Chapter 76 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   76 / 109

225K to 228K   out of 326.5K words

karshe babanku ya hada dani dasu ya koremu daga
gidan tunda dama yace nice na kama mata duk wani iya shegen da takeyi garin nan.

Ita kan tayi data sanin wanan abin yafi dubu a zuciyarta gashi tayi kwaliya bata biya kudin sabulo ba
abu ya koma mata ciki yanzu.

Ta koma kamar muji a cikin mutane sam bata da mutunci ko kima a idon kowa haka yasa ko fita nan da
can tun faruwan lamarin bata fita zuwa ko ina ba.
Gashi ko yaushe cikin fargaban matakin da mahaifinsu zai dauka take yau itace zaune tirin kamar turmi
hjy Nasare ke fadawa magana bata iya hayayketa da masifa akan hakan .

Shiru tayi tana tunanen zuci sai fadi take lalai kurciya da rudin duniya ya kaita ya baro don ko halin
tashin hankalin da yanzu mahaifiyarsu take fuskanta daga mai martaba ya isheta nadama duk akanta
kuma hakan ke faruwa.

Ga yan uwanta maza suma sun nuna ba ruwansu da ita sune ma suke tare da sayadi din kut da kut suda
diyansu kowa ya shareta ya fita batunta sai Nasare kadaine ke kulata a cikin yan uwa.

Hjy Nsare dince ta juya gun hindu tana fadin akanku duk hakan daya faru yake faruwa kan yaya ba
kamar dan banzan nan maniru shidama ba wanda yasan duniyan da yake yanzu.

Idan har gidancan suka gane kina wanan hakin ba wani aiki bane ga yaya Sayadi ya kakabeki daga shiga
masa gida don zasucene kina shiga kina masu leken asiri a gidan.

Kibar gani kina zuwa kina tayarwa uwarki da hankali tunda kinsan halinta da yarda da magana ku.

Yanzu in magaji yazo yaya tai masa magana wani fitina ya taso me zaki fada akan haka zaki iya fadan
kece kikazo mata da labarin kome ?

To ki jini da kyau kibi sannu muna kokarin koke dai muga kin samu shiga wajen mahaifinku daya nuna
baisan kuna nan ba a yanzu.

Dole ba don taso ba ta yayi shiru har suka gama saidai jinsu kawai tskeyi don abinda ya dameta ya
dameta a lokacin.

Sai tambaya kanta takeyi yakaita wajen Abba ke nan yana nufin ita ya zaba a kaina ko me sam wallahi
ba zan taba bar maki shiba takw maganan zuci ita kadai.

Kafin ta koma takaicin uwar nasu duk son kai irin na mahaifiyarsuce yaja mata hakan gashi yanzu sun
koma suna labe labe don nasu gidan ya gagaresu komawa tun ranan da abin ya faru.

Wanka nayi nayi sallah kafin na nemi waje na kwanta ina faman tunane akan hiran mu da ummu din
na ranan .

Na yarda da komai data fada kaddara akan wanda ta nufa bata wuceshi dama haka kaddaran namu yake
kamar yadda ta fada.

Ta sanadiyan wani abune duk hakan ya faru akan mu gashi a cikin mu na rasa wanda yafi wani shiga
kuncin rayuwa.

Yanzu ni a haka zan kare ba tare da nasan taka maimai din mahaifina ba kuma ance yana raye a
duniyan nan ya Allah na fada ina gyara kwanciya.

Sai naji son zuwan da nakeyi na nemosa ya fita raina a yanzu baki daya don sai nake ganin duk laifin
ma nasane da baizo da wanan tsigar auren yaudaran ba garesu da duk haka bai faru damu ba.
Sai naji gaba daya ma an zare min son sa da nakeyi ingashi da duk da abinda ya aikata muna nida
mahaifiya ta din yanzu sam banjinsa.

Naji ummu tace dani shi baikai dattijo irin mijin nan nata ba ke nan dukkansu da yarintar su sukai
wanan auren hawaye naji sunzo min cikin takaici masu zafi.

A haka barci yayi gaba dani ina wanan dogon tunanen kamo wancan saki wanan dai barcin ya daukeni.

Ba kamar zancen man da yanzu na sare masa yadda ya dauka dani hakan na shareshi dama kuma na
fahinci ba don kansa yake kulani ba don haka nima nake kokarin koyan fitar dashi a zuciyana.

Washegari misalin goma Asmau takaiwa na kusa sakon tsarabansu wanda yasa suke shigowa yin
godiya suna suratan banza don gareni banza saboda borin kunya sukeyi yanzu.

Tunda sunga idon wace suke zagi din a yanzu dole su koma kuma yabo da kame kamen fadin Allah sarki
boyar Allah ashe tana can tana aurenta kaza kaza dai haka ake ta wanan kame kamen a gaban Ammah.

Ba kamar tumba da nake son inga yaya zatayi saidai banjin zan iya zuwa gidan wanan matar gaskiya
don kai mata wanan tsaraban .

Saidai kaiwa din zaiyi amfani don zata bi unguwa tana yada sabon labari kuma dama tun zuwan mu ita
ta yada cewa ai shegiya nake banda uba har tasowan mu unguwar wanan sunan yana bina kuwa.

Asmau daice nabawa kudin mashin taje masu da tsarabansu din aiko ta dawo tana fadin yadda tunban
tayi wai sau ukku tana zama tana mikewa da Asmaun ke bata labarin dawowan nata.

Duk da hakan saboda tsaban gulma saida ta tambayi Asmau din da zata taso toshi uban nata fa da
gaskiyane zancensa yarin nan ?

Kwarai kuwa gaskiyane ance shima zaizo garin nan ya dauke ta tace umm,uuuu aiko mazo gani haka
dai tayi ta surutun banzanta har Asmaun ta fito daga gidan tace har kofan gida ta biyota.

Ni dai nagama jin shirmen Tumba na mike na shige daki abina don yanzu dole in kara nisanta kaina da
kowa tunda zama a hakan ya tabbata ke nan ba uba saidai ace ni din ba shegiya bace kawai.

Haka tun wanan fitan da mukayi zuwa gidan su umma muka kuma je gidan ummu ban kara fita ko
kofan gida ba ina cikin gida kumshe iya ka idan na gaji da kwanciya indan fito waje insha iska kuma in
koma ciki.

A yadda nake jin cewa wai zasu kauyensu tare da Ammah da mijinta suje suga yan uwasuma su ganeta
tare da yaranta sai gashi kuma Anty safiya ta dawo gidan naji tana fadawa Ammah zancen walima.

Don yanzu sun kula da anty ummin ghana da anty safiya suka hade da ummu a gidanta nan aka hadu
ana irin nasu zancen har taji zancen waliman.

Take fadin wai ai sun daga tafiyan sai bayan waliman da za ai masu zasu tafi can kauyen nasu kuma
nan Ammah ta fara fada.
Tana fadin saboda shi yazo yaga yan uwansa zai hanaki zuwa ganin naki kin dawo kasan nan nace muje
gida ansan kin dawo duk da iyayyen mu basu raye ai akwai yan uwansu dake raye ko ?

Shi yasa yarinyar nan tana da gaskiya abu daine da baka biyewa yaro amma haka shekara da shekaru
kamar baki da kowa a nan kin zauna can kin share mutane.

Yanzu kuma kin dawo kice wai mijinki ya hana sai ya gama nasa laluran zakije ganin danginki ana haka
don Allah malam ?

Murmushi nayi da take fadan hakan ni kadai a daki ina fadin yanzun kuma nice mai gaskiyan kuma ke
nan ?

Tabbas mijin tako ya fada ranan a raina nace yanzu saboda dawowansu har wani kuma walima za ai
masu su dai mutane basu raina abin bidi,a wallahi.

Sai kuma ga Ummu din tazo tana fadin dalilin waliman wanda yan uwan mijinta suka shirya don
nunawa duniya murna da dawowan shi.

Shiine suka hada masu wanan waliman yace su dage nasu tafiyan har a kammala waliman sai su tafi
Ammah dai ta nuna mata bacin ranta wanan karon .

Naji tana ba Ammah din hakkuri saida Abbu yace kina dai son ganin laifin yarinyar nan ne kinfasan irin
mazajen su da harkokinsu dole sai tabi a sannu.

Ran Ammah ya gama baci tace inma bata zuwa ai sai ta zauna ina shi dai yana cikin nasa yan uwa ni
kokari nake kije su ganki tambarin da suke maki ya goge.

Ammah ba don ke bama nifa ba zanje ba don bam manta da irin cin fuskan da sukai muna ba a baya
kune nawa sai yayan wudil kuma ina nan tare daku.

Koma me sukai maki dai yan uwanki ne Asiya ba a taba canzawa tuwo suna don haka sunyiwa kansu
kowa aiya haifa dai ko ?

Don haka yanzu dabara ya rage gareki kuma ban kara jin muryan ummu din ba sai da zata tafine take
fadin Asmau ina mummy kine tunda muka gaisa ban ganta ba kuma ?

Tana ciki tana jinki mana tunda zancen ta ya fito gashi kin nuna kowa yagani kije gida kin tsaya kina
biyewa mininki don shi yana zaune cikin nasa ?




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[10/26, 9:45 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

7️⃣9️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6



https://sitrix.africa/signup.php?ref=foleesco



Duk abinda akeyi na shirin walima ban yarda na tsoma kaina a cikin zancen waliman ba iyakata ina daki
na saka laptop a gaba ina faman bincike.

Aikina ke nan bamda aiki sai shiga na,ura ina ganin bayanan a ciki wanda hakan yasa nasan wasu
abubuwan da ban sani ba game da shiga yanan gizo.
A lokacin ma kwance Asmau ta sameni ta shigo tana gaidani kafin ta samu waje a gefena ta zauna tana
fadin mummy kina nan gashi can ana shan labari anty safiya ta dawo daga gidan ummu take bada
labarin abinda zasuyi jibi.

Allah ya kaimu lafiya na fada yau kan na yanke shawaran bincike akan na,uran mahaifina wanda koda
nayi searching sunan ya fito min wajen mutum hudu masu shigen sunan nasa.

Donshine nake shiga ina fita ina duba baya nai a kansu lalai tabbas duk yadda akayi yana daya daga
cikin bayanan dana dauko a yanzu.

Sai ga Asmau data shigo tana son ta dakatar dani ga abinda nasha wahala wajen nemansa saura kiris
nakai ga abinda nake nema a lokacin.

Mummy wai,,,, out please na fada abinda ya firgitata tadan tsaya tana bina da kallo nace fita kija min
kofa har nagama .

Ba musu ba tare data fadi abinda tazo dashi ba ta juya ta bar dakin tare da yin abinda nace tayi min din
kofan ya kulle kansa.

Haka nayi ta bin sunayen ina buncke kansu har kai ganasa kusan karshe na dan jima ina kallonsa zakice
nice a photon donshi na dauko a fuska sak.

Nashiga na kusa a cikin bayanan mutumin da nake kyautata zaton shine nayi nasaran samun bayani
akansa kuma.

Dan shekara arba,in da biyu mutumin kasan Ouman mazauni kasan Dubai dan sarauta mai mata daya
ba yaro ko daya sai tarin dukiya da akai bayani akansa da sauran abubuwa.

Haka naita bin komai nasa ina rubutawa yadda zan zauna nayi sharhi a akai sai tsawon wani lokaci
nagama abinda nake so na fito daga dakin.

Kekan bakiyi ba wallahi Ammahce ke fadan hakan ina fitowa me kuma nayi Ammah tace yanzu inba
mugun hali ba Aeesha uwarki ta bugo waya tana tambaya ku nawa zakuje wajen taron da za ayi kice a
fice a baki waje don Allah.

Ko sakon ma kinki ki tsaya ki saurara don iya shege wani irin rayuwace wai haka Aeesha abin arziki yazo
har ya wuceka saboda halin banza.

Ammah gara dasu abinda nakeyi lokacin yafi min wanan taron bidian da zasuyi muhinmamci balle ko
banza ni ba zuwa zanyi ba wajen taron.

Ai kaji irin ta dama nasan nufinki ke nan kice ba zakije ba nakai zaune ina fadin Ammah nasan halin
mutanen nan wallahi suna da wullakanta mutane.

Sunyi min nagani kuma nasan kowa nasu yana wajen mutum yaje suyi ta nunasa suna fadan maganan
da ba dadi a kansa don haka ni ban zuwa gaskiya.
Photon dake jikin wayana na miko mata ta karbi wayan tana kallo tare da fadin wanan waye kuma ?

Mahaifinane abinda nakeyi ke nan lokacin da Asmau tazo ina neman sa a yanan gizo na kuma samesa
yanzu .

Kai amma wanan yar da bakin shirme kike wallahi haukan bokon haka tabaki kuma har abin ya kai ga
fara taba kwakwalwanki yarinyar nan ?

Lafiya ta kalau Ammah zakice na fada maki kwanan nan zakiga mahaifina yazo nemana na fada ina
maida jikina bayan kujeran dana zauna ina lumshe idanuna.

Don ni kadai nasan abinda nayi a lokacin izuwa yanzu ina da basiran kutse a cikin account din mutum
inyi abinda nakeso in fito saidai raunin da nake dashi kasancewana mace.

Bayan hakan kuma ni musulmace dan nasan hakan haramun ne a gareni saboda kamar sata ko
kwacene idan ba haka ba da ace ni namijine kuma mara imani da Ammah taga abin mamaki a wajena.

Karbi wayan ki nidai ta fada a kausashe dama nasan ba fahintar abinda ke jikin wayar zatayi ba baifi
yan mintuna ba muna zaune muna hira nida ita naji wayata tana ringing.

Kin dagawa nayi don nasan abinda zai biyo bayan abinda na aikata a lokacin cikin karfin hali na cigaba
da hirana da ita tana min hiran gidan makwabtan mune abinda suka fada mata da wata ta basu labarin
karya.

Zubur ya mike zaune yana sake kallon abinda idon shi ya hasko mashi a wayansa a take ya fara neman
layin na saidai ba a daga ba.

No no no ya fada yarinyar nan kuwa tasan meta aikatawa kanta a yanzu yake fada kamar mahaukaci
shi kadai a dakin ya mike ya fito tare da waya a hannunsa.

A Falo ya samu mami zaune ita da kaunarsa husnah suna duba abu a wayan mami din ta kallosa tana
fadin nikan wai karfe nawane taron nan dai ?

Saida gaisheta da kwana yace mami inaga karfe hudun yammane a tashi shidda kamar haka suka tsara
abin .

Au kaima baka san komai ba ke nan a,a mami ai yan gidan su baffa din suka tsara mai gidan
mahaifinshi bashi ya hada abin ba.

Ganin kamar yana sauri ya fita yasa ta barshi hakana da tambaya inba haka ba tana da tarin tambayan
da take son yiwa dan nata tunda yanzu ta fara ganin hankalinsa ya dawo gida.

Alama ya nuna sun rage abubuwan da mijinta yace sunayi akan kaddarorin dan uwansu din din inda
yaran nasune sukai tsaye da wanan zancen.

Ya shiga mota har ya zauna sai kuma wani tunane yazo mashi na ya bari agama hidimar wanan taron da
za,ayi kafin ya tukari wanabmn zancen.
Tsuki yaja gami da dukan sitiyarin motan yana fadin she is tooo disturbed ya kula yarinyar tana da
matukar taurin kai da kafiya idan ta nacewa abu sai ta aiwatar hankalinta yake kwanci.

Don koda yaje a yanzu banda bacin rai ba abinda zai biyo bayan hakan karshe ta jagula rayuwan
iyayyen nata gasu suna fuskantar wanan taron da yan uwa ke kokarin hada masu yanzu.

Tsuki ya kara ja yana ya bude da niyar fita lokacin salman ya karaso wajen shi yana fadin daga gidan
umma nake yanzu tace in fada ma Ayshaa ta aika masu da sako jiya.

Sako kuma ya tambaya cikin mamaki tare da tambayan sakon mefa yace wallahi iya abinda tace in
fadama ke nan kawai.

Ok ya fada ya karasa fitowa daga motar yana jin wayarshi tana ringing ya daga tare da sallama da
meshi zanje naji ya fada har lokacin salman na tsaye a gefen motar nasa.

Sam baya jin dadin yadda dan uwan nasa kuma amininsa yake share duk wani abinda zai masa nasu
koma daidai yabi amma ya nuna masa ba haka ba.

Ya rufo kofan motan ganin har lokacin salman din yana tsaye yasa ya juyo gareshi yana fadin uhumm
da wani abune kuma ?

Babu na dai zone in kara baka hakkuri bisaga kuskuren dana aikata a cikin rashin sani wallahi rudin
shedan ne yasa na aikata hakan kayi hakkuri don Allah man hakan ba zai sake faruwa tsakanin mu da
yardan Allah.

Wani kallo yayi masa kafin yace ni ba kai min komai ba wanan ya wuce a wajena ai a,a man bai wuce
ba tunda kaki mu koma yadda muke a da dakai ?

Ga ummah tana ganin laifina har shehi ta fadawa abinda ya faru shima yai min fada Ok su suka turoka
ka bani hakkuri ke nan ?

A,a man nidaine naga dacewan hakan don har mutane sun fara fahintar da matsala a tsakanin mu
yanzu.

Don Allah kayi hakkuri hakan ba zai sake faruwa ba insha Allah dan murmushin kasaita ya sake yana
fadin salman kasan ni dan sandane kuma dan sandan kasa da kasa ba wai na iya kasa da nake ciki ba.

Ina tsoron komawa daidai dakai wata rana a biyo ta wajenka aci galabata da hakan tunda ka fara hakan
gara tun wuri in kama kaina dakai salman .

Ba wani abu we are living in one roof eating together sirinane kawai bani sharing dakai yanzu wanan
kuma dama matsalatace bata shafeka so banga wani abin damuwa da hakan ba ai ?

Murmushin takaici da bakin ciki ya kara sakewa shi salman din a fuskanshi yana mai bin dan uwan nasa
da kallo har ya shige ciki koma meye dai son zuciyarshi ce taja mashi hakan .
Ina mamaki yadda su anty da yaransu suka zake akan wanan waliman da an zauna hiran ke nan gashi
yanzu anty safiya bata zama gida ko yaushe tana can gidan wajen ummu sai yamma zata dawo.

Nan take zube muna yaranta suna walagigi a cikin gida dole na kama jawosu a ciki ina kula dasu saboda
yaran har sun tsiri fita waje wai wasa saboda basu samun kula.

Nice zanyi masu wanka in turasu makaranta har na tsiro dafa masu abincin zuwa makaranta don na
sayo masu yan kuloli idan sun dawo kuma in fito in basu abunci.

Kana kuma in tura su islamiya da yamma ta dawo tayi ta min godiya kan hidima da yaran da nakeyi har
dan sabo kuma yazo ya shiga tsakanina da yaran yan mata su biyun kanana .

Dama ance yaro dana miji kamar mage suke mai kula dasu suke bi hakan ne ya kasance a tsakanin mu
da wa yan nan yaran .

Don wallahi indai don Ammah ce ba ruwanta da tsayawa kula yaron kowa na fhincin ita haka rayuwanta
yake tun farko.

Itace ta dawo muna da labatin wai ance jallabiya ko abaya

76 / 109