Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
da kikewa bakin cikin kike wanan rama to ni nan nasan kin sani.
Saidai ina kwankwanton a inda kikaji wanan labarin shine ya daure min kai a yanzu ba wani abuba so
nike insan me aka fada maki game da mahaifiyar ki ?
Da alaman tsoro a fuskana na dago ina kallonta sai kuma na dukar da kai ina tunane tsokin takaici naji
taja tana fadin.
Ga kayan can da taba wani bawan Allah tare da kudade masu yawa ya kawo maki har damu don haka
sai ki tashi ki duba idan zaki iya don naga kin sakawa zuciyar ki abinda bashi ba a yanzu.
Kaina girgiza nace ko tsinke bana so Ammah abawa wanda duk ya dace nagode ai bankai karshe ba naji
saukan hannun Ammah a fuskana saida naje tangal tangal daga zaunen da nake don zafi.
Fada ta fara tana fadin ni zaki kawowa diban albarka Aeesha sakaiyar da zaki min ke nan a yanzu ace
na hinjiraki ban maki rikon gaskiya na tsakani da Allah ba.
Idan Nana da mahaifinki sun maki laifi da farko idan kin kula yanzu ita Nana kokarin take ta burgeki ai
taga ta wanke maki zuciyar ki.
Ina laifinta ga hakan tunda duk wani abu donko take turoshi a garemu saboda rayuwanki ya inganta ai
kada ki dauke mu bamu san abinda mukeyi ba mana.
Ko duniya Nana ta mallaka a yanzu wanan bai tsone min ido ko in kalla balle raina ya biya da ace aikin
banza takeyi a can mutumin nan saida ya rantse muna kamar yadda itama ta rantse masa da aure ta
daura a can din bayan ta koma saudiyan.
Don haka ki shiga taitaoyin ki dani kafin ranki ya baci kada ki dauko min wani surfa banza ki dagwala
min lissafi dashi yanzu kuma.
Sautin kukanane ya karu a lokacin akan nace ban karban kayan da Nana ta turo muna Ammah ke min
wanan fadan da baida tushe haka har duka abinda bata taba min a rayuwana ba tunda na tashi.
Gyaran muryan Abbu alaman zai shigo gidan a lokacin yana sanar muna hakan baisa na rage sautin
kukan da nakeyi ba wiwi ina jan majina ta hanci don zuciya daya kawo min.
Tundaga kofan gida yake fadin wai yayane meke faruwa hakane wai daga Ammah har ni ba wanda yai
masa magana a lokacin.
Sai ya cigaba da fadin tambaya fa nakeyi anyi shiru meya kawo haka kuma yanzu Ammamatan ya juya
kanta ya kureta da ido yana son jin amsa .
Haba malam kamar Aeesha zata zauna tana gardama dani yau don wani ya rutsata ya fada mata
maganan daba shiba ta dauka tana kokarin rainawa mutane wayau.
Juyawa yayi gareni saida ya kare min kallo a cikin tausayi yace haba Ammah kibi yarinyar nan sannu
mana don Allah yau ko me tayi tayisane akan kurciya da dacin rai.
Don ko an tabata dole tayi hakan ina hakkurin ki ya shiga da zaki biyewa yarinya kuna saida hali a cikin
shiya muryan kukanta har waje na tsinkayoshi.
Ai dole in biye mata malam da wani yarinyar nan ke son inji a yanzu da nata iya shegen da takeyi yanzu
ko da wanda muke fama dashi kan rashin yar uwarmu.
Duk yadda take ji mumafa muna jinsa a yanzu aiko inga dubaiya ban cancaci hakan a gareta ba a yanzu
me muka rage yarinyat nan dashi don Allah malam a yanzu ?
Umm,ummm Ammamatan ki duba lamarin nan ki auna shekaru ba daya bafa yau ace kaine hakan ya
rutsa dakai ko babban kanka ke ya zakaji abin don Allah.
Shi yaro a sannu ake fahintar dashi ya gane bada garaje ba irin hakan ya juyo gareni yana fadin ke nana
rufe min bakin ki a yanzu idan kina son muyi magana a tsanake dake ko kuma in fasa hakan inyi fushi
nima in baki baya in fita a zanceb in barki da Ammamata din kuyi tayi.
Jin abinda Abbu din ya fada yasa na sassauta kukan nawa sannu a hankali yana ganin hakan ya juya ya
fice daga gidan ban jima ba na mike na shige daki na barta a wajen cikin bina da kallo.
Ya dan jima bai shigo ba sai can naji shigowansa yana rufe gida kafin kuma naji muryansa a kofana
yana kwala ma sunana kira da ke nana fito ki karba nan .
Jin hakan yasa na fito daga dakin ya bini da kallo kafin yace ungu jeki randa ki debi ruwa ki daureye
fuska da baki kizo ki zauna kici.
Na koshi na fada a sanyayye wani tsawa ya buga min da yasa na nufi sashen randan ruwab namu da
sauri ina diban ruwan .
Zama yayi saman shimfidan da yayi a tsakat gida kodana dawo gefensa ya nuna min yana fadin zauna
nan a kusa dani .
Ba mussu nakai zaune kamar yadda yace din ya miko min leda da tun kan in bude nasan meye a cikin
ledan don kamshin dake fita a cikin takardan ga kuma nutrients milk mai sanyi har guda biyu.
Bayan na karbane ya fara kwalawa Ammah kira itama ta fito ya mika mata ledan yana fadin karbi bude
muna nan ya mika mata itama zama tayi cikin damuwa tana bude ledan daya miko mata din a lokacin.
Dan juyowa yayi yana sauke min kallo tare da fadin bissimillah mana Nana nakine wanan gani nayi yau
rayukanku sun baci bakuci abinci ba zaku kwana da yunwa daga karshe hakan ya zamo maku matsala.
Maza ki bude ki somaci kikuma saurari abinda zan fada a yanzu ina son kowa ya bani kunnuwansa ya
saurari abinda zan fada a yanzu wurin nan.
Don zancene da zanyi a matsayina na uba kuma maigida a gidansa don haka kai tsaye umurni zanba ko
wani ku a nan ko kuma doka a gidana don haka ina son kowan ku ya ban hankalinsa yanzu ya saurareni.
Ke Nana dake zan fara don haka ina son ki saurara kiji abinda zan fada a yanzu a kanki don a yanzu kece
wace kika saura da wanan zance kuma idan kinyi hakan ba laifi bane don kinyi a wajen kowa.
Ko ita uwarki gata zaune bacin raine da damuwa ya saka tayi maki wanan boren a yanzu amma ba don
taso hakan a gareki ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[8/1, 9:03 PM] Zainab Idris Makawa Writer: ELSUTRA HOME OF FASHION & BEAUTY ACCESSORIES AND
BEYOND
MAMAN BIBO KAYAN MATA
08068871330 KOKO ROAD SOKOTO
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
00️⃣77️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Nana na dauka ilimin ki da wayaun ki tare da tarbiyan ki zai saki natsuwa ki fahinci gabar da muke son
dora rayuwan ki a yanzu ?
Sai gashi kuma na hango ba hakaba a wajen ki don nayi zaton yadda ake zuzuta ilimin da kwazo a yanzu
zaisa ki hango matakin da muke shirin doraki.
Idan kinyi tunane da babu dan dana taba bari yai zurfin ilimi a gidan nan kamar yadda ke muka barki a
yanzu kina samun ilimi shin azaton ki yanzu nayi hakan ne saboda ban haifeki ba ko me ?
Da sauri na dago kai ina kallonsa cikin hawaye ina girgirza kaina a gareshi da nufin ba hakan bane yace
kamar hakane Nana a ganina.
Bari kiji dalili a yanzu na hango ilimin nan shine tsanin takawa a duniya shine matakalan cinma burin
rayuwa ga dan adam yanzu.
Inkai manomine sai da ilimin nan na zamani yake bunkasa haka in kai malamine saida ilimi kake samun
cigaba a rayuwa ke komai yanzu da zakayi hatta kasuwanci yau ya koma idan baka da ilimi hakan bai
bunkasa yadda ya kamata ga bawa.
Hakan yasa nayi amfani da wanan daman na ke kokarin ganin mun inganta rayuwanki don gabarki ki
samu makoma mai kyau a cikin rayuwa.
Alhamdullahi kuma donke din yarinyace mai natsuwa yare da tarbiya yasa muke maki hangen hakan a
kanki a yanzu don ba zanso mu tauyeki ba mu durkusheki nan gaba ba zaki fahinci mun maki rikon
tsakani da Allah ba.
Amma da ilimin nan na zamani zaki fahinci komai a rayuwa a yadda muke fata haka kuma keda kanki
zaki warware ma rayuwanki dana iyayyen ki hukunci in muna da rai da lafiya.
Idona na runtse cikin dacin rai daga inda nake zaune ina maijin yadda zuciyana yake tafarfasa lokaci
guda don ambatosu da yayi a zancensa.
Ya dora da fadin to don hakane nake son in baki dama daman da ban taba ba wani yaro ba a gidan nan
don ki samu ilimi mai inganci da zaki taka kafarki dashi har hakan ya zamo maki bangon dafawa a
rayuwan don akwai rai akwai mutuwa ga bawa in mune yau ba mune gobe ba a duniyan nan.
Amma fa duk wanan dole saina saka daga wanan arzikin da ita mahaifiyarki take turo muna hakan zai
yuyu don ke shedace banda halin wanan hasashen da nake maki a yanzu.
Don haka zancen ace kince ba zakiyi amfani da dukiyar da mahaifiyarki ta turo ba baiko taso a garemu
ba yanzu wajen ki nana.
Don koda rantsuwa nayi a wajen ban kaffara ta turo munane don inganta rayuwanki a gaba don ba
Ammamatan bane kadai ta bari ai nan najeriya suna da yawa meyasa bata turawa sauran yan uwa
kudina idan sun mata yawa ne kike gani.
Don haka banso ki zalunci kanki da kanki nana in ma wani abu kike tunane a yadda nasan Nana Asma,u
sai naga ya girgiza kai ya kare da fadin nana tafi wayau da dabara a duk wajen nan.
Don tasan inda ta fito tasan darajan iyayyenta dana yan uwa ba zata bari wani abin asha ya shigo
rayuwanta ba a can wanan yasa ina cikin wa yanda suka yarda da abindata fada dari bisa dari da wanan
kaddaran rabonki ya gittamata a lokacin.
Nasan ko waye nana a lokacin don a wajen mu ta fara zama kafin a kulla karbanta daga hannun mu
abawa hajiya Naito rikon da ya zamo sanadin komai a yanzu daga baya kuma kowa ya dare ya koma gefe
yana gulman hakan.
Ki godewa Allah Nana kina cikin gatanki da rufin asiri akwai dubunki da hakan ya rutsa dasu nana basu
san kowa nasu ba a duniya sunan nan suna walagigi da tangaririya a cikin duniya.
Ke ko uwarki tayi maki gata bata barki ba sai da ta tabbatar da ta barki a hannun yar uwarta daba zaki
taba kukan tanshita a kusa dake ba.
Don haka in dai har na isa dake ina kuma da kima a idanunki daga yau din nan na kawar da zancen
Nana As,mau a gareki har zuwa dawowanta haka kuma duk abinda ta turo da sunan naki ki dauka kiyi
amfani dashi Aeesha.
Ke kuma Ammamatan daga yau din nan bason a kara tayar da zancen nan don Allah har hakan yaba
wani daman shigowa ya dauki sirin da muke faman dannewa shekara da shekuru a zukatan mu.
Akwai sarka guda biyu da nana ta bari a lokacin suna wajen mu har yanzu mun masu boyon da ba
mahalunki da zaisan dashi a gidan nan bayan mu.
Don haka zan fito dashi a yanzu akai kasuwa a auna a tabbatar da kudinsa albashin in yaso idan
sayarwa zamuyi sai a sayar a fara shirin karatunki da kudin ni nawa shawaran ke nan a yanzu .
Sai naji Ammah ta nisa a hankali tana fadin to amma malam sai naga zancen karatun nan nidai gaskiya
bai kwanta min kawai a sayar ta fito da miji anyi mata aure kawai shiyafi a daina wanan zance ko zata
samu natsuwa itama.
Dan murmushi Abbu ya sauke tare da fadin kaiya ana baki kina roko amma na fahinci kina ganin wanan
shawaran nawa baiyi ba akan yarki ke nan ko ?
Yata kuma yau malam to Allah ya baka hakkuri in abin har yakai can amma ni bada wata manufa ai na
fadi hakan ba don kace inda mai magana yayine yasa na tofa nima.
Kayi hakkuri bana rainawa tsarinka bane a yanzu gaskiya don nasan kafimu tunane ai dagani har ita
kawai dai ina ganin auren kamar shine mafita a yanzu.
Ammah ina son karatu don Allah na fada cikin sanyin murya don jikina ya gama mutuwa a lokacin da
zantukan Abbu din dayakeyi akaina don a kainane zance ita Ammah nata mai saukine ai.
Nice dai bawan Allah keson ingatawa rayuwana a wanan zaman kuma iya abinda ya rage ke nan suyi
min a yanzu din har incinwa burukana na duniya a yanzu.
Yadda yace hakan ya faru don washegari da safe yai kirana da kansa ya mika min tulin kayan da nake
gani kamar wani shara a lokacin a hannuna ya kuma kara min nasiha akan rayuwa.
Don gaskiya Abbu ya fada ba wanda ya isa ya kaucewa kaddaransa sai in Allah yaso hakan ga bawa
haka kuma ko wace kaddara tana da wata manufa ga bawa Allah kadai ya barwa kansa sanin dalilin
hakan.
Yadda nakai kayan daki na watsa ban dago na sake waiyayansu ba duk da zuciyata tayi laushi a lokacin
amma nake ganin kayan wani mugun abu a gabana.
Don haka zan iya cewa ban bude ko leda daya na duba inga yaya kayan suke bama balle insan kallarsu
kayane kuma masu yawa da zasukai kala goma ko fiye da hakan ajiye.
Saidai kamshinsu daya ciki min dakin don kamshi sukeyi irin na turaren yan nahiyar can ta larabawa
hakan ya fara sa kaina yana dan sarawa a lokacin.
A hankali har na kai kwance ban fadawa kowa banjin dadin jikina ba a gidan sai Abbune da zai fita yake
kwala min kiran da nazo nagani .
Wanan yasa na taso a dunkule cikin hijjab din islamiyata ina dan kaduwa na nufoshi a hankali ya fara
walwale min sarkankokin a gabana inda nake tsugune yana fadin.
Kinga wanan biyun tun barin nana kasan nan data tafi ta barmu dake suke boye a hannuna wanan
kuma sune ta aiko daga bayan nan.
Saidai gun Alh sani zani dasu don akwai shagon sarkoki a kusa da shagonsa su auna su fada muna nauyi
su in yaso sai mu in dawo asan abinyi dasu din kamar yadda na fada a jiya.
Kai kawai na dukar tunda nayiwa sarkokin kallo guda ban sake dago kai na kallesu ba kuma saida na
amsa masa dakai kawai hakan yasa ya dago don ya kalleni anan ya fahinci yanayin da nake ciki lokacin.
Da sauri yake furta subbahanallahi meke damun ki haka nanata nan hankalin Ammah dake kokarin
kauda kayansu gefe daya ya dawo gareni.
Tasowa tayi tana tamba jikina ta juya wurin Abbu tana fadin jikin gaba daya ya gashe kamar garwashin
wuta kina ciwo Aeesh ba zaki fada kika kokarin halaka kanki haka ba gaira ba dalili saboda mugun
abunda kikasawa zuciyar ki.
Hannu Abbu ya daga mata ya mike da sauri yana fadin tashi muje chemist haka na daure naje chemist
din tare dashi akai min allurori masu karfi na maleria tare da magani muka dawo gida lokacin idona ya
gaba rufewa sai barci ya daukeni.
Duk suna zaune sun tsureni da idanuwansu ganin na samu barci mai nauyi yasa Abbu fitowa daga dakin
yanawa Ammah hannu da alaman ta biyushi.
Batayi sanya ba ta mike ta biyoshi din zuwa wajen cikin tausa murya ya soma magana da fadin
Ammamatan meyasa baki amfani da hankalinki ?
Wani kallo ta watso masa yace kwarai ko so kike yarinyar nan ta bijere muna a yadda muka santa a
baya ?
Yanzun ne tafi bukatanki yanzunne kema zaki nuna mata kauna da kulawan ki a gareta don ga baki
daya a yanzu bakin mu take gani a wanan gabar.
Dole sai kin kara janta a ciki sosai fiyema da da can baya ki nuna mata itama yace kamar kowa tunda
tana damu a duniya koba nana a kusa balle mahaifinta damuma ba mu sanshi ba.
Wanan abin naki zai kara saka yarinyar a wani mugun yanayi da ba zamuso ba ki kwatanta a gareki yau
ke haka ya sama a duniya ya zakiji zuciyar ki a lokacin da kika sanda haka ?.
Nan dai ya lurar da ita halin da nake ciki kuma ta gane gaskiya Abbu ke fada hakan yada dana falko
naga sauyi sosai a gun Ammah din duk da bada wani manufa take min hakan duk cikin tsawatawan su na
manya ne a lokacin.
A hankali na yaye hijjab din dana rufu dashi har kai ina kai dubana ga Ammah din dake zaune a gefena
tana yankan kubewa.
Sannu tayi min tana fadin sannu Aeesha kin falka ya jikin naki na dan juya dara daran idanuwana kafin
in koma lumshesu ina fadin da sauki Ammah.
Kokarin mikewa nakeyi zaune naga ta tashi da sauri tana kamani tare da fadin ina zaki da kyat na bude
baki ina fadin bayi a takaice.
Zaki iya ko in kamaki ta fada cikin kulawa nace cikin karfin hali zan iya Ammah na mike na fita kodana
fito na samu ta fito daga dakin ta dauki tsintsiya a hannunta.
Alwala na duka na dauro don duban yanayi da nayi ya nuna min an dade da sallah axahar a lokacin
hakan yasa cikin karfin hali na daura alwala.
Nazo nayi sallolina don tun ina alwala aka kira sallah la,asar duk da yau sauri saurine amma dai nasan
lokaci tane yayi don basu muke bi sallah ba a gidan sai hudu daidai muke la,asar.
Na dade a zaune ina mika kukana ga sarki Allah wanda yafi kowa sanin dumbin damuwan tattare dani a
zuciya wanda ba kowa zai fahinci hakan ba sai wanda kaddaransa yazo daya da nawa din.
Don ace baka da uba kasan hakan da girmaka ba karamin tashin hankali bane a wajen mutum saidai
Allah ya kyauta kawai.
A inda nayi sallah nakai kwance a hankali ina bin dan dakin nawa da ba komai na rayuwa a cikinsa sai
dan tsohon katifana da akaiwa cikon ragga gefe daya kuma dan tarkacen ghana most go din kayanane a
ciki wanda idan ya lalace nakan fadawa Abbu ya sayo min wani in canza a lokacin.
Naso in koma barcin saboda jikin