Chapter 83 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   83 / 109

246K to 249K   out of 326.5K words

an hada mata da rukiya gaskiya bata tashi yin ciwo
haka ba saida ta dawo nan gidan wanan abin dubawane gaskiya ?

Kai hjy abar wanan zance don Allah tunda har likita yace ga abinda yasa hakan gareta tunda angano
abinda ya jawo mata hakan aida sauki kuma ga sauki anga ya fara samuwa ai dama yakan faru hakan
wani lokaci ai hjy mami ke wanan maganan.

Altine me kike nufi da zancen nan kina nufin a gidan nan ta gamu da laluran nan wai meyasa kuke
sanin gaskiya ku take sanine wai ?

Duk wani hanya da zatasha kayan maye a rayuwanta na tosheshi kwana biyun nan babu yadda za ayi
kuma ta samu shine fa duk ya jawo mata wanan matsalan .

Allah sarki dama kasan ance mai kishiya bata mutuwar Allah wata kila ni suke zaton nayi mata hakan
don tana yar mijina ko ?

Umma dake gefen Abba ta fada ya dan juyo yana fadin tarrik tarrik ya isa hakan don Allah zancen nan
bai kai can ba kada ku juye wanan zance zuwa wani abu kuma ga gaskiya kowa yasani.

Dama hakan sai ya kasance da ita abin ma yazo da sauki sosai tunda tana samun kula shi Alh ai yasan
hakan zai faru dama likita tun can ya fada muna hakan .

Daddy ke fadan hakan ga matan da suka so juya zancen zuwa wani sabon abu ga ummu don a nufinsu
ummuce tayi asiri ga hindu din ta samu wanan matsalan na enxieties .

Allah da Annabinsa sunyi gaskiya akan zato zato zunubine koda ya zamo gaskiya don lamari da zargi a
duniya baiyi ba.

Karshe dai ummu mikewa tayi tabar falon hakan ya nuna har lokacin bataji dadin wanan zancem ba .

Dayawa daga cikinsu sun fahinci hakan a lokacin saidai Allah ya taimaka ba wanda yayi maganan
hakan a fili.

Nice dai bayan shiganta dakin na bita na samu zaune take bakin gado ta gama waya da Ammah na
shigo.

Ganina yasa ta dan waye tana kokarin boye damuwanta gareni maganin Aliyu nazo karba a lokacin don
yaron yana fama da tari.

Har na karba zan fita naji tace Ayshaa kinga mutanen nan suna kokarin dora min laifin matsala yarinyar
nan ?
Ina ruwana da zamanta ban taba damuwa dasu ba a duniyan nan tunda nasan kafin na auresa yana
dasu don me zan damu kaina yanzu a kansu har in tsaya ina wani asiri can ta lalace bayan nasan nima na
haifa.

Kiyi hakkuri ummu dama haka mutane suke don Allah kada wanan ya dameki ma kowa yasan tana
wanan abin saidai idan sunso ganin laifinki.

Shigowan Abban yasa na fita da maganin a hannu ina gaidashi kodana fito zanje part din su anty
baraka inda yaran suke na samu bakin sun fita gaba dayan su .




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[11/5, 10:47 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:




JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

8️⃣5️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6



https://sitrix.africa/signup.php?ref=foleesco




Zaune yake a saman wani katafaren kujera ya kurawa takardan dake hannunshi ido a daidai lokacin wani
yaronsa yashigo office din da wata yar karamar laptop a hannunsa.

Nufar mutumin yayi yana gaisheshi kafin ya mika masa yar laptop din hannun nasa dago kai mutumin
yayi yana tambaya ?

Wanan yarinyar ce a cikin kwanakin nan tana yawan bibiyan shafin mu sir tare da wasu bayanai akan
mu .

Cikin rashin kulawa da zancen da PA nasa ke fada masa yace daga ina yarinyar take me kuma take so a
kan mu ?

Kai tsaye PA nasa ya basa amsa da yar Nageria ce sir amma kuma,,,,,,,,

Shiru yayi don ganin yadda shugaban nasa ya fisge na,uran a hannusa yana mai kura idanunsa akan
photon profile din dake jikin yar computer.

Mikewa yaga yayi zubur yana fadin yatace bilal yatace ita din diyatace dake zaune Nageria.

Kallon tababbe ya soma yiwa maigidan nasa donshi a iya saninsa bai taba jin ance yayi wani aure bayan
matarsa Salima wace yar uwarsuce ta jini ita Salima din wanda kowa yasan da hakan.

Yau kuma zaucewa zaisa yaji shugaban nasa na kiran wanan bakuwar fuskan da yarsa ce yarsace ta ina
ya samo ta haka ?

Shima ya daiga kama a tsakaninsu sosai don tana da komai na ahalinsu wajen kamanceceniya amma
aida yawa ana kama din kuma ba,a hada komai ba.

Bai kara zarginsa ba ga shugaban nasa yaji ogan nasa na waya da babban yayansa yana fadin ta nemoni
Abdulrashid yata ta nemoni da kanta daga Nageria.

Yadda yake maganan yasa P A din nasa mutuwan tsaye sai yake ganin shuga ban nasa ya zare lokaci
guda don shi dai a iya saninsa yasan ogan nasa baya haihuwa akace.
Yau sai gashi kuma yana jin yana ambatan yarsace ta cikinsa kuma wanda ya kira yana fadawa din yasan
ba wasa a tsakaninsu.

Amsan da yayan nasa ya bayar da fadin Alhamdullahi ka tabbatar da Aysha ce kake magana da ita ?

Idan dai ba sherin yanan gizo bace itace nake gani ita dince ma tabbasa don hoton dake saman dp din
maishi sak itace.

Mu hadu a gidan baba dakai karfe biyu ayi maganan jin hakan yasa P A din kuresa da idanu ya kula da
hakan yasa ya sake masa murmushi yana fadin kana mamaki ko ?

Diyatace ta cikina dana haifa Allah ya baiyanar min da ita don mahaifiyar ta bakar fatace mutumiyar
Nageria sai a cikin wanan shekaran Allah ya baiyana min su.

Shikan bai iyacewa da shugaban nasa komai ba fita yayi yana dan murmushin yake cikin kibincewa don
abinda yaji yau yake gani kamar a mafalkine zancen.

Kuka takeyi sosai gaban mahaifiyar nata tana fadin maganganu marasa dadi ga tsohon mijin nata da
matarshi da suka zargawa wai itace tayi ma hindun asiri data zauce.

Dama an kulla kulleleniya ne donta koma gidan a halakata ya zamo daga diyan ummu sai su kadai a
gidan Abba din.

Uwar na zaune cikin takaici da tashin hankali donta rasa abin cewa ga yar nata dake ta karamin hauka a
falon nata kan laluran daya samu yar nata.

Shigowan yan uwanta da matansu gidan ya dan dakatar da ita ga abinda take fadi saidai suma din binta
suke faman yi da kallon mamaki ko meya sameta hakan da suka sameta.

Daddy imamune ya fara magana yana fadin ita wanan meku ya sameta haka ?

Gata nan dau duk akan abinda ya samu yar nata take wanan abin tunda ance ana ganin kamar asirine
akai mata kasan yanzu ba abinda mutum bai iya yi a zamanin nan .

Mama wa zai tsaya yiwa yarinyar nan asiri kuma kan wanan take wani zabura haka bayan abinda ta
shukane take girba a rayuwanta.

Wa ya ja hakan ga yarinyar nan idan ba ita ba yarinya tana neman tafi karfin mu a gari ko incema tafi
din wanan abin kunyar duk wa ya jawoshi idan ba ita ba.

Ita a dole gasu yan gwal ta kashe ubansu da karfi da yaji ta sakar masu dukiyansa sun wullakanta yadda
ransu yake so.

Yanzu ga sakamakonshi nan ai kin fara girban tun anan duniya kinyi arziki wallahi Amina Sayidi ba irin
zuciyana yake dashi ba .
Don da saidai yarinyar nan tabi titi saboda kwaya ba wani asiri hjy da akai mata kwayan da bata samu
bane kwana biyu yaja mata wanan abinda takeyi.

Don har ya fara taba mata wasu sassan jikinta shi sayadi ai yana da dubaiya wallahi danine hjy yarinyar
nan ta dade bata karasa bugawa ba tunda kwadayi da sakaci itin ns uwarta yaja mata hakan.

Sai zance kakeyi imamu haka kamar abin bai dameka ba akanta aka fara shaye shaye meyasa basuyi
haka ba sai ita ana maganan gaskiya ku tsaya ku duba kana wani zance can mara dadin ji kuma ?

Tunda kaji an soma fadan kamar asirine wanan abin ya kamata ku tsaya a duba tun yarinya bata
salwanta muna a banza.

Tunda kowa na zancen wanan matar daya kwaso wayau ta yayi yawa kowa bata yarda dashi ba har
yanzu cikin family din nan.

Ayya mama don Allah ku cire hakan ba wanan zancen sam wallahi haka yakewa irin masu shaye shayen
nan idan yai yawa a jikinsu hjy mami ta fada da yake ita likitace gata yasa ta aje aikinta a yanzu.

Wani kallo ta watsowa diyar yar uwar nata kuma surukar ta kafin tace a naku karyan na likitoci ba ga
zahiri kuna gani sai ku juya zancen sai abu ya lalace ku tsame hannunku kuma.

Mama daga can muke fa yanzu munje mun kara duba yarinyan nan ne kuma da alaman sauki sosai a
jikinta yanzu don mun samuma yar wajen ita hjyn shi sayadi din tana bata abinci kuma tanaci normal ba
wani garaje.

Kun daiki zance nane uwar ta fada tana kawar da kanta gefe daya cikin takaici da zancen da daddy ya
gama fada din.

Ga abin magana kura nason fada tana tsoron yan uwan nata tasa yanzu tana saka baki imamu zai mata
tas saita raina kanta tunda da fada ya shigo kanta.

Watau mama ba zaku gane bane da alama hindu ta dade tana wanan harkan ba a kula ba don haka
raba ta dashi a yanzu wani yakine kuma dole sai tayi hakan.

Wanda ke jikinta bai samu abincinsa kinga yanayi kasa bai zuwa inda yake kaiwa ya taru mata shine
yasaka hakan take abu kamar tabuwa aina fadawa su hjy Turai dazun ba duk asiri bane lamarin abin ne
yake zuwa da hakan.

Kenan haka zatayi ta hauka aji dadin fadin ta samu tabin hankali a yadawa a gari dan mutuncin daya
rage kuma ya zube ta sake tambaya.

Mama don Allah bar zancen nan wani mutunci kuma yanzu ake nema gun wanan mara imanin bayan
wanda ta zubarwa kanta.

Don dai mukan bamu zubar da kimarmu ba don munsaiwa kan mu daraja kowa kuma ya gani ai munyi
kokari da sayadi ya dawo cikin yan uwa lafiya duk a sanadin mu .
Kinga ke nan ba wanda zai zargemu a yanzu saidai ita da mataimakanta da suka salwantar da dukiyarsa
tare suke da kunya don kaf hwargwado dai duk abinda ta kadar nasa masu amfani ya dawo da abinsa a
hannunsa yanzu .

Wani kallon tsoro kura din ta dago ido tayiwa yayan nata imamu dake fadan hakan yace kwarai kinyiwa
kanki kura don yanzu wa gari ya waya ba ke da zurian ki ba don dai kinji abinda baba yace ai kunci gadon
ku keda diyan ki .

An kuma rubuta an aje zancen ya zauna a hakan shima manir muna saka ran dawowan shi nan da yan
kwanaki watau kinga ke nan shi baiyi fushi da diyansa da kika gurbata masa ba saidai ke .

Shi manir din ansan inda yake ne uwar ta tambaya a gadarance za a dai sani tunda magaji ya sa hannu a
aikin ai an gama kuma don sai ya dawo dashi gida gaban mahaifinsa.

Waya sani ko nasa haukan sai yafi haka tunda mace ma tayi hakan inaga namiji kuma shida ta sake yabi
duniya.

Shiru tsohuwar tayi na dan lokaci kafin ta dago tana fadin a takaice dai na fahinci ku da zurian ku kuke
son ganin bayan yar uwarku cikin maganan nan ?

Wani kallon mamaki sukaiwa mahaifiyar tasu tace hakane din don kawai ku tozarta kura kuka dage
tsaye kan imamu haka kamar baku san inda yar uwarku ta fito ba ?

Duk da daddy bai faye magana irin haka ba wanan karon shi ya riga kowa fadin assha mama ke da
kanki kike fadan hakan kuma ?

Sayadine fa mama shima kamar daki yake mama don haihuwarsa ne kawai bakiyi ba sai mu marawa
karya gindi ga gaskiya zahiri ?

Ai ubangiji duk sai ya tambaye mu wanan hakin idan mun sani muka take sanin akan karya ba gara
kunyar duniya da abinda bawa zaije ya tarar ba gobe kiyama ?

Nifa tun ranan da naje gidan kura na dubata na samu ta shagala da waya da wata shakiyiyar kawarta
tun lokacin ns tsawala .

Hankalina bai kwanta ba saida na gano gaskiyan wanan zancen sanadiyar hakan yasa naba magaji
goyon bayan shiga aikin kankisa na farin kaya .

Mukai nasara kuma dashi da Nasir su zamo lauya don kawai mu tsirar da mutuncinmu ga idon duniya.

Wace tayiwa mijinta na sunna uban diyanta kuma dan uwanta na jini hakan waye zata bari a cikin mu
nan gaba ?

Balle gashi ta fara shirin hada yarta da magaji don shima ta aiwatar da wanan abin exctaly akan kamar
yadda sukaiwa shi sayadi din.
Kinga ke nan ba wanda zata bari a cikin mu harke mama wanan mai idon tsakiyar kai zata iya
murkusheki akan abin duniya sanan yanzu don jin dadi ki zauna kinawa mutane kukan munafunci bayan
kece kika lalata komai da hannun ki komai ya baci.

Yanzun kan taso magana don bata san lokacin da taba yayan nata amsa da fadin aishi ba sai nakasheshi
ba saidai idan yaki biyuwa irin na wancan din.

In bashi ba me zaisa na kasheshi,,,,,, cikin hasala uwar tace Kura kinsan abinda kike fada kuwa kura
kodai kina da tabin hankaline wai ?/

Tunda Abba ya bata magana ta sauko tana kula masa da yar da suke zargin cewa itace tayi mata asiri
don ta nakasa.

Kai mutane idan kana da kishiya baka huta ba haka kuma ko yayan miji aka barka dasu duk ba hutu a
hakan ma wai ba waje daya suke zaune ba amma ummu bata tsira daga sherin da yan gidan mahaifiyar
hindu ke kokarin kulla mata a gari.

Saidai zancen mijinta yayi tasiri a zuciyarta kamar yadda yace yana son ta taimaka masa su dawo da
darajan diyansa a idon duniya.

Hakan yasa taga me zai hana shida yayi mata tsaye ga yarta ba tare da saninta ba ya karewa yarta
mutunci da martabanta da karfinsa da dukiyarsa sai nasane ita zata gaza dasu a yanzu.

Duk da tasan akwai kalubali babba cikin wanan tafiyan amma haka ta daure tasawa zuciyarta sallama
akan zata taimaka saboda Allah dashi kuma.

Hakan yasa ta kara zama dani tayi min nasiha akan kada in dauke kaina kamar yadda ta lura inayi ga
lamarin hindu din.

Don yin zai kara min martaba a idon mahaifinsu din dake jina tankar nima yarsa ce ta cikinsa daya
haifa.

Naso naki amma tunda naji ummu ta fada min duk irin kokarin da yayi dani ba tare da sanin sa sai naji
ba zan iya kyatare hakan ba a yanzu .

Saidai ina tunanen ta ina zan fara ke nan don dai gaskiya nasan ko wacece hindu yana da wuya din
itama ta saki jiki dani har muyi yadda mahaifin nata zai gamsu.

Abu na farko dana fara yi shine shiga in gaida ita da jikinta wanda a gaskiya da farko banyi hakan ba
don kada ace munji dadi sai zariya mukeyi a dakin don ganin kwam.

Don ta daina fitowa waje ga baki daya tana zaune daki ko wani lokaci saboda abin bai saketa ba har
yanzu idan ya motsa zata zamo kamar zarara ne tana abubuwa dai marasa dadi.

Yanzun ma da suka gama abinci ina zaune saina kula suna jin tsoron shiga dakin inda take yasa nace su
bani in kai mata saboda da safe anyi fama da ita don abin ya motsa mata sosai shine aka rufo dakin aka
barta don ba wanda zaije tayi ta gwaurashi a bango.
Dakin na tura na shiga da sallamata ina fadin anty hindu kina barcine har yanzu ?

Bata motsa ba a yadda na sameta tana dai kwance na aje abincin a hankali na nufi bakin gadon idonta
biyu saidai kamar bata da lakka a jikinta .

Na kara matsawa ina fadin ko in taimaka maki ki dan zauna ne ga abinci na kawo maki nan ma batayi
min magana ba sai ido da ta dan bini dashi kawai.

Hannu nakai a hankali ina yaye da abinda ta rufa dashi ina fadin sannu Allah ubangiji ya baki lafiya da
kin tashi kinci abinci ko zaki danji nauyin jikin .

Sai na kula kamar tana son magana sai kuma tayi shiru ta runtse idanuwanta sannu na sake mata nace
ko kina son wani abune ?

Kunne nakai naji tana fadin dagani don Allah in tashi na kokarta na dagota da kyar duk ta sake sosai
don wai haka alluran yake ashe .

Da kyar na samu na zaunar da ita nan na kula ta bata jikinta nace subbahanallahi anty cikin najasa ai
kike kwance ?

Sai naga hawaye yana zubo mata lokaci guda tausayi ta ban sosai na barta zaune na nufi bandakin
ruwan dumi na hada mai dan zafi nazo na kamata batayi musu ba na kaita ban dakin .

Ganin ta zauna nace bari inzo anty Hadiya mai aikinsu na kira ta taimaka min tashigo tana dan tsoro
nace haba hadiya shigo mana ai lafiyanta kalau.

Zo don Allah ki taimaka mata a bayi ni bari in gyara nan kafin ku fito tace nifa tsoro nake ji na dai samu
na lalabata tashiga nakuma a gurguje na samu na kwashe bedshet din .

Allah ya taimaka iya fitsarine ta sake don wahala ashe nayi kokarin ciciban katifan in juya saidai na kasa
don yafi karfina.

Donshi naje kofan bayin na kira hadiyan tazo ta taimaka min muka samu muka juya na mayar da wani
bedshet na gyaro ko ina dakin wasu kaya na dauko mata a cikin closet din ta na mikawa hadiya din ta
tayata sakawa.

Har kamshi duk na fesa a dakin a guguje don sai dakin ya koma fes dashi haka don ina ganin tunda ta
fara laluran nan ba a tsaya an mata gyaran dakin ba.

Gaskiya shaye shaye baiyi ba a rayuwa da lafiyan ka ka maida kanka ana kyamar ka wanan irin abin
yanzu ina yai dadi don Allah dai ?

Fadan da nakeyi ke nan a zuciyana ashe ummu ta fito take tambayana anty baraka take fada mata wai
naje bawa mara lafiyan nan abinci.

Ita din garin yaya kika

83 / 109