Chapter 3 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   3 / 109

6K to 9K   out of 326.5K words

damuwa da tashin hankali.

Balle a shekarun da nake lokacin ya kamata in fahinci wani abu yana damun Ammah din a lokacin kuma
koma meye ba karamin abu bane wanan.

Zubewa nayi akan gwiwana ina fadin Amma saboda nice kike kuka ko nice bacin ranki a yanzu na sani
sani itama ta sani don tasan haka zai faru ta gudu ta barku dani kuna kumsan bakin cikin da ba laifin ku
bane ya kawosa.

Wani irin kallon mamaki Amma din ke mun a lokacin don bata taba zato ko tsamanin jin makamancin
hakan a bakina ba don bata taba tsamanin har zansan ba ita ta haifeni ba.

Ga irin nata hikimar fada sosai ta hauni dashi tana fadin wani zancen banzane haka nazo ina mata in
tashi in bata wuri tunda bansan meke damunta ba in barta da abinda ke samun zuciyar ta.

Simi simi na mike nima ina sharab kwala zuciyana a cunkushe ji nake dama na mutu in huta da wanan
bakin ciki da nake gani a rayuwata tun ina kankanuwa dani haka .

Itama Ammah din fitowa tayi tana fadin in bata aikin in wuce islamiya kada in makara hakan yasa na bi
umurninta na shirya na nufi islamiya.

Mai karatu da zaki hadu da ire iren mu diyan watsin kano da ake haifowa a saudiya a watso nan gida
Africa a jibgemu zakiji labarin dayafi nawa daci a kunnen ki
Don saikai da hakan ya shafa kasa abinda kake fuskanta daga gida da kuma wajen jama,an gari don kiri
kira za a nuna maka rashin gata ko wani cin fuska a bainan jama,a.

Haka na nufo makaranta na samu hat an soma karatu ka,idane ga duk wanda ya makara irin hakan a
hukuntashi a kwaini da tsoron bulala duk da ba wani bulala bane mai yawa biyune zuwa ukku.

Saidai nayi sa,a ina isowa malamin namu ke fadin yau ya akayi kika makara nan na marairaice ina fadin
mahaifiyatace bata gari natsaya aiki na makara.

Karyana ya karbu don cewa yayi ban sanki da halin makara ba don baki da wasa shige ki shiga ciki har
da dan rusunnina ina godiya na shige da sauri cikin ajin na jona tare da sauran yan uwa akaci gaba da
karatu dani.

Koda muka taso na iso gida na samu har Abbu ya dawo yana waje yana yan gyare gyren wurin da suke
zama karba naje yi da sauri yace barshi nana shige ciki ki huta kinji.

Ammah na tsakar gida tana kawar da kaya nayi sallama idona kyam a kanta ina karewa yanayinta kallo
tare da gaida ita da kallo.

Cikin sakin fuska kamar ba ita na bari cikin wancan yanayin na damuwa ba tace Aeesha kin dawo ke nan
ya hanya na amsa da lafiya Ammah .

Ki dauko ledan can ki bude akwai dan tsaraba dana sayo maki a hanya da sauri na karasa ina fadin to
mama na karasa wajen ledan.

Na jawo ledan na kawo gabanta tace bude ki diba mai isan ki kije kici na duka na fara bude ledan da
dan saurina ledan yalo na fara cirowa cikin murna da ganin yalo don ina son cin yalo arayuwata naci
gaba da tona ledan nan ma naci karo ayya soyayya da gyada suya ruwa ko wani kuli daya na dauka sai
yalo guda ukku.

Na tura ledan agaban Ammah ta dago ta kalli hannuna kafinta maida kallonta ga ledan tana fadin kara
mana donki na sayo kinsan malam in yayi ya debe yalo kawai a ciki.

Nace Ammah bari inci wanan in Abbu ya dawo ya diba sai inzo in kara anjima batayi magana ba kai ta
kawar daga gareni kawai Abbu bai shigo gida ba saida yazo daukan abincinsa.

Bayan ya shigo din ina jinsa yana fadin ni zancen nan ya daure min kai mutane yanzu basu da tsoron
Allah a zukatansu kiri kiri ku dannewa mutane hakkinsu saboda wani dalili naku can dabana addinini ba
sai zalla son kai.

Naji Ammah tace ka barsu kawai ai inba nan akwai can zasu bamu inda basu dashi hakki dai kowa
yasan namune don muna da iko a acikinsa.

Ba wanan bane damuwana ba malam yadda suke muna bugun kadanya baki dayan mu damu muka
kashe mahaifin mu saboda bakin cikin dakin mu har mahafin mu ya mutu ai.
Wanan ba hujja bane Amamatan koda hakan gaskiyane kuna da hakki akan dukiyasa ai abu daine son
kai da rashin imani yaiwa mutane katutu a zukata yanzu.

Idan ita nana bata kusa ku baku kusane ko ance kada aba diya mata hakkinsune ?

Dama nasan komai dadewa sai irin hakan ya faru don mutane yanzu kiris suke jira su samu dama saisu
fake a nan su zallunce ka don zalunci yanzu ya bar birni ya koma ga mutanen kauye garama na birni suna
jin wa,azi yanzu daidaikune marasa imani kowa yana tsaye yana neman na kansa.

Nana dai komai daren dadewa muddin tana raye zata dawo kasan nan wata rana dole ko su fito da
dukiyan nan kamar kada ya fadi hakan naji Ammah din na fadin.

Kaiya malam da zata dawo gida aida yanzu ta dawo din haka dai ta zabawa kanta rayuwan nisa damu
naji yana fadin kaiya nakan rabaki da irin wanan zance Ammah .

Idan haka ta zabawa kanta me zakice ga wa yanda sukayi sanadiyar fitanta gida tun tana
kankanuwanta ko shima duk har lokacin abinda ta zabawa kanta ke nan a rayuwa.

Sam banganin laifinta har gobe a idona don yarinyar nan ba itace ta jefa kanta cikin wanan halin ba kiyi
tunanen hakan ko wani lokaci abin saidai istigifar kawai za a yi don shiya dace kawai yanzu.

Gareku iyayye masu tura diya aikatau kada kuce baku da kamishon duk halinda yarinya ta shiga ku
Allah yaba amanan rikonta ba wani ba.

Yalon dake hannuna nake zumudin ci naji kamar ina taunar tsakuwane a bakina lokacin don yanayin
dana shiga a lokacin.

Saboda zargina ya zamo gaskiya duk abinda Ammah kewa kuka bai wuce zancene daya shifi mahaifiya
ta wadda ta kawoni duniya ba a lokacin.

Muryan Ammah ce ke fadin Aeesh me kikeyi a cikin daki daba zakizo ki dauki abincin ki ba sai yayi sanyi
na fito jiki a sanyayye ina fadin na koshine Ammah.

Dagowa tayi ta kalleni kafin tace har me kikaci kafin ta rufe baki nace yalo ta tabe baki tana fadin yalo
abincine banda shirmen ki nidai dauko min kwanon can ki mikawa tabawa tsaraba.

Kwanon data nuna min din na dauko nakawo gabanta ta bude ta diban masu lokacin na dauka zuwa
gidan tabawa din dashi tunkan na shiga nake jiyo hayaniyarsu don haka sukesu da haniya kamar gidan
dambe ko yaushe.

Tana zaune tana raba abinci nayi sallama tare da gaida ita na mika mata ina fadin Ammah tace na
kawo maki yan tsarabanta tace dazun nake jin ai ta dawo a wajen yaran nan.

Juyewa tayi cikin wani kwarya dake gefenta tana fadin ai zan shigo yi mata sannu da safe ki gayar min
da ita da dawowa na amsa da to na juya na fito kawai.
Anan waje din na wuce su Abbu sunata hayaniyarsu ta maza akan siyasa kamar fada da yake akwai
duhu a lokacin ban tsaya gaiyar dasu ba na shige gida ina mamakinsu.

Ammah na daki lokacin don haka daga kofa na tsaya na fada mata nadawo da sakon ta bawa din na
juya zuwa dakina.

Kwanciya nayi don banda katabus a lokacin banda tunane da ba amsa da zuciyana ketayi akan zancen
daya shafi mahaifiyata din.

Wace fuskata yake min tsaye a hotonta dana gani wanda ban gajiya da kallo a ko yaushe ina faman
ayyana abubuwa da yawa a zuciyana game da ita.

Ina kwanciya naji Abbu ya shigo yana fadin kinga ikon Allah ko hadarine aka hada tako ina garin nan da
alaman bana ruwan sama zaiyi saurin sauka garemu insha Allahu.

Nima yanzu nake fadar haka a raina ai ganin yadda ko ina walkiya kawai ake sakewa sama makin ya
shiga daki anan suka zauna suna hira a zatonsu nayi barci ko a lokacin.

Tiryan tiryan Ammah din ke koro masa duk yadda sukayi acan din da abinda kowa ya fada akai sai
faman fadin umm,umm ikon Allah dama shirinsu ke nan Abbu ke fadin.

Kafin naji yace abinda nake so dake shine daga yau ki kawar da idonki acikin wanan zance don Allah ku
bar masu suje suci in zasu iya in ba yau akwai gobe ai a wajen Allah.

Kin ganni nan Ammah banson fitinan daya shafi gado ko kadan badai sun sayar da wajen ba to kuyi
hakkuri kusa masu ido kuga ikon Allah ai inku matane suna ganin baku da yadda zakuyi akwai maza a
cikin ku donshi dayyabu ba zai yarda ba haka kuma ba,a sab abinda gobe zai haifar ba ai ga bawa.

Jikina ya kara sanyi da zancen su kamar ranan haka na kwana banyi barci ba duk iskan da akayi har aka
gama ba ai ruwan sama ba idona biyu.

Haka na shirya washegari na fita zuwa school kwana biyu sai rama ya shigeni na fara ramewa a tsaye
don damuwa dana saka kaina.

Saukin abin karama nake a lokacin amma ibada ya shigeni sosai a zuciyana haka nake fitowa a tsakar
dare cikin sanda nakan fito nayi alwala in raba dare ina gaida Allah ina neman daukaka a wurin ubangiji.

Yadda malaman islamiyan mu sukr koyar damu a kullum wanan sai banyi wasa da hakan a rayuwana ba
na rike hakan sosai a zuciyana duk da bansan amfani hakan ba gareni.

Aeesha nayi firgigit ina dagowa dagawa tare da kallon Ammah din ina fadin na,am Ammah itama kallon
mamaki take min a .

.

Keko me kike tunane haka har kira ukku bakiji ba lafiyan ki kalau kuwa yar nan tunfa dawowana naga
sauyi a gareki kardai wani abu ya faru dake a bayana kika kasa fada min Ammah din ta fada.
Cikin damuwa da kulawa take min maganan tare da maida hankalinta gareni lokaci guda nace cikin
sauri Ammah wallahi ba komai daya faru dani bayan ki .

To meke damunki haka yar uutana yaki zo nan ki fada min ta fada tana nunamin kusa da inda take
zaune a lokacin.

Hakan yasa na karasa ina sakin hawaye nace Ammah a cikin muryan kuka sai kuma na kasa karasa
maganan dana so fada saboda tuna gatgadin da Abbu yai min kafin ya ban tarihina din a ranan.

Hankalinta ne ya tashi gashi kuma ina fadin ba komai saina fake da fadin mafalki kawai dai nakeyi akan
wata mata.

Mata kuma na gyada mata kai wace irin matace haka kuwa nashiga uku ni Ammah nidai inba manya
bace ta sa min ke gaba haka ?

Bari malam ya shigo ya bamu hayaki ayi insha Allahu inkin tirara ba zaki daina ganin ko wace muguwa
ba cikin mafalkin da yardan ubangiji.

Haka kawai ban damu da dan kowa ba balle wata muguwa tasa min ya a gaba don hassada da bakin ciki
kurwanki kurrr wallahi.

Sai ta jawoni tana shafan kaina tare da tambayana kanki dai bai ciwo ko na girgiza kai alamam a,a
gareta.

Nayi kukana ma,isha a saman jikinta kafin na tashi na fara aiyukana nagida don kada ta kara jefa kanta
cikin firgici.

Da Abbu ya dawone take fada mashi shidai murmushi yayi ya dauko hayakin ya bata ta tukaka min ina ji
ina gani ba yadda na iya da Ammah don nina jawa kaina hakan a lokacin.

Abbune ya zaunar dani yana min fada akan na natsu na cire tunanen komai a raina a yanzu in dai
mayar da hankalina ga karatu in samu inci jerabawana yayi min alkawarin ina gamawa insha Allahu gaba
zai kaini in karo karatu gaba da secondary da yar gidan malam iro ke zuwa.

Wanan magana da mukayi da Abbu ya karfafa min gwiwa yasa har nasake na koma normal na watsar
da zancen Nana a zuciyana ban mason in tuno da inada wata mahaifiya bayan Ammah.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[7/25, 9:54 PM] Zainab Idris Makawa Writer: JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

00️⃣44️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Duk wanan abindake faruwa azaton Ammah Aeesha bata sanda zancen uwarta ba duk ko da hannunka
mai sanda da Aeesha din ta dinga munawa uwar nata amma.

Hakan yasa dauke kai da zancen wata nana can a yanzu ta mayar da hankine kawai kan karatun da
Abbu ya kwadaita mama zata gaba da secondary ta karo ilimi.

Dama ta dade tana burjn hakan a ranta sai gashi yanzu Abbu da bakinsa ya kwadaitawa Aeesha din
karatun a yanzu duk da ita yarinyar tasan abin yafi karfin Abbu din a yanzu.

Don karatu ba wurin zuwan dan tallaka bane ba irinsune ke zuwa karatun boko ba don na diyan masu
hali da fada,aji acikin kasa.

Ance kwadayi mabudon wahala donko na kwadaita da zancen wanan karatun dashi nake kwana nake
tashi tunda Abbu ya fada da bakinsa nasan da wuya bai cika min wanan alkawarin ba.

Manya sunci da alkawari ga yaro gara kayiwa babba shimai fahinta ko hakan bai yuyu ba yasan kayi niya
Allah ne bai bada ikon cikawa ba.

Amma shi yaro har ya girma yana rike da wanan alkawarin a zuciyarsa bai taba mantawa da wanan
alkawarin a rayuwansa.
WANI GIDAN KUMA



Matar gidance a zaune takewa wata mace baka maidan jiki kitso sana,ar wanan mace ke nan a wuni zata
kitsewa matan unguwarsu kai a dan bata kudin da zai rufawa rayuwansu asiri a kulum.

Kitsone da ake kira da kitson hannu na gargajiya na kasan hausa ko ince namu na yan Africa da
yawancin matakeyi a kansu.

Ita wanan mai kitson tas zata tsuncewa mutum kai ko waya ga kanka saiya tambayeka a ina akai maka
wanan kitson wanan yasa take samun kasuwan sana,anta na kitson saboda matane na manya da yan
kwalisa da suka amsa sunan su a gari suke zuwa irin wanan kitson duk daba banbanta kudin kitsonta
takeyi ba amma don jin dadin kitson zasu iya daukan kudi mai yawa su bata duk da hakan bata fasa yiwa
masu karamin karfi kitson ba a daidai kudinsu suma.

Don kina matar wani idan kinzo kin samu koda yarinyace karama akan layi wanan ba zaisa taci maki
layinki ba na kitson saidai ki tsaya akan layinki har azo kanki.

Mace ta daban ita dukko da yawan surutu da akansan masu kitso dashi amma ita wanan kamar hakan
sa,an kitson tane don idan ta kama kai bata taba magana.

Saidai su yan kitson su yi ta hiransu suna zuba ana gulma wacan da waccan koda ba a san mutum ba
don daukanwa kai nauyi za a zauna a tofa miyau baki a zance.

Amma maman Aimana tana zaune gum da bakinta tana faman kwashe masu kawunansu tas in an
gama a dunkule dan alherin da aka riko mata a mika mata a asirce.

Yauma dai matane yan kwalisa sunkai bakwai akan layi gidan ya kaure da hirarakinsu daga can wata
daga cikin matan ke fadin ke,,,,

Sukai juyo suna kallonta take fadin yanzu naga wata ya a karshen layin nan saida gabana ya fadi don
kyauwonta.

Wata take tambaya halan wacece tace nima dai ban sani ba nan ta barni ina kallo zakice balarabiyace
kai duk yadda akayi dai tana da hadi dasu saidai abinda ya daure min kai shine shiganta irin namu na
hausawane zani da riga da dan kwali.

Kila yar buzayece dai inji wata wata kuma ta karba da fadin kema ai kin sani ai duk zancen nan da
sukeyi maman Aimana ta gane wa suke nufi amma batayi magana ba a lokacin.

Aeesha cefa kila ta gani Aimana dage tsaye a kofan dakinsu ta fada matar ta dago tana fadin kin ganeta
ke nan tace a unguwar nan suke aida zama.

Yar buzayece ko sai lokacin uwar ta dago tayiwa yar kallo daya hakan yasa taja bakinta tayi shiru don
kallon warning din da uwar ta jefa mata a lokacin.
Duk da wasunsu sun gane hakan amma basuyi shiru ba don wace ta fara maganan take fadin gaskiya
duk da ina mace saida na tsaya kallon wanan yatinyar yau.

Wata kila yar wani mai kudine irin matan da mazan mu kan je niger su auro din nan tazo ta haifa
mashisu haka dama abinda mazan mu keso ke nan ai.

Gidan kitso ance gidan rakwato gidan tsincen mata anan zakiji labarin auren mijin ki ko ko zancen
tarihin kishiyarki dama duk wani tarihin makiyin ki indai a gidan kitsone.

Daya bayan daya take kitsewa matan kansu suna tafiya har akai ta karshe ita mai yawan zuba din nan
ta kwashe mata kai tas tana sauri don ka,ida kitsonta karfe biyar zuwa biyar da rabi.

Zata kakabe gidanta tas ta tsabtace ko ina yadda gashin kan matan kitsonta ba zai takura masu a
girkinsu ba ko wani abinci.

Wanan aikin Aimanace yanzu data girma ta saba da hakan don a cikkn hakan ta taso bisaga irin
tarbiyan da uwar nata ta dorata a kai ke nan a kullum.

Saboda ga kitso rufin asarinsu yake fitowa inda uwar ke samu tana masu yan lalurorinsu harma dana
gida wani lokacin duba ga rashin karfin mijin da Allah bai hore masa ba sai dai shima bai zauna haka ba
don yana da sana,ar yinsa da yake daukan nauyin iyalinsa dashi.

Saida suka kare aiyunkansu yara sin zauna cin abinci maman ta fito daga daki tana fadin Aima ashe ba
nahanki zuwa inda matan nan ke taruwa ba.

Ban hanaki tsoma masu baki a zancen da zasuyi ba a cikin gidan nan ko kinga sa,ankine a cikinsu ?

So kike kija min magana kin ganinan neman kudi da bukatansu ya kawosu wurinan da badon haka ba
ba zaki gansu gidan nan ba donsu duka ba sa,oin yin mu bane kin sani.

Donshi nake kama baki akoda yaushe kan ko wani irin zance da zasuyi a cikin gidan nan daga yau nayi
maki kashe din karshe akan irin hakan.

Kan yarinyar yana duke bata dago ba muryan uban ne daya shigo yake fadin meya faru yake jin muryan
ta hakane don ita ta

3 / 109