Chapter 78 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   78 / 109

231K to 234K   out of 326.5K words

Abbu ya aika masu zancen yace ace kome takeyi tazo gida.

Wace rabonsu da gida yanzu kusan shekara bakwai zuwa takwas ke nan don tun muna tsohon
unguwarmu tazo basu sake dawowa ba sai wanan karon kuma datazo din.

Nice na shedata koshi don hausansu na can da tayi tana fadin mun dawo tazo gida ta samu babu kowa
wai mun fita Abbu yake fada mata.
Lah Anty baraka sannun ku da zuwa na fada cikin jin dadi da murnan ganinta a nan hankalin wasu ya
karkato kan sunan dana fada din.

Ihun murna anty safiya na zuwan nata don an dade ba,a hadu ba gaskiya gashi ba wanda ya kula da
yaje wajenta sai suce wuri yayi nisa.

Ammah ta kasa boye farin cikinta da ganin yar tata shigo take fadin barakafa naji kuna fadin tayi
murmushi tana cewa mune mama.

Ikon Allah yau antuna damu ke nan sannuku da zuwa ita dai bata ce komai ba tayi murmushi ta fara
gaida ita.

Koda na shiga falo a nan na samu shirgin kayansu wajen ban dai tsaya ba na shige ciki dakin na bude
nashiga ina aje jakkata na nufi bandaki fitsari nayi tare da dauro alwala nafito.

Kodana idar tufafin jikina nadebe nafito Asmau dake zaune ana surutu tsakaninsu da Samira na kira
ina fita waje ta amsa kitchen na nufa don mu dorawa baki abinda zasuci.

A kitchen din ta sameni tana fadin mummy gani na juyo ina fadin ga baki kin gani Asmau kinje kin
zauna kuma kinface baki bar abincin da za aciba da dare ?

Wallahi kan babu yanzun me zamu dafa saidai akwai miya nake gani yanzun dai bari mu hada wuta
tace to muka shiga hada wuta .

Kafin wani lokaci har mun zuba shimkafa saiga Abbu ya shigo gidan yana fadin kun dawo muka shiga
gaisawa dashi yake fadin.

Saiga baki kun dawo kun sama a gida lokacin Ammah ta fito daga daki ta idar da sallah take fadin
wutan me kuka sa hakane wai ?

Abinci zamuyi ga baki babu abinci Allah yai maku albarka yaran nan abinda ya dawo dani ke nan naji
yaya za ayi gashi na samu har kunyi dabara ashe ?

Ai laifin wanan yarce Asmau saida nayi zancen abincin nan tace ko anyu ba ci za ayi ba yanzu gashi ai
kin shiga kitchen da dare haka.

Haba yaran da sukai tunanen yin hakan bada masaniyarki ba zaki tsaya mayarwa jawabi kece ya
kamata ace kinyi hakan basu ba ai.

Malam kana son kaga laifinane dai kan wanan zancen nice dama zan fito girka masu abinci suna zaune
da girman su.

Amma da girmanki kika fita sha,anin yara ai bakiji kunyan hakan ba sai na shiga kitchen ki girkawa
iyalinki abinci don raja,a da shashanci ko ?

Munaga rasulu yanzu meya kawo wanan zance haka malam dole in fada don naga baki san ciwon kanki
ba yanzu Ammamatan kin raja,a ga duniya shi kadaine a gabanki.
Hakan da suka fara yajawo hankalin yayan nasu suka fifito har da jikokin nasu yana fadin abin kunya
wai kece da tattara matan unguwar nan zuwa shagali ?

Ai bansan kayi bakin cikin hakan ba tunda bakai magana ba lokacin da zamu tafi din zuwa walima kuma
shine dan kari yanzu malam ?

Walima taron maza da mata haka Allah yace ayi ko haka Annabi ya koyar damuyi tunkan ku dawo
unguwar nan gidan tv suka saka abinda ke wakana a wajen.

Woo hwa hooo yanzu don an haskomu a jikin talabijin shine wani abu malam yai mata wani irin kallo
yana fadin ba wani abu bane tunda kin zama uwar daba mai arna ?

Itace ko jagoran su kowa yace gaiyan Ammahce Samira waya saka bakinki cikin zancen nan naji uwar
ta kwabeta Abbu yadda kake tsamani ba hakan bane .

Na fada daga inda nake zaune ina gyara wuta nace wurin zaman mata daban da maza Nana aiba daga
nan ba wasu mazajen da suka bar matansu suka tafi sun dauka iya waliman mata kadaine ai.

Ayi hakkuri Abbu anriga da an aikata cikin rashin sani ya juya yana fadin sam banji dadin hakan ba
wallahi maganata yasa shi wuce wa Asmau ta kawo kayan miya muka fara jajage don abincin sauri dole
zamu hada don aci.

Muna aiki muna jin Ammah ta koma kan samira suna kwasa bamu tsaya ta kansu ba cikin dan lokaci har
mun gama girki an zubawa bakin don gaskiya suna jin yunwa sun kwaso tafiya mai nisa.

Shigana kitchen baisa haskena ya rage ko kadan balle yanzu daba ko yaushe nake shiga kitchen yin girki
ba ko wani aiki tunda Asmau ta karbeni.

A baya kuma bansan gyaran jiki ba kamar yanzu ina dai da tsabatana amma bana wayewa irin na yanzu
ba don ba a hada yanzu da lokacin da bansan ciwon kaina ba.

Koda muka gama muka shigo falon kowa naciki banda Abbu da sama,ila dake waje basu shigo ba na
samu waje na zauna ina kara gaida da anty Baraka din da hanya.

Ta dago tana irin hausan su na mutanen maiduguri don na fada maku ita a garin doron banga take inda
ake bussiness din kifi sosai a can take zaune da mijin da iyalinta duka .

Saidai da gani har yanzu jiya wa yaune don daga ita har diyan cikin kamanin babu suke ko kauyencine
ke damun su oho ?

Tun da ta kyala ido a kaina duk dago ido zanyi daga ita har yaranta hankalinsu yana kaina yasa dana
samu muka karasa aiki nazo gaida ita.

Wayata dana shigo da ita falon ke kara na dan duba tare da mika hannu na dauka na mike zuwa daki
don ban son aji me zan fada a wayan lokacin saboda idanuwa da aka bazo min aji ko waye ya kirani a
wayan lokacin.
Tun kan na karasa na daga nake fadin wa,alaiku,sallam kamar yadda akai min sallama a dayan
bangaren kana na karasa shigewa ciki gaba daya na rufo kofana.

Ina wuni na rigashi fada bayan gaisuwa sai naji yayi murmushi kawai bai amsa min gaisuwan tawa ba
sai nayi shiru iya nan .

Naji yace masu iya magana sunce tsakanin da da mahaifi sai Allah kamar yadda yake tsakanin miji da
matarsa sai Allah haka wani lokacin shiga tsakanin Aminai biyu shima gangancine.

A yanzu na kara tabbatar da wanan kalman ta masu iya magana ke fadan hakan tabbas basuyi karya ba
don haka zancen yake gaskiya.

Wani abu ya faru ke nan sir ya au ke baki masan ya faru ba ke nan kwarai ya faru don kin shirya da
mahaifiyar ki mu kuma yan gyaran zancen kina fushi damu har yanzu.

Nina isa inyi fushi dakai sir ai ban isa ba don koda kudi akace in gwada fushi dakai ba zan taba ai balle
haka kawai ?

Wallahi ni bani fushi da kowa gaskiyatace kuka kasa ganewa yasa kuka dauka ina fushine ko ina wani
adawa da ummu ummufa mahaifiyatace sir.

Kai kuma kana matsayin uba yaya dan uwa kuma duk a wajena akan me zanyi fushi da mutumin daya
dage ya mayar dani mutum a cikin mutane ?

Humm, naji yace kafin ya fara fadan nina mayar dake mutum a cikin mutane ko iyayyen ki komai da
kike ganin na maki yin baffa sayadine ba nawa ba Ayshaa.

Amma koma meye ni bansan wanan ba don kai nagani a tsaye kaina don haka kai za a yabawa basu
ba.

As you say amma nina san banyi komai da kike daukan nayi ba hakan dai kike gani ko kin fada a gabana
kawai .

Kafi karfin in ma karya karya kuma ba dabi,ata bace dama balle in fara a kanka yanzu in nayi laifi dai ina
mai bada hakkuri akan hakan amma ni nasan akan gaskiyana nake shine nasan waye mahaifina ?

Zaki sani very soon nasan shima a yanzu da yasan inda kike yana shirin zuwa gareki saidai kinki ki bada
daman da za ai maki bayani ki gamsu.

Ai na gamsu don Abbu yai min bayani cikin fahinta kuma na gamsu umma ma da kakai karata tayi min
nasiha dayasa na bar komai ga Allah don haka ni ban fushi da kowa bayan godiya a gareku.

No ni banson godiya ki akan me zakina min godiya da nayi maki me zaki gode min kidai godewa Allah
daya baki mahaifa irin Hjy da kuma baffa .

Nagode masa kaima kuma dole in gode maka da irin kokarin da kaimin haka muka kama dashi tsawon
wani lokaci kafin muyi sallama don hamman da yaji inayi.
Duk da mun kashe wayan na mike nayi sallah isha,i da bansamuyi ba saboda girkin da mukayi na dare
dana idar na dade zaune a wajen ina tunane kan abinda ya faru wajen waliman ranan.

Yadda suka daga min darajana lokaci guda haka a idon duniya a lokacin da ban zata ko tsamani ba
gaskiya kudi sunyi a rayuwa Allah ya horewa kowa da rabo na alheri amin.

Nakai tsawon wani lokaci ina kwance ni kadai a dakin ina tunanen abu daya har barci yazo ya daukeni a
hakan.

Washegari ban fito da wuri ba don raba daren da nayi din wanan kuma yanzu ya zamo min dabi,a sai
dare barci ya kaurace min in kama tunane a kan duniya.

Misalin takwas na safe na fito na samu anty safiya tana hada abin karyawa na gida ga manyan bread
guda ukku da kayan shayi abu ya sayo .

Bin kowa nayi na gaidashi kafin na dawo wurinta ina fadin wanan ba zai isa ba gidan nan ai Anty ta juyo
tana fadin babanki ya kawo hakana nima saidana na nasa hakan ina gudun in magana ya hauni da fada
kuma.

Sama,ila daya fito da shir n makaranta nacewa sama,ila zoka karbi kudi ka karo kayan shayin nan na
fada tare da mikewa zuwa dakina.

Bayan na dauko na mika masa kudin yaron ke fadin wancan ma kamar bashi ya karboshi don kudinshi
jiya ya biyawa su mama da sukazo kudin mota yace isa ya bashi bashi.

Nace nawane mukai lissafi da yaron nace yakaiwa isa kudin yace Abbu yace ga kudinsa ya karo masa
wani kuma na hada duka kudin nabada.

Bai jima ba ya dawo ya sameni bakin murhu tare da anty safiya dake aiki muna hira Nanata ashe kinba
yaron nan kudinsa nace eeh Abbu yace karba kayi dama shine na mika masa yakai masa.

Ikon Allah nanata hakan bai zama dawainiya ba na aika a sayo kamu a dama koko sunce ya kare ga
kuma wa yan nan sun zamo baki a barsu da yunwa.

Abbu dawainiya kuma don an sayo abincin gida ban kanso hakan ne gareki nana ba komai nake maki
ba yanzu kuma in koma ina karban dan kudin da kike amfani dashi kuma.

Abbu ban komai dasu ai don haka nake ajewa idan an ban Allah ya kyauta yace ya juya zuwa dakinsa a
raina nake tunane a wanan takin da ummu ta dawo da alheri haka bai kamata ace tabar min iyayye haka
ba.

Saidai kuma sanin halin Abbu da nayi nasan ba zai taba kaskantar da kanshi yadda wasu keyi ya koma
ya tare a wajensu ba duk da abin alherin da mijinta ya kwadaita masa zai maidashi hakan ba zaisa wai ya
zubar da kimar ya tare a wajensu ba kullum sai har insu suka nemasa.

Kaurin shayin da za akaiwa su anty din yayi anty safiyace ke tambayana hakan na dago ina kallonta
saida taban mamaki .
Don kamar ba yar uwar haihuwanta bace tazo da yaranta dan ruwan shayun can rabin jug ta zuba
kuma su ukku wai ?

Ita da yaranta mata biyu da sukazo sai bread din ta raba biyu kallon mamaki nayi mata tare da tambaya
wanan ne nata ita kadai ko anty ?

Sai naji tace waida su duk da yaran nace ko ruwan baiyi bane ta fada don kallon mamakin da nake
mata .

Haba anty wanan aiko mutum daya baya isa balle su duka sai naji tace wai naga shayine kuma baida
yawa koda yake jiya abincin nan da aka zuba masu gaba daya ita da yaran naga sun tashi dashi duk.

Mamakine ya kamani ita ba,ace angaji da ita shekara da shekaru taba gida da iyalinta amma mata daga
zuwanta jiya jiya ta nuna tafara gajiya dasu haka ?

Dama ashe ko a yan uwa haka abin ke wakana kenan bawai sai wani bareba can sabba zaka iya nunawa
hakan gaskiya halin data nuna ya ban mamaki matuka.

Da gaiya ta cika cup din ta dan kara bread nace bari a basu haka na hada masu da serches din madara
da milo biyu su kara na dauka nakai masu don suna dakin Ammah nan ta saukesu ashe.

Na samu sun tashi muka gaisa dasu nayi masu yaya hanya nan take fadin ashe mama Asiya ta dawo ?

Nayi murmushi nace wallahi anty tace harda iyalanta da aurenta kuma gaskiya abin yayi kyau sosai
wallahi naji dadi naji dadi sosai wallahi jiya da baba ke fada min wanan zance.

Wallahi maman mu harda kukanta jiya saida baban gidan nan yaita bata hakkuri yarta ke fada nace
Allah yayi dawowanta gida a wanan lokacin.

Daga ita har mijinta ashema mijin shima dan garin nan ne yanzu take aure tace haka dai baba ya fada
muna kema Allah ubangiji ya baiyana muna mahaifinki lafiya amin.

Anty akwai ruwan shayin idan zaku kara naga kamar wanan yayi maku kadan tace ai mungode Allah
yayi albarka.

Nasa kai na fita daga dakin ban koma wajen ba dakina na nufa na zauna ke nan naji muryan anty Safiya
na fadawa Ammah wai borodin bai kai ba na kwashe nabawasu baraka da yayanta.




ZAINAB IDRIS MAKAWA[10/31, 7:25 AM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu
Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

8️⃣1️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6



https://sitrix.africa/signup.php?ref=foleesco




Morning Dad mami ina kwana lokaci guda ya mikawa iyayyen nasa gaisuwa wa yanda ya samu zaune a
falon suna zancen da bai sani ba tsakaninsu saidai yanayin zamansu kawai zai nuna wani zance sukeyi
mai muhinmanci a lokacin.

Mam bashir har anfito ka tashi lafiya ya kuma hutu duk dadai wanan hutun ai ba hutu a gareku don har
yafi aiki kusan wahala.

Dan murmushi yayi yana kaiwa zaune gefensu yake fadin ai an kusa dan abinda ya rage baida yawa
daddy wanan mutumin daya tsaya ja shine kawai matsalan mu a yanzu.
Kana nufin har yanzu yana kan bakarsa sai anje kotu hakan yace amma yau zamu koma masa da wata
zance shiyasama na fito yanzu.

To Allah ya taimaka yatsare ya kareku bakidaya abinda mamaki wallahi yadda kura tasamo mutanen
nan har ta halaka kayan nan ba tare da kowa ya sani ba.

Ba aikita bane aikin namijine shi wancan daya saye incomplete din nan ai yayi muna bayani cewa Iya ya
kawo masa tallan wajen yasaya.

A gaskiya yaci ai karan kawu ga maimartaba wanan zalluncin yayi yawa haka daddy baka san wani
abuba ma kusan a tare suke raba kudin daidai don bai fada mata ainihin kudin da aka sayi wajen sai ya
dora nasa sama.

Kaji jahilci dama nasan dole ai hakan ashe shiyasa a lokacin yayi ta facaka har ya gina gidan nan ai zamu
dawo garesa idan mun gama da komai .

I see no reason da zaiyi wanan yaudaran hakan ga yar yar,uwansa kawai ku fita zancen sa ai akwai
kotoun Allah ko zaije can yayi jawabi a gaban Allah inda ba wani ja,inja.

Amma duk abinda kawu yayi da sanin yar uwarsa don babu yadda za ayi ace kawu yasa kayan hjy kura
gaba yana sayarwa hjy mama bata sani ba mami ta fada.

Kawu nefa duk yadda zaiyi ya shawo kansu aiya sani sam banson halakan wani harkalla ya hadani da
kawu ai daddy ya fada.

Magaji Allah ya shirya ka koma ince Allah ya shiryaku yanzu ashe Alh kunsan yarinyar nan ko wacece a
wajen ku kuka barmu muna haukan mu .

Murmushi yayi ya shafo kansa yana fadin amma mami aina haneki da fadin wani kallama a fakaice
tsoron sanar da wani mukeyi a lokacin don idan zance yafi mutum biyu bai zama siri ba kuma.

Yanzu aikin sani daddy ya fada ta juyo ta kallesa tana fadin amma abinda kunya wallahi ranan ai mun
hadu abinda nayiwa yarinyar lokacin yafi tsaya min a rai.

Ya mike yana dariya yana fadin mami bake kadaice baki san komai ba don ko ita kanta yarinyar aihi
lokacin bata san komai game da ita ba .

Don bata san nasan mahaifiyarta ba sai yanzu take sanin wani abin don bamu yarda ba a lokacin saboda
zance yana iya tafiya a gane baffa yana raye su bata muna shiri.

Amma shi baffa shike sakani yin duk wani abinda nake mata saboda gaskiya idan ba hakan da yayi ba
rayuwan yarinyar zai lalace nan a banza babu mai taimaka mata.

Babu kan gaskiya ba karamin hikima yaya sayadi ya fito dashi ba wajen tallafawa yar nan nasu don da
yanzu sun sameta a yadda ba a so don sai ransu ya baci mami ke fadan hakan.
Dolene ya tallafa mata don matar nan ba karamin taimakonshi tayi ba a rayuwanta don poison din da
kura tayi ta iza masa da farko ta dauka baiyi tasiri a jikinsa ba har ta juya wanan matakin nata na karshe.

Bai fara amfani ba saida ya bar wajensu dakyat da boni ya samu kansa itace tayi jinyarsa cikin dauriya
har ya samu lafiya.

Batu daine baya faduwa kawai amma kura ta cuci bawan Allah nan fiye da tsamanin ki wallahi mace
kamar ba haihuwan musulmai ba wallahi.

Kwadayin duniyane Alh inbashi ba da ai duk cikin mu tafi kowa walwala da samu amma ta raina hakan
matsalan tafa dayane irin rayuwan banzan nan ta sakawa kanta na.

A dole asan da ita watace a waje ta zamonta kowa yana bayanta sai abinda tacewa kowa yadda take so
har yanzu kuma akwai halin a gareta duk da babu din nan.

Sauratane yaja mata hakan kila haka mata ke nasu mulkin izza da kaisatansu a fili

78 / 109