Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
ba komai don nayi sa,a wata yar gidan nasu tana tare da ita lokacin na zata ai ta
fadama na tafi ?.
Bamuyi wanan zancen ba don abinda ke gabana a yanzu bai bari na zaune jin wani zance can yanzu dai
mun kammala nake gani dakon manir kawai ya tsayar dani kasan nan a yanzu.
Salman din ya tambaya da sauri yana fadin ansan inda yakene yanzu ko wani yaji labarinsa yana raye ?
Salman yaushe kazams dan leken asiri haka ban sani ba koda yake ba mamaki tunda kanawa manya
aiki ai ka dade da shiga force ba,a sani ba.
Man wanan zancen ba zai tafi ba ke nan a wajen ka don Allah kayi hakkuri please rudin shedan yasa na
aikata hakan nima nayi dana sanin rashin baka shawara kafin na aikata.
Bayan fitan hjy Nasare ummu ce ta fara magana take fadin hindu nan gidane a gareki don haka ki saki
jikinki cikin yan uwanki a zauna lafiya kada kiyi wani abinda zai sabawa umurnin mahaifinki don,,,,,,,,,
Kallon da tayiwa ummu din lokacin yasa tayi shiru don kallone na ai na sani ba sai kin fada min ba
hakan yasa ummun yin shiru tana alkawari a zuciyarta zata kiyayyi duk wani abinda zai hadata da wanan
fitsatariyar yarinyar a gidan.
Saidai ta kasa gane nufin mijin nata nason ya hada yarta da fitsarariyar yar tasa duk da a zancen shi ta
fahinci so yake yar yasa ta sauya tasan kuma hakan yana da wuya.
Sallama driver gidan ne da ya shigo da yaya babba gidan da kayanta tana fadin kai mutumi ai duk
kudin larabawan ka narka a gidan nan gida haka kamar ba a duniya ba sayadi ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[11/4, 12:30 AM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
8️⃣4️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6
https://sitrix.africa/signup.php?ref=foleesco
Tunda na shiga daki nake tunane meye dalilin Abba mijin ummu na hadani da yarsa hindatu wace sai yau
nasan yarsace ta cikinsa.
Amma neye dalilin daya nemi zuwan mu gidan lokaci guda gida naji kawai ina son zuwa don ba zan iya
zama a innuwa daya da wanan mara mutuncin yar tasa ba hindu.
Har in nace in zauna kuwa nasan za a kwasa dani kan ummu don wanan kallon rainin hankalin da
tayiwa ummu a gabana taci arzikin mahaifinta a lokacin.
Ban san ya suka karasa ba dai kota tafi ko tana gidan oho don na shiga daki na barsu nan falon saboda
ban san ko akwai maganan da zasuyi ba a tsakaninsu.
Lokacin Sallah naga ya gabato na mike zuwa bandaki na fito mukai arba da wanan dattijuwar matar da
suka kira da yaya babba dazun tsaye kofana.
Azatona batan kai tayi ba dakin taso shigowa ba ta fado min nan amma sai naji tace hakan akeso yar
albarka daga hakan ta juya ta fita kawai.
Sam ban kawo a raina cewa wani abu tazo diba a lokacin ba nadai tsaya a ta batane din ta fado min
dakin da nake ciki tana fita na tayar da sallah .
Ban daga ba ina wajen akai sallah don tun ina addua na koma harkan wayana na dade ban bude online
ba sai ranan na bude na fara bi.
Wasu sakonni ke shigo min da akayi da arabiya wasu kuma a wani yare can da ban sani ba sai na
turancin nake bi ina karantawa kan photon dana taba makalawa na mahaifina idan kin tuna mai karatu.
Na shagala dabin abubuwan da aka rubuta har ummu ta shigo dakin ban fargaba saida tayi magana na
dago kai ina dubanta tare da saurin kawar da wayana gefe daya na fara gaida ita.
Take fadin na zata barci kikeyi ai na jiki shiru tun dazun baki fito kinci abincin rana ba idona biyu ummu.
Na fada ina kokarin mikewa daga inda nake zaune don kinsan in akwai abu mai shagalar da bawa a
yanzu bai wuce wanan wayar ba da muke amfani da ita don sai ta dauke ma hankali ka manta da duk
wani abu dake gaban ka.
Hakan yasa har na manta da dan damuwan dake tare dani na zuwan wanan hindu din na shagala da
duban sakonin cikin wayana har ummu ta riskeni a hakan.
Magana nazo yi dake kan yarinyar nan da zata zauna damu gidan nan kallota nayi ban jira naji me zata
fada ba nace da ita ni gida zan koma dama ba tsayi zanyi bama balle.
Saboda zuwanta zaki koma gida da sauri nace a,a dama ina da niyar komawa gida kusan sati daya ke
nan fa banga Abbu ba kuma yace dani zaizo ya dubani nan .
Sai naga tayi dan murmushi ta soma fadin ba zaki tafi ba donta tunda yace zaizo dine ai na riga na
fadawa Abban ku zaki dan kwana muna biyu a nan don haka mukayi dashi Abbu din.
Yanzu kuma sai yaga kin juya kin koma gida kema kinsan ba zaiji dadin hakan ba sai ya dauka bakya jin
dadin gidan nan ne ai.
A,a wallahi ummu kawai dai dan su Abbu da Ammah zan koma kinsan halin anty safiya da yaranta balle
yanzu basu ganin idona sai tsiyatakun da sukai masu dama Asmau itace mai hankali a cikinsu.
Wanan shakuwa taku dai koma dai meye ba zaki gida yanzu ba ki bari a dan kara kwana biyu nan gaba
sai ki shirya ki koma gidan.
Naga kamar kin sansu tun farko to ina son ki kara kama kinki dasu don na fahinci akwai dalilin kawosu
da Alh yayi don shi nake son ki kara natsuwa don Allah nasan kinayi kici gaba da hakan.
Ki bar kumshe kanki cikin daki haka kada ta dauka don zuwanta kike hakan tunda bata fiki ba don na
fahinci bata da tarbiya ko kadan ashe .
Ta mike tsaye tana fadin dama shiya kawoni idan kin hada abinci yana dining ki fito kici nace nagode
har ta juya nace ummu ta juyo tana fuskanta na.
Wayana na nuna mata ina fadin wanan ne mahaifina ko wanan wani irin kallo tayi min tana karasowa
wajen da nake ta karbi wayan tana bi da kallo na dan lokaci.
Na fada maki kibi zancen nan a hankali kura kada kija wani rigiman da mahaifinku zai dauki mataki a
kanki don kinsa yana hake dake dama.
Amma mama daga kiran yarinya sai ya hanata dawowa ya hadata da yaya baba wani abin yaya babba
zatai mata tunda ba aure zatayi ba ?
Ba zakibi zancena ba ke nan sai kije kiyi abinda kikaga dama akai tunda ke ba za a fada maki gaskiya ba.
Ina yar nan yarsa ce dai yau ko yankata yayi kina da bakin da zakiyi magana ke banda kun zamo matan
zamani miji bai isa daku ba ?
Mama ni abinda nake duba shine ko tufafinta bata dauka ba komai data tafi dashi haka kawai yace ya
riketa a wajensa.
Bayan hakan mama ke kanki kinsan halin hindu fa anja mata kunne yaya aka kare balle ban samu zama
da ita na dorata a hanya ba.
Tunda na dauka zuwan suje su dawone kawai zasuyi wai ashe shi riketa zaiyi a wajen sa inga mutunci
aiko ke saiya fadawa niyarsa ko ?
Mutunci fa kikace bayan wanda kika zubar muna a idonshi kura bama shi kadai ba duk garin nan yanzu
waye baisan kece kikai yunkurin halakashi ba har kike zancen mutunci yanzu a garemu ?
Ke da watace mai hankali ai dadin hakan zakiji wanda ya tsameki da yaransa a jikinsa yau ya dawo ya
nuna yar nan tasace har zaki tsaya fadan hauka haka ?
Shiru tayi har uwar ta kare fadanta bata iya cewa komai ba don tasan gaskiya uwar ta fada .
Ba karya kuma ta fahinci gari anji zancen don har makwabta ba wanda ko ke lekosu a yanzu dama dai
sai jefi jefi take ganin mutane gidan nata yanzu ko babu kowa mai zuwa.
Tabbas ta zamo kura abin gudu dama kura a daji aka santa ke nan mutane yanzu sun koma tsoranta
kuma ?
Ta jima a zaune zakice bata falon uwar saida yaya imamunsu ya shigone ta dan dago tana masa sannu
da zuwa ya dan juyo yana ganin irace ya hade fara,anshi ya amsa mata a dakile ya samu waje ya zauna.
Donshi bai kaunar ganinta a rayuwansa sam ya tsani wani zance da zai dangantashi da kura din inba
yazamo dole ba ance hannuka baya rubewa ka yanke ka yar wanan shi kadaine tasu halakan dashi.
Dan dama dama daddy Ahmed zai tsaya su gaisa saidai shima ba sakin fuska a gareta yadda aka saba a
baya.
Ita wanan wai kullum sai tazo gida nan ne wai dacewa kura din uwar ta dan dago kai ta kalleta tana
fadin wai zuwa tayi kan sayadi ya mayar da yarsa hannusa jiya.
Amma wanan bata san ciwon kanta ba shine tazo fadan hakan kome ai gata nan ba fada tazo ba wai
bai fada mata yar zata koma hannusa ba sai cewa yayi Nasare tazo da ita shine ya rike ta daga nan
wajensa.
Kuma ya dauka hjy Lami babba ya hada ta dasu don naji Nasare tace harda wanan yar da akace yar
matarsa ashe tana wajensu yanzu.
Aure zai mata kila koma meye ai yarsa ce ko ita yanzu ina taga bakin magana akan hakan banda ma
dadin da zataji inga mutumci ai taimaka masu yayi.
Kiyi yunkurin kasheni in dawo ince na sanku shege nake halan ai yanzun ga zunubin ki nan kina girba
tun a nan duniya kafin kije lahira kuma Allah ya tambayeki dalilin hakan.
Kin dauka ke kinci bulus ke nan har kina dagawa mutane kai kega mai abin kanta an mutu abar maki
gado ashe bala,i kika shukawa mutane.
Sabodake yanzu mutum baiko iya fita garin nan ya sake sai kaga kamar ana zunden ka zancen nan kinja
muna mumunan tarihi a gari kawai.
Wai ina mamaki yadda zancen nan ya fita har kowa yaji sa duk jan kunnen da maimartaba yayi a
lokacin uwar ta fada tana tambayan dan nata.
Mama zamu iya tare zancen nan ga yan gidan wazirine bayan dama ga yadda aka kwashe dasu da farko
zance kan ai dole ya fita tunda ita tajawa kanta hakan.
Ni zan tafi anji zan dawo ya mike yana fadawa uwar hakan tace dama zancen me kazo dashi saida ya
dubi kura din yace ki bari idan na dawo mayi sai anjima yasa kai ya fita.
Bayanshi tabi da kallo ta juyo tana fadin zamani ni kura kin cuceni a rayuwata wallahi yau harda dan
cikinka baka da kima a idonsa duk a sanadinki kura.
Jin hakan yasa hawayen da take tarewa a lokacin ya zubo mata tana fadin mama ai ko kowa ya gujeni
banda su yan uwana dolene su gujeki kura don ki daukowa mutane zuban mutunci na har abada.
Banda mutane sun san da halin mahaifinku mutumne shi mai adalci aida zancen nan a yanzu yafi nan
daukuwa .
Da tun farko kika fito fili kika fada muna gaskiya tun a lokacin ba a zauna ba ba,a tara jama,a haka
wajen zaman da aka zauna kan zancen ku ba.
Ai da wanan tonon silan da akayi da wata kila zancen bai bazu haka a gari ba da sauri har kowa yaji.
A ina kika samu wanan photon Ayshaa ta kureni da ido tana tambayana tare da zargi karara a fuskanta
don photon na yanzune ba tsohon photo bane.
Ta miko min wayan ta juya ta fita ba tare da ta tsaya tayi min magana ba yadda ta fita rai a bace sai
banji dadin hakan ba.
Kasa fita nayi zuwa cin abincin saida darene na sameta a daki tayi zaune a inda ta idar da sallah kuma
ba addua takeyi ba.
Nakai gurfane ina fadin ummu kiyi hakkuri don Allah ko baki son haduwana da mahaifinane in hakkura
da zancensa ?
Sai lokacin ta dago ta dan kalleni tana fadin Ayshaa ke yarinyace duk da kina ganin kina da wayau a
yanzu saidai ina son ki sani wayau naki ragagene.
Duk yadda kikeji game da mahaifinki na fiki jinsa Ayshaa nafi son ai maki gatan da sai ya biyoki da kansa
nan yadda ya gudu ys barki ya dawo da kansa daukaki.
Amma kin kasa gane hakan wanan yasa kike ganin kamar ban damu da matsalan naki ba a zuciyata.
Don Allah kiyi hakkuri ummu daga yau na daina duk wani zance daya shafi mahaifina indai hakan shine
farin cikinki dani.
Ta kalloni na dan lokaci cikin mamaki kafin naji tace indai kinyi hakan kin kyautawa kanki Allah yai maki
albarka na amsa da amin tare da mikewa zuciyata cukushe da bakin ciki.
Don nasan haka zan tabata indai sai mahaifina ya tako kafansa kasan wajena zan sadu dashi a duniyan
nan.
Yadda nake jin suna zancensa yana da wuya ace yazo wanan kasan nema na balle yadda sukace saboda
yan uwansa ya gujeni saboda al,adansu.
Hakana kwanta ina faman tunane akan zancen mu da ummu din hakan kuma na karayiwa kaina
alkawarin na daina damu da akan zancesa daga wanan ranan insha Allahu tunda haka ummu ke so.
Takwas na safe ina kwance saman gado nake jin hayaniya yana tashi a gidan duk girman gidan amma
kana jin muryoyinsu cikin tashin hankali.
Wai ashe hinduce take masu kwaya a gidan haka wanan hjyn mai zageyen mu tana kuma zama damu ta
lurar damu kan duniya.
Taje tayar da ita don tayi sallah saboda bata tashi tayi sallah akullum sai tayi ta zageye tana mata cin
mutunci zata sakata gaba dole ta tashi tayi sallah.
Shine ranan tana zuwa ta samu hindu din kamar wace tasha wani abu ta rikice masu har da buga kai a
bango kamar tayi hauka.
Matar ta fito hankali tashe ta tayar da masu gidan tana fada masu abinda ke faruwa shine Abban ya fiyo
ya nufi dakin da kansa.
Yadda tayiwa matar haka tayi masa daidai ina fitowane naji yana waya cewa ku shigo muna falo ai na
rufeta a dakin.
Man ne da mahaifinsa sai daddy imamu suka shigo suma hankali tashe don Abban yace dasu ta
haukace.
Sun lekata sun fito duk muna tsaye cirko cirki a cikin tashin hankali can dubi kowansu duk hankalinsu
a tashe yake.
A hankali nake fadin wai ba anxieties ke damunta ba kuwa don wanan ba wai anihin hauka bane hakan
?
Sai lokacin ya juyo yana fadin exactly nima nayi tunanen hakan tun shigowan mu duk suka kalloni nace
shine ma don rashin shan da bata samuyi ba kwana biyu zai iya haifar mata da hakan.
Kamar lissafi ya bace wa kowa sai lokacin suke fadin hakan zai yuyu don kuwa dole fitan kwaya a jikin
mutum saika koma kamar karamin mahaukaci.
Yanzu barishi Anwar yazo na kirasa yace yana hanya daddy imamu yake fadan hakan garesu saiga
wanda suka kira Anwar din ya shigo da kayansa na likita a jikinsa ya fara gaida iyayyen nasa.
Kafin ya kallo mahaifin nasa yace tana ina gata can a daki muje daddy ya fada yayi gaba donshi
mahaifin nasu zama yayi kallo daya zakai mai ka fahinci yana cikin damuwa matuka.
Daddy dawo bari mu shiga ni dashi Man din ya fada yabi bayan likitan suka samu waje suka zauna ganin
hakan yasa nace da yaran mu shiga daga ciki don duk sun tsorace.
Tattarasu nayi muka doshi kofan dakin wani ihu data saki dole yaran suka nufi mahaifinsu a firgice
saishi hamza dake dan wayau ne ya tsaya tare dani.
Hjy Nasare naji ya kira yana fadin duk abinda kikeyi ki shigo yanzun nan don Allah ya kashe wayan yana
shafo kansa cikin damuwa.
Tun muna jin ihunta har muka daina ji can hjy Nasaren ta shigo yace a kaita dakin ummu ce ta kaita
duk hankalinta a tashe lokacin saboda bata san abinda ya samu yar nasu ba.
Zuwa can sai gata ta fito tana kuka itama tace wai hauka tayi kome yace ga zahiri kin gani tattara kowa
nayu muka bar falon iyasu kadai muka bari a falon muka shige ciki.
Gun anty baraka muka taru kowa ka kalla yana cikin damuwa yaran duk suka make min a jikina dole na
kyalesu don nasan basu saba da ganin tashin hankali haka bane.
Sai wajajen biyu muka fito lokacin barci takeyi sosai don alluran da akai mata na barci ta kuma samu
barcin sosai tayi.
Bayan sallah la,asar ne muna zaune falo don daga ummu sai wanan matar dake gidan donta suke
sintirin dubata a dakin.
Mukan bamu shiga ba har lokacin amma kowa na a cikin damuwa gaskiya don ba dadi kaga dan
uwanka musulmi a cikin wani bakon yanayi na tashin hankali haka ?
Idan kana da imani dole ka damu don kaima baka san yadda zata kasance da kai ba wata rana .
Sallaman matan nan na Royal family yasa mu dagowa muna amsa masu tare da gaidasu da zuwa suka
amsa muna anty barakace ta mike ta kaisu dakin da yar tasu take lokacin ummu da wanan matar suna
dakin suma.
Kokarin tasha maganin da likita ya bayar a bata sukeyi sai gasu sun shigo daki na mike na shiga dan
kewayawa na dan dauki lokaci ban fito ba.
Zan fito ke nan naji murya na fadin wai baki ganin wani abin akaiwa yarinyar nan ta koma haka hjy don
wanan abin abin dubawane fa hjy ?
To kina ganin wani abu akai mata kome dayan matar ta fada naji dayan tace meye bai yuyu hjy mami
tunda matar nan da gani idonta a bude yake .
Kofan na bude nafito sukai tsuru tsuru cikin daburcewa nazo zan wucesu ina gaidasu suka amsa tare da
bina da kallo a cikin tsarguwa.
An dan jima saiga Abba ya shigo dasu daddy suka shiga dubata saida suka fitone gaba dayansu a falo
suka zauna ana mayar da zancen.
Nan wace na sama tana maganan take fadin da dai