Chapter 79 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   79 / 109

234K to 237K   out of 326.5K words

yake sabanin naku na
maza daddy dansu ke fadan hakan yana kara mikewa.

Saurata ? ita mace wani saurata aka santa dashi banda zama dakin miji tayi biyayyan aure yau datayi
hakkurine ta zauna da abinta lafiya bata saka son zuciya ba wanan daulan na yanzu da yake cikinsa tunda
Allah ya rubuta masa arzikinsa a goshinsa wa zaici inba ita da diyanta biyu ba ?

Amma mugun hali da sheri ya hana kura kwantan da hankali taci arzikinta ala dole da karfin tsiya
zatacisa ?

Yanzu ga arzikin kamar banza tana gani babu halinci a gareta sai dai tagani ta hanga kamar yadda
maimarta ba yaba da umarni.

Amma da baba yai hakkuri ko gidan nan an gyara matashi da take ciki hukuncin yayi tsauri da yawa
wallahi ku ba baba hakkuri don Allah.

Ai iya adalcin da zayi mata ke nan a cikin ruwan sanyi a kuma raga mata amma da ai baba yace zai kira
hukuma su tafi da itane baba ciroma suka bada hakkuri.

Abindai baiyi dadi ba wallahi gara da aka rufa zancen nan a tsakani baifita ba duk da kusan rabin gari
sunji wanan labarin nake gani.

Au gari anji ke nan ko? dama nasan dole aji zancen nan ko don yan gidan waziri don yadda suka
zargeta tun farko abune wanda bai rufuwa dama don tayi ganganci da yawa gaskiya.

Sun dauki lokaci suna zancen har bayan fitan dansu da barrister Nasir yazo ya dauka suka fita suna
zaune suna zancen.

Daga inda salman yake zaune yana karyawa jikinsa yayi sanyi tun a wajen waliman daya fahinci
gaskiyan dan uwansa daya kasa fahintarsa a baya.
Shi yanzu duk yadda zaiyi yayi don ya shawo kan Man dayayiwa mumunan fahinta akan yarinyar nan
amma abu ya gagara.

Kawai da iyayyensu zai kara hadashi su bashi hakkuri ko zasu dawo irin yadda suke a baya don a gaskiya
abubuwa na batun tsaya masa yanzu daga albashi sai albashi ke shigo masa kawai a lamarinsa.

Haka kuma yadawo nan wajen kanwar mahaifiyarsa ne da zama duk sabodashi duk da miji da matan
duk yan uwansa ne najini zamansa a gidan baida illa amma sanadi dai ai don man din yadawo dindindin
gaba daya gidan nan.

Ina kallon ikon Allah a gidan mu da ace a gidan anty safiya anty baraka da iyalanta sukaje bakunta
bansan ya za ayi wanan abu ba.

Do yanzu ya kai sai naji anty safiya ta fice mun a rai ga baki daya abinda ya faru kuwa shine.

Kwana biyu tunda na kula da nufin anty safiya akan yar uwarta nakan fito na tsaya naga ankai masu
abinci wadatattce da zasuci har su raga.

Don tun akan shayi dana kai na fito ta rufe ido tana fada dani ba kunya wai ita yaranta ba zaikai su
samu ba na kwashe nabawa anty baraka da yaranta su ukku kadai.

Ina bata hakkuri ina fadin kinsan bakine gara a basu mu muyi hakkuri anty sai naji tace ki daiyi hakkuri
Aeesha amma sukan ina zasu samu suci inba nan gida ba.

A raina nace to wanan kamar bata san inda anty baraka ta fito ba zatace hakan ? yar uwata ce fa tillo
take nunawa hakan ?

Ammah ce ta fito ta saka muna baki cikin fada take fadin ke kan baki da hali safiya halin nan tun kina
karama nake rabaki dashi gashi yanzu ya zama maki fitina.

Na wuce na barsu a wajen shiyasa na tsaya kwana biyu na basu kula sunko fara mayar da jikinsu
gaskiya don da gani suna cikin wahala a can inda suka fito.

Ina daki ina barcin rana don jiki da naji yana min ciwo da aikin kwana biyu ga kuma yaran anty baraka
ba irin yayan anty safiya bane da gani sun saba da aiyuka tun a gida.

Don suna sallame sallah zasu fito su share gidan nan tas ko ina suyi masa kwal su tattara wanke wanke
su wanke baki ganin kazanta a gida .

Haka in ana girki zasu fito su dan kama sai yasa na kwanta daki ina rage lokaci na shaki barcina a cikin
barcin na dinga jin kukan babban mace wai ashe anty barakace.

Take kuka saboda anty safiya ta zuba masu abinci can rabin kula shine ta fito tunda itama ba bare bace
tai magana anty safiya din ta mayar mata suke musayar baki sai kuka.

Dana fahinci ba mafalki nakeyi ba na saurarara da kyau naji anty baraka na fadi a cikin kuka haba safiya
yau ko yaran nan kadai na turo gida kyayi masu haka ?
Yadda kike da iko a gidan nan haka nake dashi tunda mukazo bansan me zamu tare maki ba nake ganin
kina muna ganigani kina muna abu kamar mu wasu barene can.

Jin hakan yasa na mike da sauri na fito wajen ga Ammah tsaye takasa magana sai cin mutunci sukewa
juna a tsakaninsu duk da dai ita bakuwan ba wani mugun kalami take fada kamar ita safiyan ba dake
kado manyan magana.

Haba anty wanan abin bai kawo kallo ba wallahi a gaban mu kuke wanan abu haka tsakanin ku hakan
zaisa kan mu yara ya hadu waje daya.

Saida na fadawa maman abincin nan bai isarsu ai tace in bata waje kada,,,,,,kallon da anty safiyan taiwa
Asmau yasa ta fasa karasa zancenta.

Nima ban koma magana ba wajen abincin dake rufe din na nufa akwai abincin da yawa a wajen nace
Fattu da cewa yar anty baraka din da sukazo.

Dauko abincin akara maku anty safiya ta kalloni kamar zatayi magana sai kuma tayi shiru saida nacika
masu kula ta kalla ta juya ta wuce zuwa daki.

Anty baraka din na fadin aidama kin barshi Aisha tunda shine ranon mu kinsan yanzu mu bakine ita da
yaranta yan gida.

Ban dau kulata ba na zuba abincin na dago ina fadin Asmau in wanan bai isarku ki girka wani sai lokacin
naji ammah na fadin bai isarsu kamar ya karshe nan zasu barshi ya kwana sai an zubar.

Nasan Ammah bata fadi karya ba don haka halinta yake almajirai zasuyi ta bara tana Allah ya koro ina
jinsu amma da safe zakiga abinci anfito dashi ya lalace.

Iyayyen sunyi fada har sun gaji sun saka mata ido saida shi Abbu idan ya gani har gobe yana magana
kan hakan.

Asmau ta dauki abincin ta kai mata sai gashi tace a fito dashi a dawo dashi kitchen Ammah ko ta shiga
rigan arzikinta da zagi.

Nashigo tana fadin masu gida sunyi yadda ya dace me zance shiyasa banson mu hade da baraka gidan
nan tun fil,azil .

Wanka nashiga na fito na shirya da niyar shiga gidan akwai don nasan yinin ranan habaici zata wuni yi
ba sauki sai wajen Allah.

Muryan Ammah ya dakatar dani da shirin da nakeyi da naji tana fadin butulci dai irin naki safiya sai
halinki yanzu meye laifin yarinyar nan Aeesha a ciki don ta raba maku fada ?

Tsakaninki da yar uwarki shine kuma abin ganin laifinta mama ina fa zance Aeesha tayi laifi yanzu tunda
itace mai gida ai bata laifi yanzu a wajen kowa ?
Wani zance kike son daukowa ke nan ita Aeesha din daban take daku da ta zama mai gata fiye da kowa
gun mu ?

In bashi ba mama har Aeesha ta isa ta nuna banyi daidai ba tsakanina da baraka ina ruwanta damu ko
kuwa don raini zata ce min hakan ta kwashe muna abinci ta mika masu.

Amma ke kan kinji kunya wallahi na yarda baki da wayau da malam ke fada yau.

Kiyi hakkuri anty safiya banyi hakan da wata manufa ba nayine don kuna nawa duka anty baraka kuma
kamar bakuwace yanzu a cikin mu shine dalilina nayin haka.

A,a fa ai kiyi abinki nan duk arzikin ki mukeci yanzu ba dole muga komai ba in badon shi daya watsar
damu ba ina za a ganin har haka ya faru.

Ammah ce ta kalloni take fadin ke koma daki kyaleta tayi tayi daidai da ita yana zuwa tunda ita inba an
shiga rigan mutuncinta an fita ba bata gajiya da fitina.

Juyawan nayi na koma cikin da Ammah tace dani lokacin na samu wayata na kara na duba ummuce a
layin na dauka.

Muka gaisa take fadin sai ban kirata nai mata bangajiyan taro ba nace wallahi naso zuwane har gida sai
kuma zuwan anty baraka ya dauke min hankali.

Waiba muryan yaya bace nake ji haka ita dawa take fada haka nace anty safiya a takaice .

Assha meku safiyan tayi haka nake fada mata dan magana daine tace maganin safiyan ke nan saida
nace ta dinga zuwa nan taki bansan me take zamanyi a gida ba.

Ummu anty baraka nake son suzo gidan ki su kwana biyu don Allah su huta anty safiya ta sakata gaba
da yaranta da tsangwama.

Tace jam itako safiya meya sameta haka har yanzu tana da halin banzan nan haka suke fa tun muna
yara

Yo barakan suzo mana tazo da yaranta yanzun nan zan aiko a dauketa suzo nan suyi zaman su su huta.

Sosai naji dadin hakan sai nace angode ummu tace dame fa da kikai hakan wallahi matar tausayi take
ban tunda tazo garin nan ga kuma anty safiya ta hanata shakat.

Abbu kuma baida kudi a hannusa wallahi ga gida ya cika masa da iyali ba isashen kudi hannunsa maneji
yakeyi.

Jam garin yaya hakan ya faru nace ban sani ba amma naji wai shiya biya kudin motan anty safiya da
yaranta barshi zan turo masu da sako ta fada.

Tana batun kashe waya nake tambayanta yaran tace min suna lafiya suna kewana zanzo ai yarage
gareki ai yanzu ta fada ta kashe wayan.
Zama nayi a bakin gado ina bincikan wayata baifi dan tsawon wani lokaci ba na dinga jin ana sauke
abinci gidan namu hakan yasa na fito daga dakina.

Asmau ta tareni tana fadin ummu ta aiko da abinci tace kuma mama baraka su shirya ga mota nan a
waje suje wajenta su kwana mata biyu.

Nunawa nayi kamar ban san abinda ya faru ba nace yama fi mata suje can din su dan huta kwana biyu
nima zan tafi na kwana biyu .

Gidan ummu din ta tambaya da sauri nace eeh gara inba anty waje zaifi don maganan data fada dazun
kamar nice nake sa tana fada da iyayyenta ?

Don mama zaki tafi mummy ina jin tsoro kada kije ummu ta rikeki can gabadaya don yana da wuya ta
bari ki dawo gidan nan kuma inkinje.

Nabar Abbuna dawa Asmau ina nan zandai jene tunda ta matsa banje na kwana masu biyu ba su hamza
suna tambayana ?

Anty baraka suka shiga shiri ta rasa me zata dauka gashi ance gidan manya ne nashiga dakin nida Asmau
nake fadin ashe gidan ummu zaku tafi ?

Tace yanzu fa ta bugoma mama ga mota nan zata turo a daukemu zuwa gidanta zamu kwana mata
biyu a can gashi na rasa ma tsun man da zan dauka ?

Dariya nayi ina fadin aiba damuwa gidane ina ganin ba wanda ya damu da wani a gidan amma bari
inzo na juya zuwa dakina wardrobe dina na bude gefen kayan dana dade ban saka ba ina da wasu
zannuwa da riga da banjin dadin sakasu yanzu.

Suna fiddo dasu nata kala ukku yaran sun samu kala biyu dogayen rigunan atamfa nakai masu sukai ta
murna a raina nace zaku samo wanda yafisu a can ai.

Kayan nan anty baraka bata bar gidan nan ba saida ta nunawa kowa tana fadin Aisha ta bani nida yara
mu saka.

Abbu da akaiwa waya ya dawo tun a waje driver su ya tareshi ya bashi sakon sai gashi ya shigo gida da
murna yana fadin Asiya ta kirani tace inzo ina da sako a waje ana jirana yarinyar nan kuma tana son taje
suyi mata kwana biyu can.

Ai dole malam hakan ma yafi sauki wallahi don safiya tasa yar uwarta a gana da cin mutunci ta hanata
shakan a gidab nan yau tonon asiri tayi muna akan abinci ba wanda taragawa daga baby din har Aeesha
har ni gidan nan.

Zata aika idan safiyace nasanta sarai zata aika banda cin mutunci ba abinda ta iya a duniya banda
yanayin lokaci zaki ganta gidan nan ?

Don tashin hankalin nan nace ta dawo gida har abin nan ya lafa don hankalina ba kwance yake ba da
suna can din.
Data fiki hankali ai batazo da diyan duka ba matan kawai ta kwaso tazo dasu tabar mazan can da
ubansu.

Keba yafiyan tafi da gidanka kiyo muna ba kika kwaso kwanki da kwarkwata kikazo muna nan da kikazo
waya hattareki yasaki gaba dake zaki saka yar uwarki haka ?

Zaman nan naki daki keda fitsararan yar kin nan mai sunan kwano a gidan nan ya mara kunya da
gadara kun kai min ko ina wallahi.

Kuka anty safiya ta sake daga daki yace kukan munafunci wallahi kika matsa min ko kasheku zasu sai
kin koma da yaran nan wajen dagin ubansu can garin.

Bazance a,a ba kan tunda abin nata ya zama iya shege yanzu banda tsiya laifin me yarinyar nan Aeesha
tayi don ta raba maku gardama keda yar uwarki.

Sai kawai ki saka yarinya gaba da gori da cin mutunci yanzu me aka kawo nan ba abinci bane wa zaici
inbake da diyan ki ba ko nayi rantsuwa ban kaffara har abincin nan ya kare Aeesha bata cin cikon dan
roban nan tunda ita ba abincine ya dameta ba.

Amma keda yaranki ku zaku amfana dashi to don wa aka kawo badon Aeeshan da Allah yayi rayuwanta
cikin mu bane alherin yake zo muna hannu a saukake dukda Asiya tana yar uwata wani abin aiba zan
gashi ba haka dai ?

Ba a ragawa dan uwa ita Asiya da nake yarta ta mayar da mu uwa da uba yanzu a duniya keko yadda
nake zumunci da yan uwana wanan bai isheki koya ba wayansan wanda nasa zai zamo wani abu gobe sai
Allah.

Kuka kawai anty safiya keyi saida taji Abbu ya fitane ta fara magana tana fadin in badon Sahabi daya
gudu ya barni ba me zai kawoni gida haka in zauna ?

Sai ki shirya kije nemansa duk inda yake yafi muna zaman ki kina muna tujara Ammah ta fito daga daki
tana fadan hakan gareta.

Ammah don Allah barta zancen nan ya wuce hakana muka fita raka su anty baraka wace Ammah ke
kira da baby kasancewar yar farintane bata kiran sunan ta baraka.

Itakan ta tafi da yaranta can zasu kwana biyu a yadda ummu ta fadawa iyayyen na kuma ji dadin hakan
sosai ko ba komai dai fitinan zai rage a gidan tsakanin su mu zauna lafiya.

Har muka dawo tana kan Abbu daya sai abinda ta manta a bakinta kowa ya fita batun ta yadda take
aibantanine naji ban iyaji da yamma sai gani na fito da shirina da yar jakkata nida Asmau dama mun
kitsa hakan nace wa Ammah zanje shagon Abbu na sallameshi zamu gidan ummu mu kwana.

To dada safiya kinga yadda kike so yau kin samu abinda kike nema zaki raba muna kai dani da yan
uwana yau sanadin cin mutuncinki.
Idan Aeesha ta taka wajen uwarta kinsan ita da gidan nan saidai ziyara idan tazo muna kuma don rike
abinsu zasuyi tun da mun gaza mu.

Ke kuma ki sani watan zaman ki gida ya kama ke nan a yanzu mudin yarinyar nan ta bar gidan nan yau
malam ya dawo ba zaki kwana masa a gidansa ba keda iyalan ki idan kince karyane ko ki sa ido ki saurara
mu gani.

Asmau ne ta kalloni cikin sanyi jiki dan maganan da Ammah tayi a kan tafiyan mu but samira dake cire
uniform ta fito daki itama da sauri tana fadin .

Dama haka ai take so tunda na dawo na samu tana sakin magana haka na shiga nayi mata magana ta
koromu nasan sai wani abu ya faru irin haka ?

To to to Abbu dan halas ya shigo da kayan cefane yana fadin hakan Ammah tace gara da Allah ya kawo
ka dai malam gata can bata bar zagin ba har yanzu .

Ita kuma Aeesha ta debo kaya tace zata wajen uwarta shika sama munayi yanzu ta fada cikin kunan rai
da da lcin zuciya kan safiyan.

Kallon da Abbu yai min yana aje kayan daya shigo dashi a leda wanda Asmau ta nufeshi ta karba a
hannunsa yasa da sauri na bude baki nace a,a Abbu ba tafiya zanyi ba zan dai je can ne na kwana biyu .

Affa Nanata kamar kin tafine ai wallahi abbu ba wai tafiya zanyi ba ai nana daki tafi ki barni saidai ita
yau ta bar gidan nan .

Zaifi min sauki amma ita bata kai min can ba wallahi ina take ta fito yanzun nan ta tattara diyanta tabar
min gidana amma ke baki zuwa ko ina inba gidan ubanki bane yazo garin nan wanan banda ikon hana
hakan a kanku ubankine shi.

Yaran anty safiya suka saka kuka gaba dayan su lokaci guda gida ya hargitse Abbu ya kafe da lalai sai
sun bar masa gidansa a ranan dole muka shiga ban hakkuri da kukan mu.



ZAINAB IDRIS MAKAWA

[10/31, 9:52 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:




JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

8️⃣2️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6



https://sitrix.africa/signup.php?ref=foleesco




Tafiyan da banyi ba ke nan don maganan Abbu naso naje na wanke laifina gun ummu dake ganin naki
sake jiki dasu har yanzu dama masu fahintar hakan.

Allah yagani halittanace hakan banda sauri sabo da mutum haka farat daya lokaci guda haka yasa har
yanzu nake jin ban iya sabo da ummu lokaci guda yadda ake nufi din nan.

Itama ta fahinci hakan yasa take kokarin mu saba don lokaci lokaci zata kirani a waya tana jana da hira
ban iya bata amsa da zan iya sakin jiki da ita haka farat daya sai ehh ko a,a shine nawa.

Ko a gidan mu sai in wuni ban leko waje

79 / 109