Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
manna maki sabo dashi daga baya kuma ya gudu ya barki suma yan
uwansa suka dora da maki gargadi akansa.
Basu da laifi ko kadan wallahi don sam ban ga laifinsu ba don sunyi min haka ?
Asima sunyi kokari dani fiye da mutanen da sukai sanadin zuwana duniya suda suka haifoni kuma suka
wofintar dani a cikin duniya.
Waini irin juyowa yayi yana min duban mamaki kafin ce dani sister kin ko san abinda kike fada a
yanzu ?
Ko duk son ne haka ya makantar maki da zuciya haka har kike son ki aibanta iyayyenki da bakin ki kan
wani namiji sam ban tsanmaci jin hakan daga bakin ba wallahi.
Ya yazid ke nan kana tunanen ko na tabu ko har akwai wani da namiji da sonshi zaisa na zargi iyayyena
kake gani a yanzu.
Gaskiyar ce dai na fada maka ai yarda da kai yasa na bude bakina yau ina wanan zancen dakai kan
damuwata .
Kaima kuma saboda naga ka damu da damuwatace kana zaune dani tsakani da Allah a zuciyar ka ka
daukeni tankar sister hafsat .
Yasa na dan fada ma gefen zuciyana abinda na fada ko kaine hakan zakayi hukunci a kanka ba wai na
fada bane don wani ra,ayi iya gaskiyar ke nan dai.
Kallo kawai ya bini dashi muka shiga cikin gidan da megadi ya bude get don horn din da yazid din yayi
mashi tun isowan mu bakin get din.
Addah murja ce a waje kamar tana neman wani abu hakan ya dakatar damu da zancen muka fito daga
cikin motan.
Lafiya Addah naganki haka take fadin wata yar arnakuce ta kafe mun kofan gidan nan tun dazun wai
tana jiran watace tace damu.
Kallona yayi sai lokacin na tuno da serah naji yace yar gidan mutanen can data barone tazo neman ta
dazun muka hadu da ita da safe.
Ai haka zancen yake nasha ai wani iya shegen tazo yi muna nan nikan na korata ta tafi da kayan
tsiyarta.
Ganin yayi gaba yasa nabi bayan shi zuwa cikin gidan inna kadai muka samu a falo ta kurawa tv ido tana
kallo jin shigowan mu yasa ta mayar da kallon zuwa wajen mu tana fadin.
Dan ina kaje ka zauna haka uwarku tana ta kiran mutane hankali a tashe sai yanzu suka kammala
aikinsu na daukota .
Ka fadawa uwar taku ko yanzun zata dawo itama ya bata amsa da hakan yau ba zuwa ball din ke nan
tunda kakai wanan lokacin a waje.
Ko zakizo muje tarene ya fada ya mike zuwa ciki lokacin na shige ko daki tunda muka gaisa da inna din
kayan jikina na debe na saka wani dan wando baki da yar t,shirt din shan iska baka itama.
Naso cin abinci amma ba zan iya ciba don tuwone a lokacin yasa na fito falon na zauna zamana yayi
saidai da shigowan mum da hafsat gidan daga can hafsat ta biya ta dauko uwar don mota biyuce a gidan.
Ta zuwa school din yara saina uwar dashi yazid yaje daukoni muka gaisa yadda aka saba kafin Adda ta
gabatar masu da abinci don ganin basu da niyar shiga dakinsu lokacin.
Saida ta soma cin abincin ta kalloni tana fadin yau wani irin aiki kukayi haka ya tsayar daku har yamma
Aisha ?
Wallahi mama tunda naje suke abu daya kan wasu harkers dasuka bude wani account an kasa gane ko
daga ina suke wanan aikin amma an gane ko daga inane matsalan yake.
Kice kin gano ko daga inane matsala yake dai mum yar nan taki manyar nau,urace duk manyan offoce
din nan sun kasa gane matsalan amma ita tagano inda abin yake.
Haba dai karka sakani zuwa gobe naji komai Allah zaifi kije mum don kin san wanan ba karamin abu
bane gaskiya zuwanki zaisa su san tana da wanda yake mata tsaye a nan.
Kai ka dauka zanje wanan wajen nasu mai tsaro dasu da jami,ai fa daya suke wajen aiki don sune suke
binciko mai laifi su dankawa jami,ai su baka ganin su ko yaushe a cikin wanan bakin corth din suma.
Amma ke baki ci abincin ba Adda ta tambaya na dan girgiza kai alaman banaci akan me Aisha ba zakici
abinci ba ?
Just mama kawai abu mai dan ruwa nake son something liquid haka ga yazid idan anyi sallah ya fita
daku ki san samo wani abu.
Tana fadin hakan ta mike ta shiga daki don magariba yayi lokacin bayan mun idar saiga shi yana fadin
mum tabani dubu ukku mu samo wani abu kizo muje tare banki ba don ina son fitan lokacin.
Sister muje nace da hafsat duk da nasan bata fita damu saidai nayi mamakin jin tace ku jirani in fito
nice na zauna baya suna gaba.
Mun dan bar gida yake fadin ina zamuje hafsat din tace sahad mana mu sayo wani abin nawa mum ta
baka yace three thounsands only .
Nima yau kwadayi nakeji bana iya cin wanan tuwon da Addah take muna kullum saboda mum
takeyinsa donshi tafi so yazid ya fada.
Mundan zaga ta dai dauki abin 1k da tace tana dashi abubuwa da dama tana so a wajen saidai bata da
kudin saya ta nuna karshe dai duk abinda suka nuna saina dauko.
Ko kaji shidda aka saka muna a leda ga abin sha mukaje biya na mika katin bankina suka zare kudinsu
akayi muna parking muka fito.
Ina kallon yadda hafsat kemin wani kallon mamaki kafin mu iso gida ruwa ya sauko haka muka shigo
mama din duk suna falo Addah na zuba abinci zasuci.
Ya shigo da ledojin niki niki ta bishi da kallo cikin mamaki wanan kayan kuma daga ina haka ka samu su
sai ya nunani da yatsa daga wajena.
Aisha ina kika samu kudi haka suna account dina mama na fada ina zama tauuuu tafa cikin mamaki
karki zuba Adda ko ku nasan ba zakuci wanan abincin ba yanzu.
Yafara fitar da kayan da suk abinda suka sayo an daici kajin da annashuwa amma uwar hankalinta bai
kwanta ba lokacin kudi yana kudi tasan ba karamin kudi na kashe ba.
Lemun kwali na dauka da rabin kaza nace zan tafi daki in kwanta nagaji wanka na soma na fito na
shirya zan kwanta aka turo kofan na juya mama dince ta shigo dakin .
Gaida ita nayi kafin inga takai zaune tare da fadin zauna Aisha magana zanyi dake jin hakan yasa na
zauna a rusunne bakin gadon.
Aisha ta kara kiran sunana kafin tace ba wai ina zarginki bane a,a duk uwa tagari hakan ya dace taiwa
yarta don haka kada ki damu da tambayana a yanzu gareki.
Kayan nan da kuka sayo nasan ba karamin kudi kika kashe ba wajen sayan su bafa zarginki nakeyi ba
don banga wani alaman rashin da,aba gareki tunda Allah ya hadamu.
Amma saidai ina kika samu kudi haka Aisha dan guntun murmushi na sake kafin nace mama nagode
amma da kudina nazo garin nan suna account dina sune na taba.
Mahaifinki ko mahaifiyarki ke baki ke nan nace mahaifiyatace take turo min su daga saudiya sai naga ta
dan saki rai kafin tace a saudiya take zaune ke nan nace ehh mama.
Mahaifinki fa shima a can yake zaune saidai ban san suba har yau din nan abinda kawai na sani Abbu da
Ammah sune ke rikona a hannunsu na taso har na girma.
Ok na gamsu da bayaninki a yanzu kada kice ko ina zarginkine a,a duty din mune iyayye mu saka ido
akan yayan mu nagode mama na fada ganin ta mike tsaye zata bar dakin bayan ta gamsu da amsa na a
gareta.
Washegari gidan yayi tsit don ba wanda zai fita a cikin mu yasa kowa ke barcin safe inba Yazid daya
fita wajen ball dinshi ba.
Karfe takwas na tashi na fara gyaran gidan har kitchen ko ina lokacin Adda ta fito muka gaisa ta dora
dumamen abincin jiya da ba suci ba.
Bayan na gama nayi wanka na dan jima a daki ban fito ba ina kwance saiga hafsat har dakin muka gaisa
take fadin sister nagode da turaren da kika saya min jiya.
Haba dai ba wanan a tsakanin mu ai tayi shiru tana murmushi kafin tace nayi bin mum ta saya min taki
tace nice na bata motan da muke hawa sai anyi gyara.
A cikin hiran mune nayi subul da baka nace nima nasan ina koma dole sai anyi gyaran tawa motar
tunda ta jima ajiye ba,a shiganta.
Dama kina da mota shine baki zo dashi ba sister naga ba zama zanyi a nan ba kuma bansan irin
masaukin da zan sama ba idan nazo.
Zance dai shirin mu da ita hafsat ke nan kan wanan abin da na saya mata har take fadawa uwar ashe
ina da mota a gida uwar tace taga alaman hakan tun ranan da yazid yazo yana magana ai naji ta fadi
abinda ya tabu na tuhumi hakan.
Kinganta nan dama na fada maku akwai abubuwan da bamu sani ba da yawa akanta kawai dai don bata
da rigimane inna .
Jiya nake jin ashe Abbun nan da take yawan kira ba mahaifinta bane na ainihi ashe iyayyenta suna
saudiya da zama .
Haba nikan naga tayi min kama da diyan kwara sosai wallahi ni dai ina jinsu ban kuma yi niyar fadan
komai ba bayan hakan.
Mafalkin da nayi a daren sunday washe gari monday na fita aiki da safe saidai zuciyana yana da
yanayina a ranab ina jin wani iri.
Office din mu na nufa da dan sauri ina rataye da dan karamin bag dina baki sai kuma wayata da naji
tana ringing na dauko Asmau ce ta kirani tana sheda min zasu fara exam a ranan nayi mata fatan alheri.
Na mayar na dago kai da zuma shigewa idona ya saukan kan fuskan da ba zan taba mantawa ba ko a
mafalki na ganshi kuwa balle a fili .
Dan murza idona nayi na dauka gizaune idona yayi min tabbas shine dai nagani ba kama bane tsayin
nan nasa yana nan yayi wani irin haske da kyau.
Saidai a cikin tarone don shigowa na naga motocin presidential a waje har yazid na fadin yau gidan
naku har da bakin shugaban kasa gareku.
Mam Bashir na furta a bakina a hankali cikin mamaki kamar in rugu da gudu zuwa gareshi wata zuciya
tace min ke din ?
Zan taka zuwa inda suka shiga sai kuma wani zuciya ya gargadeni da baki da zuciyane ke Aeesha har kin
manta da kashedin da akai maki dashi ?
Kawai saina dake na shige office din mu madam zebeth nagani zaune a cikin fara,a tunda na karaso ina
gaida ita .
Sai ta tare ni da fadin na makara gashi an tashi yau monday da baki daga USA kan signal din da muka
tura masu ranan friday.
God so kind abin yazo muna da sauki yaron dake claiming din shi dan Nageria ne yanzu an gano karya
yakeyi shi dan Rwanda ne ashe.
Gasu dai can suna kara meeting da IG namu yanzu kokarin wucewa nake in zauna don kafafuna basu
daukana nake ji a lokacin.
Itako sai fadi take wanan abin ba karamin daukaka ya jawo muna ba miss Aysha ta sanadin ki.
Thank god da irin tellent din da Allah yai maki a kwakwalwanki da wanan shekarun naki kike da wanan
kaifin basira haka ?
Nagode na fada na a dan gundure ina kokarin wuce inda zan zauna sosai na mayar da hankalina ga
aikin gabana a wajen .
Sai bayan kamar awa daya da shigowana naji mrs zebeth take sheda muna za a hadu a babba taro na
ma,aikatan ta fadi sunan wa yanda zasu halarta harda sunana a ciki.
Sam banda niyar tashi saboda nasan dole zamu hadu dashi awajen hakan yasa wanda ta fada din suka
fita zuwajen suka barmu a katafaren dakin computers din mai dauko bayanai daga ko ina a fadin duniya
da kasa baki daya.
Don ba karamin tsara wajen akayi ba don a nan zaka binciko komai kan abinda ka iya kai da koma a
cikin duniya da yake wajen rabin mu sun fita zuwa wajen taron.
Sai wajen yai shiru don bamu da yawa a zaune a lokacin kaina na mayar awajen fitar da wani zargin
yanayi da ake saran zai iya aukuwa ko a,a ina zakula yuyuwanshi da rashin yuyuwana ta cikin bayanan
computer din.
Kamshin turaren nan dai nasa da yake amfani dashi a baya hong kong guy shine ya daki hancina lokaci
guda.
Wanda rabona da jinsa tun wasu watani baya ko kuma shekara a yanzu rabon da naji kamshin irin
hakan sai ko yanzu daya baiyana a gaban kamar a mafalki.
Wani yanayi na daburcewa na kara shiga a hankali na dago kaina a dan rikice na sauke a kanshi yana
tsaye ya tokare bayansa saman table din tare da harde hannayesa waje daya ya zuba min ido yana kare
min kallo kamar a mamaki ?
Tare dashi MD din mune a gefenshi amma a can dan nisa kadan damu shiya tsaya cikin dakewa da
basarwa na matse fuska na furta barka da zuwa sir a takaice gareshi.
Ido naga ya lumshe yana rausaya kai cikin kasaita kafin ya furta ya kike ya aiki na amsa da lafiya sir don
nasan yai min kashedin kiransa da hakan a baya.
Bana son sir din nan please ki kirani da Man Bash dina ko mam bashir yadda kowa yake kirana dashi ya
fada min wata rana a office dinsu sai naji yace .
GF fushi kike danine wai ?
Na dan dago kai na kalleshi sai kuma na dukar da kan da sauri don irin kallon kurullan da yake min a
lokacin zakice a ranan ya fara ganina yayin da kallon nasa kai saukar min da kasala a jikina.
Ganin na kasa bashi amsa yanayina kuma ya sauya naji yace don ga alaman hakan nan na gani a fuskan
ki idanunwanki sun nuna min hakan a zuciyarki.
I know you GF meya faru da har baki farin cikin ganina a yau gaban ki, ko don ban sanar dake zuwana
bane a yau din kike wanan daure fuskan gareni ? .
Dan guntun murmushi na sake a fuskana tare da fadin ai na gaida kai sir ya aiki ya mutanen can still
yana min wani irin kallo har lokacin da ba zance na meye ba.
Saida ya nisa naji yace lafiya kalau GF ya aiki i hope wajen yayi maki daidai da mafalkinki ko ?
Tuno da abinda yasa yace min hakan nayi lokacin da nake zayyana masa mafalkim tayuwana a kan
karatuna a baya.
Ba matsala sir komai daidai yake tun tafiyanka nagode don nasan da ga garekane wani abin tunda
Allah ya nufa kaine kuma sanadi.
Murmushin abinda na fada yayi kafin yace na dan fahinci hakan don nagwada kin kuma kinyi pass saura
muji abinda zai biyo baya .
Kai na dago na sauke mai kallo cikin mamaki dana kasa boyewa don jin abinda ya fada nace still kuna
amfani dani din zaka komayi har yanzu sir ?
Kamar yadda mallam salman ya fada bayan tafiyan ka kumana yarda da kayi amfani dani a lokacin karo
na barkatai cikin rashin sanin hakan ?
Ya katseni da fadi Salman ?
Salman ya fada maki wanan yaushe hakan ya faru akan me nayi amfani da daman ki yes ya fada kuma
na yarda da abinda ya fada din .
Sir MD ya ambata daga bayanshi ya zo ya rada mai wani magana a kunne ya gyada kai yana fadin Ok
ya dan juyo kallon inda naken zaune.
Yana lumshe ido kafin ya bude ya girgiza kai tare da fadin zan dawo gareki ina da wani dan uzuri a
yanzu bye sai ya juya har ya soma tafiya muryana ya sauka a kunnena da.
No way na fada saboda salman ya fada min komai Auwal shedan hakan ne a gareni don na sanar dashi
komai a lokacin .
Dan ja yayi ya tsaya kamar zai juyo gareni sai kuma naga yaci gaba da tafiya abinshi cikin kasaita md din
mi na binshi a baya.
Kamar in kurma wani ihun takaici naji a lokacin don ji nayi a raina kamar kada ya tafi ya tsaya muyi ta
muharawaran dashi har abada amma ina hakan nima nasan ba mai yuyuwa bane a lokacin.
Nan ya barni da tunane a zuciyana dama yakan shigo nan ke nan to waishi wani irin aikine yakeyi haka
na komai da ruwanka ko ina ake ganinsa ?
Ban bari an dawo break dani ba titi na nufa na tare taxi sai gida don wani zazzabi naji yana neman
rufeni lokacin badon kamahin turarensa daya manewa jikina ba nake jinsa har lokacin don dan tsayawan
da yayi a kusa dani da sai ince mafalki nakeyi bashi nagani ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[9/11, 10:16 PM] Zainab Idris Makawa Writer: JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
4️⃣7️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ONLINE TRAINING!*
*ONLINE TRAINING!!*
*ONLINE TRAINING!!!*
*Are you looking to level up your game with traditional spa?*
Whether you are married woman, bride to be or some one who loves to master the art of *traditional
spa*, *natural aphrodisiac* and *Traditional incense* asalin kamshin shuwa look no further in this
article *@sady_aromamist_and_spa* have got you covered
Imagine you know all the ingredients used on your skin to moisturise, nurture and revitalise it, *intimate
confidence* and a good long-lasting Traditional scent.
Transform your space
Transform your skin and have that intimacy confidence. Join our online training
Wa.me/9048763046
learn the connection between *skin care,* *Traditional incense* irin kamshin nan mai kama jiki and
*natural aphrodisiac* masu matukar kyau with zero side effects 😍
Sign up now to join the waitlist(https://chat.whatsapp.com/EDJan6LcDjGDrh6geC0Bk5)
Early birds 7500
Actual price 15k
Follow our IG handle for free recipes @sady_aromamist_and_spa
Start Transforming your body
Tunda na koma gida a cikin ciwon kai na kwanta nan falo wurin inna ban shiga daki ba kada damuwa yai
min yawa ya saukar min da zazzabi nayi hakan.
Jefi jefi muke hira da inna da Addah murja da