Chapter 7 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   7 / 109

18K to 21K   out of 326.5K words

bai sakeni ba amma sai hakan ya gagareni sunayen Allah mai girma na
ringa kira don na samu natsuwa a zuciyana a haka barcin ya soma daukana kuma.

Saida naji muryan Ammah a kaina tana fadin haba Aeesha duk da ciwone ki dan tashi zaune barcin
yamma baida kyau aiga musulmi.

Hakan yasa na mike na zauna na jingina da bangon dakin nawa ina faman raraban ido tare da tunane
kala kala a zuciyana don ji nake na gudu naje saudiyan ayi wadda za ayi acan din nida Nana idan naje.

Amma a take zuciyana ta tambayeni da wani kudi zan tafi din nida banda ko dubun dayan kaina a jikina
nake zancen zuwa saudiya a yanzu.

Wasa wasa kwana biyu nayi ina fama da wanan zazzabin na karaf daya kuma nasha allurai gareshi na
samu na mike kacar majar daga zazzabin.

Son gaskiya gun iyayyena na samu kulawa sosai har ina mamakin hakan saidai sanin halinsu na kirki
yasa banyi wani shakkun hakan da yawa ba.

A dan wanan takin kuma nayi iya bakin kokarina da shawaran da zuciyana ke ban na watsar da zancen
Nana da wani mahaifina wanda ma kowa bai sanshi ba a yan uwa.

Ya zama dole gareni in rugumi iyayyena dana taso na sani a matsayin iyayyen haihuwana din don sune
dai sanyin idanuwana a duniya.

Don a duniya sun min komai a rayuwana banga abunda zaisa a yanzu in nuna masu wani halin banza ba
in tayar masu da hankali alhalin su basu gujeni a yadda nake ba.

Musanman ma Abbu da ban hada komai dashi ba amma ya rikeni riko na fissabillahi in ace ita ammah
yar uwatace shiko fa mena hada dashi kuma cikin hakan kuma bai kasa dani ba.

Zance Alhamdullahi a dan takin don yawan addua da kuma kulawan iyayyena yasa na daina wanan
tunanen na rugumi kaddara a zuciyana duk da dai ba zan taba manta hakan gareni ba a rayuwa.

Sai hakan yaiwa iyayyen nawa dadi don sun nuna min hakan zaki samemu zaune da Ammah muna
hiran mu ta duniya gwanin ban sha,awa duk da ba fita dai nakeyi ba ta gaji ta saka min ido tunda haka na
zabawa rayuwana ta barni.

In Abbu yaji tana min fada yakan ce ikon Allah wasu na neman nasu su zauna a gida haka ke Allah ya
baki salihar ya kina fada akan fita kuma ?

Ammah din kance malam ace ya mace kullum kumshe a gida ina zata samu manema da zasuso aurenta
haka ?

Yakanyi murmushi yace wata rana kyace nace don sai kin kore a gidan nan hakan bai kan gamsar da
Ammah din don takan amsa masa da Allah yasa kawai.
Ko jikina ka kalla zaki san hankalina ya kwanta a yanzu don har dan jiki na fara girkawa alaman
kwanciyar hankali dai a tare dani din lokacin.

Saidai kullum ina a cikin zullumi da tunanen makoma na haka wani abu dake tsaya min a rai shine
wanan kudin da nana take turo ma su Amma din akan meye shi ?

Ita tasani ni dai ban bukatan komai nasu na iyayyena ya wadatar dani a yanzu nakan fada a zuciyana
idan nayi wanan tunanen.

Damuwata alokacin jerabawana ya fito yayi kyau in samu zuwa gaba da Abbu yayi min alkawari kullum
hiran mu dashi ke nan isan mun zauna.

A wata rana naje islamiya nake jin labarin fitowan jerabawan mu din na dawo gida da murna ina
fadawa Ammah itama murnan tayi tare da min fatan alheri.

Haka yasa na kwana ina addun,a da rokon Allah samun nasara akan jerabawan namu don tsoro daya
kamani kuma don jerabawa sa,ace akace ba wai iya kokarin kaba.

Banyi sanyi a gwiwa ba washe gari na shirya zuwa duba don an fada min yadda zanyi saukin abin tare
da Abbu zamu tafi duba don haka yake da kula akan komai na iyalinshi.

Tun shigan mu school din Abbu ya shedawa kansa yadda na kasa damu suke murnan ganina suna fadin
ga anty Shu,wa ga anty social don nina rike wanan mukamin saboda tsabata a lokacin.

Ba wanan ne a gabana ba sai addua nake faman yi a zuciyana tunda muka tunkari office din examiner
da yar fa,asab ya tarbemu yana fadin.

Mahaifinki kega nace masa ehh naji yana fadin baba Allah yasa kubar yarku nan taci gaba da karatu
don nan gaba insha Allahu akwai alheri idan taci gaba da hakan .

Yakai zaune yana zaro wani dogon takarda a gabanshi yana dubawa tare da fadin saidai muce
alhamdullahi baba don bana jerabawa yayi kyau gaskiya munyi alfahari sosai da yaran nan.

Sunana ya dago yana tambaya na fada masa har lokacin jikina yana dan rawa ya dan tsaya dubawa
kafin ya sake dagowa cikin fara,ansa yana fadin Alhamdullahi.

Sunanta ya fito a cikin special list baba yanzu zaka biya kudi sai kuje kuyi print out a wancan malamin
ya nuna muna inda zamu.

Abbu sai hamdallah yakeyi yana samin albarka kafin ya maida kallonsa ga malami yake fadin malam
nace ba wai da naso ta danci gabane a karatunta kafin miji ya samu.

Shawara nake nema gareka wani makaranta jerabawan nan nata ya dace taje don Allah kasan ba sanin
kai nayi ba ni .

Baba a cikin fadin kasan nan yanzu wanan jerabawan nata za a iya daukanta a ko ina kuka nema don
jerabawa yayi kyau sosai gaskiya.
Ehh to ai alhamdullahi amma karin haske nake so dai tunda na fadama ba sanin kai nayi ba nan malam
din yace dashi ehh to baba saidai bansan ra,ayinta ba ita yana kallona.

Na danyi kasa da kai nace teacher nake son zama Abbu malamin ya kwashe da yar dariya yana fadin
irin mu kike son zama ke nan a rayuwa.

Hakan ba laifi bane gaskiya amma zan baki shawara da ki dan canza wani ra,ayi ga hakan don
jerabawanki gaskiya tayi kyau sosai zaki iya yin litanci ko aikin jarida ko lauya ko dai gasu nan dai da
yawa ana neman mata masu kwazo a wanan fannin.

Lauya nake so na fada sai naji malamin yana fadin hakan ba laifi bane ya danganta da abinda suka baki
dai a can din .

Nan Abbu ya kara fadin a inane yace ko nan jami,an gari ai zaki iya zuwa don yanayi bayan haka kuma
idan akwai hali akwai sauran jami,oi a sauran jahohin kasan nan haka kuma nan ma makwabtan mu
akwaisu yanzu kuje dai can ku karbi sakamakon inyaso daga baya baba zaka iya nemana idan akwai wani
taimako da zan maka bayan wanan.

Yadda yace haka mukayi din don bamu dawo gida ba saida muka karbo komai a ranan muka dawo
gidan namu.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[8/2, 10:15 PM] Zainab Idris Makawa Writer: ELSUTRA HOME OF FASHION & BEAUTY ACCESSORIES AND
BEYOND

MAMAN BIBO KAYAN MATA

08068871330 KOKO ROAD SOKOTO




JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
00️⃣88️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Duk wani fadi da Abbu yayi a kaina wanan bawan Allah ya taimaka hakan ya samu har Allah ya nufa na
samu gurbi a jami,an BUK anan kano.

Saidai matsala dayace yai mun nisa da gida sosai gaskiya ga kuma Abbu yace shi bai yarda da kwana a
can ba yafi amincewa jeka ka dawo.

Hakan ya jawo dan cecekuce da tsaiko ga tafiyan nawa saidai ina zuwa yin abubuwan da suka dace
wanda kafin a fara karatu akeyi.

Saidai ina shan barazanan kallo a wajen mutane wajen bama maza ba har gun mata yan uwana wanda
abinda na tsarga ke nan a rayuwata yawan kallo din nan ga mutane.

Yadda abin ya faro a rana ta ukkune da naje school din hijjab dina tare da face mark dina like a fuskana
don bata da kama.

Amma sai wanda zan gani din ya sawa takardan nawa hannu akace ya fita baya nan don haka saina jira
har na dan zauna inda sauran dalibai irina ke zama na suna ta hiransu har na kusa dani suka dauko
zancen mutumin da zamu gani din duk abinda suke fada akunnuwana.

Hakan yasa naji na kagu don tsoroma saina bar wajen kawai na koma can wajajen da motocine aka jera
birjit masu kyau da ma marasa kyau don kada in bata jikina na hari wajen wata mota dake rufe nasan ko
maishi yayi hakan ne don yawan kuran da akeyi da iska a lokacin.

Durkushe nakai a wajen kaina kasa yayin da hijjab dina ya baje a kasa ya rufe min kafafuwa sam banji
zuwan mutum ba na daiji kamshin turare a gabana kamar an kura min ido wanan yasa na dago darara
daran idanuwana mai suffam na juda na sauke saman kafan maishi ina dago da kaina zuwa kallon shi tun
daga kafa har zuwa kai.

Hakan yasa na mike zubur tsaye yayin da naga mai shi ya danja baya ya fara waige waige kafin ya mayar
da kallonsa a takardan dake hannuna yana fadin.

Excuse me a dan siririn murya da bai fita kamar a cikin izza da isa da takama meka fada yace bakiji bane
kauce a nan ki ban waje please ni ai ban tare ma waje ba na sake fada.

Ina jan tsuki cikin takaici nake fadin in badon wanan mugun mutumin mai izzan tsiya ba da akace ni
bakako ganina wajen nan ai.

Kamar yana son tantace wani abu naga yakai kallo ga kafana da hannayena ya koma fadin zan shiga
mota hakan yasa na juya da sauri ina kallon motan sai kuma nace yi hakkuri fa hauahin wanan bawan
Allah daya shanya mu tun safe yasa na dan dumaice na jaye kadan daga gefensa naga wani yana yaye
mai motar wa iyazu billah na fada a raina ashe gun motan manya naje na tsaya ban sani ba.

Hakan yasa na juya na fara takawa a hankali raina a bace sanin yau jumma,ace kuraren lokacine gashi
monday ake son mu fara daukan lecture din mu don har ance wai wasu sun fara attending ko.

Motar naji an tayar don ni har na juya zan bar wajen cikin mutuwan jiki kafin naji dayan mutumin na
fadin ke kawo takardan a gani hakan yasa na dan juyo na kallesa ina fadin waini ?

Ke mana bakiji me nace bane tunane na dan tsayayi kafin kuma na daga kafa zuwa inda suken don ban
sani ba ko zai iya taimaka min ga hakan.

Karba yayi don har lokacin shi yana tsaye waje bai shiga motar ba tunda na mika mai naga ya kalla yayi
murmushi kafin ya mikawa na cikin motan.

Ina nan tsaye jin kaina a kasa can ya kara miko min yana fadin karbi zance ya kare ko inji dayan
mutumin dake waje tsaye shima farine sol kamar dayan a cikinsu bansan wa yafi wani haske ba a idona
tunda ba kallon kurulla nayi masu ba.

Karban takardana nayi na juya ina kunkumi cewa gulma yanzu har da maza kunsa ba taimakona zakuyi
ba kuka tsaya min tsegumi da sa ido.

Ke ya sake fada na juyo cire face mark din nan naki ban tsaya ba na furta akan me zan cire abuna kaji
mai kai da wani magana kuma ?

A rainon Ammace da Abbu fa shagwaba har sari don ma ban da time din shiga mutane balle yanzu da
nasa a raina kowa yaimin zan masa don in tsira da raina wajen mutane masu bibikon kan asalina.

Daga cikin motan naji anyi min wani tsawa daya firgitani nakai hannu na sabule dan facemark din
kadan ina murguda baki baifi second ba na mayar da sauri yadda yake sai karan tashin motar naji a
kunnuwana da sauri sun bar wajen.
Bin bayan motar nayi da kallo number kano ce a motar saidai special number ce a motar nagani hakan
yasa naja kafata a raunane zuwa inda na baro sauran dalibai irina zaune suna dakon mutumin.

Dan wuri na samu nisa dasu kadan na tsaya nakai minti goma kamar ance in sake kallon takardan dake
hannuna sai naga is signed abin ya ban mamaki matuka har ina furta la,illah a fili.

Dan tunane na tsaya nayi kafin na nufi inda zanyi surmitting na mika ta dan kusuwa naga da sauri
maishi ya lekoni haka sauran ke bina da kallo yace dankari kinyi sa,a ke ashe ?

Haka na fito duk suka bini da ido suna kallo ganin an karbi takardan nawa alaman ke nan an saka min
hannu a nawa naja zulunbun hijjab dina na bar wajen a hankali duk da nasan idanuwasu a kaina yake.

Titi na nufa na tari abin hawa sai gida a gajiye nake kamar nayi wani aiki don wahalan da nake sintirin yi
a yan kwanakin Ammah kawai na gayar da gida na shige daki na kwanta ban falka ba sai bayan la,asar
koshi yunwa ya tayar dani.

Fitowa nayi na debi ruwa a bucket na daureye jikina tunda ina fashin sallah a lokacin har brush saida
nayi kafin in nemi abinci.

Abinci naci sosai inaba Ammah labarin na samu na kammala komai a cikin sauki ba yadda nayi tunane
tace Aeesha kin fita da albarkan iyayye fa akafanki .

Addu,an mu iyayye an fada maki yana faduwa kasa banzane ni dai ki kara tsare kanki don Allah wanan
wurin da zaki wurine daya tara mutane daban daban daga yayan manya har tallakawa don haka ki zamo
mai natsuwa da kula da wa yanda zakiyi hurda dasu don Allah.

Nan nace ni zan baki labari yau Ammah ba iya yina ya kwasheni zuwa wajen daba jama,a ba na tsaya
nan na kwashe labarin kaf na bata.

Tana dariya kuma ga tsoro a fuskanta tace dama nasani kabu kabunki da ji dai kai din nan naki sai ya
kaiki da haka to shi wanda kika zaga din gabanshi har yasa maki hannu ba mamaki ma shi dinne ya saka
maki hannu ai.

Shi kuma na fada a zabure tace kwarai in bashi ba haka kawai zai karbi takardan ya saka maki hannu
akan wani dalili kuma su karba bayan kin kai ?

Na shiga ukku indai shine Ammah din na zagesu tas a gabansu nikan shiyasa nake cewa ki rage wanan
girman kan naki malam yace wai in barki a jinin ki yake na sani ko ke din yar sarautane ?

Allah sarki kilama yar mai wanki da gugane nacen din wani dan sarauta zai auri bakar fata a can hakan
yasa Amma dagowa tana kallona niko na fuske.

Sai naji tace koma dai waye ai dadin abin ta hanyar halas aka haifeki Aeesha kuma Allah maji rokon
bawansane ako yaushe .

Abbu ya dawo da yamma da ledojinsa niki niki ina daki ina jin muryansa na fito ina taroshi kayan na
karba yana a hannunsa.
Ya miko min leda biyu daya fara saukewa sama kekensa nakai dakin Ammah zan shiga ya juyo yana
fadin yaki Nana ajeshi nan waje inzo don haka na dire a inda yace din na aje na koma na dauko sauran
nakawo na juya zan shiga daki yace yaki zo nan ai.

Hakan yasa na juyo zuwa gareshi Ammah ce a lokacin take shimfida masa tabarma tare da gyara kayan
nan dai na dawo na karba a hannunta kafin mu dukka ukkun mu samu wuri mu zauna.

Ammahce ce take fadin arziki haka malam jabe jabe daga ina nunani yayi yana fadin duk na yatace ga
baki daya don shirin karatun ta da zata soma jibi.

Ikon Allah har haka malam anya ba bata yarinyar nan zakayi ba da hakan kai ya girgirza tare da fadin
assha Ammamatan banyi zaton jin hakan a gareki ba kan yata.

Da sauri Ammah din ke fadin sam malam ba hakan nake nufi ba gaskiya to banda abinki Ammah nana
shiyafa yaro ga iyayyensa ya kamata ace ya dogara.

Su tsare mai komai na rayuwa da karfin su ba sai yaje yana hange a waje ba wanan wajen wajene na
mabanbanta mutane zata shiga a yanzu.

Yau in mun tsare yar mu da dan abinda Allah ya hore muna wanan zaisa hankalinta ya kau akan duk
wani abinda zata hango a wani zata tsaya iya karfin mu ta goga da kowa a wanan wajen haka kuma zata
fita daga kaidin tarkon dake dakon ta a can sunan jami,a ke kikeji a baki Ammamatan a yanzu.

Hakan yasa naje gun yarinyar nan mai dinki na gaban shagon mu nayi mata bayani da yake yar arzikine
kudin yadi dana kayan aiki kadai ta karba a waje sai gashi yau wai har ta gama komai ta miko min kin
gansu nan sune nan data dinkawa yar mu nana ya fara jawo kayan yana fitarwa daga ledan.

Dan murmushin jin dadin nake fitarwa daga fuskana don Abbu ya gama min komai a rayuwata kuma
gaskiya ya fada kan tsarinsa.

Murnushina ya dakatane a daidao lokacin da ya furta kinga idan ta hada da wanan da wanda nana ta
turo mata nasan zasu kaita wani dan lokaci tana ja.

Take naji fuskana ya tsuke lokaci guda don ambantan sunan wanan matar da yayi a lokacin gaba bansan
sanda bakina ya bude ba nace.

Abbu wanan ma ai zai isheni ko ban hada da wancan ba,,,, nanata da wancan nake son ki hada Abbu ya
juyo yana fada min a cikin wani murya a kausashe wanda saita baci yake irinsa.

Da sauri nace yi hakkuri Abbu ya juya baice dani komai ba sai ransa da bai sake ba har lokacin Ammah
na zaune ta saka muna ido ba tare data tsunka ba.

Sai zuwa can take fadin kafiya irin na yarinyar nan ni yana ban mamaki kafin ta karasa hannu kawai
Abbu ya daga mata taja bakinta tayi shiru a zancen.

Mikewa nayi da sauri ina tattara kayan don ganin ya dauki buta ya fara alwala a lokacin ina furta
nagode Abbuna.
Jeki kawai Allah yai maki albarka na amsa da amin Abbu na shige dakina da kayan naji yana fadin na
bata kudi ta sayo maki takalma da jakka da zakiyi amfani dasu.

Saidai matsalan ba a san girman kafanki ba tace kafan na juyo tare da dakatawa ina fada nagode Abbu
Allah ya kara girma da nisan kwana Allah ya barmi ku Abbu

7 / 109