Chapter 90 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   90 / 109

267K to 270K   out of 326.5K words

ubangiji.

Gashi a yadda yake jin cewa mahaifin nata baida wasu diya a duniya sai ita kadai tuna hakan yasa ya
dan rutse idanunsa tare da sakarwa kansa ruwan shower daya kunna yana huci a bayin shi kadai.

Don a yanzu kan yana da wuya gaskiya iyayyeb yarinyar nan su barta taci gaba da rayuwa a Nageria
kuma.

Kai inama ina ace tun farkon haduwansu ya furta mata kaunan da yake mata a zuciyarsa ne ?

Koba komai zata dinga tunaneshi cikin irun mutanen arzikin data zauna dasu a baya akasha soyayya da
zaman lafiya.

Haka ya fito daga bayin cike da tunane a zuciyarsa a gurguje ya shirya don ya kusa makara zuwa wajen
aiki a lokacin.

Yayi nisa ga tafiya bayan yabar gidansa yaji kamar wayarsa tayi kara ya dauka yana dubuwa mamakine
karara a fuskansa ganin wace ke kiran nasa har two miscall nata ya sama.

Bin kiran yayi ya maimaita yayi da yai sa,a ya shiga saidai ban daga ba a bangarena lokacin yasa ya
hakkuri amma zuciyarsa yana cike da mamaki hakan ?

Bayan fitan su Abbi din daga dakin shirune ya dan biyo baya kafin Abbu ya kawar da zancen da fadin
da alama ki samu katbuwa sosai a wajen mutanen nan nana.

Duba ga yadda tsohon nan ya damu yake kuma kara rokon ki gafara duk da bashine yayi maki laifi ba .

Amma ya dage akan ki furta kin yafewa kowa nasa alaman yasan addininsa matuka baya kuma son
hakkin wani akansa ko kadan.
Kaiko malam ba dole yasani ba sune tushen addinin fa larabawa dan murmushi Abbu yayi da Ammah
ta fadi hakan yace kaiya .

Larabawan mafa suna suka tara ko baki sanda hakan ba akwaisu kan da rikon addini gaskiya ta,ayin
rikau haka kuma har yanzu a cikinsu akwai wa yanda basa musulunci fa ?

Ni malam ai naso ace wanan abin daya faru a Nageria ne ya samemu don da wallahi na koma tsohon
unguwarmu nayi shela suzo suga mahaifin Aeesha da idonsu.

Gashi shiru shiru dashi bawan Allah tun jiya nake kula da dabi,un shi waje taron nan sam baiyi wani
magana ba har aka watse daga taron kamar abin duniya yai mai yawa a rayuwan sa ?

Shine ai balle babu komai insha Allahu kila haka rayuwansa yake zan iya cewa shi nana ta biyo wajen
rashin son magana da yawan shiru shiru din nan nasa.

Malam tu yanzu ai ganin tsoro mukai masa ba zamu iya cewa ga halinsa ba ai yanzu inko irin
rayuwansa Aeesha ta dauko lalai akwai aiki kuwa ashe ?

Dan kallon Ammah din nayi duk da raina yana jagule a lokacin lissafine iri iri kasan zuciyana nakeyi a
lokacin akan makomar rayuwata a yanzu shine naji Ammah na fadin wanan magana.

Nanata wai kin kira yaron nan da yaita dawainiya dake shekara da shekaru kin sanar dashi abinda ke
gudana Abbu ya katse min tunanen da nakeyi a lokacin.

Abbu wa ke nan fa na tambaya ina kallonsa don bansan wa yake zance akansa ba don ban dauka man
yake nufi ba ?

Yaron nan dan wajen su Alh Asiya mana yarima yake ko magaji dan murmushin yake nayi ina fadin man
bashir ke nan ban kirasa ba Abbu layinsane yana da wuya a samesa sai idan shi ya kira mutum.

Don shi bai faye zama waje daya ba yana da yawan tafiye tafiye saboda yanayin aikinsa da yake hakan.

Wayata dake hannuna nake jagula ina neman layin nasa duk da nasan baya shiga gaskiya don kamar
yadda nace din ne ba a samunsa haka kai tsaye shi.

Saidai Abbu ya cigaba da fadin ya kamata ace yaji daga bakinki Nana kafin wani ya fada masa komai
don yaron yayi kokari a cikin rayuwanki matuka duk da sakashi yayi akasashi amma yaron nada mutunci
da sanin ya kamata sosai wallahi.

Haka yai ta tallafa muna cikin hikima ba tare da kowa yasan manufansa ba sai a karshe ya zauna dani
yake sanar dani komai kuma ya rokeni da kada in yarda ki san komai da ake shiryawa akan ki din.

Garesa nake jin su Asiya zasu dawo gida lokacin saidai ban fadawa kowa hakan ba saida suka iso aka
gansu yaron yana da mutunci sosai wallahi.

Wanan nasan wani abin bama suke sakashi ba a cikin jikinsa dai yake tallafa muna kawai don abin
gaskiya yayi yawa sosai wallahi.
Koda Abbu ke wanan zancen kasake nayi ina kallonshi cikin mamaki watau ya tabbata ke nan Abbu
dama yasan komai akan su ummu tunkan su dawo amma ya boye muna.

Ammah ce da mamaki yasa ta kasa shiru tace yanzu malam dama kana da labarin Asiya kasa muna ido
kana kallon mu munata shirme don Allah ?

Nasani saidai sanin nawa duk bai wuce shekara biyu zuwa uku ba gaskiya tunda ya rokeni kinga aibana
saba alkawari ba ko ?

Cabdi jam watau dai maza a barku kawai da mune mata ai babu abinda zai hana na yada cewa yar
uwata ai zata dawo a cikin daula.

Murmushi Abbu yayi yana fadin yanzu ai ga daulan yarki ta samu a hannunta sai ki baza a faifai ki shiga
talla gida gida idan mun koma.

Dagudu kuwa don muna komawa zan taka gidan raba kaya dasu zan fara ba don kowa ba kuwa sai don
hjy Agina dake sakin baki tana yada cewa Aeesha shegiyace bata da uba karya mukeyi don a rufane
kawai ake fadan hakan .

Kaiya ai kafin kije gidan Audu raba kaya ki fara a gidan ki kuma dakinki don da safiya ya kamata ki fara
hakan har in zakiyi don ban taba gani butulun mutum irin yarinyar nan ba safiya.

Naji dadi matuka da komai ya faru gaban idonta ta sheda kuma ta gani sai ta koma taje itama ta baza
ke nan tace ai zancen data fada a baya ba gaskiya bane ga yadda zancen yake.

Ita safiya dai malam safiya tamu kake nufi da wanan abin yace kwarai kuwa lokacin da naci mata
mutunci ai duk baku sani ba ku akan nana.

Shine kikaga tashiga hankalinta da bayan nan don kashedin da nayi mata tasan kuma tund na furta zan
iya hakan ba wasa a cikin zancena.

Kofan da aka murdane ya hana kowa tankawa a lokacin matar nan mai hidimace ta shigo cikin
fara,anta tana gaidamu.

Wani abuncin ne kuma ta kara shigo muna dashi ta kwashe kayan wanda muka karya dashi da safe ta
fice dashi din zuwa inda ta fito.

Allah mai iko ita wanan din yar aikice ko matar gida Ammah take tambaya bayan fitar matan daga part
din da muke zaune.

Ai wanan da gani mai aikice wanan Abbu ya bata amsa ashe suma suna aikatau a yasu,yasunsu fararen
fatan ?

Keko da shirme kike wallahi halan duka aka taru aka zama daya suma ai dole akwai tallakawa a cikinsu
akwai kuma masu kudinsu.
Wanan Matar daice taa sake dawowa dakin ta shigo da sallama muka amsa cikin ladabi ta fara min
bayani yadda zan fahince ta .

Na amsa mata da nagode ta juya ta fita su Abbu na kalla ina fadin wai tsohon nan yace na shirya gasu
nan fitowa Ammah ke fadin shine take faman mismismis da baki kai jama,a.

Saiki matsa aiki ya sameki yanzu kuma koyon wanan yaren naku mai wuya me zata koya a cikin yaren
kuma yanzu tunda duk abinda suka fada tana ganewa.

Ki dai yi mata fada akan ta kara sakin jiki dasu don Allah iyayye ba abin wasa bane nanata su din dai
ubangiji Allah ya kaddara sune iyayyen ki .

Zancen tsohon nan ne da yace ksun gode Allah ba zina dansu yayi ya haifeki ba aure ne ya samar dake
tsakanin su.

Ko wanan ya isa ki saka su alfahiri dake dasu har Asiya duk da mukan a bangaren Asiya musan baki da
matsala kin dauki tarbiyan da mukai maki kuma.

Kamar yadda tsohon yace katfe hudu bayan anyi sallah muka shirya fita din saidai lokacin na sauya
tufafina zuwa jallabiya a lokacin.

Wata tsararrar mota muka shiga na dauka dagani sai shine fitan sai da nashiga motar naga ashe har da
mahaifina a cikin motar da kuma yayansa din nan da aka gabatar min dasu a matsayin yan uwan
haihuwan iyayyena.

Shiga da sallaman da nayi masu yasa tsohon sakin murmushi yana kada kai alaman yayi ya nuna min
wajen da zan zauna a kusa dashi na nufi can na zauna a cikin kame jikina.

Ba tsohon ba dukkansu sunji dasin hango natsuwa tare da addini a kwayan idona don ban zauna ba
saida na furta bissimillah a cikin siririyar murya da har suka dan jini lokacin.

Nifa renon izzalace ta Nageria akida har wanda ba a saka ba malam mu sun koua muna tun ina
ficiciyata a islamiya don me ba zanyi koyi da akidar tawa ba a yayiyin dana tsunci kaina tsakiyar
larabawan aslin irin haka ?

Dama nakan ji ana fada cewa addinin bahaushi idan ya riketa tsakani da Allah ko wata akida ya fito
indai dan Nageria ce sai ya bambamta da wasu idan ya shiga cikinsu saidai ga wanda yai sakaci da
addininsa shine har za a ga gazawan shi.

Don Allah yaiwa al,umman kasan Nageria baiwan arziki da rikon addini fiye da zaton mai zatan koyi
mukeyi da larabawa din dan Nageria shi kaifi dayane a zuciyarsa kan addininsa Allah yasa mu dace amin.

Sam ban dauki hakan da nayi da wani manufa ba don kusan abin ya bi muna jiki a nan koyi da addini mu
kama kan mu mussanman mu mata hakan kuma nake ko a zahiri ina koyi sosai da abinda na taso a
cikinsa sosai.
Masha Allah jikan tawa ashe mahhadaciyace nake gani tsohon ya fada a cikin zolaya da son bugun
cikina yaji yawan zurfin ilimina a lokacin.

Dan juya daradaran idanuwa na nayi ina murmushi ba tare dana bashi amsa ba yake fadan da alama na
haddece alkur,ani mai girma na gyada masa kai da hakane habibai.

Yai murmushi ya fara jero min tambayoyi ina bashi amsa a tsanake yayin da idona ke akan titi ina
karewa garin kallo .

Don iyakar inda na sani da farko wajajen masallacine kadai inda Abba yai muna masauki da zamu zauna
muyi aikin umuran mu mu koma gida.

Sai gashi Allah ya nufa zansan wasu wajajen ta dalilin nasaba da mahaifina na asali da yanzu ya baiyana
min a rayuwata.

Sam banyi mamakin irin tambayan da yake min ba don ummu ma da mijinrta munyi hakan dasu
zuwana gidansu.

Sai can na tuno da zancen man da yake tsawata min cewa an kaini gidan su ummu ne a lokacin don na
saba da wasu akidu da ake sona dashi ga gaskiyan zancen ya fara tabbata tun ba,aje ko ina ba a yanzu.

Ban damu ba don nasan gwargwado ina da dan sanina saima bokon dana koma yasa ban zurfafa can
nayi mugun nisa a cikin addini ba sosai dama kuma ilimin mace ai ragagene ba kamar namiji bane.

Masha Allah gaskiya Allah ya sakawa iyayyenki da suka reneki tabbas mahaifiyarki ta fito tsatson
mutane arziki ita din ba mutumiyar banza bace yadda mutane ke daukansu a nan.

Jin hakan yasa na dan juyo na kallesa ba tare dana iya amsa addu,an dayaiwa iyayyen nawa ba a
bakinsa.

Sai kuma naji yace dani why kika canza wanan kayan al,adan ku kayan sun matukar karban ki sosai kici
gaba da saka abin ki kada ki manta da al,adan mahaifiyarki.

Murmushi nayi kafin na kalloshi ina fadin ko acen irin kayan da nafi sakawa ke nan don dashi na saba
sosai wacan kuma muna amfani dasune occasionally ba ko yaushe nake sakasu ba duk da al,adan kasan
haka yake.

Ke din yace ta kwarai abin alfahari ga iyayyen ki don da alama akwai baiwa mai albarka da ubangiji ya
halittoki dashi kinsan ko wani mahaluki yana da kalar baiwan da Allah yai masa.

Sai lokacin yayan mahaifina yai magana ya dan juyo yana fadin Abbi ita sin hazakice ta na,uran mai
kwakwalwa kasan abinda muke nema ke nan yaran mu sun kasa tsayawa suyi wanan karatun kuma.

Masha Allah kace min yar taka ashe dai yar baiwace ta gaske da Ubangiji ya azurta ta a cikin mu .

Gaskiya naji dadin jin hakan sosai wallahi dama na fada maku mutanen nan hazikaine da wuya kaga
bakar fata mara amfani a rayuwansa.
Bamu dawo gida ba sai dare sosai wasu manyar kamfuna mukai ziyara sun kai guda ukku a cikin garin
ni dai ban gane ma,anan fitowa dani ba a lokacin.

Saidai ina kyautata zaton don kawai su samu kebewa danine su binciki wasu abu daga gareni kamar
yadda har muka dawo tsohon nan bai daina jefo min tambayoyi ba akan rayuwana har na karatuna saida
muka fafata dashi.

Na kara godewa Allah da iyayyena su Abbu da suka tsaya tsayin daka sukai min tarbiyan mai ingaci da
yau ya tallafa min a rayuwata.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[11/18, 9:38 PM] Zainab Idris Makawa Writer: ake14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:




JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

9️⃣2️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6




Abinda dai nake gudun shi ya faru don ko iyayyena maza cewa sukayi dani zasu wuce zuwa dubai naga
gida zan kwana biyu a wajensu zan dawo gida na karasa karatuna a cewarsu.

Ranan da Abba yazo min da zancen nayi kuka sosai amma Abbu yayi ta karfafa min gwiwa da dadadan
kalamanshi har naji karfin gwiwa a zuciyata.

Na zan iya binsu din ba tare da fargaban komai ba tunda kamar yadda ya fada a yanzu dai nasan ciwon
kaina ba wani abinda za aimin bansan yadda zan nemawa kaina mafita akan abin ba.

Da ace ni karamace yace ba abinda zaisa na yarda su tafi dake nanata don nasan cutar dake za ayi ba
tare da sanin mahaifinki ba.

Amma yanzu ga shekarun nan naki banjin ko darr game da hakan kanki nana don nasan zaki iya dako
wani irin taro sukai maki a can din.

Kada ki yarda rudin duniya ya rudeki ki sakaci da ibandanki nana taimako da saukin kai gana kasa dake
kamar yadda na sanki dasu ki bisu da al,adansu yadda suke gudanarwa matukar ba sabawa Allah hakan
yayi ba .

Ire iren zancen Abbu ke nan a kaina kusaan wuni guda da mukayi dashi a masaukin iyayyena sako na
aikawa Maryam da Farida Asmau sai Samira dasu Nusaiba har mamata ta Abbu haka na zauna na rubuta
na kowa a jikin takarda na liki jinkin kayan .

Sun rigamu barin Saudiya don sai mun kara kwana hudu kafin mu bar kasan nan kan na kasa daurewa
don saida nayi kuka bayan na bude ido naga babu kowa nawa yanzu a tare dani sai Allah sai mahaifina
da yan uwanshi kuma da yanzu zan koma sabon rayuwa a cikinsu.

Duk da ummu har wajen wanan hjyn gwaggonta da yanzu ta zamo tsohuwa sosai shirin komawa
Nageria takeyi a yanzu ta gama cin saudiya .

Ko ince ruwa ya karewa dan kada bai gama wanka ba don ko tsufa yayi kabbara a gareta ko neman
kudin a zaune yanzu yana batun gagaranta yi.

Don babu baya babu kafafuwan tafiya hakan yasa take shirin koma gida ko a mutu a cikin yan uwa
Sai dai zuwan su ummu din bata zaci hakan ba don ma da farko bata shedasu ba saida akai dogon
bayani ta dago tana dafa ummu din sai hawaye tana fadin Asiya ki gafarce don Allah ki min aikin gafara ?

Kece nan ummu tace nice gwaggo ga yar dana haifa lokacin da kika aurar dani ga balarabeb Ouman
nan ta dago tana kallona da yakusasun idanuwanta.

Tana furta Allahu akbar ta nufoni da niyar dafani na danja baya ina kaucewa tace Allah sarki yar nan ku
gafarceni don Allah aikin shedane da son duniya.

Hjy ai hakan a yanzu ya zamo masu alheri a rayuwansu don mahaifin yar nan ya karbi abinsa yanzu
haka muna tare dashi ga kuma basaraken dake auren ita Asiya din Abbu ya nuna mata Abba da hannu.

Sai kuka tana wani yarfan majina nidai ina faman bin inda suke rayuwa a kazance sunan ana saudiyane
kawai amma a cikin takura suke zaune suke wanan kazamin rayuwa bindan kudin gaskiya a yadda
nagani.

An dai mata alheri aka bar wajen yanzu kan dangin mijin ummu sun yarda cewa ummu ba yawon
bamza tayi ta haifeni ba don abinda tsohuwar ke fadi.

Zaman ne a waje daya tun safe bayan tafiyan iyayyena ina dakin nan da nake kwance ni kadai sai mai
kawo abinci idan ta shigo mu dan gaisa ta juya ta fita sai wani lokacin kuma idan ta dawo kawo min wani
abin.

Duk da nasa amma sai zaman ya fara gudurata a dakin ashe gara gida ko ina daki inajin hayaniya ko
motsin yan gidan mu wani lokaci.

Nan ko ba motsin kowa saidai idan na kwatanci lokacin sallah yayi in mike inyi sallah a dakin kafin
wajajen karfe biyar naji an turo kofan dakin nawa again.

Wanan matar dakan shigo ta kura min ido kamar suna nazarin wani abu game dani sune ko a lokacin
suka shigo dakin su biyu again.

Saidai wanan karon bada dayan matar da suka saba shigowa tare tazo ba addu,an da Abbu yace na
dingayi ko a yanzu shina ja a kasan zuciyana dana gansu din.

Kamar yadda ta saba idan ta shigo ta kura min ido hakan ne ya faru ko a yanzu din don idanuwata
dayasha bakin kwalli ya juya kamar wata halitta shita kasheni dasu tana bina da wani kallo mai kama da
tsana a idanuta.

A yanzu kam ban raba daya biyu don Abbi ya fada min cewa ita din matar mahaifinace kuma yarsace
don dan uwanshine ya haifeta.

Wanan yasa nake fassara kallon da take min da kallon tsanace kawai ba na wani abu ba saidai na daure
don huduban iyayyena dake min yawo a kaina lokacin.

Izuwa yanzu na haddace gaisuwan su don hakane na gaida ita da wuni cikin ladabi irin namu na al,adan
hausa kamar yadda na

90 / 109