Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
bafa kace bashir yasa hankalinsu ya koma akansa daga can bashir din yake
fadin aina fada ba zanzo ba ko mutuwa tayi ta dauka wasa nakeyi dama ?
Mun zuba hakan ne ai dani da ita aga wanda Allah zaiba sa,an kwasa a tsakanin mu dasu yanzu bashir
ne ko yayan nasa ya fada daga inda yake tsaye ya gyada masa kai alaman eeh a garesa.
Kada Allah ma yasa yazo dan iska mara mutunci da tarbiya wake bukatan zuwansa dama tunda mu
data haifa munzo ai shike nan.
Kyalesa kawai Ahmad yasan me yakeyi fiye damu kada kaga laifinshi ka daiji abinda baba ya fada tun
farko don haka ka barshi kawai yanzu.
Amma yaya don me zai fadi hakan ga kakanshi shi kadaine wai da zai dinga irin hakan ga hjy don Allah
mami ta fada a cikin yanayin damuwa .
Mami karki sa ranki a damuwa bashir yarone mai kaifin basira kakarsace ba uwa ba kina jin yasha fadan
hakan ai mu data haifa ba gamu dole munzo ba a yanzu.
Shiru tayi don jin amsan da yayan nasu ya bata a lokacin yaci gaba da fadin sam ki bar kula rikicin hjy
da bashir a ranki don inda sabo ya kamata ki saba da hakan yanzu.
Aikuwa kuci gaba da daurewa karya gindi don tana kakansa shine akace kada ya nemi albarkanta kome
ai yadda zaku saka mai albarka ya bishi haka itama idan tayi akasin hakan zai bisa don haihuwa ba wasa
bane.
Nan tayi ta babatunta ba wanda ya tsaya kulata a lokacin suka koma zancen jikin tsohuwar tasu kuma
kafin su kama gabasu daya bayan daya saidai su mazan suna zaune har lokacin.
Wayan ya aje a hankali yana murmushi a fuskansa dashi yasan abinda ya sakashi a murmushin lokacin
kafin ya jingina kansa saman kujeran office din nasa yana lumshe ido a hankali.
Tunane ya farayi a zuciyarsa ta yadda hjy zata yarda da zancen yarta har ayi wanan abin kuma yanzu su
so su kara maimaita hakan akanshi cikin ganganci bayan tasan waye yar nata.
Ko tana ganin shi ba zata iya irin abinda tayiwa mijin nata bane lokacin akansa tunda duniya ya rufe
mata ido da zuciya .
A sannu yake son garasu ta yadda sai sunsha wahala kafin ya fito asak dinsa nakoshi waye a yanzu don
kallon dan karamin tsako sukewa lamarinsa a yanzu din.
Abubuwa yake tunane wajen da dama yayin da yake faman juya kujeran da yake zaune akai idonsa a
lumshe yana nemo mafita gareshi.
Zakice komai bai faru tsakanin ma,auratan ba inba damin girman bakin da aka bar ita basir din dashi ba
sai gashi muna daki da Amira muna kallon cartoo ba kunya tazo ta tsaya min a kai tana fadin.
Zamuje nan clinic mu dawo Aisha saidai ban sani ba ko zamu dade a can don Allah ga Amira nan tunda
kina gida basai na fita da ita ba.
Jin ta ambaci sunana yasa na dago kai na kalleta bakin data tallabe tana magana yayi wani ja yayi
sundum dashi nace ayya sai kin dawo don iskanci sai tace min aida baba Amira zamu tafi shida yayi min
akan shi zai kashe kudinsa ai kwadala ba zan kashe bani.
Nikan ta fita ta barni da mamakinta fam ganin safiyace yasa na fito falon don babu kowa gidan lokacin
zuwa nayi kitchen don neman abinda zan karya dashi tunda tun safe bamuci komai ba a gidan don matar
gidan bata kunna wuta ba da sunan girki.
Fita nayi na kulle gidan zuwa dan wani kasuwa dake bayan su suna kiran wajen AIT na hado kayan miya
tunda naga suna da shimkafa na dawo a gurguje ruwan ya tafasa shikafa na wanke na zuba a tukunya.
Kafin na zauna gyara kayan miyan cikin dan lokaci na dafa abinci lafiyayye na gyara komai na kara
tsabtace masu gidan yayi fes na bude ko ina iska na shigowa Amira ta tashi nayi mata wankan na shirya
ta na kaita falo ta zauna na zuba mata abincin sai uku saura suka dawo gidan da yarsu dake zaune tana
cin abinci suka fara karo a falon.
Ba kunya mijin ke fadin a,a Amira kece nan tare da anty itako matar na fadin ay ba zata amsa maka ba
ta samu abinci haka na fada ma ba zata damu ba ai.
Na dago daga inda nake kwance ina masu sannu da dawowa kafin yaya ya zauna kamar bashi ba yana
fadin a,a Amira babu ko magana ?
Ko dago kai batayi ta kalli yan iska ba sai uwar ke zama tana fadin anty ta saya mata abinci ina zata
jimu yanzu lokacin na dago ina fadin a debo abincin ne ?
Wai dama ku kuka girka shine Aisha wallahi yunwa nake ji kuwa mara kunyar ta fada yasa na karasa
mikewa zuwa kitchen din plate biyu na zubo masu na kawo da ruwan sha duk na aje nakoma daki na
kwanta.
Sai surutu sukeyi ba zaki taba cewa sune sukai hayanin yan jiya ba a tsakaninsu wanda hakan ya daure
min kai nima dai kamar yadda suka dake haka na dake a zuciyana har fili kamar babu abinda ya dameni a
zuciyana lokacin.
Sai faman sakawa da kullawa nakeyi a zuciyana a kansu na kasa cinma manufata har lokacin sai Allah
Allah nakeyi gari ya waye in fita aiki.
Ranan kuma na fahinci wani abu ashe yan uwan basira din duk basu sallah don ko naga sun dawo daga
coci suma suka zauna suka kwashi girkin da nayi din.
Da yamma ma na fito nayi girki tuwon shimkafane da miyar ganyen egu sai agushi da stock fish dana
sayo a kasuwan dana shiga dazun da safe.
Nan wanan yarinyar da muke kwana tare ta shigo tana tayani aikin take min hira wai ashe talla suke
zuwa yi tunda safe da suke fita.
Wai mazan uwarsu daya da ita basira da wanan macen da suke kira da Bidi itace dai suke baba daya da
su take fada min suna son su ikantata taki yarda shiyasa bata kwana dasu falon .
Nan dai take ban labarin abinda ya tayar min da hankali fiye da wanda nake ciki tanayi tana lekensu ko
wani zai shigo ya ganta wai sai kana kwance kaji namiji yana shafama jiki.
Hankalina ya daga ainun saidai ban nuna mata ba sam tsab na hada lafiyan girki lokacin yaya ya fita
baya gida amma mun saka mai nasa a wani kula dana gani mai dan dama a kitchen din .
Mun rufe masa gefe daya nace ta fadawa yayanta idan ta fito don tana daki tana barcin maganin data
sha da zafin duka kuma.
Bayan mun gama na kimtsa kaina ban sake fitowa wajen ba nan wace daki gabana har lokacin ina
fargaban abinda ta fada min kan samarin nan.
Ina kwance a dakin sai gata ba kunya naji tana fadin anty Aisha ko yaushe ku cikin busy kuke ne hakan
yasa na dago kai nace sannu da gida anty .
Kece za a gayar yau ai kinsha aiki Bidi ta fada min kece kikai girgi koda yamma gasu can suna ta karin
abinci yau yan iska shine nazo in baki hakkuri kan abinda ya faru rudin shedani ne wallahi da
makwabciyata data zugani.
Ai baban Amira saida ya samu mijinta dazun da safe tace itama wai rudin shedanine don taga kyauki
yayi yawa kada mazan mu su soki .
Anty Basira ke nan na fada ina aje Laptop dina gefe daya nace kinyi kuskuren fahintana da hakan da
kika yarda kikayi akan yaya ko wani yace min zakiyi min hakan ba zan taba yarda dashi ba .
Mijinki ki tambayeshi da ace ina sonsa da an min aure dashi yanzu ko, don ko umma taso hadani dashi
tun ina karama ki tambaya kiji don umma kawar Ammah ce.
Ko wanan zuwan da kukayi saida aka tayarda zancen nice na nuna masu sam ba haka ba na kuma yiwa
umma din kashedin hakan a kaina
Amma duk muka ki hakan akan mu yau kece da yi min hakan sai naji tace dani haba komai ya wuce
don Allah kuskuren shedanine .
Shima din yayi min bayanin komai ya fada min jinya kiyi hakkuri please nima ina kunyan abinda nayi
maki bayan kaunan da kika nuna min da yarinyana na amsa da ba komai.
Safiyan monday na tashi da wuri na shirya don zuwa aikina gudun makara a gurguje na shirya na bar
gidan ban tsaya yin aikin komai ba don na riga harsu yan kasuwa saurin fita ranan.
Saidai titin ba kowa hakan yasa ban sauri fita da safe sosai don haka na dan fara takawa da kafa badon
wai nakai office a,a saboda in rage tsayin da zanyi waje daya.
Akwai motocin dake dan wucewa ko a lokacin to amma ba commacial cars bace wata parado ta biyo a
guje ta wuce sai kuma naga tana danyi baya baya kadan zuwa wajena yaja ya tsaya.
Aka sauke glass din motar a hankali tare da fadin morning queen na dago kai na tare da sauke mai kallo
matashine shi sosai mai jini a jika da jin lokacinsa shine ke jan motar.
Kai na kawar gefe daya daga kallonshi ina cigaba da tafiya a hankali yan mata ina zaki haka da safen nan
ba a samun mota a wajen nan yanzu .
Wanan karon muryace ta mace nakeji kuma ba muryan yara bace a lokacin maishi ke magana dashi
hakan yasa na dan duba da sauri koshi ke wanan maganan da nake jin din kuma a lokacin.
Wata mace ce a bayan motan zaune a cikin shiga ta kamala da mutunci tana kallona take sauke wani
murmushin a fuskanta tace kyale wanan kinji akwaishi da zolaya ga gidan mu nan kinga maigadi na rufe
get shigo mu saukeki ta kara fada.
Aiya nagode mama zan iya samun abin hawa can gaba kadan ,a,a diyata bakya son mu samu lada da
wanan safiyan wani yazo wucewa da kayan juging dinsa naji yace barka da fitowa doctor ta amsa mai
hakan yasa na yarda na shiga motan tasu.
Saida na zauna dake na fara gaida ita da hausa don jin tayi magana da wancan mutumin a cikin hausa
ba tare data amsa ba take fadin ai nasha keba bahausace ba ?
Nayi zaton dai kin shigo nan yin wani abune don kina da zube da yan Aran sosai wallahi ashe hausa
hakan radau na dan gyada kai tare da furta eeh.
Ni yar kanoce nazo wani training ne a nan din na yan kwanaki tace Ok kuma a wanan unguwar kike da
zamane ?
Indai tambayace sai ban shiga waje ba balle wanan ya damemi call ta daga tana magana akan wani abu
da aka tambayeta a lokacin daga gida.
Naji tana fadin ki duba don Allah ba mai taba ransewa ke din kin iya hausan kozo in kasheki kina ji ai .
Wallahi nasha dai bakuwar kasance yan bude ido ke har mun shige ki ai naga kamar sauri kike ki samu
abin hawa a nan din hakan kuma is a risky wallahi gareki.
Don saboda akwai bata gari yanzu garun nan ba security sosai yasa nace dashi ya dawo mu taimaka
maki mu rage maki hanya.
Nagode mama na fada naga ta lumshe idanuwanta sai cewa tayi ina zaki sauka na fada mata wajen sai
naji tace ai na gabane kadan damu.
Yazid ka sauke ta sai mu tafi kabi sannu don Allah ta fada a karshe don gaskiya gudu yake sosai a
lokacin .
Shiru ya dan biyo baya kafin kuma ta kara jefo min tambaya nasan taga kankantana ace ina aiki a wajen
yasa take tambaya na da zakije ganin wanine kuma dai gaki da shiga irin nasu.
A,a na fada a ladabce nace nazo trainin a wajen ne na wata uku daga kano ban jima da zuwa ba sai
naga ta jijina kanta tana fadin, what gaskiya kinyi kokari .
A wace makaranta kike karatu a kanon na fada mata tace masha Allah gaskiya abin yayi very interesting
kinyi kokari yata.
Kai kaji ka duba wanan da shekarunta don Allah har tazo yin IT amma hafsat ta tsaya tana ta shiririta
shekara da shekaru don Allah zanso taga wanan yar wallahi.
Yazid din yace amma ai kamar bata da nisa sosai damu mum ina iya kai Hafsa din ta ganta idan tayi
muna kwatancen inda take.
Na danyi murmushi nace a cikin area din nake zaune gidan yayana saidai zan nemi wani wajen don
matarsa ta nuna bata iya zama dani.
No no no akan wani dalili ita kuma don dan kwanakin da zakiyi dasu murmushi nayi ba amsa baku da
wasu yan uwane a cikin garin nan bayan su ?
Nace a,a shi din dan yayan babane dama yake aiki a nan garin bayan hakan akwai maza a gidan nima
zaman bai mun dadi ba haka.
Donshi zan nemi wani wajen in zauna a kusa da wajen aikin mu kai gaskiya kema din dai tsayin mu
gareki a yau sai ince wani hikimane daga ubangiji hakan ?.
To abin ne yanzu wallahi sha,anin taimaki ne a yanzu yana da wuya shiyasa kowa ke tsoron ttaimakon
yanzu don akasin da ake samu daga baya .
In bashi ba sai ince zaki iya dawowa wajen kiyi zaman ki har ki karasa aida na shina kowane balle ke
yarinya haka bai dace kije neman waje haka ba a yanzu.
Wayarta ta miko min tana fadin saka min layinki a nan saki kira naki zan kira in an jima muji in sha
Allahu nace lah mama wallahi ba matsala zan samu akwai inda wata wace muke tare ke haya dama sai
dai matsalan ita ba musulma bace amma zanyi manage in zauna da ita hakana.
Baki yarda da fadan dan uwanki bane da yace Allah ne ya hadamu a yau din don shi yasan halina ban
tsayi idan mun fito zuwa office amma kwatsam nida bakina yau nace a tsaya mu taimaka maki din to ki
yarda Allah ne ya jefo mu sin mu taimaka maki din a halinda kike ciki.
Shine amfanin adduan mu iyayye a gareku me yuyuwa inda kike shawaran zuwa din a yanzu bai da
amfani a garekine .
Yasa ubangiji yai hikimarsa akan mu dukkan baki daya da safen nan don na hango natsuwa a tare dake
dan zaman nan na yan mintuna da mukayi yanzu a nan daken.
Mum kofa zamu ajetane Yazid din ya tambaya tace ka shiga idan suna bari wajen ne nasu da yawan
tsaro wallahi .
Ai ina ga in sun gamu a tare zasu bari a shiga kila a hankali nace eh zasu bari din card dina na nuna
masu suka barshi ya shiga ba bincike.
Wurin nan naku badai tsaro bakan ko villa sai hakan naji uwar tace dashi kaiko sune kamar idon kasa fa
komai dake faruwa suke bada signal din hakan .
Inda ake parking suka tsaya zan fita naji hjyn na fadin idan kun kusa tashi sai ki kira waya yazo ya
daukeki shi kuma a lokacin naji yana gaisawa da wani officer a wajen .
Kafin mutumin ya tako yana gaida ita da doctor ashe tare kuke tace wallahi yata na tsaya mu sauke ya
kalloni yana fadin wanan yarkice ashe nakan ganta a nan wani lokaci haka ?
Nan na barsu bayan na kara mata godiya na shige suka ja mota suka tafi jin mutumin nan ya kira hjyn
da doctor yasa na fahinci likitace matar ashe .
Haka na shiga ciki a ka,ida duk wani babba aka hadu zaka gaidashi kamar wasu yansanda muke akwai
ban girma sosai a wajen.
Gashi wajene babba mai hawa da yawa office office ne gasu nan jere ko wani bangare daban suke
muna hawa na biyune mu manyan ke can sama.
Iyakata saman mu ko na dayan ban taba kallon ko ina ba idan na shigo amma yau ina zuwa ga mamaki
sai wata mai dan buje ta tareni da fadin .
Miss Aysha mahamud nace yes mah sai naji tace dani flow me na juya na kalli bayana ba kowa dana
sani a wajen ba abinda ya fara zuwa min rai sai abinda ya faru ranan jumma,a ya fado min a raina .
Lokacin guda wani tsoro ya mamaye zuciyana na gabana ya shiga faduwa na fara kiran sunan Allah a
can kasan raina.
Gata da shegen sauri fit fit da ita da dan buje mai tsaga a baya muna zuwa elevetor naga ta dana biyar
a lifter muka haye cikin yan mintuna sai gamu a wani katon waje mai kyau ba yawan mutane ko
hayaniya a wajen .
Ko don hakan safiyace mutane basu gama fitowa ba alokacin naji wajen hakan oho ?
A bakin wani office taja ta tsaya ta juya ta kalleni tana fadin inshaga madam tana ciki da mamaki na
tura kofa na dauka mutum daya zan sama kamar yadda tace min din sai naga sabanin hakan don ko
mutane sun kai goma sha saman kujerun dake wajen zaune.
Saidai akwai wata dake a saman wani babban table farin shigowa wajen tayi min hannu na karasa zuwa
wajenta kai tsaye.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[9/5, 9:15 PM] Zainab Idris Makawa Writer: JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
4️⃣2️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ONLINE TRAINING!*
*ONLINE TRAINING!!*
*ONLINE TRAINING!!!*
*Are you looking to level up your game with traditional spa?*
Whether you are married woman, bride to be or some one who loves to master the art of *traditional
spa*, *natural aphrodisiac* and *Traditional incense* asalin kamshin shuwa look no further in this
article *@sady_aromamist_and_spa* have got you covered
Imagine you know all the ingredients used on your skin to moisturise, nurture and revitalise it, *intimate
confidence* and a good long-lasting Traditional scent.
Transform your space
Transform your skin and have that intimacy confidence. Join our online training
Wa.me/9048763046
learn the connection between *skin care,* *Traditional incense* irin kamshin nan mai kama jiki and
*natural aphrodisiac* masu matukar kyau with zero side effects 😍
Sign up now to join the waitlist(https://chat.whatsapp.com/EDJan6LcDjGDrh6geC0Bk5)
Early birds 7500
Actual price 15k
Follow our IG handle for free recipes @sady_aromamist_and_spa
Start