Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
baki san dawowan mahaufinku
bako hindatu ?
Mahaifin mu ?
Wake nan mummy ta juyo tana tambaya a mamaken tace yaya sayadi mana daya haifeku shine ya dawo
gari akace .
Na zatafa yana gidan nan sai gashi na kira yaya wai itama bata ,,,, zancen ya makale a daidai lokacin da
tayi arba da yar uwar nata dake zaune kasa a cikin wani yanayi na tashin hankali.
Yau me zan gani hakane kuma yaya ta karasa wajen yar uwar tana tabata ta juya ga yar tana fadin
kawo ruwa hindu da sauri don Allah ?
Ta juya aguje takawo ruwan suka yayyafa mata sai wani ajiyan zuciya ta rike hannun yar uwar tana
fadin Nasare wai da gaske kikeyi ko ba,a kice min ba,a kike min don Allah ?
Haba yaya keda zaki fi kowa farin ciki hakan kuma kike furta wanan magana haka don Allah bari mana
?
Allah yasa dagani sai yarkice kika fadi hakan ai sai a zargeki su dauka gaskiyane yanzu ina yake Nasare
tana tambayan yar uwar nata a gigice.
Haba yaya ki natsu mana ansan dole ki rude haka mutumin da har kayiwa wanka ka kaci arzikin abinda
ya bari yau kuma ace maka gashi ya dawo dole ka rude ai haka?
Bake ba ninan wallahi duk a rude nake na rasa daga ina zan kama wallahi balleke yaya amma don Allah
ki dan natsu duk da ansan dole saikinyi hakan.
Ina ya tsaya da baizo gidansa ba don ita hjy data kirani bata tsaya min bayani ba don ta daukama na
sanine sai daga baya tagane ban sani ba.
Tace tun jiya cikin dare ya sauka har taronsa akajeyi da daren nan don da yawa sunsani sunsan da
zancen dawowansa zuwa yamma aka sanar da hakan.
Amma shine mu ba wanda ya sanar damu komai akan zancen dawowan nasa me ake nufi da hakane ko
gidama basu sanda dawowan nasa bane wai ?
Anya ko Nasare sayadine ya dawo mu dai bincika da kyau zaifi don dukan kofan da akeyine ya dakatar
dasu daga zancen suka mike dukkansu.
Sarkin motane kofan gida tsaye yake sallama suka gaisa da hjy Nasare dake da dan karfin hali kafin ya
sanar mata da yazo daukantane gida na can ya fara cika ba a gansu ba hjy tace un maza inzo in daukoku
kafin a kara yawa.
Ya tabbata shike nan ya gama tabbata shi dinne Nasare tabbas shine ya dawo suka juyo zuwa cikin
gidan don ta dan kimtsa jikinta.
A gurguje ta kimtsa din suka fita zuwa gidan shi suka bi ita nasare tace zata bi motar ta ta samesu a can
gida.
Ta baya yabi dasu don haka bata samu ganin dandazon mutanen dake mskwabtan gidanta ba a lokacin
ko a gidansu din ma kofan baya ya biyo dasu har suka samu shiga cikin gidan nasu kai tsaye.
Sunyi sa,a ba wasu mutane sosai part din hakan ya basu daman shiga ciki kai tsaye zuwa fallon mai
babban dakin gaskiya taci sunanta din mai babban daki kuwa.
Don ko part din yafi ko wani part a gidan girma sosai sunkai kurya suka sameta a kishingide sai mai
aikinta dake bata maganinta a lokacin.
Babu gaisuwa sai fadin hjy zance haka gatsau yazo muna wai yaya sayadi ya dawo hjy Nasare dake
kaiwa zaune take fadin hakan ?
Bari nima haka na tsunci labarin daga sama wai ashe duk dadewan nan sayadi yana raye a cikin
duniya ?
Ya dawo harda iyalinsa dazun da safe mahaifinku ke sanar muna zancen dawowan nasa amma har
yanzu koshi banjin ya samu ganinsa .
Yazo da mace akace harda diya dukka maza hudu nasa saidai har yanzu ba wanda yakai ga ganinsa ido
da ido andai zo an sanarwa fada dawowan nasa.
Diya hudu maza hjy diya hudu fa aka ganshi dasu sabuwar matar nasa daya aura a can ta haifa masa su
nima tun dazun ina nan cikin tashin hankalin wanan abin
Abin ya daure min kai ace sayadi yana raye tsawon wanan lokacin bai taba tuna da yadawo gida wajen
iyalinsa ba sai yanzu ?
Wanan abin akwai daure kai sosai wallahi ko kurciya akai masane dama hjy amma ai yaya tazo da
evidence cewa bama shi daya ya mutu ba a lokacin.
Hakane mana nida aka kawowa kayansu sun kone kurmus daga shi har driversa nayi signing akan
karban gawansa a can ivory cost din da abin ya faru.
Ido suka kafa mata da take wanan maganan babu kyatawa ga kallonta saida ta gama mai babba daki
tace koma meye dai alama ya nuna shi Allah yai masa gyadan dogo ya tsallake rijiya da baya ke nan ?
A zuciyan kura tace ba kadan ba yako tsalake da baya din don ba karamin shiri akaiwa hakan ba amma
yau ace wai ya dawo ya dawo daga ina ke nan daga lahira ko balaguro ?
Babu abinda gabanta keyi sai harbawa fafafafafa a lokacin kadan kadan tayi ajiyan zuciya ta dan motsa
daga yadda take zaune da suna da kula yanayinta kadai zai nuna bata da gaskiya a lokacin.
Amma su daukan hakan sukeyi da zallan rudewane da tashin hankali tare da tunanen makoma akan
salwantan da dukiyansa da sukayi gami da cin mutuncin da akaiwa yan uwansa musanman ita.
Imamu ne ya shigo hankali tashe kamar magana ya kawoshi a lokacin ganin dakin a ciki sai kuma ya
fasa yai kamar zai juya yaja ya tsaya yana gaisawa da mahaifiyarsu.
Yanzu ina shi Sayadi din bayan sun gaisa ya tambaya shine akayowa rakiya zuwa wajen baba tare da
iyalinsa yaba mahaifiyar nasa amsa ya juya sai kuma ya juyo yana fadin Nasare zo ?
Ta mike da sauri ta bisu da kallo don akwai wani zancen siri da yake son yi da nasare din a lokacin wai
sayadintane aka rako suwa suka rakosa ke nan take tambayan kanta a lokacin ?
Sayadi din ne yau har da samun yan rakiya kamar wani sarki ko gwauna da za ace an rako illa dai ya
shigo din da iyalinsa nasa ai ciki su ganesu ?
Ai ita tasan sayadi din ciki da bai don haka koma waye keson masu yawo da hankali akan shine ya
dawo zata gane ai .
Kodai da yaron nan magaji sukazone dai naga gashi can mota daya suka shigo dashi shine ma ke
jagoranta kai akwai tausayi abin bakiga yadda ya fashe da kuka gaban maimartaba ba daga shi har matar
nasa da sukazo tare da yara masu kyau wallahi.
Wai matar nasa ashe yar kasan nace itama yadda naji su zagi na fadi dazun da suka iso ashe mai
martaba ya dade da sanin sayadi yana raye.
Kai karima tun kina fada muna saurarenki har zaki surka da karya ba dai kunce kunga sayadi ba din da
idon ku hakan ya isa don Allah kuje mujira shigowansu.
Ai yaya Imamu yace a gyara waje ga iyalin nasa nan shigowa don maza sunyi yawa a can waje din zata
shigo nan ta zauna wajen hjy.
Nasare ta katse masu kawo gulman da fadan hakan data shigo saiga masu gyara sunzo don kara gyara
falon don tasan a nan dai zasu zauna din ba har sun shiga can ciki ba.
Muryan uwar taji tana fadi a kasaice hakan ba zasu iya zama bane sai an kara gyaranshi kome idan
hakan da muke zaune a ciki bai masu ba ku kaisu inda ya dace fiye da nan din .
Hjy bakine fa bakonka Annabinka kuma sarakuwa zuwanta na farko ke nan gidan nan aiko dan darajan
yaya kura muja mata girma da kima mu kara gyara wajen ta sameshi a mutunce.
Wani tabe baki tayi tana kawar da kanta gefe daya don abinda yar ta fada kuma gaskiyane duk da taso
ta sake layi gaban kowa a lokacin.
Ta nuna kishin tana bayar yarta ta manta da itama sarakuwace ga matar dan rikon nasu da uwarshi ta
kwanta dama ta hada shida imamu da Ahmad dinta a lokacin ta tayar don kansu daya lokacin.
Hakan yasa ya taso a wajenta tun bayan rasuwan mafiyarshi da take itace kanwa ga maimartaba wace
Allah yaiwa rasuwa tabar yara biyu a raye kanana don basu kai munzali ba a lokacin.
Karshe kuma shi maimartaba ya wanke kura ya hada dashi aure wanda akai zaman dai ba dadi a
tsakaninsu kacal aka haifi yara biyu sune Munir da hindu.
Kuma tundaga kansu bata kara haihuwa ba har yanzu da girma ya fara kamata ba zancen haihuwa a
gabanta.
Kinga inga kara itama bakuwar matar sayadi din tazamo sarakuwa a gareta ke nan kuma kishiyar yarta
kura .
Dole uwar naki tana kallo aka gyara ko ina a gagauce da karshe yasa ta mike zuwa ciki ta barsu ita da
yarta kura suka shige don su zanta tunda Nasare ta shagala da zuwan wanan bakuwar bazata din da ake
faman rawan kafan zuwansu.
Shiru na dan lokaci ya biyo baya kafin ta kalli yar tace ki natsu ki kwantar da hankalinki don tun dazun
naga kina abu kamar mara gaskiya ?
Girma da kimarki a yau yafi nako wace irin mace sayadi zai shigo muna da ita gidan nan don ko dame
tazo anfita a nan kudi mulki ko ilimi balle sarauta nasan ba zata kama kimarki a idanun kowa ba.
Amma fa sai kin natsu kin daina wanan shirmem kidimewan da kikeyi a yanzu din don hakan zaisa
girman ki zubewa a gaban kowa.
Hjy mamakine ya kasheni yaya za ayi sayadi ya dawo duniya bayan ina da yakinin cewa ya mutu tuni
baya raye ?
Allah mana kura, ko kin manta da ikon Allah ne shi yafi komai zai fada ai komai dadewa zai kumayi
bayanin komai idan ya huta dolene wanan bayanin.
Ajiyan zuciya ta sauke mai karfi kafin ta gyara zama ta hanyar jingina kanta da makarin kujeran data
zauna a kai ta dan lumshe idanuwanta.
Tabbas dolene ma ya zargeta dolene ya zargi wani abu a ranan wajenta yadda ta dinga yi kafin ya
bargida abune da bai taba faruwa ba tsakaninsu.
Wai a wautanta tana bankwana dashi cikin kisa tare da fatan bukantata ya biya a lokacin da take ganin
ya tare mata gaba da baya cikin al,amuranta na yau da kullum.
Ashe bata sani ba zamansu dashi shine gatansu fitansa ya nemo ya kawo shine rufin asirinsu
samuwansa shine dagawan darajansu ita da yaransu duk wanan sai a bayasan tasan hakan.
Ina ,ma ina,ma ace hannu agogo ya dawo baya rayuwa ta koma na farko data mutuntashi data
darajashi data daukakashi duk ita daya ke wanan tunanen a wajen.
Har mahaifiyar nasu na magana da ita bataji ba saida takai ga kiran sunanta da dan karfi yasa ta dan
zabura tana fadin na,am hjy ?
Wani tunane kikeyi hakane kura kada ki saka damuwa akan sayadi ya dawo da wata mace a garin nan
bayan ke ?
Kada hakan ki bari har wani ya gano ki a samu daman ganin galabanki a wajen mutane zuwa da matar
nan idanuwan mutane zai dawo kanki ko don aga yaya zaki kasance ?
Hjy ba zuwa da matar bane damuwana yadda akace tun jiya yake garin nan da dare amma bai
nememu ba shine kawai damuwana a yanzu.
Dolesa ya nemoku ai dole ya nemi inda kike da yaranshi karki dauka don macen da yazo da itane yasa
hakan ?
Haba dai ni mace tana daga min hankali ban daga mata nata ba kawai dai abubuwa nake dan tunane
hjy.
Jin hakan da yarta tace yasa ta dan sake murmushin yake a fuskanta don tasan yar nata zata aika yadda
ta fada ko wacece ake ganin sayadi yazo da ita garin nan zata hadu da yar nata ai idan yana ganin yayo
wani aurene a can ?
Shigowan hjy Nasare inda suke yasa suka maida kallonsu a kanta saida ta zauna tace wai wai gata nan
ta shigo da yaranta suna falo a zaune.
Gaban hjy kura din ne ya bada rass a lokaci guda ta kallo yar uwar nata tana fadin don sun shigo su
zauna mana waya gaiyacesu nan inba gulma ba.
Ke in baki gaiyacesu ba ai hjy ta gaiyacesu tunda dantane da matarshi suka zo gaida ita wai bakiga
yadda yaya sayadi din ya koma ba wallahi.
Yanzu suna ina ne wai kin tsaya kina muna surutun shirme gasu nan a falon hjy din zaune dasu yaya
yana fadin ina ummashi ?
Nace tana ciki barin shigo in kiranta hausansa ma ya juyo kalan na larabawa a yanzu sak.
Innalillahi ta ambata yadda ta saba ambata bata karasawa saida hjyn ta shaki iska ta mike ta fito suna
biye a bayanta.
Tozali tayi da ahalin masu suffan larabawa a cikin shiga ta alfarma tare da wata matashiyar mace fara
sol mai kyau diri da shekarunta zasu kai arba,in a gefenshi zaune.
Itama ta saka abaya pech colour sai dan gyalensa dayi rolling din shi a wuyanta zuwa kai su kuma yaran
kayane launin na turawa a jikinsu masu tsada da kyau.
Daga gefe kuma su imamune da Ahmad diyanta tare da yayansu Nasir bashir da hamza a tare dasu shi
bashir shine kusa da baffan nasa zaune suna dan magana lokacin da suka fito din.
Masha Allah umma sannu da fitowa ya fada da hausansa daya sauya a yanzu zakice wani balarabeneshi
dama ba wanda ya tashi a garin ba.
Sayadi kaine ashe kana raye sayadi katafi ka manta damu haka ina ka shige tsawon lokacin nan ba
wanda yasan da kana raye ?
Murmushi yayi ya mike zuwa inda taken ya riko hannayen tsohuwar biyu ya rike yana sumbatar hannun
nata kafin ya duka ta dafa kan nasa sai kuma ya rungumeta.
Yaya sayadi kaine wai ya dago ya kalli Nasare din dake fadin hakan ya gyada kai a hankali yana fadin
Nasare ashe da rabon mu sake haduwa a rayuwa ?
Ga yaya kura saida ya dan ja da baya don ambatan sunan da tayi kowa dake wajen ya gane hakan da
yayi din daga ambata sunan sai kuma ya dake ya kallo kura din da kaduwa ya hanata motswa ta karaso
falon inda kowa yake a lokacin.
A hankali ya jaye daga wajen tsohuwar zuwa inda ya taso da farko ya koma ya zauna ya kasa boye
komai a lokacin haka kuma ido suka zuba masa ba wanda yai maganan rashin kula iyalinsa da baiyi ba
din.
Sayadi ina ka shiga haka duk dade wanan babu labarinka bayan nan labarin mutuwanka ya riskemu har
matarka tayi takaba da duk wani abinda ya dace ayi na addini sai gaka kuma ?
Hjy umma wanan matatace ga jikanki hamza wanan mebi masa Abubakar sai umar sai Aliyu ya nuna
yaran ko wani da sunansa.
Kace ka tara khalifai a gidan ka dan uwa yace kwarai da gaske sunansune na saka masu wanan kuma
mahaifiyarsuce itace nake aure a yanzu ita ta haifa min yaran nan ga baki dayansu.
Sai lokacin matar ta motsa tana gaida tsohuwar da hausan da yafi na mijin nata bacewa kafin yaran
nasu su fara sambado mata larabci ta juya harshe itama tana fada masu su gaida kakansu da yan uwa.
Cikin dan hausan da take koya masu sun iya gaisu suka yi banjintasu suna gaida hjy din aka kwashe da
dariya sam zukata sun shagala da kallonsu an manta da zancen kura data kasa fitowa a lokacin sai
gaisawa akeyi da juna.
Wai ina kurane ba zata zo ta taresu bane yaya imamu ya ambata yana kallon hjy Nasare tace ai kuwa
tare muke yaya fito mana kiga yaya sayadi ta juya bata ganta a bayanta ba lokacin.
Hakan tace duk ta dumauce baki daya ita har yanzu bata yarda wai yaya bane ya dawo ta juya zuwa ciki
duba yar uwar nata nan ta sameta a yashe ta fadi some.
Don duk abinda ake fada ita bata yarda ba saida ta leko tayi tozali dashi tun lokacin ta zube amma basu
fargaba a lokacin don farinciki.
Innalillahi yaya yaya ta fada da karfi hakan ya jawo hankalin mutanem falon dake hayaniya awajen suka
nufo inda take sallatin .
A kawo ruwa a kawo ruwa suke fada yakalli iyalin nasa yana fadin suje ko suka mike suka bar falon
banda su man da su Nasir dake tare dasu ba kowane yasan fitansu daga falon ba.
Kai tsaye gidan suka bari tunda ya gaida iyayyen nasa sai daga baya suka gane su suntafi ma ashe basa
falon.
Wanan halin kon in kulan daya nuna mata yasa da dama suka sha jinin jikinsu da abinda ke faruwa a
tsakani tuni wasu sun fara zargin akwai wani abu a kasa fa.
Badai kamar hjy dake ganin anwa yarta wullakanci ai matarka ta fadi ta suma don ganinka amma kasa
kafa ka fice babu kulawa ga hakan?
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[10/4, 10:08 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
6️⃣4️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
[9/21, 9:44 Safiya] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/EzUtkmPPD3K2H5WdQeOg83
08066136431
✍️Jari kike nema shigo METAFORCE
✍️Marayu gareki shigo METAFORCE
✍️Bashi ake binki shigo METAFORCE
✍️Kayan daki zaki canja shigo METAFORCE
MENENE RIBAR WANDA YA SHIGA METAFORCE❓❓❓
Akwai riba da yawa g Wanda ya shiga metaforce amman zamu lissafa 5 dga ciki kuma muyi bayaninsu 1-
after d other
1️⃣kyautar TR coins bayan gama register
2️⃣Referral bonus,kudin gayyato mutane
3️⃣Spillover,kyautar da metaforce ke bayarwa ga yan team din da suke aiki ga Wanda Allah ya cida
4️⃣Overflow,d same with spillover shima kudine kuma zaka ciresu
5️⃣Zaka hadu da mutanen da baka ta6a tunani ba
"B" zaka kara samun experience
"C" zaka iya siye da siyarwa d wnn kyautar TR din,after lunching n tectiles good
"D" zaka San ilimin cryptocurency
"E" zaka San yanda ake duba farashin dollar hawanta da saukanta
"F" Zaka San yanda ake canja dollar tadawo naira🥰🥰
08066136431
YAUSHE METAFORCE TAKE BIYA❓❓❓
Ko a yanzu yanzu kikayi aikin da metaforce tace kikabi tsarinsu na gayyato mutane yes zaki samu kudi
kuma ki ciresu anan take
08066136431
SHIN METAFORCE HALATTACEN KASUWANCI NE❓❓❓
100%halak sbd a team bake daya zaki samu ba,Ku samu na kasa dake ya samu,n sama