba inda zani Ammah a gida zan zauna .
Kafin in rufe baki naji tace dani akan me wai nifa yanzu na rasa ganr inda kika dosa Aeesha cikin kwana
biyun nan komai sai ki dinga jan kanki a baya.
Bukin dan hjy karime din ne zakice baki zuwa matar da idan ta ganki take rasa inda zata sakaki tana
fadin ke yartane yanzu kice wai baki zuwa sha,aninta wanan ma wasa kikeyi don ko malam ba zaiji dadin
hakan ba ai ace bukin dan dan uwansa zakice kr ba zakije ba Aeesha ?
Baki na turo gaba ina bata rai nace Ammah ni wanan irin abinda suke min a cikinsu bana so sai a dinga
nuna mutum haka kuma duk inda kabi idon mutane yana kanka wananne bana so wallahi .
Yo me ruwanki dasu din kedai kiyi sha,aninki kawai kibar mutane don ba,a iya masu makin in bata amsa
ko in tsaya saurarenta don ma ta gane ban son zuwa din ai yasa na mike din na barta a wajen.
Ina ji can dare da Abbu ya shigo Ammah din ta kara tayar da zancen bukin kuma tundai inajinsu har
barci ya daukeni a haka sai washe garine na tashi naga Ammah din tayi kumshi ashe a cikin daren don
fara rage hanyar tafiyan dake gabanta duk a cikin garine bukin amma ai kwana zatayi a can har biyu ko
ukku.
Na fito da shirina tsab na school tana zaune tana saka taki a kafanta ta dago ta kalleni tana fadin aina
zata yau zaki huta ki danyi gyaran jiki kije gun maman Aimana kiyi sammakon bin layin kitso ?
Shiru nayi nan ma banyi maganan ba hakan ya dan harzukata tana fadin amma kinji mena fada kon
kyale kinyi shiru ni wanan takama da izzan naki ya fara isata wallahi.
Yarinya a magana sai faman miskilanci kike zubawa kamar bakijina don wullakanci jin hakan yasa na
juyi ina fadin nifa sai asabar zan tafi kitso inna kada inyi yanzu ya walwale min a kai kinsan kitso baya
kwana biyu a kaina bai tashi ba.
Ikon Allah ana gabas kina yamma yar nan ko kin manta da zancen bukine wai yau da gobene kadai
muke da lokci a gidan nan.
Ammah nace fa ban zuwa kuje sai kun dawo amma ni ba zanje ba gaskiya don,,,,,,, dakuwa data miko
min tana fadin karbi naki ni kike mussu dani haka Aeesha ?
Muryan Abbune dake fitowa a daki yake fadin haba wai meke faruwa hakane tsakaninki da yarkine tace
bata zuwa ki barta mana tunda bata ra,ayin hakan.
Koke ai don zuwan naki ya zamo kamar dolene da bakije ba don ba lokacin hakan amma hjyce nasan
yadda kuke da ita yasa zan barki badon shiba babu mai zuwa a gidan nan gabaki daya tunda bamuji a
cikin lokaci.
Amma dai malam za ace hjy tana bukin danta yadda muke ace yarinyar nan tace va zata taka ba duk
yadda muke naji Abbu din yace Ammamatan ina gargadin ki da ki kyale yarinyar nan don Allah tunda
tace ba zataje ba ki barta.
Ya juyo gareni yana fadin jeki ke ki shirya kada ki makara don lokaci na kurewa maki ya juya ya shiga
dakin kuma tsaye tayi cikin mamaki tana bin bayansa da kallo a cikin mamakin kafin ta maido kallonta
gareni tana fadin kiji dashi.
Wanan yar ga baki daya kin sauya min a yan kwanakin nan na rasa inda kika dosa Aeesha yarinya da
izza da jinkai kamar wata yar basarke haka ?
Nikan a gurguje na shirya da saurina na shiga daki na dauko jakkata banko tsaya karya ba kodana fito
na samu Abbu a tsaye kofan dakin yana dakon fitowa ya miko min dari na na karyawa na rusunna har
kasa da hannu bibiyu ina karba tare da godiya .
Na juya na fita na barsu nasan a bayana zasuyi zance a yadda na barsu din don kowa dai ransa ya baci a
lokacin kan zance .
Inda niko iyakar gaskiyana ke nan na fada masu ba zanje ba don in ban manta ba zuwa na karshe
sha,aninsu da kukana na dawo gidan kan abinda akai min lokacin.
Muna fada irin na yara na dan duki abokiyar wasan tawa tasa kuka ranan yan gidan su Abbu suka taso
min kamar zasu cinyeni danya Amma sai hakkkuri take basu suko inda suke shiga ba nan suke fita ba a
lokacin .
Wanan yasa banji marmarin komawa ba sha,aninsu lokacin ban ma san asalina bake balle yanzu din
dana sani cewa ni din ba yar kowa bace ashe.
ZAINAB IDRIS MAKAWA[7/31, 10:10 PM] Zainab Idris Makawa Writer: ELSUTRA HOME OF FASHION &
BEAUTY ACCESSORIES AND BEYOND
MAMAN BIBO KAYAN MATA
08068871330 KOKO ROAD SOKOTO
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
00️⃣66️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Ammah naji tana gani haka ta tafi wanan sha,anin ta barni duk da bata so hakan ba amma ba yadda ta
iya tunda na kafe akan ba zanje ba yasa Abbu yayi mata fada sosai akan matsa min din da tayi a lokacin.
Taso zuwa dani din ne tayi kwanakin da take sonyi acan din sai naki zuwa dole yanzu in angama ta juyo
don hankalinta ba zai kwanta ba a can din ni ina gida.
Gashi a can din kuma yara da manya suna tambayanta ina Aeesha maman Aeesha saita labe da cewa
bata zo dani bane don ana makaranta don hakane ta barni gida.
Sai kuma bata samu kan ita uwar bukin ba a wanan karon don uwar bukin kowa yana complain din
fuskanta a daure yake lokacin sha,anin yasa an gama buki washe gari karfe biyu sai ga Ammah din ta
shigo gida dawowana ke nan daga school ina zaune ni kadai a tsakar gida nayi tagumi ina faman tunanen
duniya ta shigo.
Na mike da fara,ara ina taron ta itama fuska a sake da murnan ganina ta rugumeni yadda nayi mata na
dauki kayan ta nasa daki kafin in firo in karbo mata ruwa na kawo mata tasha.
Tun a nan ta fara bani labarin kan bukin tana fada min abubuwan da suka faru inda ta dora da fadin ai
gara da bakije bama Aeesha .
Saina koma ban ganin laifinki kuma na matsa makin da nayi sai muje tare don muma da mukaje din
munyi dana sanin zuwan tunda damu da babu mu a wajen uwarsu daya.
Ke bari yar nan hjy ta ban mamaki wallahi matuka don banyi zaton hakan a wajenta ba sai lokacin na
bude baki nace Ammah kuma ke nan balle ni da duk da sun saba ganina amma haka zasu samin baki da
ido suna tambaya a kaina wanan yasa ban son shiga mutane yanzu wallahi.
Budan bakin Ammah din tace aiko sai ki zama kofin rijiya don ko mutane haka su a ko ina da saka ido
kan abinda bai shafesu ba yanzu.
An daiyi bidiri kan gaskiya an kumaci an sha gaskiya tubarkallah wallahi don buki yayi kyau amarya
kuma sun iso tun jiya daga yola.
Shima Allah mai tangaram ance nan da wata ukkune bukin yayansa anma so a hada da wanan gidan
iyayyen ita wanan yarinyar suka matsa ayi don su sun shirya sukace.
Na dago ina fadin gidan su anty mami ke nan tace aisu mami din nake jin za aiwa auren ko kuma dai
bada ita ba amma dai cikinsune su ukkun .
Allah sarki sun karasa karatun nasu ke nan nidai suna birgeni wallahi don babu ruwansu da daukan kai
faran faran dasu ko wani lokaci.
Amma ita wanan da akace yar matarsa na yanzun ce itakan saboda itace ma banson shiga gidan su
wallahi.
Keko ai dole tunda uwata ke mulki a gidan su uwarsu ta rasu tun suna kanana shine ya auro hjy Binta
din itama ta dinga haihuwa kamar tururuwa masa.
Dariya zancen ya bani har yasa na dan murmusa ina fadin kamar tururuwa kuma tace ehh mana kin san
mu mata ai wani lokaci kan kishi kishi ma harda wanda bai duniya in aka hadu da marasa tsoron Allah sai
kiga anyisa ai.
Mun kai wani lokaci a wajen zaune muna hira saida akai sallah la,asar ne muka shiga daki bayan mun
fito ne ina shirin islamiya tacigaba da min hiran.
Don nice dai abokiyan hiran Ammah din a gidan don Abbu ba zama yakeyi ba ko yaushe kasuwarshi
yake zuwa yaci sai yamma yake dawowa gida ko yadawo din kuma yana waje gun abokan hiransa suna
rage dare a wajen.
Ankai wasu yan kwanaki aikin ke nan bada wanan labarin bukin a bakin Ammah din duk da tace an
masu wullakanci hjy ta nuna kamar bata sansu ba wanan karon amma kuma tana yaba kyau bukin.
Jerabawan mu na karshe yazo haka muka zanashi cikin yardan Allah muka koma kuma zaman gida
zaman jira jin sakamakon daga Allah don jerabawa dai irin wanan dacene sai wanda Allah yabawa sa,an
cinyeta yake hayewa.
Duk wanan zaman dakon kuma da mikeyi ban taba jin Abbu yayi min maganan makarantana ba da
yaimin alkawarin karasawa gaba a lokacin.
Niko zamcen yana a kasan raina don gaskiya ina sha,awar karatu nikan a rayuwanta duk da nasan
iyayyena basu da halin hakan don karatu na masu karfine.
Ga zaman gidan dana sawa kaina a yanzu ya fara isata nima banda wajen zuwa sai dan aiken daba,a
rasa ba da nakan jewa Ammah a makwabta shine kadai zance yana sani fita.
Gashi kamar kada ace na kare karatun nan wani irin girma yazo min a lokacin halittana na asali ya kara
baiyana a fili sosai har yasa idan zan fita a yanzu na tsiro saka nikaf a fuskana don bat da kamana saboda
ido akaina yake ko wani lokaci nake gani.
Ranan na dawo daga islamiya wajen hadda na samu Abbu a gida nayi mamaki kwarai haka kuma a
yadda na sameshi yana dauke tabarma da buta da kofin ruwa yasa nagane yayi bako a lokacin.
Don gaskiya ba lokacin dawowanshi bane a lokaci haka kuma dana shiga gidan na samu yanayin
Ammah acikin damuwa zan ma iya fadin har kuka tayi a lokacin haka kuma gata saye da hijjabi a jikinta
yasa gabana kara faduwa.
Saidai banyi magana ba bayan gaisheta daki na nashiga na aje jakata na dan jima ban fito daga dakin ba
sai can naji Abbu ya shigo daga baya sun shiga daki suna zance kus kus kus a tsakaninsu.
Duk da kasa kunnen da nayi don in fahunci kome ke faruwa ban gane komai ba cikin zancesu hakan
yasa nima na koma sukuku a ranan.
Ban taba kawo zancen Nana ba araina lokacin yo ina zan kawota ma kusa matarda ba wanda yasan ina
ta shiga ko a saudiyan zanyi zaton daga wurinta hakan ya fito.
Wai asheko itace tayowa su Abbu sakon kudi masu yawa a lokacin kuma mai sakon yazo da albishir din
cewa tana nan lafiya a wani gari tana aure har ta haifi yara biyu a lokacin shi shedan hakane don sun
jima dasu a cikin masallaci a madina a nan suka hadu dashi har ta yaba da hankalinshi mutumin ta yarda
ta bashi sako zuwa wajen iyayyen nawa na yanzu.
Wanan yasaka Ammah kuka a lokacin don jin labarin yar uwarta da kuma tarin sakon data bashi yazo
muna dashi abin mamaki kuma shine.
Ita tana da labarinsu su daine basu da nata a yanzu amma har inda suka koma ta sani don itace tayowa
mutumin ma kwatancen gidan namu yazo.
A yadda mutumin ke fadi ita nana din a yanzu tayi karfi a can itama don tana business dinta tana
samun kudi sosai yadda ta bashi labari har ya bukaci ya ganeni akace dashi ina islamiya.
Bayan fitan Abbu gidan kawai ina bakin murhu ina hasa wuta naji Ammah ta saki wani irin kuka daya
tayar min da hankali lokaci guda har bansan sanda na fada dakin ba a razane cikin tashin hankali.
Wurin Ammah din dake durkushe ta zubawa wasu kaya idanu na nufa ina tambayanta a gigice da
Ammah waya mutu meya faru anyi wani abune ?
Duk lokaci daya nake wanan babatun cikin tashin hankali a gareta kafin idona yakai ga kayan dake
gabanta a take zuciyana yayi wani irin ras ras a wajen .
Hakan yasa nakai durkushe a hankali ina bin kayan da kallo da ido abinda ya fito bakina lokacin shine
Nanace ko Ammah ?
Wani irin kallo Ammah din ta watso min a lokacin sai kawai na mike na fice daga dakin lokaci guda cikin
karfin hali na nufi wajen aikin dana soma naci gaba ba tare dana sake waigen dakin Ammah din ba kuma.
Fitowanta cikin mamaki yayi daidai da shigowan Abbu gidan dauke da kayan cefanen daya sawo muna
na dago da idanuna da sukai ja ina masa sannu ya amsa da fadin dama nasan haka Nana ina sauri da
Allah Allah karkiyi talge kafin na karaso.
Kayan da Ammah ta karba a hannunsa nabi da kallo da dan buhun daya nuna abincine a cikinsa daya
aje gefe daya sai kuma na kawar da idona da sauri akan kayan na juya zuwa aikina ina jin Ammah na
fadin malam zo nan ya bita zuwa daki.
Abbu bai karasa shiga dakin ba Ammah din ke fadin yau naji abin mamaki a bakin yarinyar nan da sauri
ya juya ya kalleni yaga ina gyaran wuta ya juyo gareta yana fadin meya faru kuma ?
Tayi ajiyan zuciya mai nauyi ta sake kafin tace sunan uwarta naji ta ambato min a bakin ta kamar a
mafalki fa malam da cewa Nana ko ?
Dan murmushi yayi kafin yace kin dauka duk tsayin nan bata san komai bane ta sani tasan komai game
da uwarta don har hotonta ta gani a dakin nan ai ranan.
Kirji ta dafe tana fadin na shiga uku malam garin yaya haka ya faru yace ban san ya akayi ba amma ta
gani ta kuma san komai zaune takai saman dan gadonsu na katako lokaci guda tana dafe kai.
Wai meye hakan data sani tayi wanin abin asshane a gareki ki natsu kibi yarinyar nan a yadda ta bimu
ban son tashin tashin da zai kawo bacin rai a yanzu kuma.
Hakan bai sa Ammah shiru ba sai bayan sallah insha,i Abbu ya dawo daga sallah ya fita ta zauna a inda
muke zama nan tasa min kira daga daki na amsa na fito zuwa gareta.
Tana zaune a cikin damuwa har lokacin nafito ina fadin gani Ammah ta dago tana fadin barci zakiyi
bakici abinci bane Aeesha ?
Na koshi na fada a razane ta dago kai tana sauke min wani kallo tare da fadin me kikaci kika koshi dashi
ba komai na fada ciki ciki a wani irin yanayi na damuwa.
Waime ke damun rayuwankine haka kika sakawa kanki wanan damuwa haka to ki jini da kyau wallahi
Allahma shedanane Aeesha dani da bawan Allah nan don bamu rageki da komai ba a rayuwan ki .
Yau abinda bawan Allah nan ke dauka a kanki kodashi ya haifeki ya tsaya a nan amma kin bi kin damu
kanki kin tsiro da wasu halaiya na daban a yanzu akan abinda bashi bane gareki.
Yau dai nasan duk abinda wani zai fada maki a duniyan nan mukace dake ga gaskiya dole ki yarda da
hakan a kanki don shine gaskiyan gareki.
Don ba zamu fada maki abinda zai dawo ya cutawa rayuwanki ba daga baya muma ya cutar damu don
muke tare dake ako wani lokaci.
Kuka na dan farayi naji ta sake min tsaya tana fadin ba kuka na zaunar dake nan ki mun ba kiranki nayi
inji waya fada maki wani labari a game damu ko ke ?
Kaina girgiza mata a lokaci alaman ba komai a rayuwana saidai ina mai jin wani iri kasan zuciyana
kamar in kashe kaina don bakin ciki.
Nake ji a lokacin abinda yasani dagowa shine muryan Ammah din dake fadin duk da kin kasa
tambayana labarin