Chapter 73 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   73 / 109

216K to 219K   out of 326.5K words

na tambaya a dan tsiwace tace na mutan saudiya mana su hjy ummu kayan su sun
iso shine ta aiko akawo muna.
Kallon anty safiya nayi nace anty safiya mutumiyarki ashe tana gari bamu sani ba ta dago tana fadin wa
ke nan nace mutumiyar ghana mana anty ummi naga kuna together da ita.

Ai don Allah dai tazone ashe kice na hada kaya ke nan dama munyi waya tace zatazo don mahaifinsu
baida lafiya zuwan ummu ne ya dauke min hankali na fita zancen.

Gobema nake son zuwa in dubo jikin mahaifin nasu da mamansu ni har kunya ma nake ji wallahi don
ban taba zuwa nagaida tsohuwar nan ba.

Saiga Abbu ya fito daga bayi nida Asmau muna rige rigen gaishesa yace Nana ashe jiki yayi dama na
dawo akace min kin fita zuwa gidan akwai wajen yaran nan.

Nace wallahi Abbu na dan fita ko jikin nawa zai sake yace hakan yayi ga akwati can tsarabace inji nana
Asiya ta aiko dashi wancan akwatin da sunanki yazo nakine mu kuma ga namu gana Ammamatan gana
yar mariya nan dana yaranta ta tsaro komai daga can.

Abbu ina naka na tambaya ina kallon kayan naji Ammah tace aidama nasan abinda zaki tambaya ke
nan babu ko mungode kamar kin aike ta yarinya da bakin rai haka dai ?

Gun guni na wuce inayi nace aiban rasa kayan sawa ba daga kawai na tambayi na Abbu sai ace wai
banyi godiya ba ?

Yaki nan taho nanata kyaleta baki rasa kayan sakawa ba zo ga nawa a nan ki gani kamar inci gaba da
tafiya tunawa da Abbune fa ke magana .

Don a duniya Abbu ya gama min komai ko da bansan dadin uwa ba nasan na uba don ko Abbu ya zame
min uwa uba a duniyan nan.

Don haka ban kaunan ganin bacin ransa a kaina tun ina karama kuwa bansan komai ba nake hattara da
hakan kan Abbu.

Ba zance Ammah batayi min ko ita don ko sun tsaya a kaina dukkansu biyun tankar su suka haifeni
saidai na Abbu din yafi min na kowa a duniyan nan.

Mutumin da tun ban san hankalina ba dashi na bude ido a duniyan nan makaranta daya sakani a
kullum har nakai aji biyar na primary sai yaga shigata aji zai juya.

Hakama dana kai secondary bakon wake shike rakani kullum saida nakai ss sheri yayi min yawa ya
daina rakiyata duk safe haka idan an tashi kuma zai koma ya dagoni saboda gujewa sheri yara da sukaso
haukatani ina karama da sherinsu don kawai siffana daya bambanta da nasu .

Da ko dan gidan waye ya tabani Abbu saiya sallamawa ubansa yayi masa kashedi a kaina don me a yau
idona zai rufe akan abin duniya in manta da Abbu ?

Dole ko in tambaya nasa kafin na kowa wai kuma hakan laifine gun Ammah don kawai tana jin
haushina kamar ta makeni don ban tsaya nuna rawan jiki kan abin duniyan da ita yasa ta manta da
fushin da takeyi da yar uwarta .
Suna ganin rashin kunyata ni kuma nasan abinda nakeyi sarai don ban yarda nayiwa Ummu wani rashin
kunya ba ai ?

Hakan kuma da nakeyi inayine donsu fahinci dacin raina inkuma yi daraja a gurinsu amma haka kawai
zan nuna zallama akan abin duniya da nake gani a yanzu ya rufewa dayawa ido an manta da baya.

Kodana juyo din ido na sauke kan kayan da Abbu din ke nuna min yana fadin kingani ko nanata wanan
duk nawane ga kuma kudi sun dakatar dani fita ko ina sai dai in dauki yaron shago sukace.

Haka kuma shi Alh yace yana son in koma na hannun damansa in dinga kulamai da wasu harkokinsa na
rayuwa.

Duk da na fahinci abinda na hannun damansa ke nufi kamar Abbu zai koma yaron mijin ummu ne banji
dadin hakan ba saidai a fili dan murmushin yake nayi a fuska na juya ina fadin Allah yasa ka more Abbu
yasa hakan yafi zama alheri a rayuwa.

Su kuma Allah ya saka masu da alherinsa ai na zata ba zakiyi masu addu,a ba sai gyatumin ki ? Ammah
ce ta sake fadan hakan gareni.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[10/23, 10:26 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:




JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

7️⃣6️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6



https://sitrix.africa/signup.php?ref=foleesco




Kayane nagani na fada ko Abaya ashe suna suka tara manshafi turare masu tsada da takalma da jakkuna
kamar an aunani ga komai sai kuma sarkan yari ta gwal da banta amfani dashi ba da awarwaro masu
tsadan tsiya.

Na juya na laguda don in fitarwa maryam da farida suma daga ciki amma nakasa hakan don na rasa
wanda zan debe masu.

Dabarane ya fado min na mike na jawo jakkan dana dawo Abuja dashi cikin kayan da muka sayo da
maman Abuja na daure na ciro biyu na aje a gefena na hada turare da niyar washegari na aika masu.

Na jima a dakin banyi barci ba sai wajejen karfe biyu na samu barci mai nauyi ya daukeni ban tashi
falkawa ba sai biyar da rabi da dankai har anyi sallah gari ya soma haske a lokacin.

A gurguje na tashi nayi sallah ina idarwa ana kwankwasa kofan dakin nawa na mike na bude Asmauce
yake fadin.

Mummy baban kano ya damu mutane wai baiji motsinki ba tun dazun nace wallahi makara nayi yau
Asmau yasa ban fito ba.

Tare muka fita inda na samu Ammah tana faman jinini akaina tana fadin bakin hali irin na Aeesha sai
ita daki kai kadai zaka kwana a cikinsa yarinya haka bata da son mutane.
A,a mama kowa da irin rayuwansa fa ko tsabta irin na Aeesha ba zai bari ta zauna tare da wani a daki
daya ba ai ta dai dinga nikan wucesu nayi banko tsaya gaidasu ba naje wajen Abbu dana hango yana
gyaran kwatan ruwa dake fita waje daga cikin gidan mu.

Har kasa nakai kamar yadda na saba gaidashi muka gaisa yake tambaya nace makara nayi yau Abbu
jiya nayi gyaran dakine da dare yasa na makara.

Har na daga naji yace nana ashe bakije kin gaida dan uwanki da baida lafiya ba na juyo ina fadin wani
dan uwana Abbu ?

Yaron nan mana dan wajen hjy Asiya uwar ta bugo tana korafi wai kinki zuwa wajen su balle kiga yaron
kuma yarab syn matsa mata da tambayan ki ?

Yake nayi nace wai haidar zanje Abbu nima yana raina don banjin dadine ai dama ka kyaleta in bakije
ba mu mun tafi ba ?

Ai abin ke nan ace wai kada a fada ta yaya yaron nan yayi ciwo kowa yaje ya dubashi amma ke kiyi
kememe kike zuwa don bakin rai ?

Kai kai kai ya isa don Allah jiya da jinininki yarinyar nan ta kwanta barci yau kuma tunda farar safiyan
nan zaki dora inda kika tsaya haba don Allah ?.

Ina tace zata tafi bashi ke nan ba zance ya kare dai ,Abbu na fasa zuwa tunda su Ammah sun tafi ko
hakan ya isa ai tunda ba bashi bane ace sai kowa yaje.

Kaji ja,ira ta fada ta bini da zagi Abbu yace itace daidai dake ai tunda inkin kama zance guda kin kama
ke nan baki san ki sake ba na rasa me yarinyar nan tayi maki kike mata haka ?

Gani nayi tana son mayar da mutane sakarkaru kamar ita kadaice farau din haka banson abu da
shakiyanci wallahi.

Anty safiya na tsaya na gayar dana samu a falo bayan ta amsa take fadin kai mama dai ina zancen nan
jiya da dare ummu ta kira take fadin kinki zuwa duba haidar kuma ita bata fada da wani manufa ba.

Kawai dai nasan tana son ganin kine tunda kowa yaje ke bata ganki ba ni dama nayi niyar zuwa na
karbo laptop din na wajensu.

Amma Ammah ta kama fada haka aikinsan mama niko harda tsufane oho abu kadan yanzu zakayi mata
ta hauka da fada.

Ni yaushe hjyn ghana zata komane ina son in nuna mata wasu kaya lates da suka fito masu kyau daga
maradi aka hado minsu kayan anyaba wallahi sosai maman bibo kayan matane suna da kyau sosai ba
laifi.

Yau zan tafi nagaida mahaifin su insha Allahu zan tambaya maki yaushe zata koma din koma in biku ko
zan gantane ?
Haba mama ki bimu kamar yaya don Allah Asmau dake sharan falon ta dago tana fada keko zaje natane
mana mukan fita da itane dama in ba yau ba ?

Asmau zanci abu kazan ubanki fa naga raini yana son shiga tsakanin mu to mama don Allah mu da
zamu fita iyamu yara ina zaki shiga cikin mu kuma ?

Dafa su maryam da farida duk zamu fita koba haka bane mummy jiya naji kina fada masu zamu fita yau
?

Idan na shirya ki hanani balle bamu da wajenki anty gaskiya Asmau ta fada ina zamu da jakkan kayan
mata muna yan mata don Allah ?

Saida tayi dariya kafin tace dani au to kin kamawa yarki ke nan ku tafi ai nasan hanya idan natashi zan
tafi ya daifi sauki na fada ina dariya.

Saida na gyara dakina tsab na shiga wanka na fito nasawa Asmau kira tazo kayan dake saman gadone
na nuna mata nace kinga su maryam nake son ba tsaraban ummu ?

Mummy wa yan nan kayan masu kyau haka baki taba amfani dasu ba fa nace haba Asmau aiba zaka ba
mutum abin banza bako ?

Allah yace idan zakai alheri kayi ta yadda hagunka ba zai gani ba menene a ciki ba gashi Allah ya ban
wasu ba jiya ?

Banyi zato ko tsamanin samunsu ba Allah ya kawo min balle maryam da farida sun fi hakan a gareni ai
ko me suka gani gareni suke son zan iya basu shi a rayuwata.

Don zaman mu ba kissa ko munafunci dasu kema kin sani tun muna kanana muke tare dasu har yau
kuma ba,a taba jin kan mu ba dasu.

Gaskiya mummy keta dabance wallahi gaskiyan Abbu dayacewa Ammah ki jiya ta biki sannu ke din
basarkace jinin sarauta ce ke binki hakan .

Wai basaraka kai Abbu hoo Allah dai ya barmin gyatumina mu raka da juna aisai ki daukeshi ku tafi
ranan da zakiyi aure ke nan iyaka dai ke nan ko ?

Banson iskanci na fada cikin daure fuska ina fadin da ana zuwa aure da uba aiba abinda zai hana in tafi
da Abbu ko zai huta da jininin Ammah wallahi.

Kai daga ke dai sai Ammah ki nace wallahi da yanzu kuma zata ga wani bacin rai a kaina sai inda
karfinta ya kare wajen fada da maishi duk wanan abinda kikaga tana min kwanan nan kuwa.

Ai barta saina kada ta mu gani anjima ki dai kadani zaifi maki sauki sai kuma ta juya zancen da fadin.

Mummy wai kinsan me nace a,a ina kallonta take fadin wallahi kwanan nan kusan sau ukku ke nan ina
mafalki da baban mu .
Jiyama na gansa a cikin damuwa sai nake fadin baba tashi muje gida mana ka zauna nan ya dago ya
kalleni yace kizo zan shigo yanzu Asmau.

Dama munfi shiri dashi sosai ko abu za ai mai nice zai kira in masa nima wallahi kwanan nan duk sai
tunane ya koma kansa mummy bansan abinda yasa hakan ba?

Asmau watakila kuma kuna ransane balle dole haba rai shidda ai dole ya tuna ku mana kila hankalinsa
ya dawo garekune yanzu.

Mummy shekara bakwai ke nan fa rabon mu dashi nidai nafi zaton zuwan su ummu da akace kusan
shekara goma sha takwas dana tuna da baban mu din yasa abin ya tsaya min a raina ?

Allah yasa duk inda yake yana lafiya Allah kuma ya juyo muna da hankalinsa zuwa gareku ya sameku
lafiya Amin na fada itama ta amsa da Amin din.

Ta mike zata tafi nake fadin Asmau don Allah idan kin gama sai kizo ki mika masu kice tsaraban
ummuce nace a kawo masu.

Ta amsa da to mummy bari inyi wanka nazo na kai masu kafin su shigo naji kince shadaya zamu fita ko
shiyasa nake ta aiki kafin mu fita din.

Wai Samira fa ko bata nan ne dazun naga ta fito ta tafi gidan Dije mai waina ta sayo ta zauna falo taci
har mama na mata fada ta hanawa diyanta.

Wani bakin rai take ji dashi yanzu tunda kikai mata maganan nan niko wallahi ban damu ba gaskiya na
na fada saidai ta mutu.

Ni abin samira na ban mamaki Asmau amma barta ai akwai inda zan kamata kyaleta nayi kawai wallahi
.

Jiya fa mummy kan kayan tsaraban nan namu da nabi ta nata da anjimu agidan nan da ita na dai
kyaleta kawai don kada mu zamo daya.

Kyaleta din don Allah kada kibi nata zata zo ai ta sameni na fada bayan fitan Asmau daga dakin na
zauna nan nayi tunane kala kala a dakin kafin na kwanta.

Zuwa goma da rabi na fara shiryawa lokacin har Asmau ta dawo daga gidan akwai da taje take fadin ta
samu hjy Aginatu a gidan tasan zataje ta barada a unguwa .

Ita ta sani don Allah jeki shirya na fada naci gaba da shirina koda suka shigo har na riga dana gama shiri
Asmau muka tsaya jira lokacin.

Farida ta mike ta shiga wajen Samira sai gasu tare tana fadin mummy ashe fita zakuyi shine baku fada
min ba ?

Ai ban zata kina gidan bama naga tun ranan da nayi maki magana kike jan kamshi da kowa gidan nan
kin dauka wanine ya fada min ni kuma fadan so kanki nayi maki.
Mazan nan yadda suke ganin ki haka sai suzo maki da tsigar yaudara basai kin kulasu ba zaki biyosu
Samira.

Mazan arziki suke biyo mace har gidan su ba dai mace ta bisu ba naga ta kalloni nace kwarai ni banjin
tsoron fada maki gaskiya samira.

Duk abinda mutum keyi yanzu ana kiwonsa wallahi mutane su zasu fadi halin mutum bakayi bama ance
kayi balle anga kanayi ?

Kinje school antashi kin dawo cikin lokaci basu kara ganin ki ba sai gobe kuma komai sherin mutum
dole ya sarara maka ko baiwa Allah kuwa ?

Amma suna ganin ki wanan yazo ki fita ko yaushe yanzune yan daban isa zasu saka maki suna a
unguwar nan kema kin sani ba saina fada ba.

Wallahi ba karya bane indai wa yan nan munafukaine shiya Abba ya hana su yaya zama wajen yace
basu komai sai aikin gulma.

Kin gani ba kowa yasan su da sheri ni shiyasa kin gani nan ban damu da kowa ba iyakata dasu in naji
zan iya gaisuwa.

Kije ki shirya mu tafi farida ta fada ta nisa tana fadin ni abin ne ya ban mamaki amma ba komai ta fita
din tunda tana son zuwa.

Yadda muka saba dai haka muka fita nida maryam a gaba su ukku baya sai da kyat muka gane unguwar
kofan gidan shehi din muka tsaya da mota.

Muka fito mun hangoshi a inda yake zama tare da mutane muka nufi can don mu gaidashi ya kuma ji
dadin hakan don yana ta sa muna albarka.

Saida zamu tafine uace bai sheda mu ba mukace kawayen khairat ne mun muka zo mu gaidashi da
jikinsa Allah yai maku albarka na gode ya sake fada.

Cikin gidan aka nuna muna hanya muka shiga tare da jagoran wani matashi dake daukan karatu a
wajensa.

Suna falon uwar har anty ummin nasu a nan muka samesu mukai sallama muka shiga suna gani mu
suka shiga murnan hakan.

Muka gaisa da mahaifiyar nasu duk da acikin gida suke amma katon hijjab ne a jikin dadtijuwan matan
malamai ke nan .

Akai yaushe rabo yaushe rabon aga juna kafin khairat tace dani dama umma ke son ganin ki muka
kiraki da dabara don in an fada maki baki zuwa .

Na dago ina fadin ni kuma nayi laifi ko kinyi mana kinsan yadda umma ke ji da zancen ki amma ko
daidai da rana daya baki taba zuwa kika ganta ba .
Murmushi nayi ina noke kai anty ummi din ke fadin man ya kawo karanki wajen umma jin hakan yasa
na dago kai da sauri na dan kalleta.

Sai naji umman tace kai ummi kin faye zuba aisai ku rudata ta dauka wani laifi tayi zo muje daga ciki
kinji yata hakan yasa na bita zuwa uwar dakinta.

Zama tayi a bakin gado na zube kasa tana fadin subbahanallah kasa yata tashi ki zauna ga kujera nace
umma nan yayi min na matsu inji abinda yace nayi din.

Umman tace ikon Allah ashe akwai yara masu irin tarbiyan nan a zamanin nan tona gode kinji Allah yai
maki albarka naji dadin albarkan nan nasu da nake samu a bakunansu yau.

Malamai haka kuma dattijai suna saka maka bakin albarka ba abinda yafi wanan dadi hakan yasa nake
kara son Abbu don sakawa mutum albarka ni kuma hakan na min dadi.

Yata nace a kira min kene don banji dadin abinda naji ba sai kace ba yar musulmai ba gaki da hankali da
tarbiya ina hankalin naki yaje da zaki nunawa mahaifiyar ki haka ?

Iyayye ba abin wasa bane banson wani tashin tadhin zance don Allah abinda nake so dake ki nunawa
duniya uwarkice.

Uwarkice ta dawo kowa ya sani wanan haukan kurciyan da suke fada ki dainashi daga yau din nan kinji
abinda na fada ko na amsa da eeh umma nagode insha Allahu na daina.

Allah yai maki albarka ta mike tana fadin tashi kije gun yan uwanki kada suga kin dade su dauka wani
abune can na daban .

Tana gaba ina bayanta tana kara min nasiha muka fito wai umma har angama anya kuwa anty ummi ta
fada datake hakkince zaune saman wani laulausan kujera mai fadi ta dora kafafunta a kai ta harde a waje
daya.

Babu ruwanku ta

73 / 109