Chapter 88 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   88 / 109

261K to 264K   out of 326.5K words

hatsabibin duniyane hjy Nasare ina tsoron lamarin magaji wallahi yanzu yarin nan yasan
yarinyar nan ko wacece amma ya sa muna ido muna fadan kalman da Allah zai iya kamamu da laifin
fadan hakan akanta.

Mami aini bakina ya mutu wallahi abu dai sai kace almara don Allah abubuwa sai faruwa suke muna a
baiyane haka lokaci guda.

Yau naso ace yaya kura tana wajen nan ta gananwa idonta abin nan da yaya zataji don Allah shiyasa
mutum da kake gani ba abin yaddawa bane dan adam .

Ka barshi kawai a inda ka gansa shine sauki yanzu mutanen nan a ganina fa sarakunane ko wasu
hamshakai da ake ji dasu a kansasu mu ina za a iya wanan wai kawai aga ya don Allah ?

Naku ke nan ai ni me zance nidake taya hauka bori in ba yau din nan dana sheda ba da idanuna ko wani
ya fada min zan musa masa kan yar nan .

Yanzu wancan din shine dai mahaifinta shine mana suka kallo baraben daya mike tsaye yana gyara yafa
mayafin daya yafa a saman tufafin jikinsa na sarauta a lokaci.

Wurin tsohon yazo gaban sa ya dan rankwafa yana masa magana a lokacin suka mike zuwa garemu
suka fara gaisawa da iyayyena Abba yana masu bayanin alakata da kowa har yazo kan Abbu da Ammah
da muke lake da juna a waje daya.

Ya gabatar masu da Abbu da Ammah tare da dan kara mashi bayani a gurguje yadda zasu fahinta.

Hannun Abbu tsohon ya riko yana sumbata tare da jefa mai addua masu zafi da akeso daga bakin
muminin bawa.

Sai kallon Abbu da Ammah sukeyi kan kokarin da sukayi na tayar da yar da basu san komai akan ina
mahaifinta yake ba.

Haka dai akai ta nuna alhinin haduwan ga juna ina lake tare da Abbu ban yarda nabi kowa a cikinsu ba
sai iyayyena dana bude ido dasu.

Ashe hakan kuma baiwa su Abba dadi ba na fahinci hakan ne daga yanayin daure fuskansu da har shi
Abba din yakai ga yi min maganan cewa bai kamata in nuna hakan ba a yanzu.

Don ban nuna jin dadi da ganinsu ba ko wani abu na nuna a fili nafi daraja Abbu da Ammah ako
yaushe.
Har yana fadin wanan ke hadaki da mahaifiyar ki ko wani lokaci zaki kuma maimaita hakan yanzu kan
mahaifin ki ?

Abbane yau kam ba don shi bane yazo yana rada min wanan zancen da maishi ya jini a lokacin saodai
duk da hakan yasha fada kasan zuciyana da kuma irin kallon mamakin dana jefa masa wanda ban zaci jin
hakan daga bakinsa ba.

Daurewa nayi na cije amma ban gusa daga gun Abbu din da yake nufi sun kasa fahinta sun kasa gane
me yasa hakan ke kasancewa dani sai laifi suke kokarin dora min a yanzu kuma ?

Ta yaya zan iya juyawa bayin Allah nan baya a rayuwata mutanen da ruwa da iska dare da rana sayi da
dama sukai tsaye a kaina har nakai yanzu.

Ko so ake yanzu da Allah ya nuna min asalina na butulcewa bayin Allah nan din naga kudi idona ya rufe
in barsu da bakin cikin akaina su fara darsa min Allah waddai a zukatansu.

Bama zan iya ba din Allah ya gani ya kuma sheda bawai ina dafe da Abbu da Ammah bane don inba
wani haushi a zuciyarsa .

A,a Allah ne shedana har cikin zuciyana haka abin yake min sai yanzune ma zancen Abba ya dan fargar
dani wani abin har na gano nufinsu na in nuna rawan kafa akan daulan da Allah ya fito dani a cikinsa.

Sai naji hakan yai min dadi a zuciyana da ubangiji bai yarda na shagala da rudin shedan na juyawa
iyayyena baya ba akan dattin duniya

Sai a yanzune nake nasu bayan sun gama guduna a lokacin daya dace ace da yana mane da mahaifansa
da Allah ya kaddaroni da yin hakan ke mai karatu dasu da muke wajan a lokacin.

Kune mutum na farko da zaku zagene akan abinda nake aikatawa din don ba zaku kawo shaukin da
mararin ganin iyayyena yasa nayiwasu Abbu din hakan ba.

To na godewa Allah da babu wanan zancen a zuciyana sam kawai dai na gansu naji dadin ganin su a
yanzu kowa yasan dani ba shegiya bace yadda harni kaina nake zargin hakan.

Yau da ace basuyi min rikon gaskiya na tsakani da Allah bane lalai da komai zai iya faruwa baiyanan
iyayyena gareni din nan to amma hakan sai ya nunawa kowansu irin rikon gatan dana samu a garesu din.

Nasan zafin dukkansu din sai dai a gaskiya na sake na zage shine babu a yanzu ban sanarwa zuwa gaba
ba a yanzu dai ina karkashin Abbune da Ammah.

A haka abubuwa sukai ta gudana daga nan aka dawo masauki a cewan su a barni zuwa safe a wajensu
saidai kafin su farga nashige mota tare da Abbu har mun zauna ko a seat daya.

Don kaina ke min wani irin ciwo a lokacin ina son samun wuri na kwanta na dan huta tun daren jiya
ban samu hutu ba don tun cikin dare muka fito zuwa masallaci .
Abbu suka kira sukai magana dashi daidai lokacin na dago kai na kallosu naga Abbu din dasu suna
kallona kaina sada a kasa yake fada masu yanzu nagama hade magani .

Amma bari ya fada min shine Abba yake masu bayani da sauri wanan ke fadin a kaini asibiti zaifi .

Allah sarki wai akan ciwon kai kawai za a kaini asibiti don samun waje hakan yasa shima Abbu din yin
murmushi ba don naso ba dole muka sauko nidasu har Ammah da zamu tafi asibitin a tare dasu din.

Lokacin da naji ni kaina saida nayi murmushi dajin hakan can mukaje suka kashe kudin banza aka
hadoni da magani muka juyo na zata masaukin mu zamu tafi amma sai naga sabanin hakan .

Wani gida aka tafi damu ashe nan ne gidansu a cikin garin makka nan kowansu yazo yake sauka a cikin
gidan daya kumshi dakuna masu yawa.

Kuma suna bayar da haya ga mahajjata wani lokacin amma saman iyasu kadai da iyalinsu suke sauka a
cikinsa.

Dakina ni kadai aka ban ita kuma Ammah da Abbu kasancewar su ma,aurata aka basu daki daya mai
kyau komai akwai cikin dakin tun daga tv fridge da sauran tarkacen jin dadi dai.

Wani abincin aka shigo min dashi dakin badai abinci bane irin namu ganyene sai kayan fruit da aka
gyara aka shigo min dasu dakin .

Tunda nasha magani nayi wanka na koma na kwanta banko bi ta kan abincin ba kuma barcine ya
daukeni don a gajiye nake ciwon kan nason ya zama min zazzabi a lokacin.

Ban falka ba sai karfe hudu na asuba ko shi don alarm din dana seta ne don tashi ya tayar dani daga
barcin .

A gurguje na shiga bandaki na yo alwala na fito don sallah nafila kada lokaci ya shige ban samuyin sa
ba ina saman sallaya zaune naji an turo kofan dakin.

Matan larabawan nan ne guda biyu don nasheda fuskansu a wajen taron suka shigo dubani bisa
umurnin mazajensu ganina ina sallah yasa suka juya suka fice daga dakin .




ZAİNAB İDRİS MAKAWA

[11/14, 9:53 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

9️⃣0️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6




Zaune take tana kallon masu wucewa ta gabanta zaka dauka hankalinta yana wajensu saidai a zahiri yake
hakan can kasan zuciyata bata bin takan mutanen dake gilmawan a gabanta.

Farko har lokacin data bar kano hankalinta ya kasa kwanciya da wannan aure tatafi don abu biyu na
farko mahaifinta daya kafe akan sai tayi wanan auren .

Na biyu kuma don kawai burinta ya cika asan ta auri mazaunin kasan waje duk da munin halittan da
Allah yai masa ta dai fita din a sanadin aure.

Saidai tun zuwansu wanan kasan abubuwa suka sauya mata wanda a farko take gani da sauki nan dai
ba yunwa ba kishin ruwa saidai kadaici dake damun ta da matsin wanan halittan mijin nata bayan haka
kuma yanzu da take cikin laluran laulayin ciki sai ya bijiro mata da zancen sana,a don ba,a zama haka a
turai baka wani abin neman kudi da zai tallafawa rayuwa.

Gaskiya dai hjy saratu ta cuci rayuwanta zatace ta kuma ha,incesu data boye masu asalin waye dan
nata mijin nata data aura mata a yanzu ?

Hangoshi tayi zuwa shagon daya tillasta mata saida ta bude shagon da maza da mata ke shigowa kitso
irin namu na nan africa wanda shi kadaine Allah ya taimaka mata ta iya a rayuwanta.

Koshi da yaya ta tsaya ta koya akan kanneta da take jagula masu wani lokaci duk da hakan bata gwaune
ba kamar yadda hannun uwarta ya nuna a kitso.

Amma dauko sallon kitson uwar nata data koya tana kwasan tsaga da tsunkea maimakon hannu yasa
suke ganin ai ita din gwanace har suke turereniyar zuwa wajen nata da yan canji suna ribibi ga makitsiya
sun samu gwana.

Haka kuma zasu aje mata makudan kudi idan ta gama don gaskiya ba laifi yafi kitson wasu da ake masu
a kai kallon sha,awa.

Yanzun ma wasu gungun maza mawaka yan black ta gama kwashewa kai suka zube mata kudi suka tafi
inda take hadawa da zanen siffan da muka koya a jikin littafan mu na makaranta ko a lokacin ta iya
zanashi sosai don da sallah tanawa mutane ana bata kudi a nan gida.

Sai gashi a can tafi cin moriyan abin yanzu bisa ga nan don zata iya cewa a yanzu tafi mijin nata samo
masu kudi ga komai da dan zuwanta kasuwa ya budu mashi abin sai sam barkah a garesu gaskiya.

Takardun hannusa ya dire mata a gabanta ya koma ya haye kujeran shagon dagerger yayin da
kafafuwansa suke lilo a kasa zakice yaro karamine a zaune yake fadin .

Ga takardan umuran namu ya fito madam gara muje umura mu gaida ubangijin mu yasan mun gode
masa kan irin samun daya buda muna a yanzu.

Kallon takardan tayi shekeke tana fadin wanan takardan ne kake ta faman gilo akansa wata da watani
aka kashe kudi masu yawa akansa.

Kallon mamaki shima yake mata yana fadin Aimana ko nawa zamu kashe indai akan lamarin ubangiji ne
ni bana ganin tsadansa matukar nasan Allah naiwa bauta da kudina .

Yanzu ke hakan ba abin alfarihari bane a gareki kije dakin Allah da zufan ki shi lamari na duniya yana
son tunawa da ubangiji a cikinsa ba mutum ya shagala akan duniya ba kawai.

Yanzun mena fada ta fada a gundure da gajiya da nasihan da yake son ya fara mata saboda shi Allah
yayisa mutum mai tsoron Allah da yawana ibada a rayuwansa.

Dama hjy kan fada tace danta shehi ne shi don yawan zama yana wazifa da komai irin na akidar da yake
bi sosai bai yarda komai na addininsa ba a zaman shi turai din.
Don hakane yake kokarin ko yaushe yaga ya tursasa mata wanan akidan nasa har abinda zasu haifa a
rayuwansu su taso a cikin hakan suma don yanzu ga shigan ciki nan a jikinta Allah ya bayar a dan
zamansu tare din yana lalaba abinsa.

Shigowan wata farar fata da yaranta mata biyu shagon ya dakatar dasu daga abinda sukeyi tsakaninsu
ta fara taron customers din nata cikin haba haba tunda a yanzu ta gwane da abin.

Kwatance matar tayi mata yadda take son a gyara kan yaran cikin dan lokaci kankani ta gyarawa yaran
kai tsab ta yi masu kwashe gida biyu manya aka dora masu ribon akai.

Kudi masu yawa matar ta zube mata saida tayi mamakin hakan akan dan wanan shirmen kitson mutum
zai baka wanan uban kudin me yawa haka gaskiya akwai bambanci sosai a tsakaninsu da yan Africa da
zakaiwa mace goma kitso a wuni baifi ka samu dubu uku ko hudu ba a wajensu.

Sai masu tsoron Allahne zasu iya zube ma kudin da zakaji dadinsa hakan yasa ta manta da bacin ran da
take ciki a lokacin har dare tana tsaye tana dan gyarawa mutane kawunansu kafin su rufe su nufi
gidansu.

Washegari bayan tagama duban takardun nasune mutum na farko dataga zata iya kira ta fadawa a
lokacin itace Aeesha don Aeeshace ya kamata ta fara sanin yanzu likafanta yaci gaba yanzu ba irin da
bane can baya don gashi har zata rigasu taka saudiya a rayuwansu duk da Aeesha din asalin iyayyenta
yan can ne amma dai ai bata taba zuwa can din ba dai.

Dolene ma ta kira Aeesha din duk da tasan ba lalai bane ta fadawa wasu hakan amma ko yayane dau
zataji zafin hakan a ranta ai idan taji zata rigata din kai dan Adam hooo.

Ina kwance barcine mai dadi ya daukeni musalin takwas na safe naji kiran waya yana shigo min hakan
yasa na tuna da wayata dake cikin jakata don kusan baida amfani a gareni tun zuwana saudiya don ban
faye ma tunawa dashi ba a nan.

Da kyar na daga na lalubo wayan can kasan jakata dake gefen gadon da nake kwance din a cikinsa ina
duban wanda ke kiran nawa a lokacin.

Aymanace nagani saida nayi mamakin hakan saidai a zatona yayin wayan nan na dauka taji cewa na
hadu da mahaifinane ta kirani don taiyi min murna akan hakan ashe ba hakana bane ita.

Ina dauka nake fadin madam Aymana yau an tuno mune ko ?

Sai naji tace wai madam ke na kirakine mu gaisa tunda ke baki damu da kikira kiji ya mutum yake ba ?

Dan murmushi na sake ina fadin haba dai ku din ne sai ayita kira ba,a samun layinku wallahi yasa ba
bar kira ai sai naji tace amma ai akwai whatsap ko idan kiran bai shiga ba ?

Murmushi nayi ina fadin afuwan please katseni tayi da fadin ke dama na kirakine in fada maki two
weeks comoing zamu shiga umura dani da maigidana wallahi ya biya muna kinsan dama ashe yana zuwa
shi sosai saudiya.
Allah sarki gaskiya nayi maki murnan hakan sosai wallahi bari ke dai Allah ya nufa duk cikin mu ashe
nice da rabon fara dafa arfa dan murmushi nayi ina fadin kila hakan ne kuma fa ?

Sai naji tace ya kila hakan ne kuma abinda nace maki nan da sati biyu insha Allahu zamu shiga saudiya
din.

Allah sarki kila koda zakuzo lokacin mun koma gida aimu don yanzu haka da muke maganan nan ina
tsakiyan saudiya kwance abina don a garin makkas ma nake yanzu haka wallahi.

Ke don Allah kibar zancen nan nace Allah ko munzo dukka mu da Abbu dasu Ammah ina nan kwancene
a dakina na suna dakinsu su.

Aeesha don Allah da gaskiya kikeyi maganan wasa ya wuce please abin ya ban mamaki nace yaya zanyi
wasa da kalman Allah Aymana ?

Wallahi satin mu na biyu ke nan muka shigo yanzu kinsan ummu mahaifiyata ta dawo mijintane ya
kawomu tare da yan uwansa.

Sai gashi kuma nazo mun hadu da mahaifina a nan din jiyama akayi waliman haduwan mu dashi din da
daren jiya shiyasa na gaji wallahi.

Ke dakata don Allah Aeesha yanzu ana nufin mahaifinki an gansa hakama mahaifiyarki duk an ganosu
kuna tare ?

Hakane wallahi Aymana ganima a gidan mahaifina kwance nan muka kwana nidasu Abbu su ummu
suna masaukin da muka sauka a nan din.

A,a lalai Aeesha kice mu daina takara dake daga yanzu shike nan yanzu kuma kin koma yar saudiya sai
naji wayan ya dauke dip lokaci guda na duba ya yankene kuma baya shiga.

Yasa na murmusa ina fadin Aymana ke nan har yanzu halin ashe yana nan bata daina ba na zata zaman
turau din zai sauyata ashe hali zanen dutse a zuciyar mutum.

Kwankwasa kofan da akayine yasa na tashi zaune wata farar dattijuwace balaraba ta kawo min shayi na
ganye zallah irin nasu tana ta watsa min larabcin nidai na gaida ita da kwana ina kokarin mikewa tsaye.

Ban dai gane abinda take fada ba ta juya ta fice daga dakin ba,a jima ba sai gata dauke da jakkan
kayana dana bari a can masaukin mu din na farko.

Ban iya tabbatar dashi bane sai bayan ya fitane na bude naga tabbas kayanane a cikin yar jakkar na
lumshe idanuna ina fadin ko yau ma anan zamu kara kwana ke nan ashe ?

Wanka nayi na fito na gyara jikina na dauko wata bakar jallabiya zan saka a jikina sai kuma naga gara
kawai ma inyi shigata ta hausawa a wanan lokacin.
Hakan yasa na dauki wani buje da riga dinkinsa half gown ne atamfan da akai dinkin babban atamface
suna saka a jikina na daura kallabina akai sai gani na fito shar dani cikin kayan dama tufafin sabbine
zuwana abuja na sayosu nazo dasu nan saudiya .

Shayin na dauka na kurbe ina jin wani iri don ba galmin sugar aciki sosai yadda na saba shansa a gida
haka na daure na zuke ruwan wanan shayin ina bata fuska.

Son ganin iyayyena nakeyi hakan yasa na mike na dauki mayafina pink wanda yai matching da kayan
na yafa na nufi kofan na murda .

Don in fita in tambaya ko wani daki suke a zaune in gaidasu sai naji an turo kofan za a shigo dakin a
lokacin hakan yasa naja baya naba wanda zai shigo waje.

Wasu matane su biyu suma dai a cikin shigar bakaken tufafi a jikinsu na fara gayar dasu a cikin ladabi
irin na al,adan bahaushe da sai an dan rusunna din nan haka a gaida mutum.

Wani kallo suke min dana tsargi kaina ga fuskansu a daure ba zance zasu haifeni ba ba kuma zance
basu isa ba dai haihuwan sa,ata.

Da farko na dauka saboda shigata suke min wanan kallon kurullan haka naga har kafata sun bi da kallo
kafin ta birkitani tana neman wanan tawadan Allah da nake dashi baki a bayan wuyana din.

Naji tace kalas wanan yarsace gaskiya ko ba ai DNA ba komai nata

88 / 109