Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
na yan zuri,an mune gaskiya dayan
matar ta fada tana kallon yar uwar nata.
Bayani take mata da cewa kowanen mu yana da wanan dingon tana kokarin ture gashin ta baya ta
nunawa yar uwar nata dingon naji ta dakatar da ita da hannu tana kuma kare min wani irun kallo mai
kama da tsana a fuskanta kafin ta juya ta fita dayan matan ma tabi bayan ta da sauri suka fita daga
dakin.
Ajiyan zuciya na sauke ina rufe kofan nanufi wajen mirron dakin na tsaya a gaban madubi ina kokarin
kallon wanan tabon da suke magana akai.
Ban mantawa ina karama ina yawan kwalbatansa waina ciresa a jikina wajen yai ta jini sai ya warke
kuma ya koma yadda yake ashe ban sani ba hakan zai min rana irin ta yau don sheda ce a gareni daga
Allah.
Ita ko matar tana fita daga dakin ta koma wani daki tana waya a cikin kuka take fadin wallahi baba
komai nashi tana dashi a jikinta hatta wanan digon bakin da kace akwaishi a daidai inda nasa yake
hakama yatsun kafanta iri dayane da nasa kaf.
Hakkuri aka bata akan ta bar komai zasu kara binke da kansu gashi kuma zancen zuwa asibiti ai gwaji
da akace za ayi tabar komai gaskiya zai fito insha Allah.
Nayi mamakine baba ace ni ya kasa ban haihuwa amma ya iya zuwa yabawa wata bakar fata zuriansa
ni yakasa ban komai a rayuwan zaman mu ?
Yi hakkuri ba zamu taba yarda wanan abin ya yuyu ba dolenema yarinyar nan ta kama gabanta don ba
wanda ya sheda aurensa da ita kaf din mu.
Munsam ta yadda zamu fitowa mahaifinsa ai tunda shiya kama zancen ya kauda duk wani al,ada na
kabilan mu saboda dansa ba zamu taba yarda hakan ya faru ba mu hada jini da bakar fata ina sam hakan
ba mai yuyuwa bane gaskiya.
Fitowan nayi daga dakin ina kallon yadda suke barin aiyukansu suna bina da kallo cikin mamaki Allah ya
taimaka na hadu da wanan dattijuwar dauke da kayan abinci data dauko wani daki.
Cikin dan gwalancin larabcina har ta gane su Abbu nake nema ta kaini har inda suke ta nuna min nayi
mata godiya ta tafi.
Dakin na kwankwasa sau biyu naji ana budewa daga ciki mukayi arba da Abbu dake saye da farar
jallabiya a jikinsa har kasa.
Murmushi nayi ina gaidashi ya amsa yana fadin yanzufa muke zancen ki ashe kema kina neman mu
shiga nayi daga ciki na samu Ammah a zaune saman kujera tayi tagumi .
Gaida ita nayi kafin ta amsa na jefo mata tambaya da lafiya dai Ammah ?
Tace bari yar nan kedai tunanen duniya dai ya isheni a zuciya yau mune cikin irin gidan nan ana muna
gata haka ke dai ?
Murmushi nayi ina zama a gefenta nace nima na matsu mu koma gida wallahi naga ta juyo ta dubeni da
sauri tana fadin kaiya wani gida kuma yar nan ?
Aida alama kamar kinzo ke nan ba komawa kuma yadda nake ganin take taken mutanen nan a idona
gaskiya kamar so suke su tafi dake gaba daya zuwa kasansu fa.
Wani kasa kuma Ammah ni ba inda zan binsu gaskiya saima nake ganin kamar da gangan Abba yazo
damu umuran nan kamar dama sun shirya komai akan hakan.
Wa zaisan angano mahaifina tunda ba a gida ya samemu ba Abbu dai yana zaune yana jin hiran mu
baisa muna baki ba saida yaji na fadi hakan yake fadin kaiya.
Bokon nan dai naku da alaman ya ratsaki Nanata inma hakan ne ai alheri yai maki ba cutarwa ba yau ina
laifin mutumin da yayi kokarin sadaki da mahaifin ki Nana ?
Murmushi nayi na dago ina dan kallonsa kafin nace ba wai laifinsa nagani ba Abbu yadda dai abin
yazone yasa nake wanan tunanen duba ga yadda tun farko yaita abubuwa a kaina ko ummu bata sanda
yana hakan ba a lokacin.
Haka yasa nake ganin kamar yana sane komai ya gudana har tafiyan nan namu din zuwa nan duba ga
yadda ya kwaso yan uwa haka donsu sheda komai kuma a gaban idon su.
Koma me Alh yayi yayi muna komai a rayuwa sai mu gode masa da ya zamo sillan cikar burin mu Nana
tun jiya nayi dawafin godewa Allah daya sadaki da iyayyen ki muna raye muka karas da idanuwan mu
Alhamdullahi da hakan .
Abinda nake so dake shine ki bi mutanen nan yadda suke so a yanzu don banji dadin yadda kikai masu
jiyan ba tsakani da Allah nanata kina da ilimin boko dana arabiya gwargwadon sani kin samu.
Yau ba inda zaki shiga ki kasa fita da kafan ki a duniyan nan wanan shine dama burin mu akullum
addu,an mu ke nan kuma Allah ya karba muna shi a yau gamu zaune gidan mahaifinki da rayuwan mu
mungani kowa kuma ya gani.
Yau in mutum dayan muyaga hakan kamar kowane a can gida ya sheda hakan don haka kada naji ko
inga kin kara mussun kowa akan mu don Allah.
Mu dai nakine nana duniya kuma ta sheda hakan baki muna butulci ba kin nunawa duniya
muhinmancin mu a gaban kowa ko haka wallahi mungode nana.
Kukane yazo min lokaci guda kafin ma ya karaaa zancensa na fahinci inda zancen nasa ya dosa .
Don kamar Abbu na min nunine da nabi mahaifina a lokacin wanan ya sakani fashewa da kuka lokaci
guda.
Abin da kamar wuya yau rayuwata ta koma wani wajen ta daban inda ban saba rayuwa ba a baya cikin
mutanen dabama jin yarensu nake ji ba.
Ammah daga gefena kuka ta fashe dashi tana fadin Aeeshata ki yafe min don Allah idan nayi maki ba
daidai ba a zaman mu na rayuwa don dan adam dan tarane bai cika goma ba .
Kofan akayi nocking alaman sallama hakan ya dakatar damu daga zancen da mukeyi muna kokarin
saita kan mu a lokacin .
Mahaifin nawane ya shigo tare da dattijun nan ganina a dakin yasa ya kalli dan nasa yayi wani magana
sukai murmushi.
Ya dogaro sandarsa zuwa inda muken da Ammah tayi saurin tashi larabci ya fara muna kafin naji ya
juya min zuwa turanci yana fadin.
Kuka kikeyiwa iyayyenki da alama sun bataki da yawa ni sanda na zan saka na make ki dashi gaki kin
koma Afriaan black saidai duk da hakan kamanin kina ubanki da kika dauko bai gushe a gareki ba yata.
Ki saki jikinkinki da kowan mu muma nan iyayyen kine don dake zan wuce zuwa dubai kije kiga yan uwa
acan kowa ya sanki.
Saidai sun fada muna kina karatu ko da dan saura ki kammala donshine zan bari ki koma Nageria a
yanzu.
Jin hakan yasa na dan dago kaina na dan dubeshi ya kada kai alaman ehh hakane muma muna
bukatanki a cikin mu yanzu.
Muna kaunarki muna son mu nunawa duniya ke a matsayin ya a garemu kamar kowa kema kiyi alfahiri
da fitowa daga tsatsona kamar yadda ko wani da a cikin mu yakeyi a yanzu.
Wa yan nan mutanen bamu da abinda zamuce dasu sai godiya da fatan samun kyakyawan sakamako
daga ubangiji kamar yadda suka rike muna ke a cikin aminci.
Kwarai na yaba da irin tarbiyan da suka baki na kuma sheda hakan tunda kinsan rike ibadanki da kuma
mutuncinki.
Ga mahaifiki yana jin nauyi da kunyan abinda kurciya yajasu suka aikata maki saidai Alhamdullahi
tunda hakan bai kasance ta tsigar zina ba a garesu duk da wasu na kallon hakan sabawa shariace.
Saukin abin ga nasa ya kafa shedun aure ya zauna da mahaifiyarki tsawon shekara biyu a tare da ita
wanan ma kawai ya wadatar a shari,a da wasu suke ganin ba daidai ba.
Zan rokeki a yanzun din na aribaki na roka mashi gafaranki ki yafe masu kuskuren da suka aikata maki
a baya don Allah.
Wanan yasa nazo dashi a gaban iyayyenki ba tare da kowa ba don ya nemi gafaranki a gabansu akan
kuskuren da suka aikata da kurciya.
A hankali na fara kada kaina ta hanyar girgiza masa alaman a,a a,a na samu na bude baki da kyar ina
fadin shi mahaifinane inma raina ya vaci dashi a baya na yafe komai a yanzu.
Masha Allah Allah yai maki albarka naji dadin hakan tunawa da hakan yana hanani sukuni da barci wani
lokacin.
Don bansan da wani ido zamu iya kallon ki ba gaskiya tarbiyan wajan ku akwai sauku sosai da ma,ana
tunda har mutum na iya yafewa mutum laifinsa lokaci guda haka ba tare da yasa masa wani taraba.
Alhamdullahi zamu karasa magana zan baku waje ku samu ku karya kafin ku fito dama wanan ya
kawomu wajen ku sai gashi na samu kanku a waye kuke ba wani fitina a bayan hakan ?
Yadda tsohon ke jero turancine yake ban mamaki zakice shu din ai tsohon baturene wai kuma a hakan
balarabene yaji turanci a bakinsa kamar haihuwan turai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA[11/16, 8:15 AM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu
Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
9️⃣1️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6
Zaune take a bakin gado ta kafawa kasan dakin ido haka ya turo kofan ya shigo ya sameta a zaune cikin
damuwa da yan kwanakin nan haka rayuwan nata ya koma.
Zai iya cewa a yanzu ba wani jin dadin aure ko zaman lafiya a tsakaninsu don ko yaso hakan bai
samuwa ga matar nasa a yanzu.
Ya rasa meyasa ta juyawa farincikinsa baya haka a nasa zato ko tsamani itace zatafi kowa farin cikin
hakan a garesa na baiyanar yarsa a garesa a saukake da Allah yai masu.
Amma sai gata tafi kowa daga hankalinta ita da yan uwanta a da can idan ance zatayi hakan a kansa zai
iya mussawa ko waye a lokacin.
Sai gashi abinda takeyi a yanzun din sam bai taba tunanen haka ba a kanta balle wani nata su din
dukka yan uwane .
Ya zata damuwansa duk damuwansune ashe abin ba haka yake ba su a zuciyarsu sunfi son ya mutu a
hakan babu da babu jika a rayuwansa.
Da kyat ta iya dago ido ta kallesa tana kawae da kai a gefe daya shima yi yayi kamar baisan tana wajen
a zaune ba abinda ya kara bata haushi ke nan .
Don a iya sanin da tayi mai shi mutum ne mai kokarin kula da hakkin iyalisa mutum ne wanda yasan
darajan dan adam mutum ne wanda baya wasa dabawa duk na tare dashi hakkinsa.
Zaka iya min hakan a yanzu tunda kana ganin hasken idanunka kamar ya budu saidai ka sani ina nan
akan bakana ban yarda da yar nan taka bace sai anyi gwajin asibiti an tabbatar da hakan a kanku zan
yarda.
Haka kuma ban yarda asibitin ya fito ta wajen ku ba sai wanda ni kaina na yarda dashi zamuje a
tabbatar da komai a kan ku .
Ka rasa wace zaka sheke ayan ka da ita sai karuwan black karuwai masu baro kowa nasu suzo neman
mazan mutane da sunan aiki ?
Kai baka jin kunya yau duniya ta sanda zancen nan a kanka cewa ka taba auren inma har auren kayi da
ita sai lokacin ya dago kai ya kalleta cikin bacin rai tare kuma dan sakin murmushin bakin ciki a fuskan
nasa.
A yanzu nasan manufarku a kaina salma nasan badon Allah gaba dayan ku kuka hada halaka dani ba ?
Wani irin dagowa tayi tana kallonsa ganin ya koma mata sak umar dinsa na baya yasa tayi saurin
kwantar da idonta don bata taba zaton kalman hakan daga bakinsa ba .
Don a ganinta baisan duk abubuwan da suke shiryawa akansa ba din wanda mahaifintane yake dorata
ga komai har garama uwarta takan nuna rashin yardan ta wani lokaci.
Me kalamin ka yake nufi a yanzu sai sautin murmushinsa taji kawai bai tsaya bata amsa ga zancenta ba
ya shige ban daki ya rufo.
Zaune yake a gaban laptop dinsa daddy yana fada mai duk yadda komai ya kasance a cikin farin ciki shi
kuma yana sauraren mahaifin nasa.
Kafin ya lumshe idanuwansa ya dan shafo kansa a hankali ya koma bude idon yana fadin a takaice
komai yazo karshe kamar yadda baffa ya tsara abin ?
Komai yazo karshe tayi mai halarci ya saka mata da alherinsa tunda yabi duk wani hanya ya sakata farin
ciki a yanzu shima.
Good Allah ya tsare gaba kuma daddy don ba namijin kokari baffa yayi ba ya kuma kashi kudi sosai kan
zancen nan gaskiya.
Hakane mam bashir gaskiya ne hjy Asiya ta cancanci hakan wajen sayadi koma fiye da hakan ai uwar
yayansa kuma ko banza kaga akwai kyautatawa a tsakaninsu.
Hamma yayi alaman barci a idanusa yana fadin is ok daddy zamu kara magana dakai next yanzun dai a
takaice yarsu tana hannunsu ke nan dai ?
Tana can wajensu a yanzu bamu san ya zasu yanke hukuncin inda zata zauna ba dai sai zuwa nan gaba
yanayin fuskansa a tsuke yasa mahaifin nasa ya fahince shi.
Be cool my friend rabon mutum baya wucesa duk inda yake su kaita nan da bangon duniya in Allah ya
kaddara yarinyar nan rabonkace zaka sameta.
Daddy ya fada da sauri mahaufin nasa ya murmusa yana fadin i know you mam bashir ba zaka iya boye
min komai ba a zuciyarka ?
Nasan ka fada son yarinyar nan a yanzu wanda da farko ba haka bane amma yanzu ka fada wanda
hakan kuma kanata kokarin danne hakan kada a gano ka amma saidai ni na dade da gano hakan a
kwayar idanun ka.
A yanzu yarinyar nan kowa yasan idan kace kana son ta hakan ba laifi bane ko illa a wajen kowa don irin
nasabanta da yanzu ya baiyana.
Daddy mu bar zancen nan please ya fada yana harde hannayesa a waje daya sai uban yai murmushi
yana fadin akan me zamu bar zancen tunda kana sonta.
Daddy yarinyar ta faye akida da yawa tun tana talka dinta ina fama da ita balle yanzu da zata kara bude
ido daga wasu abubuwan nan gaba.
Kaji ka da wani zance shi balarabe dama ai haka ya gada baida tsoro ko shamaki akan abinda yai niyar
yi a rayuwansa .
Su haka Allah ya haliccesu da wani irin baudaden ra,ayi a rayuwansu kaga ko tunda akwai wanan jinin a
jikinta dole sai tayi wanan akidan koda a cikin rashin sanin tanayinsa kuwa.
Sun dauki lokaci suna wanan muhawaran inda yake fadawa uban kawai dai muna mutuncine daddy
amma ban taba furta mata wani kalman so ba gaskiya.
Uban ya tareshi da fasin saidai wanka da kamar jurwaye ko dole itama zata fahinci akwai sonta a
idanun ka saidai halin mata tunda baka fito ka furta mata hakan da bakinka ba.
Mami ce ta shigo dakin tun bude kofan ta hango dawa yake magana ta nufe shi tana fadin nasan
nemana ma bakayi ba magaji.
Amma gashi ka kira mahaifinka online kuna video call haba mami shi ua tayar dani daga barci yanzun
nan tashina ke nan .
Ashe jiya kunsha dinner a saudiya ta hararesa tana zama take fadin bari kai dai munga mamaki jiya
wallahi abubuwa da yawa a wajen nan suka faru.
Naso ace mummy kura na wajen nan naga yadda zatayi akan yarinyar da take faman aibantawa kan
mahaukaciyar yarta.
Haba dai yar uwarkace fa hindu kabar aibanta tamana yake fadin kun dauka wanan abin da takeyi
saboda ta daina shan kwayane ko ?
Hinda ta bata rayuwanta abun baida dadin ji ko kadan mami wani kungiya ta jefa kanta a ciki ummi ce
ta fara kirana tana fada min daga ghana.
Ni wanan abin nasu sai ince duk alhakin yaya sayadine ke fita har akan yayansa wallahi yadda suka
kama dukiyan bawan Allah nan suka wullakanta a banza wallahi.
Ai gara dukiya da rayuwansa data so salwantawa akan abin duniya ta dauka zataiwa Allah waysune ita
kanta ai a haukace take ba yar kadai ta haukace ba a yanzu.
Don bata da kunya tana son ta zargi mata wai hjy Asiya ce tayiwa hindu asiri ta dauka kowa irintane
mara imani .
Yanzu kan ai jiki magayi don kunyan duniya dai tajishi saura na lahira kuma jiya yaya imamu ke fada
min wai saida baba yasa a koreta cikin gida ta shigo tana masu hauka wai an munafunce ta don aga
bayanta dukkan mu munafukaine tunda tare da yaya sayadi muke yanzu .
Ta zauna tana faman jan Allah ya isa a tsakar gidan zalla kunya da takaici saida mama ta tura aka
shedawa maimarta ba ya shigo ciki.
Allah ya kyauta mami ta fada tana karawa da fasin to banda abin hjy za a ki yaya sayadine yanzu
saboda ita ?
Mutumin nan alheri yai muna ina laifinsa inda wanine ai ba zai kara yarda da kowa daga cikin muba
amma har yanzu mune daine yan uwan nasa kamar yadda aka san shi damu abaya.
Ni yanzu ai nauyin wanan yar da take muna kallon mun tsaneta tun baya shine damuwana gashi ko
banza muna yawan haduwa da ita a gidan uwarta yanzu wanan abin yana matukar damuna sosai wallahi
idan na tuna.
Gashi kuma in Allah yayi sun barwa sayadi kila zata zamo sarakuwarki ba nan gaba saidai abinda ya fito
daga Allah kuma.
Hiran iyalan gwanin ban sha,awa zolayace na hankali da nishadi sukai tayi a tsakaninsu kafin suyi
sallama da juna su kashe na,uran .
Sai dai tunda sukai waya da mahaifan nasa yaji yana son kiran Ayshaa din saidai wata zuciya da shedan
ya shigo masa cikinsa yana zugashi da cewa itace ya dace ta kiraka ai ba kaine zaka kirata akan zancen ba
.
Abubuwa da dama ya dinga tunawa da suka faru a tsakanin mu yana jin wani iri a zuciyar shi dama
haka duniya take shiyasa ba,a son ka raina mutum.
Yau gashi yarinyar da sukewa kallon kaskantatta yar tallakawa mara uba itace bin ya juye ta koma mai
uba da gata a cikin duniya.
Yau itace ake kyautawa zaton yar miloniyar nan mutmin daya fito gidan sauratan kasar Ouman
mazauni Dubai wanan hukuncin sai