Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
don
shine na fito a yanzu din daba zaka taba ganina ba kuma again tunda na gane yaudarata kukeyi ashe ?
Sai naji yace dani dakata Aisha ki saurareni don kina kara ban mamaki a cikin zancen nan a yanzu .
Yadda yace din dani na daka nayi cikin kura masa ido inji me zai fada min lokacin sai naji yace zancen
yaudara ko wani abu a tsakanin mu kinsan wallahi babu shi alkawari na daukarwa kaina da hakan.
Kema kin sani tun farko wallahi balle shi oga bash a rayuwana tunda na sanshi ban taba jin wani
mahalukin da yace bash ya cutar dashi ba tun tasowan mu har yau din nan sai ko yau a bakin ki da kika
fadi haka har naji kuma ban yarda ba.
Duk da nasan ba halinki bane akasi aka samu ko a yanzu din sai dai abinda nakeso dake shine ki
kwantar da hankali don Allah.
Har zuwa lokacin da zamu gano gaskiyar wanan maganan me Salman ke nufi da hakan da yayi a gareki ?
Shiru na danyi cikin nazarin zancensa kafin in nisa nace abin mamaki wanda ban tabo tunane ko zato
ba saiga malam salman a gabana yana fada min wayan nan maganganun haka ?
Audi ai bai fadawa talle hakan dake dashi dani da kowama yasan waye Oga Bash yasan mutumin
kirkine akan meke zai damfareki karamar alhaki a dake wajensa .
Idan ya damfareki Aisha yaci riban me ga yin hakan idan yayi maki yaudara ?
Yaja wani huci yana fadin lalai Salman inda wani manufa ko wani ya turoka ka tafka babban kuskure a
nan wanan karon don har Man bash yaji wanan akwai rigima a tsakaninsu gaskiya .
Wallahi koda ya kirani jiya yana fada min sakon nan zai iso na tabbatar da kuma ya iso hannuna na
kawo maki shi don zaki bukaceshi a yanzune.
Saida nace a zuciyana lalai kina da wani kima da daraja da nauyi a zuciyar Oga Bash yadda ya ke
magana dani a jiya din.
Don haka har in kin yarda kibi wanan shawaran tawa ki bari mubi zancen nan a sannu mu gane meke
faruwa dayasa Salman yin hakan .
Amma kuma nafi kyautata zaton kamar dai wani ya turosa yai maki hakan don cin ma wata manufa na a
raba alakan da ake tunane akwai shi tsakanin ki da Oga Bash.
Na katseshi da fadin wace halakace banda kyautatawa da mutuncin dake tsakanina dashi da har za a iya
turo salman yai min hakan.
Yace ke kike ganin hakan Aisha kibar abinda baki sani ba akan baki sanshi ba tunda ba,a taba ganin ya
kula wata ya mace ba a cikin garin nan saike a karo na farko.
Ai koda ya kulani Auwal tsakanina dashi mutuncine kawai da girmamawa dan bai taba nuna min wani
alaman so ko wani kalman banza daga gareshi ba.
Asalima duk zan shiga wurinshi shi malam salman din yana a office din mafiyawan lokutan suna tare
koda nake shiga din .
Amma sai cewa yayi dani wai daga taimako na dauka man bash yana sona ne idan haka nake tunane na
yaudari kaina.
Har Inma wani abune nake tunane ai Man Bashi din ya biyani amfanin da nayi mada don haka kada in
sake nemansa da sunan son jin labarin Bash a bakinsa.
Alhali ni kuma naso in fada masa zuwan wasu manyan mutane da sukazo gidan mu wani rana suna
tambayana wai lamban Man bash suke nema da ake samunsa a waje na ?
Wanan naso fada masa amma saiya tare da wanan kalaman marasa dadin ji daga bakinsa har yana
ikirarin cewa haka mu mata muke da munga wani dan oppotunity yanzune sai mu lakewa mutum don
kwadayi.
Sunana ya kira da Aisha na dago na kallesa kafin yace kiyi hakkuri don Allah zanyi bincke kan wanan
zancen .
Do min ina ganin akwai wani abu a kasa wanda bamu sani ba koma meye zamu sani insha Allahu nan
gaba.
Don maganan nan da kikayi a yanzu cewa anzo wajenki neman number Oga Bash yasa na danyi tunane
su waye zasuzo gidan nan wajenki neman layinsa.
Waya nuna masu gidan ku har sukazo dole akwai dai akwai akwai abinda ya faru har salman din yayi
hakan gareki?
Yanzu kiyi hakkuri don koshi bash din banson yayi saurin fahintar da matsalan saboda yadda suke dashi
salman din don banjin yasan da wanan zancen ayanzu .
Ya juya zuwa wajen mota da sauri ya bude baya ya fito min da wani babbab jakka haka irin na kasan
waje din nan da ake tura sako dashi .
Ya dawo inda nake tsaye yace ga wanab in kawo maki kayan aikine a ciki zaki bukacesu a yanzu wajen
da zaki iya bayanin da yai min ke nan.
Murmushi nayi na kalli jakkar a lalace nace Auwal na fada maka sabon yaudarane wanan kuma me zan
bukata dani ban sani ba sai shi zai aiko min tun daga can ?
Ki karba don Allah Aisha kada daman nan ya wuceki oga dai ba zai taba yin abinda zai zubarwa da
mutuncin gidansu ba kin sani.
Wanan kalamin yayi kama dana Asmau yasa na karba sai naji abindake ciki yana da nauyi kara kallon
jakkar nayi nace kace nagode na juya na shiga gida kai tsaye.
ZAINAB IDRIS MA
[9/2, 5:17 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [8/15, 07:30] Seenabu Makawa: M/C COLLECTION MAKAWA
COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES, BAG,
COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER
KIDS,FASHIONS etc
LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
3️⃣8️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1ftp
Duk da Auwal yace dani urgent ne sakon hakan baisa na bude a ranan ba saboda ina zargin wani tarkon
irin yaudaran nasu suka hada min kuma.
Takaicin hakan ya hana in bude inga meke cikin jakkar alokacin saboda gudun sabon yaudaransu gareni.
Hakan yasa sai washegari da asuba bayan na idar da sallah lokacin ba wanda zai iya shigo min daki na
jawo jakkar na bude.
Idona ya fara tozali da na,auran bincike irin ta siri wanda ban taba mafalkin mallakanshi a duniyan nan
ba saidai ingani a wajen wani kila balle a yanzun da nake daliba ?
Yau sai gashi a matsayin nawa wai cigaba nayi da zaro abubuwa duk na,uran ukku wanda zai
amfanenine wajen aikina da zanje koyo har Abuja da schoo din mu ta turamu yi.
Sai kuma sabuwar waya dal da hannuna ya dauko karshe wayace ta gaba da wanda nake riko yanzu a
hannuna can a cikin kwalin karamin na,uran na tsunci wani envelop a cikinsa da rubutun Man Bash a
saman takardan ido na tsura rubutun nashi na dan lokaci ina tuno abubuwa da dama a zuciyana hakan
yasa.
Jikina na rawa mika hannu na nake kokarin bude takardan acikin tsoro tare da fargaban abinda zan iya
samu rubuce a cikin takardan.
Ina tura hannu don zaro takarda sai na zaro kudi suka zuba daga ciki irin kudin kasashen wajene sabbi a
mike cikin takardan da nake zaton wasikace da farko .
Duk da a lokacin bansan darajan wanan kudin ba ina dai ganin su sometimes a photuna ko a film don
haka nasan abune mai daraja sosai.
Ina kai ido sai ya sauka ga yar farar takardan dake a nade tsakiyan kudin na dauko na bude nan na fara
ganin bayanin komai dake cikin wanan jakar ya tsara min yadda zanyi amfani dashi har kudin dana gani
din saida yayi min bayani akansu.
Kudine da zanyi amfani dashi wajen cin abinci zirga zirga da sauran abinda zai saya inyi daraja a gaban
kowa koda wajen aiki ba,abamu alwances ba a ma,aikatan ya kasance ni ina da kudi a hannuna haka yai
bayani a gajarce.
Bayan na gama karantawa na koma na nikesu yadda na samesu baki a laikum ciki da mamaki fam a
zuciyana.
Don haka lokacin haka na koma gado na lafe kwance ina tunane a kan halin Man Bash din.
Zuciyana fam cike da tunanen shi wanan Bash din wani irin mutum ne wai haka da bahagon rayuwa
sunan wani littafin makawa.
Monday da safe sako ya shigo min na accepting letter dina da cewa next week coming zamuyi
reporting a ma,aikatan don fara training din mu a can din don haka bani da wani dogon lokaci yanzu.
Dole na fara shiri saidai banson barin garin ba tare dana tabbatar da fara karatun yaran antyna ba da
yanzu na kwallafawa karatunsu rai kuma ina cikin process din zancen tafiyan yazo min.
Don haka ban bar gari ba saida na tabbatar da yaran anty sun fara karatu samira taje sokoto kwananta
biyu ta dawo da takardun su kananun na jefasu primary din da Sama,ila ke zuwa ta gwaunati .
Inda Samira ta samu gurbi a COE amma late addimition muka samu ita kuma Asmau zata yi jerabawan
waec ta maimaita shekara mai zuwa inda zata dinga zuwa makaranta daukan darasi.
Bayan na gama dasune na fara shirina na tafiya abuja a gagauce ba wasu kaya mai yawa na dauka ba
dan akwatina na tsakiya shina zuba tufafin da zanyi amfani dasu.
Sai kayan amfanina a cikin karamin kuma na loda sauran tarkacen unders dasu mai da sauran abinda
zan iya bukata a can din.
Tafiyace wadda ban taba yin irin saba haka zanyi inama nake zuwa nidana tashi a kifin rijiya bansan ko
ina ba sai wanan garin kawai.
Mun dade da Abbu da Ammah a daren da zan tafi din suna jamin kunne tare da dorani a hanya kan
zama a bakon waje da zanje yi a yanzu.
Kowansu yayi min iya nasihan daya dace inji daga gareshi don Abbu cewa yayi shi yayi niyar kaini da
kansa har gidan yaya habib din amma yaya din yace basai yazo ba ai zan iya.
Don hakane tafiyan ya fasu dashi din yanzu ni kadai zan tafi kamar yadda yaya din yace dashi da mun
kusa sai in kira waya sai azo a daukeni duk inda nake.
A karshe Abbu ya ciro kudi a aljihunsa ya miko min da sauri na girgiza masa kai ina fadi Abbu ba sai ka
ban kudi ba duk abinda zamuyi sun bamu kudi a kansa da suka turo muna jiya a banki.
Ai kaji saukin abin naku ba sai iyayye sun wahala ba dai nikan karatun nan naki yazo min da sauki
Nanata duka duka ban kashe wasu kudi daga aljihuna ba akan karatun ki sai nake gani ke mai sa,ace
nanata.
A raina nace munyi sa,a dai Abbu Allah ya tsaya muna ya turo muna Man Bash a rayuwan mu mu duka
komai yake zo muna a saukake a rayuwa.
Zance rakiyana kamar na barin garine a lokacin saboda gaiyan yan rakiyan dana samu zuwa tasha
maryam farida samira da Asmau yar gaban goshina rike da hand bag dina a cikin damuwa.
Don hakane mutane da yawa a unguwar mu suka sanda zanyi tafiya a ranan har gareji mukaje tare dasu
munyi sa,a saura mutum biyu motan ta cika.
Ba a dauki lokaci ba sai gata cikon biyu ta iso motan ya cika don duk uban sammakon da mukayi motan
farko ta riga data wuceni a ranan.
Saita biyu muka samu a lokacin don haka ba,ama gama saka kayana ba cikon ta bakwai tazo zamu tashi
ke nan mubada kudi.
Na mika masu nawa tare da kirga wasu kudin na mikawa maryam ita da farida tace haba dai Aeesha
kada kimin hakan nace ba zaki samin albarka ba ke nan ?
Jin hakan ta karba sai kuma su asmau duk da na basu amma bai hana in kara masu ba nashiga mota
bayan adduan da Abbu yace inyi tunkan in baro gida na tawakhaltu illa,lah lahaula wula kuwatu illabillah
na shafa a fuskana sau uku.
A baya muka zauna mu mata da wata musulma da wata kabila don ta shiganta na gane hakan suna
tsaye mota ya tashi naji idona ya ciko da hawaye lokaci guda.
Har na daina ganin su sannu a hankali muke fita garin ta bangaren da ban taba sani ba a cikin kano har
zuwa lokacin da muka hau titi da kyau driver ya fara sharara gudu damu a motan.
Inda wasu na waya wasu kuma suna hira irin ta kusa dani ke nan mai bakin surutun tsiya da son a sani.
Irin mu dai sai faman raba ido nakeyi ina bin ko ina da kallo tare da karanta sunan yan kauyukan da
muka shigewa a hanya wanda nake jin sunan su.
Ta gefena dake zaune a tsakiya ta dan kalloni tana fadin you seens worried baki so barin yan uwa ba ko
haka gida yake ba dadin rabuwa wallahi ?
Murmushi na juya ina danyi kafin na lumshe idona tacigaba da waya da aka sake kiranta a lokacin ina
jin damuwa don surutun da takeyi har cikin raina hakan yasa na dan ja tsuki ina gyara zama ta hanyar
jingina kaina da gefen glass din mota.
Tana aje wayan ta juyo take fadin akwai sauran zama har yanzu shiyasa nafi son inbi jirgi don yafi min
sauki da shiga motan nan sauki .
Sai naji dayan matan ke fada mata ai don yau babu jirgine kuma tana son shiga office da safe itama ta
biyo mota.
Ban tashi ba ina dai kwance ina jinsu nayi shiru saida muka kai kaduna driver ya tsaya wai za a duba
mashi mota wanan yasa muka fito daga cikin motan .
Ina kallon yadda suke sayayyan abubuwan ci saidau ni komai ban saya ba da sunan ci a wajen a hankali
na tura hannuna a cikin jakana na dauko air pies dina na makala ina sauraren sheck albani zariya.
Inda yake bayani akan sallah don kullum ban gajiya da saurarensa shine best malamina a lokacin
wa,azin albani.
Hakan yasa nake bin kowa da ido wajen har zuwa lokacin da aka gama duba mai motan cikin abinda
baifi minti talatin ba muka kama hanya kuma.
Saidai tun a nan yanayin garin ya sauya sanu a hankali hadari ya hade ko ina bakikirin ba,a dauki lokaci
ba kuma ruwa ya sauko mai karfi haka muka iso Abuja ana lema ruwan sama.
Wanan ya tayar min da hankalina gashi ban kira yaya ba kamar yadda yace na kirashi ko matarshi idan
na kusa isowa Abujan amma don ganin ruwan saman da akeyi din yasa ban kirasu ba a lokacin.
Ga ruwan sai an dan tsagaita sai kaji ya dawo kuma dole haka na daga waya na kira yaya habib kira
biyu bai dauki wayan ba yasa na gwada kiran matarsa basira itama bata samu dagawa ba.
Ya sallam na furta a fili yasa wanan bahaushiyan da muka shigo mota daya dan kallon inda nake tana
fadin wanda zai daukekine baki samu ba ko nace wallahi.
Nima gashi ina kiran gida amma sunki su daga call din may be suna can suna barci tunda ban gida.
Shekaran jiya na bar nan Abuja naje buki kano shine na dawo yau wani unguwa zaki ke ta tambayeni
nace garki which erea nace erea ten yadda naji a bakin basira din matar yaya habib .
Sai naga ta dan tabe baki tana fadin ni gwarinpa zani ba waje daya zamu ba dana daukeki sai ga
wayana yana ringing na daga da sauri yaya habib din ne a layi yake fadin.
Aisha kun kusane nace ina tasha tundazun naga ana ruwane ban kira ba yace kinaji Basira zatazo ta
daukeki don ni ina nan nashigo Nasarawa ban kusa da gida yanzu.
Ok to yayi nagode naji ya kashe wayan shi tace kin samesu ko nace eh nagode da kulawan ki sai wajen
kamar rabin awa anty Basira din ta iso tana dan waige waige hangota da nayi yasa na fito daga cikin
motan har lokacin ana dan yayafi mai karfi .
Kwankwasa mata glass nayi ta juyo tana fadin to har zan juya na dauka ba nan suka saukeki ba ai a nan
muka sauka na bata amsa.
Ko ina akwai na Allah wani dan tashan ne ya taimaka min ya kwaso min kayana zuwa bayan motanta
muka shiga na fito da dubu biyu na mika mai yana tayi min godiya.
Taja mota muka tafi tana fadin shikan yau babu kamarsa ai yafi driver ma samun riba na daiyi mata
murmushi ina fadin mun sameku lafiya ?
Wallahi lafiya kalau Aisha yaya hanya ya kano kuma kai ina su mummy da kowa gida nace suna gaidaku
anty ya kuka dawo kwanaki kuma ?
Kai bari bari duk a cikin hausanta da harshenta keda surki da yarensu take fitar da harafinta amma ina
ganewa tsab don hausane amma fitan harafi ne ya banbanta.
Kano kan wai badai kuma yanzu ba gaskiya wanan bukin ma don na fatine naje wallahi ban iyawa da
banje ba .
Irin ginan nan ne mai hawa hawa ta tsaya gabanshi muka fito na dauki babban jakkar tawa da karamin
ita kuma ta dauko min dayan dayafi karanta.
Tana gaba ina baya da kyat na iya hawa saman na biyun da suke da kayan hannu ta sanya ta danna
bell ba bata lokaci naji ana kokarin bude kofan ta ciki.
Wata nagani mai dan buje da kitson attach akai tayiwa yarinyar yare tare da dan gusawa ta jaye naji
tace min you are wellcome tana mika hannu in bata kayan na mika mata dama a gajiye nake lokacin.
Abunda mummy gidan Rabakaya maman yaya habib ta fada min da naje sallamanta dashi na fara arba
don cewa tayi Aeesha zaki iya zama gidan yaron nan don na sanki da yawan addini.
Shiko gidansa kamar gidan kafirai yake don yan uwan matan nasa dake zaune taba agidan ba sallah ba
salati sai kafirci.
Zan iya mummy na fada a kunyace tare da nuna mata ba komai a zuciyana don yadda tayi maganan
cikin yanayin damuwa fam a zuciyarta .
To ki hada da hakkuri kije kiyi abinda ya kaiki ku rabu lafiya kinji don basira bata da dadi wallahi duk da
farfar din da tazo nan tanawa mutane na