Chapter 71 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   71 / 109

210K to 213K   out of 326.5K words

zata fita tana fadin nikan zan fita saina dawo ina zuwa anty Samira na fada daga bayan ta
hakan yasa ta juyo tana fadin wai ashe kina gidan ,?

Ina zani Samira tunda nagama school ina kuma zan tafi yanzu inban zauna gida ba ta dan kawar da kai
tana fadin na dauka kina can gidan da sukajene ke ma ai.

Samira yanzu ina zaki don Allah yau dai ba ranan zuwa school din ku bane samira yanzu ina zaki haka
mutum fa yanawa kansa fada ko ba ai masa sai ya dubi matsalan wani ya shafawa kansa ruwan sanyi.

Mace kike amma kina fita haka yadda kikaga dama kin fake ga karatu kina son ki batawa kanki rayuwa
an kawo ido kuma ansaka maki an rasa wanda zai tsawata wa hakan da kikeyi.

Kiwa kanki fada samira don ku samu kada ku tabe yasa na dage na tsayawa karatun nan naki yau samira
idan zuwa makarantan zai jefa ruwan ki cikin wani haline ai gara a bari tun wuri basai wuri yazo ba.

Wai mummy kina ta magana tun dazun kamar an fada maki wani magana a kaina nifa zanje muna
lesson ne da course mate dina dama yasa zan fita.

Haba samira haba samira ko ba ai muna fada ba ya kamata muyiwa kan mu fada kan abinda ya dace da
rayuwan mu karatun nan na fahinci yana shirin sauya maki dabi,un ki.

Kallona tayi na dan lokaci nima ita din na kurawa idanunu a lokacin sai naga kawai ta juya ta fita ba
tare da tace min komai ba.
Daga inda Asmau take ta zuba muna ido take fasin mena fada maki mummy aidama nace dake wallahi
ta sauya yanzu sosai wani ke zuwa ya dauketa fa,.

Ban iya ba Asmaun amsa ba na juya na shiga dakin Ammah din ina karasa gyaran da nakeyi a lokacin
can naji motsin samira din ta dawo.

Ke nan bata tafi ba har na sharo dakin na fito falo ina gyara sanan ta fito ta sauya kayan jikinta a
lokacin zuwa na zaman gidanta.

Zama tayi kofan Abbu dake rufe ta harde kafan tana fadi nasan sheri ake son a kulla min gidan nan
shiyasa na dawo.

Ni ban hana mutum yin abinda yake so ba amma ni kome nakeyi ido na sama ana kallona har za ai min
kazafi uwata kike da aka fada maki da zaki tsine min.

Ko yanzu na dawone inci uban munafuki a gidan nan ba wani abu yasa na tsaya ba don nasan inda
zancen nan ya fito .

Dagani har Asmau banza mukayi da ita muna aikin mu tagaji da suratanta takuma koma fadin mummy
kunyi waya da Aimana ?

Sai lokacin na dago na dubeta nace tunda suka tafi bamu waya da ita kila bata samu layin can bane har
yanzu.

Aikuwa ni munyi waya wani dan unguwarsu ne ya ban lambata Aimana fa tace kwarai kuwa har yanzu
suna Niger Republic tare da mijin nata ai.

Daga haka ban kara ce mata komai ba don daki na koma na kwanta sai bayan azahar su Ammag suka
dawo gida amma ba tare da ummu ba din.

Abakinsu muke jin mijinta yace ta zauna gida tunda tagane mu yanzu kuma ansan gidan shike nan a
raina nace Allahu akbar dama bai kai ciki ba zuwan.

Ina zata iya zama a nan an saba da zaman kasan dadi muko muna nan cikin wahala anty safiya naji tace
ai tace idan zamuje gobe muje mata da wasu kayanta amma ba duka ba.

Dabi,atace nayu rub da ciki a saman kujera ta baya ina saurare wanda ke zaune ko yanzun ma hakan
nake bawai zama nayi ba dama na daga ina fadin Ammah Abbu baiyi ajiyan panadol ba don Allah ?

Ta dago tana fadin anya amma dai bari na duba maki ingani ko yana dashi din ta fada tana yunkurawa
take fa Aeesha abinda nakewa gudu ke nan ta juya zuwa dakin Abbu din bata jima ba sai gata da boska
shina hade na koma dakina.

Washegarine sai ga anty safiya har dakina take fadin Aeesha nace yaya zancen zuwa dubo yaron nan
dayani mukaiwa ummu kayan datace na amfaninta ?
Ba zan samu zuwa bani bana jin dadin jikina na fada ina gyara kwanciya saita bini da kallo na shareta
ban kara motsawa ba zuwa can naji tafita daga dakin.

Muryansu naji da Ammah dake fada tana fadin inma kin zuwa tayi ai kanta tayiwa mutumin nan dai bai
daukeki matsayin wani abu ba yana iya kokarinsa dake har yan uwansa.

Yau ance dansa baida lafiya ko yayane aikya lekasu dai ko don yaron ku tafi tunda tace bata zuwa bata
zuwa din ne ai kunsan halinta.

Kememe naki zuwa duba yar on tare dasu suka kwasa sukaje duka gidan aka turo mota ya daukesu ni
kuma yinin ranan duk ban fito ba ina daki abina.

Ga Ammah tayi fushi ko lekoni batayi ba saida Abbu ya dawone yake tambaya har yanzun yaran suna
can gidan Nana Asiya din ne ?

Suna can basu dawo ba amma ita Aeesha tana nan daki bata je ba tace bata jin dadin jikinta tun jiya .

Ikon Allah meke damun ta tace ya wuci dan sadanta ciyon kai kullum ai ita shine ciwonta shiru naji yayi
bai tanka mata ba sai zuwa can na mike zuwa wajen na sameshi an zuba mai abinci yana ci.

Abbu sannu da dawowa ya dago yana me kureni da idanunwasa tare da amsawa yana fadin Nanata
ashe har yanzu kina jin kan bai sakeki ba ?

Nace ya dan lafa dana samu barci nayi amma gefe daya nake ji kamar ya daure min waje daya to kedai
ba wata babba ba balle ace hawan jini ya kamaki Ammah dake gefenshi ta fada.

Jam jam keko dai wani irin hawan jini kuma don Allah kibar mata wanan mugun fatan haka da
kurciyarta ?

To malam ai dole yarinyar nan ta dauki mugun hali ta dorawa zuciyar ta kamar ita kadai akaiwa laifin
nan koma meye ai yanzu dai komai ya wuce ko tunda gata dai ta dawo kuma ai,,,,

Don Allah kibar yarinyar nan da abinda daya dameta Ammamatan banson irin hakan da wane kike son
tajine wai duk abinda tayiwa Nana a yanzu sam banga laifinta bani.

Saidai aimata fada kawai ta sausauta a yadda ta cije din nan tana nuna halin ko in kula da ita .

Toba shi bane nake magana don wa muka riketa mu ba don nana din bace da takewa mutane iya shigen
banza da wofi haka ?

Kama min bakinki haka ya isa don Allah banson maganan yai yawa don Allah haka har kina batun sakin
layi wajen zuban banza .

Ai dole malam abin yarinyar nan yayi yawa dame tafi mahaifiyar nata datake rainawa ni zan bar goyon
bayan karya haka wallahi don abinki yayi yawa.
Nace dake zancen nan ya isa ko dadin abin dai bake kadaice kika riketa ba har takai hakan ai kuma ni
ban riketa wai don nana Asiya ba kijini da kyau ?

Na riketane don Allah da ma,aikin don ba a san me hakan ke nufi a wajen Allah ba daya tsamota daga
can ya kawo muna ita nan muka rike ta don hakan banson irin zancen nan kinji.

Ya juyo gareni yana fadin tashi kije idan dai kinji jikin bai sakeki ba kije chemist da wuri tun dare baiyi
ba ki kumayi hakkuri da lamarun duniya kada Allah ya kamaki da laifin hakan.

Ki godewa Allah wasu basu ga uwan basu ga uba don abola ake yadasu karshe su taso wullakance a
gidan marayu idan kika samu kanki a wanan halin da yaya ke nan zaki nanata ?

Don haka wanan abin ya isa haka don Allah kibi mahaifiyarki sau da kafa kada Allah ya kamaki da fushin
haksn ki godewa Allah kuma daya bata zuciyar imani da bata watsar dake ba a cikin duniyan gudun
kunyar duniya ta manta dana kiyama ?

Zuwa lokacin hawaye kawai ke zuba min na share fuska na dago ina fadin nagode Abbu sai naji Ammah
tana cewa muda baki godewa ba ki godewa azaban ki .

Mun dai wuce wullakaci a wajenki don kin fito a gutsun mu bari ganin kamar kin zama wani abu a
yanzu yasa baki kallon kowa da daraja a idon ki?

Nana dai ko yanzu ta wuce wullakancin duk wani mahaluki a garin nan inma wani ke zugaki kinawa
uwarki irin hakan ?

Au to aisai yanzu na fahinci inda zancen ki ya dosa kai tsaye ke nan nine mai zugata din ai ban fahinci
me kike fada ba tun dazun sai yanzu da kika fayece min komai a baiyane.

Ni badakai nakeyi ba malam yaushe kuma daga baya ke nan nida na tsaya ina lalashinta a yanzu nike
zugata ashe lalai duniya ?

Malam bafa da kai nake zancen nan ba ni a,aha ai kin makara kuma Ammamatan nidai na shige daki na
barsu sunayi a nan din.

Tsaye suke bakin motanshi su ukku shiyana waya saidai hankalinshi naga wa yanda suke fitowa daga
cikin gidan.

Da alama suma dai kallon sani sukeyi masa don ya fahinci suna zancene a kansa lokacin.

Asmauce tayi karfin halin fadin daddy Man yadda ta saba kiransa a waya idan muna waya dashi su
gaisa take kuma gaidashi a cikin wayan.

Wayan ya sauke yana kallonta kafin ya fadi daughter nako ta Aysha tace ashe kaganeni daddy sai kuma
ya dago kai kamar yana duban wani abu iya suke ke nan suka fito daga cikin gidan.

Zasu shiga motar baffan nasa da alama gida za a kaisu lokacin don sun fito ke nan mutumiyarka tana
gida bata zoba ita.
Kantane yake mata ciwo tun jiya Asmau ta fada don ta fahinci ni yake duban fitowana a lokacin .

Wani kallo yai mata yayin da yan uwansa suka zuba masa ido suna mamaki ina yasan Asmau ne don
basu sanshi da magana da mata ko wasu wa yanda bai sani ba haka ?

Tun jiya fa kikace tace jiyan ma saida tasha magani yau kuma koda zamu fito tana kwance Allah sarki
ku gaidata don Allah ya fada kana ya juya kamar bashi ba yaci gaba da wayan da yakeyi.

Wacece kake magana da ita mami din ta tambayashe a cikin waya yace wasune baki sansu ba mami
yaci gaba da maganan da yake mata din kafin Asmau ta katseshi.

Yana gamawa suka shiga ciki a falo suka samu baffan nasa zaune tare da matarsa da yaransu suka gaisa
nan suka fara zancen daya kawosu din gidan lokacin.

Zancene akan wani filin gona nasa daya gada gun mahaifiyarsa wanda bayan mutuwan wacin gadinsa
hjy kura ta sayar dashi a banzace duk da babu takardun filin a hannu yanzu daya dawo shine aka tura a
duba wajen don yana son ya karbi abinsa.

Wanda ya sayi wajen a banza yana murnan ya samu banza ta fadi sai gashi daga sama ankawo masa
sammaci mai fili nason filinsa zaiyi gidan gona a wajensa.

Ya tayar da fitina shi saya yayi wajen Manir da mahaifiyarsa da aka matsa masa da tambaya ya fada
akan nawa ya saya ya fada saidai kowa ya kama kansa don ba shawara takeyi da kowa ba a lokacin daga
ita sai danta kawai suke abinsu.

An amso kaddarorinsa da dama data salwantar ita da dan nasu Munir a hannun mutane ana mayar
masu da kudinsu don a ciki akai wani katon gida nasa da maishi ya kai kara kotu kan ana son nuna masa
karfi a kwace masa kaddaransa daya jima da saya.

Akai bincike dole a karshe ya yarda yayi hasara yabi banza yana ganin yaci bulus sai gashi liki yazo ya
tashi an karbe gidan ya koma jawa hajiya kura din da danta Allah ya isa.

Ko akan wanan zaman dole sai anje kotu da maishi saboda an fito masa da lumana yana ganin shi
kuma za a raina masa wayaune donshi ne sukayi wanan zaman suji yaya zasu bulowa zancen kafin aje
kotu din tunda yaki yarda ayi sulhun gida dashi a bashi kudinsa.

Nasir ya kula da hankalin man din baya tare dasu kamar yana tunanen wani abu kafin ya tuno da
kalman da Asmau ta fada mai da zasu shigo.

Don haka ya dan rankwafa yana tambayanshi da who is she ?

Ya juyo da sauri a dan kidime yana fadin who ya daga mai gira yana fadin wace aka fadama bata da
lafiya naga ka dan damu dajin hakan ?

Dan hannu ya kai mai kamar zai dokeshi ya noke yana dariya yace na kulla baka cikin hankalinka tun
sakon da yarinyar nan ta fadama nata.
O Lord sheri kuma zakayi min yanzu wani ban tare daku bayan gani zaune ina sauraren ku ina nazarin
zancen kowane kafin nayi magana.

Meya faru kuma baffan nasu dake kallonsu ya zuba masu ido yake tambaya da sauri shi man din ya
dago yana fadin nothing kawai dai.

Gara ka fadawa baffa ka tashi ka tafi kada ka rikice muna a nan kuma yanzu mu kasa gane kan ka
kuma ?

Murmushi baffan nasu ya danyi kafin yace kalas zamu iya bari sai kwana biyu ko daya aje kotu din sai
mu binciki ita kura din muji abinda zatace .

Babu abinda hjy mum zata fada tunda da hannun yajin ku a ciki don yanzu na fahinci kamar duk abinda
tayi da sanin hjy din a lokacin.

A kwarai ma kuwa aiko shi baffa yasan da hakan don ya kasance dai hjyrce yayi shiru amma tun a
zancen wancan mutumin na baya ya nuna ai don hjy ta saka baki ya siya.

Daga inda man din yake zaune yace ta zama dillaliyar zaune ke nan dama nasan tasan komai da hjy
mum zatayi saidai yanzu data kwabe masu ta nuna babu hannunta a cikin zancen.

Amma tasan komai da akayi da saninta akai komai wanan tsohuwar mai idon cin naira ya dago a daidai
lokacin baffan nasa na miko masa dakuwa da hannu yana fadin.

Dadin abin dai tare da uwarku suka aikata kowa kuma yasan halin kura da kafewa hjy bata isa ta hanata
abinda tayi niya ba maganan gaskiya.

A duk cikin nazarina akan zancen nan wanan ke daure min kai sam hjy bata iya musawa hjy mum ga
duk abinda ta sakata yi ko da tasan abin nan ba daidai bane kuwa.

Yanzu dai abar zancen a haka zuwa jibi din sai a tuntubeta aji gaskiyan zancen a bakinsu da ita da hjy
din ga baki daya ina ganin haka zaifi sauki.

Sukai mashi sallama suka tafi saida suka fitone Nasir din ya kara fadan zan rakaka zuwa can ne ka
dubuta ?

Yana kallonsa yana masa dariyan shakiyanci ya kara fadan ko gida zan sauke ka don a motan Nasir
sukazo gidan bada nasa ba.

Kaini gidan shehi can zanje yau wajen umma tunda nazo banje ba har ta soma fada mun daina kulata
yanzu saika barni can Auwal zaizo ya daukeni idan nagama.

Ai ba kai daya ba nima dole in shiga in gaida ita ai duk da nasan zansha fadan rashin zuwan da banyi
gashi tana biye sunan Nasir dinta a kaina sosai.

Tare suka shiga gidan duk da ya fahinci da salman na gidan lokacin don motarsa daya gani a waje ji yayi
kamar yace su koma sai wani lokaci don bai son haduwansu da salman din a gaban umman.
Amma saidai kuma an riga da anga zuwan su har manyan almajiran gidan sun taso zuwa garesu donsu
gaisa saboda sun riga sun saba dashi akan yawan zuwan da sukeyi gidan da salman.

Ciki suka shiga kai tsaye part din umma din zaune suke falo dukkan su har anty ummi datazo daga
ghana yayi mamakin ganinta don baisan tana gari ba dama a wajen Salman zaiji yanzu kuma ba shiri a
tsakaninsu.

Sunyi murnan ganinsu sosai aka dan gaisa tare da raha kafin umma din tace dashi nasan kaika jawo
min Nasir gidan nan yau don yaushe rabonsa da wajena tun yana dan matashi lokacin nakan gansa .

Dariya Nasir din yayi yana fadin nafada masa hakan ai kiyi hakkuri unma bana zama garin ina Abuja
wallahi yanzu ma don case din baffa sayadi nake garin nan kwana biyu.

Hakafa ikon Allah sayadi ashe yana raye bai mutu ba sai ga labari muji wai ya dawo naketa wakan
zuwa masa barka da arzikin dawowa gida ban samu lokaci ba kuma don ance mutane sunyi yawa a
gidan.

Yanzun ma daga can wurun shi muke andai dan rage amma akwai mutane har yanzu ai dole ya gana
dake mana umma idan kinje tunda kece yasanki farin sani kuma.

Ai zanje wanan mashiriricin nake ta son ya kaini badai lokacina ta nuna salman din dake zaune a falon
kamar ruwa yaci sa tun shigowansu baiyi wani motsi ba.

Wai tsaya Man kardai ince har yanzu ba jittuwa a tsakanin ku da dan uwar naka don na fahinci hakan
anty ummi ta fada tana kallonsu dukkansu biyun .

No ina dai busy ne ai kinji Nasir ya fada kan zancen baffa muke kasan nan shiya tsayar damu so banda
lokacin kaina ma a yanzu.

Filayensa da gidanjensa da hjy mum ta salwantar muke kokarin kwato masa a hanayen mutane shine
abinda ke gaban mu.

Ummi koma meye salman din yajawa kansa hakan kowa nan ya sani tsakaninsu sai Allah don me zai tari
gaban yarinya ya fada mata ba daidai ba game da dan uwarsa ?

Ko hjy kura tacima mutunci tace ka aiwatar ai sai ka tuntubi dan uwanka kaji ta bakinsa kafin kajeyin
abinda ta sakakayi tunda kai ba sakarai bane.

Barshi kawai yai masa hakan gobe in halinsane ya koma indai hjy kurace hjy mum kam yanzu aita
kanta takeyi bata wani ba Nasir ya fada daga inda yake zaune din.

Ai dole mutum ya mutu har kayi mai takaba sai kuma rana tsaka ace yau gashi ya dawo bayan ka gama
murje komai nasa.

Murmushi man din yayi yana fadin ai tasan inda ta turashi yasa ta zauna taci arzikin umma tunda dama
shi takewa ta turashi din da Allah ya nufa baida amananta ai gashi yau ya dawo gida cikin yan uwansa.
Innalillahi kardai abinda yan gidan waziri ke fada ya zamo gaskiya kan kura na yaushe kuma umma
Allah dai ya sauwaka kawai za ace yanzu kuma.

Innalillahi ance harda iyali kuma wanan abun kunyar da hjy mum

71 / 109