Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
yaken yana ayyanawa a zuciyarsa keba kowa bace Aeesha amma kuma kina da
komai da ko wani namiji yake son mace dashi.
Lokaci daya kin yaudari zuciyata da dabi,unki Aeesha dariyan ta da murmushinta kadai ya canza dukkan
rayuwata a yanzu ga baki daya lokaci guda.
Anya zan iya jure rashin mace irin ki a rayuwata yanzu don kallo daya idan nayiwa yarinyar nan yana
wanke duk wani matsalan rayuwansa a yanzu duk akwai yarinta da kurciya a yarinyar haryanzu saidai
tana Abu kamar babba saboda tarbiyan data samu run farko.
Ya sauke kai a karshe yana anyana kota tsiya kota arziki malaki Aeesha a rayuwansa don sai ya kauda
duk wani tsarko da zai kawo masa cikas a rayuwansu.
Ajiyan zuciya ya sauke yana bude ido suka hada ido da mami dake tsaye tana kare mai kallo cikin
yanayin mamakin ganin yadda ta sameshi a lokacin shi kadai yana faman murmushi tare da sauke bacin
rai a karshen tunanensa.
Fuska ya tsuke lokaci guda don ganin mami din kada ta fahinceshi ta masa kan wani dalili nata da
baison ji a yanzu wanda kusan yana son kawo baraka a tsakanin suma ko har ya kawo din zaice.
Uwar ta gane sauyin fuskan nasa a lokacin hakan yasa itama ta hade nata fuskan ta zagayo da abin
awon data shigo don' ta aunashi tana fadin da alama na katsema jin dadin ka ko ?
Ina jin dadi ga wanda ke zaune ya fada cikin bacin rai yanayinka ya nuna kana cikin shauki da damuwa
wani abu da kake gap da rasawa ko ta jawo kafan nasa tana fadin hakan.
Dan kara ya sake kafin ya kalli fuskanta yana fadin ni dai zanso daddy ya canza min wani likita mai
tausayina a yanzu gaskiya.
Bissimillah ko yanzu kana iya kiransa ya sauyama din nima nagaji da duban wanda baijin maganata
wanda bai san na isa dashi ba.
Mami ke nan indai akan wanan yasa ake min keta a kafata yanzu ki daina donni nagama abinda ya
kawoni nan very soon zan barku in koma inda na fito.
Wani kallo tayi masa cikin shock tana fadin watau dai har yanzu kana da ra,ayin komawa kasan nan ke
nan duk da mai martaba ya nuns maka baison hakan garemu yanzu.
Rayuwansa daban tawa daban don haka ba abinda ya shafesu dani saiku yayansu ni ban cikin tsarinsu
nasha fadan hakan ko yaushe.
Dan matse kafan nasa tayi da gangan tana fadin ina tausayinka yaron nan da kafiyan nan naka ka amsa
da yes kawai zance ya kare asha buki ka dauki matarka ku tafi taje can ta idda karatunta wazai takurama
ga hakan kuma ?
Bai kara magana ba har tagama mai dressing ta fita yana zaune ya rike habarsa ko gezau bai kara mata
ba tasan halin miskilin dan nata hakan yana nuna yayi fushi da zancen da take masa a lokacin.
Ta fita tana mamakin hali irin na hjy kura da zatasa su takura wa yaron nasu kan wani dalili nata duk dai
haka all,adan masarauta yake dama kusan sums duk hadine irin ta masaurata akansu din.
Amma yanzu zamani yazo da ko wani da yake da right din zabawa kansa abinda yake gani daidai a
garesa ba tare da takura irin na baya ba.
Ita kanta saboda halin hjy kura bata son wanan hadin da sukeson yi a yanzu din taxi bukatan abinda
danta keso amma ba halin ta mara masa baya ya zamo na farko wajen bijerawa iyayyen nasu a tarihin
gidan.
Ina shiga dakina tsaye nayi ina mamaki yadda ya koma cikin dan kankanin lokaci kamar rufe ido a bude
komai ya sauya a dakin ga baki daya lokaci guda haka.
Dan madaidaicin gadon mai ban sha,away da komai nasa set gaba daya nabi da kallo ga akwataiyana
dana aje gefe an sauya masu waje a yanzu.
Kalmanshi ya fado min a rai da yake fadin nerve given up in life rayuwa zata iya sauyawa bawa ko wani
lokaci yau gashi na sheda hakan kuwa.
Ya sauya min rayuwa dani dani da iyayyena har da yan uwan dana sani a lokaci guda.
Hakan yasa na sauke ajiyan zuciya tare da zama a bakin gadon karo na farko a rayuwata da zan zauna a
saman gado cikin gidan mu run tasowana a rayuwata ke nan yasa na zauna da bissimillah a lokaci a
zuciyana.
Ajiyan zuciyana sauke ina dago wayata dake hannuna wanda tun shiga gidan akwai yake hannun farida
sai da zan shigo gida ta mika minshi.
Bude wayar nayi sai ga soko nagani na bankina na bude sakon daga MB kamar yadda nayi serving din
sunansa nagani ya turo min da kudi daidai adadin yawan abinda na kashe a jiya din wajen electronic din
da muka sayo.
Mamakine ya kasheni da sauri na duba massage dinsa ya rubuto ba nauyiki bane yin hakan nauyin
bawan Allah nan ne duk wani jindadin ku a yanzu wanan nauyinane ga kudinki nan na dawo maki dashi
da sauran abinda na manta nayi maki na rayuwa.
Shine na rubuta masa why MB zakayi min haka kada ka manta ni yar tallakace kada ka saba min da
dadin da ba zan juri gushewansa ba fa ?
Dadi kin kama jinsa ke nan a rayuwanki tunda kina tare da MB a yanzu sai kince yayi maki yawa zan
daina.
Kada kasa iyayyenka suyi kuka dani a yanzu fa kan hakan suce ina kwashewa dansu kudi ina kaiwa gidan
mu mb yana ciyar damu da komai nasa.
Ki sani MB ki ba rago bane daya dogara ga a bin iyayyensa nashi yake nema ta hanyar halakan irin ku
dubu Mb zai iya kula dasu yarinya a yanzu.
Niba kudi ko kyalkyal banza nake son gani ba mb nake son gani gaba da gaba naga halinda yake ciki a
idanuwana .
Karki damu da hakan gone Auwal zai kawoki nan har wajen mb sai ki shirya haduwa da mb din shine
na mayar masa da amsa da yasashi dariya har salman din ya fahinci dani yake online a lokacin.
Wanan ya kawo badakala a tsakaninsu har mami ta shigo ta samresu saidai bata fahinci kan musayar
bakimsu ba lokacin harshi salman din ya fita
Babu komai a zuciyana ranan sai farin ciki kusan duk wanda ke gidan mu ranan da abinda ke cikin
zuciyarshi a lokacin musan man nida iyayyena da abin ya shafa kowa da abindake yawo a zuciyarsa.
Ni dai a bangarena ina ganin nayi dace a lokacin don ba kowace mace bace zatayi sa,an dace irin wanda
nayi na haduwa da MB a lokacin.
Sai har na kasa hango matsalan dake akwai a tsakaninmu wanda zai iya haifar mana da matsalolin da
ba a so masu muni daga baya saboda idona ya rufe a lokacin na fada tarkon soyayya lokaci guda nake
ganin ba abinda zai iya kawo muna tsaiko a rayuwa.
Yayin da Abbu da Ammah su kuma da zullumin hakan suka kwana don sunsan yana da wuya iyayyen
Man Bashir su yarda da auren mu ba tare da sunsan waye takamaimai din mahaifina ba.
Abu daine idan rabon mutum ya ratsa a jikinka sai kaci rabonka don haka wanan abubuwan da yake
min a yanzu yana yin sune akan rabonane naci dani dasu daga gareshi kawai.
Don sun dade a daren jiya suna tataunawa a tsakaninsu karshe dai sukai min adduan fatan alheri da
samun sauki a rayuwa na mafita mai kyau.
Washegari kan ban fadawa kowa komai ba na shirya tsab da zuman fita school amma a zahiri kwaliyan
zuwa wajen MB nayi in dubashi idan mun fito break kafin mu koma Auwal zaizo ya kaini ingaidashi.
Anty safiya kasa daurewa tayi saida tayi magana nace kinsan yau Monday ce anty ko bature yana
girmama ranan ai.
Yan aji dai sai satan kallona sukeyi ban kula kowa ba ina Allah Allah lokaci yayi in ware saima naga
lokacin yai tsawo a ranan daya da wani Abu kuwa Auwal yazo ya daukeni shima sai sheri yake min
bandaiyi magana ba na kyaleshi.
Komai na jikina marching color ne shigar ya tafi daidai nasan gidan wancan zuwan da mukayi in group
da sauran course mate dina don haka wanan karon ban tsaya mamakin mansion din ba saboda nayi a
wacan karon da mukazo a cikin taro.
Saidai motocin da muka ganine a haraban gidan yasa Auwal fadin akwai baki a gidan bari na kirashi
muji saidai yayi kira bai dauka ba yasa yace mu shiga kawai ciki kai tsaye.
Wani hanya muka bi ba wancan da muka shiga wacan karon ba wanan ta baya yake wajen lanbunsu
muka bi.
Sai gamu a katon falon dayake mallakinsa .
Falon daya sha kayan alatun zamani iri iri farare kal dasu ga kayan motsa jikinsa nan a gefe daya zube .
Yana bude kofan ya tura dariyansune ya shiga kunnuwan mu a lokacin yayin da su kuma suka juyo
lokaci guda garemu.
Kasa hade dariyan dake fuskansa a lokacin yayi yana mai zubo muna idanusa yana bin mu da kallon a
cikin mamaki fuskansa daya baiyana karara a lokacin.
Sannu a hankali duk suka juyo suna sauke kallonsu a kan mu suma don suga meya dauke masa hankali
haka har ya sake kafan daya hana mami tabawa a lokacin.
Inda nima kallon kafan nasa nakeyi cikin tashin hankali don ban dauka har ciwon yakai haka ba ashe
ban damu da duban ko suwaye tare dashi ba a lokacin ga damuwa karara a fuskata dana nuna lokaci
guda ina bin kafar tasa da kallo.
Sai mahaifin nasane yace ku karaso daga ciki mana sannu ku da zuwa Aeesha ko dalibar man bashir
ashe kin samu labarin abinda ya samesa ?
Lokacin naga matan dake falon tare dash cikin shiga ta alfarma duk sun sake kalloni da yar kunya na
karasa dan takowa saidai har lokacin banyi nisa da kofan shigowan ba don girshin da mukai masu.
Au ko itace yar kwara din tasa data dauke masa hankali take kokarin hanasa yi muna biyyaya a,a lalai ?
Lokacin na dago ido daga kallon kafan nasa dana shagala dayi tun shigowan mu na sauke kan wace ke
magana din bakace yar karfafa da ita ga kuma alaman hutu ya nuna a jikinta.
Amma hakan bai hana aga bakinta na asali daya baiyana ba a jikinta duk da gyaran da jikin ke samu na
gata.
Dan tattara natsuwana nayi na fara gaidasu ina fadin ina wunin ku ya mai jiki kuma cikin jin kunya tare
da girmamawa ?
Jiki Alhamdullahi ai da sauki gashima ana daga dashi ya taka yanzu yana shagwaba abu ga dan dangi
dan asali.
Au ko kece Aeesha da nake jin labarinki a wajensu lalai tubarkallah masha Allah, ashe kuna tafe kin
samu labarin gwarzon naki ba lafiya ke nan umman salman dake gefen kafadan shi zaune take fada na
dan fadada murmushi nace jiya nake jin abinda ya faru cikin sanyin murya.
Karaso ciki mana ku zauna Auwal ka tsaya da ita daga kofa kuma tana nuna muna kujeran da ba kowa a
sama dake gefe daya.
Wai hjy hafsat dama haka kuke barin ko wani banza na shigowa gidan yadda sukaga dama ko wani
lokaci babu kwabo ko security a kansa?
Dayan matan da tunda muka shigo batayi magana ba sai bina da kallon banza tana watsarwa da takeyi
run shigowan mu.
Wanan dai da gani kin san barbaran yanyayawace ba tarbiya garesu ba hjy kubura irin yayan nan ne na
tsaraban saudiya saiko dai idan ubantane ya auro yar gantalin Arab yazo da ita oho ?
Dayan tace kinsan maza da son farar mace wanan inba fari ba meya gani a wajenta shi zamanta kwara
din ne ya baka sha,awa kome ?
Dadin abin dai dan asali sai yar asali ko mutum yaki kuwa don mu da asali muke ado ka rike wanan
kalman tawa ka aje.
Ta fada tana mikewa wanan dai matar dake magana a gadarance ta sake fadan hakan ta mike tsaye
tana gyara gyalen jikinta.
Har zan kai zaune saina fasa da sauri ina mikewa sai naji umman salman na fadin haba dai da girmanki
kuma kike wanan abin gaban yarinya karama hjy kura.
Nan daddysa ya dauka da fadin no bansan yaushe zakuyi girma da wanan halin naku na nunawa dan
adam Shiba komai bane.
Common, come here, naji ya fada ba kuma kunyan hakan a gabansu yasa na danyi kasa da kaina lokaci
guda son kunya.
Come closer, come and have you sit here ya sake fada wanan karon tare da dan dagowa yana nuns
alaman dani take tare da nuna min wajen da mahaifiyarsa itama ta mike daga zaunen da take gabanshi
saman Stoll.
Gashi ya tsureni da idonsa akaina alaman dai dani yake a lokacin kan in taho inda ya nuns min in zauna.
Kije Auwal ya rada min hakan yasa nabi umurninsa na taka zuwa garesa din na zauna a Inda ya nuna
min ba tsoron komai a zuciyana lokacin.
She is my girl friend and this my aunt's ya nuna min su da hannu sai hjy my lovely umma and my mami
too you already know Dad before na dan gyada kai alaman eeh sai kuma ya juya wajen umma din yana
fadin.
Hjy wanan ce Aeesha daliban da tafi kowa hazaka a fanin mu kuma nake ji da it'a sosai a ,,,,,,,
Kai dakata da wanan iya shegen naka na banza kaji ni da kyau ke ki jini da kyau in kina jin hausa in
kuma sai turanci ko larabci ki samu wanda zai fassara maki hakan.
Wanan da kike gani ke ba hadin kifi da kaska don yafi karfin ki wanan maimakon taga fushi a fuskana
sai murmushi na sake cikin karfin hali a fuskata.
A cikin harshen larabacin dana matsa kaina na koya don bacin rana irin wanan tun ina karama na koyi
larabci kuma na iya.
Umma since take magana tace na dauka duk abinda suke min a wasane don haka kada in damu dasu
na gyada mata kai da na,am.
Sai naji suka mike fice da ita da mami din nasa ganin abinda yan uwan mijinta ke shirin aikatawa a
lokacin.
Suna fita naji daddy din yayi wata tsawa tare da fadin hjy Amina bazan dauki cin zarafin kowa a gidana
ba
Damage nasani ai yaya da saninka make komai dake faruwa ta juya ta fita tana sababi tana aibantani
haka yar uwar ta watsa min kallon tsana itama ta fice daga falon.
Sai lokacin na kula da wanan hindatun da suke zaune ashe falon sums kamar basu cikin falon a lokacin .
Naji mamaki kwarai yadda yayi mata tsawa ta fice da sauri tare da yar uwar ta lokaci guda har suna
hada kafa wajen fita.
Dan shirune ya biyo bayan fitansu kafin daddy nasa yace kada wanan abin ya dameku Ku barni dasu
kawai zanyi maganin su shima ya fita.
Shi ko dan nasa sai faman murmushi da yakeyi a fuskansa baice komai ba har daddy din nasa dana ga
alamun so karara yakewa dan nasa ya fita.
Sai can ya kalloni ina zaune na sada kaina kasa zuciyata tana min suya da kokarin rufewa lokaci guda
kan abinda ya faru din.
Muryan shi yane naji ya ratsa min kunnena da fadin .
Are you OK hakan yasa na dago naga yana kallona na daga masa kai alaman eeh iam OK din kamar
yadda ya tambaya .
Sai naji yace right yana kokarin daga kafar ya sauke ta kasa yacewa Auwal ya dauko min abin sha
lokacin nace dashi.
No iam going dama nazo naga jikin nakane kuma Alhamdullahi naga da sauki so ni zan koma don ina
da lectures three .
So yanzu kin gani hankaliki ya kwanta ko na dan kara murmushin karfin hali ina fadin gaskiya hakane na
mike tsaye ina karasa fadin hakan.
It's means kin dauki zancen su da zafi ke nan ko na ji ya jefo min tambayan a bazata.
Da Saudi na girgiza masa kaina cikin alaman dakewa nace ba komai ai Allah ya kara lafiya na juya ta
hanyar da muka shigo na fita da sauri Auwal ma ya biyoni yana kirana saidai ban kara juyowa ba.
Saida na fita na hango fitar matan tare da yaran nasu gidan sai lokaci naji hawayen bakin ciki yana
sauka min a fuskata lokaci guda
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[8/19, 9:03 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [8/15, 07:30] Seenabu Makawa: M/C COLLECTION
MAKAWA COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES,
BAG, COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER
KIDS,FASHIONS etc
LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
2️⃣6️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1ftp
Hjy kura dake tuki a haukace cikin tashin hankalin abinda idonta ya gano mata ta juyo tana fadin watau
hjy Nasare matukar ba rabashi da yarinyar nan akayi ba babu yadda yaron nan zai lankwasu muna a
yanzu matukar wanan tana cikin rayuwansa.
Abune mai wuya hjy kura rabashi da ita yadda like nufi farat daya haka don ni kaina badon na daure ba
ba zan iya ciwa yar nan mutunci haka a gabanta ba don' yarinyar nada kwarjini matuka a idon mutum.
Gumi taji ya zubo mata kamar wace aka watsawa ruwan zafi ta dankai hannu ta share kafin Dan juyo
kallo year uwar nata tana fadin .
Nasare ki duba fa yaron nan tunda ya kyala ido yaga yarinyar nan gaba daya lokaci guda ya birkice har
ya manta ko suwaye a tare dashi hankalinsa gaba daya ya koma gareta.
Amma aisu iyayyen nasa basu kula da hakan ba basu san babban illa bace jefo iron su a cikin zuria don
a karshe gaba daya zata jaye masa hankalinne ga kowa sai ita da yan uwanta ai mugun abin a cikin jini
yake masu rabu da mace maikyau kinji hjy balle wanan din da idonta ya bude haka lokaci guda .
Ki duba sai wani nuna yakeyi tankar baisa damu a wajen ba tunda tazo fara,a ya sauka a fuskanshi
danice ke kawai hakkura zanyi da zancen hadin nan yaje ya karata da ita shi zai