Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
taja muna ina zamu dashi garin nan ?
Umma ki shiya gobe da safe indan Allah ya kaimu idan yayi maki zanzo in kaiki ku gaisa dashi har iyalin
nasa ba tare da kin tsaya zaman jiransa ba.
Masha Allah dan albarka ai gara dai hakan zaifi min sauki idan ba haka ba sai ya zama min waka kuma
inzo banje ba.
Nasir ya mike yana fadin man zan barka nan ni zan tafi yake fadin bari ka saukeni kawai tunda gobe
zan dawo .
Nasir din yaiwa umma alheri suka fito tare da anty ummi data rakosu zuwa wajen motar ta nan suka
dan dade suna surutu a tsakanin su.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[10/23, 10:17 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
7️⃣5️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6
https://sitrix.africa/signup.php?ref=foleesco
Zaune nake a tsakar gida dani da Abbu daya kirani bayan ya dawo dauke da yar ledan magani daya hado
min shine ya kirani inzo insha .
Bayan nasha na zauna wajenshi muna dan hira jefi jefi dashi wanda hiran nasa ma akan mijin ummune
da yake ban labarin yadda suke da gidan maimartaba dashi din.
Sosai nayi mamakin jin alakar tasu ashe babbace sosai dasu man ke nan bata wasa bace zumuncin su
dashi a raina nace sukan ai sunji dadi suna tare da kowa nasu.
Don ni sai yanzu na fahinci ko yan uwan uwa bandasu bayan Ammah da yar uwarta da kawai nasani sai
kuma yaran Ammah din sune zance ga yan uwana najini na a duniya.
Haka kuma ko ita gwaggon bansan yayanta ba gaskiya na daiji Ammah tace tana da yara a yadda na
fahinta kamar mijinta ne yayi ma yayansa da mu iyaka don yace shege a waje yana taushe yan gidane a
karshe.
Tun wanan zuwan da Ammah tayi dani bata sake zuwa dani gurin gwaggo ba sai dai idan zuwa ya
kamata ta barni a gida da Abbu taje ta dawo.
Yanzu kam nagama fahintar kaf yan uwan uwarta basu son in rabesu don acewan su a sanadiyar
haihuwanane suka rasa iyayyensu kuma mutuncin gidansu ya zube a idon jama,an gari.
Hakan yasa nima a yanzu babu burbushin su a raina kamar yadda mutum kanji dangin uwa sun shiga
ransa tunda sun nuna suna kyamata tun ban girma ba har na kaiga girma na fahinci hakan a wajensu.
Muryan Abbuna ya katseni da yake fadin watau Nanata mutane na shagala da son duniyan nan har su
manta da akwai gobe ranan tsayuwa.
Jin hakan yasa na katse tunanena na dago ina kallonsa yake fadin wai ace matarka ta sunna uwar
yayankace zata so kashe ka kan abin duniyan nan dan kalilan nana ?
Abbu matar kuma har da yara ?
Yace kwarai kuwa shine mana ya faru da mijin ita nana Asiya matarshi tayi yunkurin kasheshi a lokacin
Allah ya kawo Asiya a rayuwansa lokacin data barmu dake nan zata neman mahaifinki ?
Sai Allah ubangiji cikin hikimarsa gurizirinta ya kare a hanya suka yada zango anan ta zaune kusa dasu
har Allah ya kaddara taji shirin kasheshin da suyi din.
Nan Allah ya bata ikon dabarab sanar dashi shine tsiransa da kika gansu a tare yanzu inba hikimar
ubangiji ba ko waya kai can ?
Sunbar kasa daya kuma gari daya sai a wata kasan ubangiji ya hadasu da yake akwai rabon zuria a
tsakanin su.
Katseshi nayi da tambaya Abbu dama ana iya kwanaki a hanya ba akai saudiya ba ni nakanji mutane na
fadin ansaka mana idan suka tashi zuwa saudiya ?
Kai kurciya ho ya fada yana murmushi kafin yace da nana wayansan jirgin nan da mota da kafane
tafiyan sai ga mota daga nan kuma sai ga jirgi.
Amma har gobe akwai masu zuwa da mota idan sunkai gaba sai a tsalaka dasu ta ruwa da jirgi gaskiya
Abbu bansan da hakan ba na fada.
Watau nana hakan nada hatsarine yasa kikaga ba,a damu da zuwa ta wanan hanyar ba ai amma har
gobe wanda baida karfi yana hakan aidai akwai wahala sosai wajen yin hakan.
Itako tun farko da hjy mai gwal ta dauketa tanan ta nuna mata hanya yasa da zata koma ta koma ta nan
kuma .
Ai ke dai bari nana sai muryan Ammahce kuma ya sake katseshi ga abinda zai fada da take fadin cikin
tsomawa hiran mu baki tace.
Aini malam zancen matar nan ya daure min kai tunda najisa ace matarka ce zataso kasheka kan abin
duniya don Allah ?
Nawa akayi har wanda ma yafi hakan ai anyi ke dai Allah ya sauwaka kawai za ace amma abinda akeyi a
cikin duniyan nan bar zancen kawai Allah ya kara muna imani da tsoransa a cikin zukatan mu amin.
Kinji yadda akayi suka hadu don haka duk surutun mutane na banza da suke fadan wai tana can tana
barikanci a kasa mai tsarki karyane ga gaskiyan zancen tun bayan barin ta nan gida tana da aurenta.
Ai malam ba sai an fada bama masuyi sun daiji kunya ko don gani yaran nan zangada zagada ai ya
ishesu jin nauyin hakan Ammah ke fada taci gaba da fadin.
Ni wallahi yanzu zuciya na fes banda sauran kunci ko takaicin kan yar uwata tunda Allah ya wanke
muna ita fes a idon jama,a.
Da zata dawo ta dawo da mijin da duk gari suna fatan samun irinsa a garin nan ni yanzu ai kallon masu
shagube nakeyi kar wallahi.
Kallonta nayi kafin na mike tsaye zuwa dakina tun ban karasa shiga ba naji Abbu na fadi ai ba shine
damuwansu ba yau da mahaifin nana zai baina kowa ya gansa to komai zai gushe cikin zukatansu amma
ba waban bane damuwansu ai kema kiyi tunanen hakan.
Yarinyar nan tafimu gaskiya na zauna nayi tunanen abinda ke matsalanta nasan kuma ba zai wuce
wanan ba kuma gaskiya ne hakan ai.
Don wanan kaf idan ba ai hankali ba duk saiya shafe gaskiyanta a zuciya da idon kowa su dauka karya
takeyi hakan dai aka samu nanata din ba uba a lokacin.
Shiru naji tayi bata kara magana ba saida nashiga daga ciki nake jin tana bambami daga wajen tana
zage zage ni dai ban fito ba.
Kamar yadda yai alkawari da umman haka ya cika karfe goma da rabi ya shigo gidan baffan nasa da yar
mahaifiyar nasa da yayanta da suka take mata baya tare da abokiyar zamanta mota biyu suka shigo dasu
gidan.
Yasan komai na gidan a wanan lokacin ya kwatanci da baffan nasa ya gama karyawa da iyalinsa bai
kuma fara ganin kowa ba a lokacin.
Kai tsaye ya nufi ciki dasu duk masu tsaron gidan sun sashi kusan shinema ya daukesu aiki matasane
majiya karfi dayasa aka nemo masa.
Suna falo zaune sukai sallama suka shigo ganinsa yasa baffan nasa bai damu ba don yasan zuwansu
yana da muhinmanci a wajensa.
Saida suka zaune aka gaisa kafin shi man din yace baffa ka ganesu kuwa ya dan juyo garesu yai masu
kallon second kafin yace kamar hafsatun shehi ko suka dan dara umma na fadin ashe baka mantani ba ?
Haba dai hafsatu ai ba zan taba mantawa dake ba suka kara gaisawa tare da masa barka da arzikin
dawowa gida da yayi da fatan Allah ya kara tsare gaba kuma.
Suka gaisa da ummu dake gefen mijin nata kafin ya dan dauko bayanin cewa ai duk da ina can
hankalina yana nan gida hafsatu ba abinda yafiwa bawa dadi kamar gida.
Yau gamu zaune tare da kowa namu cikin jin dadi da anna,shuwa ai wanan rahamar ubangijine ga
bawansa lalai a lokacin da akai yunkurin kasheni da Allah ya basu sa,a da yanzu kashi ya zama kasa ko.
Ikon Allah abin ba dadin ji wallahi Allah dai ya kara muna imani da tsoron sa a zukatan mu yasa mufi
karfin zuciyar mu Amin aka amsa dashi falon.
Umma ga mahaifiyar mutumiyarkifa yana nuna mata ummu din dake dan nazarinsu ta kallo ummu din
cikin yanayin rashin gane ko wa yake nufi da mutumiyarta.
Wallahi ban gane ba magaji ta fada tana kallon ummu din ko zataga wani kama da zata tuno fuskan wa
yake nufi amma ba wanan gaskiya.
Umma itace mahaifiyar Aisha dasu hjy ke kira da yar kwara ke khairat kin dai gane ai da wani irin
mamaki tace umma Aisha balarabiya fa yake nufi.
A,a,a dan albarka kace min diyata balarabiya ai sai infi ganewa ai tsaya dai wanance mahaifiyar ta ta
cikinta kake nufi ?
Yace itace ta haifeta mahaifinta balarabene mutumin kasar Oman amma yana zaune a Dubai duk dai
kasan nasune acan yakeshi da zama.
Ikon Allah ga yarsa a nan ita kadai kun koma can kun barta nan Allahu akabar ashe yata na cikin farin
ciki haka ban sani ba gaskiya nayi mata murnan hakan.
Sai kuma ta juya wajen shi man din tana fadin wai tsaya dai in tambayaka amma yaron nan kasan kan
tsiya wallahi.
Da ace mutumiyar banza nake lokacin danai ta baku hakkuri ku riketa da daraja ku tausaya mata ka
nuna min kai baka ma san inda ta fito ba a lokacin.
Amma dan yau sai a barku duk tsawon shekarun nan wanan abinda ake famanyi wai ashe yaron nan
kasan ko wacece yarinyar nan kabar a na wanan shirmen haka ?
Kome yayi hjy hafsat nina sakashi yin hakan ko ita uwar yarinyar bata sanda hakan ba balle ku nan mun
bata kyakyawan tsoro da kulawa yadda ba za,a dinga muzanta taba a idon jama,a.
Hakane kuwa Alh don gaskiya tayi daraja da kima da kwarjini akan haka ake ta fama da kakansa da yan
uwa dake fadin bata da asali .
Amma kuma ya dafe mata ba zasu taba yarda ya bata irin gida ba da dauko yarinyar da bata da asali
yace zai aura an daiyi rikici sosai kan hakan.
Ashe yaron nan duk kallon mu yake kawai yasan abinda ya taka suke ta hawa sama shi da hjy mama kan
zance guda.
Umma ko yanzu akansa ne yasa nace zanzo dake da kaina kiwa Baffa murna da arziki don akwai
matsala gaskiya.
Wa,iyazu billahi duk da ga zahiri sungani matsala akan me kuma yace ba wanan ba umma ita dai Aishan
taki yarda ta tari iyayyenta da hannu biyu wai tana fushi sun tafi sun barta a cikin kunci da bakin ciki data
fuskanta a rayuwa.
Allah sarki kurciya kada ranku ya baci da hakan don wani gun tana da gaskiya saboda ba karamin cin
fuska ta fuskanta a rayuwanta ba gaskiya.
Amma yanzu ai tunda kunzo iyayye sunfi da hakan kurciyane ke damunta tunda bata san duk gatan da
magaji ke mata daga wajenku ya fito ba hakan .
Amma a sannu da lalashi da ban baki da fadan a sannu zata sauko insha Allahu amma wanan gaskiya sai
hakan ya fito dama .
Zamanin wayewan kai din nan da muka shiga a yanzu sun san abinda kai babba ba zaka kawo a ranka
ba akwai wanan umma don Aisha ta waye fiye da tsanmani nikai na har tsoron hakan nakeyi idan na
ganta.
Kaji wanan suka fada suna dariya yace ba wasa ba yarinya ce mai basira da kwazo dan kallo daya
zataiwa abu ta haddaceshi a kanta.
Don shine nake son zanyi hanyar da zatazo gida wajenki don Allah umma a tsawata mata kan wanan
fushin da takeyi hakana ta barshi.
Hakan baida matsala indon wanan kwarai umma nasani baki san ko wacece itaba amma kin nuna
kaunarki akanta ita kuma tasan da hakan ga ummi nan ga khairat sai ku san dabaran da zakuyi tazo
wajen umma din.
Don ni kaina yanzu sama sama muke da ita tunda tasan hakan tana kallon hada kai mukayi dama dasu
baffa don haka takewa kowa kallon makiyinta.
Abin ai baiko kai can ba ke yanzu kharat saiki ki fada mata ina gari ina nemanta ina gidan umma munzo
gaida baba da baida lafiya tunda baba din dama nazo gaiyarwa.
Sunjima ana zance kafin ummu ta mike tana fadin hjy mu shiga daga ciki kuga waje aikuwa dai hajjaju
don haka suke kiran mutumin daya zauna makka yayi haikjn hajji ba iya ka da hajjaju.
Duk da akasari sunfi kiran wanda take zaune a can tana zaman neman kudi amma sunan ba wai illa
bane don ankira mutum da hakan.
Sunshiga sunga waje inda shi maigidan ya fita wajen jama,a shi kuma man ya zauna a nan falon yana
tura wasu sako da suka dauke masa hankali.
Sun jima a ciki suka fito da alheri don zumunci ya kullu sosai a tsakaninsu da ummu din don sunyi hira
akan tafiyanta da abunda ya faru da mijin nata wanda batayi da wani ba sai a lokacin.
Ko su din dai sama sama ta basu labari sunyi da anty ummi zata dawo gidan washegari zata nuna mata
wani vers da sukai maganan sa a lokacin.
Shiya maida umma da kishiyaeta gida anty ummi kuma taja kannenta zuwa wani gida da take son zuwa
sun tafi suna al,ajabin abinda ya faru din .
Ina kwamce Asmau ta shigo tana fadin mummy barci kikeyine idona biyu Asmau na dai kwantane
kawai mummy ke baki gajiya da wanan kwanciyan ne ko yaushe.
Idan nice da jikina ya dibgi yayi nauyi sam bana son kwanci iri haka wallahi saukin abin ke kikace ni bake
bace ai Asmau ?
Ta kalloni ta kwashe da dariya kafin tace wai jiya munga duniya ashe gaskiyan mama data rude haka
taga abinda idonta bai taba zaton zaigani a rayuwanta .
Sukan su ummu sun more duniya Allah yasa can su tarar da abinda yafi hakan nace amin yabawa kowa
nasa rabo na alheri duniya da lahira.
Ta kwashe da dariya kafin tace wai bari mummy abin nema bai faduwa wallahi ban masan ta ina zan
fara ba wallahi.
Naga daddy man fa bai kira ki ba na fada masa baki da lafiya mun fito sun tsayar da motarsu a kusa da
wace zamu shiga.
Naga ya kallo mu nagaidashi wallahi ya ganeni da farko ya dan tsaya yana mamaki sai kuma koya tunane
yace daughter,,, nace Asmau yace yes muka gaisa dashi nake fada mai baki da lafiya baki zo ba.
Dama baki fada masa ba wallahi na fada ina daure fuskana lokacin aka kirani a waya na daga sunan
dana gani ya ban mamaki.
Don anty kharat dinsune a layin nace ji sister dinsa ke kirana fa yanzu muna zancensa na daga wayan
muka gaisa naji tace dani .
Wallahi Aisha baki da zumunci shiyasa na shareki kwana biyu yanzuma anty ummi ce ta tambayeki
shine nakiraki kinsan baban mu baida lafiya shine tazo duban jikinsa .
Subbahanallahi wallahi ban sani ba kuwa da sauki daiko tace Alhamdullahi ya samu sauki har an
sallamoshi daga asibiti ai.
Nace jam anty ashe abin babbane har asibiti ya kwanta Allah ya bashi lafiya shida sauran musulmai tace
amin anty ummi tana gaidake .
Zanyi magana naji an kashe wayan nabi wayan da kallo cikin mamaki sam ban dauki hakan as a plan ba
ko set up akaina don nasan sun damu dani ko banza sai naga ban kyauta ba ai.
Na kara kiranta akan insha Allahu zanzo in duba jikin baba inga anty ummi din mukai sallama lokacin
Asmau tabar dakin ni kadaice a dakin nawa kwance.
Mikewav nayi na je gaban mirro na gyara jiki na yafa mayafi na fito ina fadin Asmau ina samira muje
gidan akwai ?
Samira kan bata gidan nan tundazun ta fita wai zata karbo abu a waje bata dawo ba dan shiru nayi
kafin nace kina aikine yanzu gidan su maryam nake son zuwa.
Yauce rana farko da zan fita tun bayan baiyar mahaifiyata don haka nasan dole a zuba min ido din
mutane akwai gulma kan abinda bai shafesu ba a yadda nake gani.
Tare da Asmau muka fita gidan aikuwa dai kusan abinda nake zargine ya faru don ina fitowa wajen isa
aka zubo min idanu caaaa na kawar da kaina kamar ban gansu ba.
Nasan sunsha gulma har sungaji sun fadi abinda bashi da wanda shine kuma duk akan zance guda
mukai sallama muka shiga.
Matan gidan suna zaune a tsakar gida suna aikin girki muka gaidasu nan suke min murnan dawowan
ummu din suna fadin ranan sun shiga ai basu ganni ba ance nayi barci.
Ni dai murmushin yake nayi muka wuce zuwa dakin su maryam din na samu maryam tana wanka sai
faridane kwance tana kallo a wayanta.
Zama nayi akan kafanta don har yanzu muna wasa da juna akan yaya sulaimab dinsu tana ce min matar
yaya ni kuma ince ai sun hana banson zolaya.
Yauma hakan ta fada nace matar mai rabo ai kun hana keda umma ta kwashe da dariya tana fadin
kinga dadin da yaya yaji dana fada mashi mahaifiyarki tazo gashi gashi.
Kinga murnan da yayi sai fadi yake alhamdullahi wallahi yaji maki dadin hakan sosai wallahi kinga yanzu
sai a maida hannun agogo baya ke nan ki shiga ta biyu tunda yanzu zai fara auren wanan nan.
Allah dai ya tsari gatari da saran kashi mu dai zauna yaya da kanwa din zaifi don kada a bar zumuci
koshi.
Ta kwashe da dariya tana fadin ana dai son ana kai kasuwa yarinya dakin more inda kin yarda kin shiga
ta biyu wallahi muka sa dariya gaba dayan mu.
Maryam ce tashigo dakin tana fadin tunda naji dariyan ku ai nasan kun shigo ke nan ina Allah Allah
infito kamar kinsan kina raina yau wallahi.
Munyi hira sosai don ban bar gidan ba sai wajajen magariba muka fita zuwa gida bayan mun aje idan
Allah ya kaimu zamu gidan su kharat mu gaida mahaifinsu daga can mu wuce gidan wata kawar mu da
zatayi aure.
Muna shiga gida ana kiran magariba saidai mun shiga mun samesu a tsakar gida ga wasu akwatuna
wai ashe tsaraba ummu ta aiko muna dashi don kayansu sun iso.
Samira cikin murna take fadin yauwa mummy gara da kika shigo yanzu don Abbu ya hana kowa taba
tsarabanki wai sai kin dawo za a bude mugani.
Tsaraba me kuma