Chapter 45 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   45 / 109

132K to 135K   out of 326.5K words

wanab kafirci dai baiyi ba wallahi jam
ita har yanzu tana kafircin ne ta juyo tana son amsa a gareni.

Kafin ta koma fadin ganin ina hawaye take fadin keko tsiyana dake saurin hawaye kamar bakin famfo
wallahi daga yar magana kin zauna kinawa mutane hawaye haka kuma ?

Dole tai hawaye ai don baki iya magana ba wani lokaci idan idon ki ya rufe Ammamatan Abbu ninasan
irin rayuwan kuncin da nayi a wanan gidan wallahi amma yanzu Ammah laifina ta gani.

Tiryan tirya tundaga farko na kwashe komai na fada masu tace nashiga ukkun dasun tona min asiri
garin nan zam zam Allah yaiwa matan na albarka kuwa.

Shiyasa ake son halin alheri ga mutum da Allah baiga zuciyar ki ya turo muna matan nan ciki rayuwanki
ba Allah kadai yasan irin halin da zaki shiga a garin mutane lokacin.

Yanzu shi ha,bibu dama gidansa haka yake amma inyazo nan ka ganshi fes fes dashi ashe dan banzane
bai iyawa gidansa bama balle wani ?

Shiyasa ban fadawa Abbu gaskiya ba wallahi tun lokacin don nasan ransa zai baci sosai ya daga zancen
kowa yaji cikin bacin rai .

Azo daga baya a juya maganan ana fadin kafiri yai min fyade saboda nasan halin mutane da tsegumi da
sheri yanzune zasu juya ko ita wanan matar da nake hannunta wallahi ban fada mata ainihin zancen ba
har yau din nan.

Nanata Allah yai maki albarka haka zancen yake tabbas yanzune a take zancen nan zai juya ya koma na
sheri bayan kece akaso a zalunta .

Dadin ilimin ke nan wallahi tunda Allah ya kare muna ke suyi can ajiyarsu ta kare akansu dole tayi
kazanta ga kafirci Ammah ta fada daidai lokacin Abbu yace.

Ke kuma wallahi kada koda wasa dadin zance ya kwasheki ki fadawa wani zancen nan ko a gidan nan
har in najisa wallahi ranki zai baci dani.

Shidai habibu har abada nasan ba zai fada ba tunda ta iya rufa mai asiri haka abu dayane muyi mashi
addua Allah ya kwatoshi daga kafiran matan nan yanzu.
Mikewa nayi ina daukan wayan da Asmau ta kawo min don naga bakin number ke kirana a lokacin na
dauka da sallamana a bakina aka amsa min.

Saidai ban sheda muryan maishi ba gaskiya yasa nace waye naji anyi murmushi kafin yace bakonkine na
dazun cikin jirgi.

Hakan yasa nima na dan murmusa nace umm,humm tauu an isa lafiya ya mai jiki kuma da sauki ko ?

Abba jiki da sauki sosai yanzu hakama yana waje yana shan iska masha Allah na fada na kai zaune a
kofan tsore din mu inda Asmau ke saka kayan tsaraban cikin store din.

Naji yace dama na kira naji yaya kika isa gida nace lafiya kalau nagode gaskiya na fahinci wanan kalman
godiyan ya zauna a bakinki sosai hakan yasa naga kina burgeni wallahi.

Haka dai ya dinga jana da hira duk da ban bashi amsa daida daga eeh sai umm,umm nake fadi har
mukayi sallama dashi na kashe wayan.

Ajiyan zuciya na sauke lokaci guda ina lumshw idona a rayuwata banson guri ko wani abu makamancin
hakan ya shafeni zancen Ammah ya tsaya min a raina lokacin.

Tambayan kaina nakeyi wajen meyasa sai dai Ammah amma ba Abbu ba da ya kamata ace shiyake min
hakan da Ammah kemin kamar ba jininta nake ba ?

Ba komai bane na fada a raina illa fushin abinda Nana uwata data haifeni ta aikata mata na sulale jiki ta
gudu ta barta dani tana hadiyan bakin cikin daya kamata ace itace take hadiyan abinta tunda itace tayi
abinda ta samoni a can ?

Banda wanan banga dalilin da wani lokaci zai sa Ammah tana fadan maganganun da bai datace ba daga
bakinta game dani ?

Idan ranta ya baci dani wani lokacin a bakinta ni din abin kyamace a cikinsu watau tunda banda asali
sun rufa min asiri yanzu na koma har zan fara kyamar masu asali irin su yaya Habbib.

Shike nan don ina shegiya sai in tsaya a lalata min rayuwa don rashin gata kome ai,,,,,,, mummy wai ina
matazun dinkine ?

Muryan Asmau dake tsaye a kaina take tambayana hakan dan murmushi mai hawaye makale a fuskana
na sauke mata ina fadin .

Matazun yana nan lafiya muna waya dashi na fada cikin karfin hali halan meya faru mummy ta fada
tana kaiwa zaune gefena cikin nuna damuwa ga yadda ta ganni ?

Babu komai Asmau da komai mummy wai jikin baban kano kike damuwa ai baba yaji sauki sosai wallahi
da farko inkin ganshi ne zakice ko zai mutune ai ba yanzu ba daya samu lafiya.

Dauko min jakata mu fita insayo fruit nan waje na fada hakan yasa ta shiga ni kuma na mike ta fito min
da jakkar nawa muka fita take fada min ta samu Addah ta tashi zatayi sallah.
Itama Hafsat ta tashi a lokacin ta barta zata kewa tace muka fita zuwa wajen masu fruit din unguwar
mu Asmau tace mummy don Allah meya sameki ?

Babu komai Asmau zancen Ammah daine ke tsaya min a rai Asmau yau ko wani ya nuna yana kyamata
ya dace Ammah ta furta min hakan a bakinta don Allah ?

Tunda baki da wani abin kyama ajikinki inma na rashin gane iyayyenkine wallahi tunda baban kano ya
nace akan kina da uba ke din ba shegiya bace nasan wallahi kina da uba saidai nisa a tsakanin ku dashi.

Ajiyan zuciya na sauke na soma fadin yau ko rashin ji nakeyi sata ko bin maza ko tsage,ranci baici ace
Ammah ta furta min hakan ba ai na kwashe komai na fada mata ?

Tace kai itako Ammah wallahi nakan rasa meke damunta wani lokaci take hakan kan dangin mijin nan
nata kowa tanawa haka wallahi haka da bakya nan sukayi da samira ga baban kano a kwance yana jinya.

Ban nemi inji me sukayi ba nace akan irin furcin nan nakan ji wani lokaci kamar in nisanta da kowa in
koma rayuwa inda kowa bai sanno ba .

Amma saboda Abbu ban iya yin hakan yanzu wallahi don Abbu ya gama min komai a duniya yai min
gatan da ko mai uba bai samu ba don bai bar rayuwata ta wullakance ba.

Har mukaje muka dawo muna magana na debe manyan nace ta gyarawa Abbu da baki shi sauran kuma
ta bayar asha a gida na shiga wurin su Addah don nima inyi sallah.




ZAINAB IDRIS MAKAWA[9/16, 9:22 PM] Zainab Idris Makawa Writer: ELSUTRA HOME OF FASHION &
BEAUTY ACCESSORIES AND BEYOND

MAMAN BIBO KAYAN MATA

08068871330 KOKO ROAD SOKOTO




JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
5️⃣1️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Sosai su Addah sukaji dadin yadda ake taronsu cikin mutunci da girmamawa a gidan mu haka kuma har
yan uwa na kusa suna zuwa yi masu sannu da zuwa suna masu godiya.

Ni kaina naji dadin halarcin yan uwa da abokan arzikin mu yadda suka daga darajana a idon bakin
namu yayin da ni kuma ina manne da Abbuna ina matsa masa shan magani da cin abinci wanda na kula
da baison hakan.

Ji nake kamar kada in koma Abuja ace nagama ke nan na dawo gida gaba daya lokacin in zauna in kula
da mahaifina.

Saidai kash zuwa jibi da safe dole zan barshi in koma inda muka fito koda dare yayi mun kai wani lokaci
wurin Abbu nida Addah muna masa hira.

Har anty safiya da suka gama kallon wani film ta samemu tana fadin dama saidana fada baki nan
Aeesha .

Nace da kina garin nan abin nan ya samu baba kece zakiyi jinyarsa da kanki a gidan nan gashi kuwa kin
nuna hakan.

Anty ji nake kamar kar in koma wallahi don kona koma hankalina ba zai kwanta ba can saboda zullumi
kafin in rufe baki naji Abbu yace.

Ko kusa kina nan ko can Allah ne maiyin abinda yayi niya ga bawansa ki koma ki karasa karatunki ki
dawo tunda ba dadewa zakiyi a can ba.
Rankai dade yazo ya dauki likitan da zai dinga zuwa kwana bibiyu yana duba min jiki ko dazun kafin ku
iso yazo ya dubani da safe.

Balle idan har aka kai wanan matakin ga karaya ana sa ran samun sauki ga mutum insha Allahu don ma
yana jikin girma ne dai .

Bamu jima ba mukaje muka kwanta saman gado Addah ta bar muna ta kwanta a kasa saman wani
babban zanin gado nida hafsat data jima da barci muka kwanta saman gadon.

Duk da barcin da nakeji hakan bai hana tunanen duniya shigowa rayuna ba a lokacin tunanen halinda
Abbuna ke ciki na soma ya matukan ban tausayi a lokacin.

Kana kuma na koma na bayin Allah nan da suka rakoni ganinsa kafin mam ya fado min a zuciya don ba
karamin fitar damu kunya yayi ba wanan alherin daya turo mu dashi din .

Haka kwarkwasan nan Asmau itama da nata hikima ba hayani don banjin cewa su Addah sun san da
zancen tsaraban da naji tayi magana .

Bawan Allah nan yana ta dawainiya damu haka nida iyayyena alhalin yasan iyayyensa ba zasu taba
yarda koda gigi ya aureni ba dai ?

Haka kuma ni dai a nawa dan fahintar dai wani lokacin macen da kasan kana so zaka aurane kakewa
wanan dawainiya haka idan kana da zarahin yi.

To amma shi man meye nasa dalili wai abin nan fa yayi yawa yayi yawa sosai wallahi tsakanin mu kuma
kome nayi don ya barni yanzu kada ya samu matsala da iyayyensa kamar baisan inayi bane.

Yanzu ki duba yadda muka rabu bayan lokacin da muka dauka bamu hadu ba amma naki yarda wani
sanyin rai ya auku a tsakanin mu ta yadda zaiyi fushin zuciya ya barni .

Sai gashi kamar ma baisan nayi hakan ba har mu ukku ya turo zuwa kano ganin Abbu bayan alherin da
yai masu a nan yakuma hadomu da tsaraba sak zakice mu mukazo dashi daga Abuja lokacin.

Don kawai nasan mu dadada wa bakin mu rai yayi hakan kwai soya breakfast ga kayan shayi da sauran
tarkace ido na lumshe ina jin tausayin kaina wajen.

Duk da mutum ne shi mai daraja na tare dashi amma wanan abin ai yayi yawa na fada a zuciyana kafin
kuma shima naji tausayinsa na hagon rashin kyautatawa a gareshi a jiyan .

Allah sarki bawan Allah banda abina meye nasa a ciki tunda ya nuna mamakinshi a fuska abinda Salman
yayi din baisan da hakan bama sam.

Ga MD da yanzu nagane suna tare ashe har dashi akazo gidan mama ganina amma na rufe ido na nuna
ni bansansu ba a gaban kowa.
Na MD ai mai saukine idan na tafi yaushe zai kara ganina kuma inba wani ikon Allah ba can kuma amma
shi wanan da yake daukaka rayuwata haka yaya zamu kwashe dashine wai tunda baima san inayi ba ai
nake gani tunda gashi yauma ya sake min alherin fita kunya na bazata haka nasan kuma don bakinane.

Duk da nasan alheri garesu gadone duk dan babban gida irin wanan ai da alheri aka sansu ga
tallakawansu amma ba irin wanan alherin ba nasa abin yayi yawa gaskiya.

Na nisa ina tuna yadda gidan mu ya dan sauya duk kuma ta dalilinshi hakan ya faru a gidan namu nakai
wani lokaci kwance ina nemawa kaina mafita karshe na yanke shawaran abinda nake gani mafita yanzu
gareni dashi,

Washegari tunda nayi sallah asuba na fito muna hada abin karyawa nida Asmau samira kuma tana
gyaran gida daga nisa daidai Addah na fitowa samira ke fadin mummy mootar nan sai an wanketa kafin
ki shiga ko ?

Samira ba inda zan tafi balle in tsaya wani wanke mota yanzu saidai Allah ya dawo dani lafiya kaita
wajen service daga can a wanke.

Suna ganinta suke gaisawa da Adda din da kwana bata hade mamakinta ba take fadin ina motar Aisha
din garejen daya bullo a dan filin cikin gidanmu dake rufe daga waje ta nuna mata .

Na zata ta fita zancen ai sai gashi bayan sun karya taja Hafsat zuwa wajen motan sun jima suna duba
na fito daga wanka suka shigo Addah din ke fadin amma yar nan .

Motarki haka mai kyau kika barta nan nifa da Yazid ke fadin kina da mota ai ban dauka gaskiya bane
nazata shirmensa yakeyi.

Don me zaki dauka shirmene duk abinda kikaji ya fada kan Aisha gaskiyane ai tunda shine abokin
shawaranta.

Kafin wanin mu yayi magana muryan Aimance daga falo take fadin nasan zata iya wucewa bata zo
gidan mu ba ai yasa na taso yanzu tunda nasan gobe monday.

Wani dan gulman ya fada maki nazane wai na fada ina karasa saka riga a jikina suna da yawa ta fada
takarasa shigo dakin sai kuma tayi turus ganina da baki dakin don ta dauka ni kadaice.

Duk da hakan saida tace min jar uba Aeesha kice min gidan kudin ma kika fito gaba daya kinga yadda
kika koma kuwa !

Kema zaki dora naki na fada ina murmushi nace su farida sun gama ke kuma yanzu kinzo ki dora inda
suka tsaya.

Allah ba wasa bane ta fada tana zama tare da fadin ashe da baki kike tafe sannu ku da zuwa tana
gaidasu suka amsa nace Amarya Amarya tayi dariya.

Au aure zatayine Addah ta tambaya nace aure zatayi Addah murja har Canada zamu kai ta hafsat ta
dan juyo ta kalleta ta kawar da kai.
Kinga idan kin iya sana,ar hannu acan kin huta nayi zama a can da mijina na farko a min aure can aka
kaini daga bauchi haba nan Aimana ta lake mata tana jin labarin turai a bakin Adda din.

Hafsat uwar yauki sai wani abu takeyi da baki na ta gaji da zancemsu dariya sosai ya kumeni a lokacin
ganin hakan yasa na dauko mata tsohon laptop dina cikin wardrop tana kallo dashi ta basu baya nima
fita nayi daga dakin.

Muka gyarawa Abbu kayan marmari mai yawa muka kai mashi suna zaune da Ammah na aje a
tsakiyansu Ammah race main wanan ai barnane Aisha gobe idan kin wuce was zai says mashi kuma ?

Ai ya dinga sha ke nan insha Allahu Ammah anjima ma wani za a sayo Asmau data dinga gyara mashi
kafin in dawo gara dai da kikace Asmau,n dan dama dama don tana iya bakin kokarinta gaskiya koda
bakya nan din.

Asama,u dake shigowa tace yanzu Ammah nice dama dama ai zaki gane kince Abbu ya tare da fadin
halintane kuma baki sani ba ?

Ai ita bata da gwani a wajenta kowa mai laifine amana dai ke akabawa shi yanzu ai tace shike nan
baban kano na koma dakin mu na zauna.

Har lokacin suna ta hiransu kamar sun san juna na zauna ina saurarensu Addah na fadin aina fada maki
duk turai ba Kasan da ake kwamacala kamar Canada gasu Canadian's din suma yan iska dasu can ke dai
bari.

Ko a jikinta yadda na kula ga wani girman kai da jiji da kai data dorawa kanta wai ita tayi sa,an mini ta
dara sa,ointa ina jin yadda take shara karya wasu Addah din ita a dole ta burgesu tunda taga yan birni.

Karshe juyawa nayi wajen hafsat muna kallon film din Asmauce tazo ta kirani nafita dakin abinci muka
raba na kaiwa Abbu na zauna na zuba mashi yana fading yayi yawa nace nama ne a saman ai.

Baya son cin abinci na fahinci hakan yasa na zauna da kaina na gyara abincin na mika mai na cire
kanshin naman na aje a gefenshi yana hadawa dashi sai goran ruwa mara sanyi dage gefe daya.

Yaci sosai sauran days rage na dauka ina ci samira data shigo take min sheri wai ragowan tsoho nake ci
na daiyi murmushi sai kokarin kwatar masa da hankali nakeyi tare da bashi shawaran yasha magani yaci
nama da yayan icce yace zai dinga ci insha Allahu.

Sun fita dasu farida da samira sun raka su Addah kasuwa har da Aimana suka barni da Asmau gida a
lokacin lokacin na samu kara tataunawa da iyayyena basu dawo gida ba sai wajajen tara na dare suka
shigo.

Washe gari ban dauki komao ba sai yar handbag dina kawai Dana koma dashi a nan nabar komai dana
zo dashi gida don in rage nauyin kaya idan zan dawo.

Dakyat na iya barin Abbu na fita dakin ina hawaye sai fada Ammah keyi dani tana fadin said kace ba
nan da sati biyu kikace zaki dawo ba zaki dinga yiwa mutane hawaye kamar baki dawowa ki sameshi ?
Barta tayi abinta mama kinsan fa yadda duke da shakuwa a tsakanin su balle ta ganshi cikin wanan
halin haka dole tayi kuka ai Anty Safiya ke fadin hakan.

Auwal na kofan gida shiyazo daukan mu zuwa airport din mukai sallama muka tafi bayan na kara rokan
Asmau akan Abbu don't Allah ta kula da bashi abinci da magani akai akai.

Saida muka dan fara tafiya Hafsat ta nisa tace ina son irin wanan gidan ga kowa naka ko yaushe cikin
hayaniya ake Auwal ya tare da fadin sums dai yanzu ne ai dawowan yan sokoto din nan garin nan da
zama.

Duo hiran da akeyi a motar kafin mukai airport ban saka baki ba saida muka sauna nayiwa Auwal din
magana ina masa godiya yace haba dai mukai sallama muka shiga.

12 daidai ina office din mu don't daga airport office yazid ya saukeni dayaje taro mu su kuma su Addah
ya wuce dasu gida kai tsaye.

Zaune yake yana tara wasu bayanai a takarda dake gabanshi yana hadawa cikin computer dinsa sakon
Auwal ya shigo mai yana sanar mashi da tashin mu din.

Ok kawai ya bashi amsa yaci gaba da abinda yakeyi na dan lokaci ya ture laptop din yana furzo iska a
bakinsa ya fesar ya mai da kai baya ya lumshe idanuwansa.

Abinda ya faru falon mummy Rahima ya tuno ya dan murmusa watau su mata komai kankantansu sai
sunyi wanan jan ajin tsiyar ji yadda KB da girmansa ya tsaya bawa yarinyar nan hankura tana wani
yanga .

Duk da baiga laifinta ba nan don Allah kadai yasan me salman

45 / 109