Chapter 42 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   42 / 109

123K to 126K   out of 326.5K words

photon shine a daidai lokacin da hakan yake faruwa.
Basu bar wajen ba sai wajajen shabiyu na dare yana zaune yana masa gargadi da jan kunne kan ita
mummy kura dama kowa don kasan,cewanshi na kusa dashi da za a iya biyowa ta wajensu a cuta mashi.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[9/13, 8:28 AM] Zainab Idris Makawa Writer: JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

4️⃣8️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



*ONLINE TRAINING!*

*ONLINE TRAINING!!*

*ONLINE TRAINING!!!*

*Are you looking to level up your game with traditional spa?*
Whether you are married woman, bride to be or some one who loves to master the art of *traditional
spa*, *natural aphrodisiac* and *Traditional incense* asalin kamshin shuwa look no further in this
article *@sady_aromamist_and_spa* have got you covered

Imagine you know all the ingredients used on your skin to moisturise, nurture and revitalise it, *intimate
confidence* and a good long-lasting Traditional scent.

Transform your space

Transform your skin and have that intimacy confidence. Join our online training

Wa.me/9048763046

learn the connection between *skin care,* *Traditional incense* irin kamshin nan mai kama jiki and
*natural aphrodisiac* masu matukar kyau with zero side effects 😍

Sign up now to join the waitlist(https://chat.whatsapp.com/EDJan6LcDjGDrh6geC0Bk5)

Early birds 7500

Actual price 15k

Follow our IG handle for free recipes @sady_aromamist_and_spa

Start Transforming your body




Cikin shigan da shi yake ganin ta bajintace agareshi ya karasa gidan kakanin nasa da safe misalin tara
saura zuwa lokacin yasan kafin ya gama da fadawa awaje tara tayi daidai a lokacin don shi ba mutum
bane mai saba lokaci.

Hakan akayi yanayi yana kallon lokaci daga inda yake zaune a cikin mota yana kuma karba gaisuwan su
tare da mika masu guzurinsa kafin ya mike daidai saura mintuna ukku ya doshi kofa kodaya isa tara
daidai ake sanarawa mai martaba isowanshi.

Duban lokaci yayi ya dan murmusa tare da fadin bakin bature mai wuyan sha,ani ya iso daidai da
lokacin dana bashi ba kari.

Zuwa lokacin labarin zuwansa yakai cikin gida wajen mata mai babban daki taji zuwan jikan nata tayi
mamaki don bataji shigowanshi kasan nan a bakin kowa ba sai yanzu da take jin hakan.

Sallama yayi irin ta musulunci ya shigo maimarta ban yana zaune yana kalacin safe wanda ba wanda ya
isa ya shigo a lokacin saiko jikan nasa da yanzu ba shamaki yashigo mai a lokacin.
Bayan ya amsa kalman farko a cikin nune ya umarci jikan nasa dayazo su karya kummalo tukun kai ya
girgiza masa tare da fadin Alhamdullahi grandpa.

Umurnine ba tambaya ba ya fada a takaice ba don yasa ba ya karasa wajen shima ya zauna a kasa ya
tankwafe kafa yadda kakan nasa yayi don girmama abincin yadda addini ya koyar suka soma cin abincin
a tare da jikan nasa cikin isa da kasaita da komai na halayesa bai rage ba wanan yasa yake kara son dan
tsokan dansa da komai ba rago masa ba na halinsa.

Ya riga kakan nasa fitar da hannu ga abincin saidai ya kasa tsoma hannu ya daure don kada yai rashin
kunya garesa ya gane nufinsa hakan yasa ya dan sauke murmushin manya a fuskansa yana fadin
bissimillah mana tunda ka cire hannu.

Shima murmushi yai masa duk da umurnin baisa ya daureye hannunnasa ba saida kakan nasa ya tsoma
ya dora nasa hannun a sama yana daureye masa yace.

Yau na tabbatar da zargina a kanka nasan kasan komai a ka,idance kana dai nuna masu baudaden
halinkane don ka tserar da kanka garesu.

Shima dan murmushi yayi kafin yace da kakan nasa idan na biye masu zasu kashe min zuciya da
aki,dojinsu na koma maijin kai da daukan ni wanine da baida wani zarra sai na jiran gado.

Na dade da fahintar ka nasan kai namijin duniya ne ai amma ka sassautawa hjy hauwa haka nasan zaka
shiga ku gaisa ai idan mun gama tana maradin son ganin ka sosai a yanzu tunda har ta kasa hakkuri takai
ga tambayana labarin ka ?

Zancen daya kawoshi da maimartaba ya nemeshi akai suka tattauna ya kawar da wancan zancen a cikin
hiransu don bai bukatan ganin tsohuwar a yanzu.

Saboda ita din maj laifice ta ko ina a garesa yana ganin da saka hannunta akaiwa baffasa komai daya
faru wanda hakan yasa yake kara ganin bakin su a fuskanshi.

Muryan kakan nasane dake fadin na dade ina zargin hakan tun da imamu yazo min da zance an kasa
gane gawan Sayadi haka dai a kai masa zana,ida .

Kaga akwai ayar tambaya anan amma yar nan gaskiya har inda hannunta cikin zancen dama duk wanda
ke cikin zancen ba zan yafe masu ba.

Dan murmushi mai saurti Bashir yayi yana fadin yafewan ya zama dole yallabai don ko yanzu Allah ya
nuna masu isharansa kan abinda suka aikata din.

Banga wani abinda za a tsayawa tonon asari ba anan kawai kyalesu shiya fi a yanzu har zuwa lokacin da
kowa zai gane gaskiya akan zancen.

Sun dan dade suna tatauna har yakai lokacin zama fada ya dan gwauta hakan yasa suka hakkura suka
rabu da junansu bayan ya kara lurar dashi kan wasu abubuwa.
Sun rabu yana jin wani irin son jikan nasa yana karuwa mai a rai saboda hinmar shi da kwazon shi da
yake dashi ga budi na alheri da sanadin jikan nasa ya jawo masu.

Ko kallon kofan shiga cikin gidan baiyi ba kai tsaye ya fice zuwa wajen motarsa sai fadawan dake biye
dashi suna mashi kirari a baya.

Saida ya zaune ya bude wani waje kudi ya mikawa dayan yana fada mai wanan nasune wanan kuma ya
kaiwa su jakkadiya a ciki su raba nasune mata bai samu shiga ciki ba yatafi.

Mai babban daki na zaune akaiwa jakkadiya sallama ake sanar mata ta kuma ji guda da kirarin da
jakkadiya ke mashi a lokacin.

Saida jakkadiya ta natsu tazo tazo ta zaune take fadin dan gidan Ahmad ne ko yayo maku sako ?

Shine rankishi dade fari mai farar aniya icen gora angan an barka don baka lankwasuwa garesu wane,
sunan, gaiyan suna aka tara muna yan sarki idan jinin Bashir da bashir basa waje suke gurnani.

Ya isa don Allah jakkadiya har nawa ya bakine wai kike wanan bambadancin haka mai kyauta da
gadara ?

Kasa tayi da kai tana fadin uwar dakina kura aikinsan gadara gadon kune dubu dari biyu ya turowa
mata nan cikin gida a raba.

Tsuki taja tana fadin shine zaki cikawa mutane kunnuwa haka don Allah sai kace wanda ya biya maki
kujeran maka ?

Hakan na tafe ai hjy da rarafe yaro yakai ango ai wata ran za a kai ga hakan jin abunda ta fada yasa hjy
mai babban daki yin guntun murmushi daya dan fito fili.

Hakan yasa hjy kura din kallon mahaifiyar nasu tace wai dama da mara kunyan yaron nan baba yake
ganawa akace min wai na dakata yana da bako a ciki suna ganawane .

Yo har ankai matsayin da magaji yafini matsayi a cikin a gidan nan ke nan a yanzu da har za a dakatar
dani kar inshiga ganin maimartaba ashe ?

Saida ta sauke murmushin takaici tace kina wani zance kura yau in sarauta ya fadi ai zai iya mulkin
garin nan da komai dake cikin garin nan harke da sauran iyayyensa.

Don hakan ba wani abin mamaki bane a wajen ubangiji shifa na miji Allah ya yayosa kuma a cikin jinin
sauratan na Allah ya halittosa ai.

Kuma ko yanzu da kakansa ke a ra,aye idan Allah yace ya mulkemu duka sai ya kawo wani sanafin da
hakan zai faru me zakice kuma a nan kan hakan ?

Shiru ta danyi na dan lokaci kamar tana tunane kafin ta sake wani nishin ciki mai nuna magana gareta
da zance da mahaifiyanta din ta fada a lokacin.
Kai tsaye gidansu ya nufo don koda ya fito bai fadawa kowa inda zai tafi ba saijin tashin motarsa sukaji
tunda safe wanda hakan ba al,adabsa bane a baya.

Zaune ya samu mami falo tare da salman kallo daya yayi masu ya kawar da idanunsa kujera dake kusa
ya zauna yana gaida mami din da kwana.

Ta amsa tare da jefo masa tambaya daga ina haka da safen nan shima bai tsaya bata lokaci ba wajen
bata amsa yace daga gurin maimartaba nake.

Wani kallo zargi sukai masa lokaci guda wanda shi ya san me hakan yake nufi a kansa lokacin amma sai
ya dake kawai yana shakan iska.

Badai akan yar kwara din ka samu maimartaba ba wai me kake son jawo munane kai a rayuwan ka
magaji akan wanan yainyar mara asali da tushen kwarai ?

Ko su kake a fara a kanka abinda duniya basu taba gani ba koji ace kaine na farkon taka doka a cikin
family ?

Nina rasa me ka gani a gun wanan yar haka da kake son nacewa zancen ta na sauka a yanzu ka fita
zancen yar nan kasan gaskiya.

Har kazo don dan uwaka yayi abinda ba zaka iya ba kai kaso kaga laifinshi yo koda kura bata saka yai
mata haka ba aini zan saka aimata har iyayyenta ko a garin nan saina wullakantasu ga baki daya.

Murmushi yayi kafin ya dan gyara zama yana fadin mami da kinji nauyin hakan da kikayi ranan da kika
san waye Aeesha din da kuke zance.

Yo waye ita din kuwa banda yar shegiya, shegiyar ma yar takari yar tsaraban saudiya mara asali da gata
da aka haifa ta tsigar zina ko ?

Wa,iyazu billah mami kada ki aibanta yar mutane haka don Allah yarinyar nan ba shefgiya bace da
ubanta da gatanta kuma ?

Matsalan ke nan irin na mutanen mu saurin yankewa abu hukunci cikin rashin sani gaskiyan abin yanzu
kazo nan ka zauna ka fadi abinda ba shi ba amma ka kasa fadawa mami gaskiyan abinda kai ka aikata
kai .

Wani gaskiya kake son ya fada bayan wanan Ok ya fada yana mikewa ya saka hannu a cikin aljihun
wandonsa yace ni zan shiga in shirya don zan koma yau gobe zamu bar kasan nan nida abokan aikina da
muka shigo.

Har ya taka sai kuma ya tsaya ya kallo salman din yace a duniya na dauka kaine mutum na farko da zai
fahinceni idan na kafewa abu a rayuwana.

Saidai kash a yanzu kasa na daina yarda da kowa kuma bayan kaina salman ka ban kunya da har za a iya
hada baki dakai aga bayana.
Bayan yardan dana baka nake daukanka kamar wani bangare na ,,,, kai dakata don Allah akan mace
zaka tsaya kana fadawa dan uwanka maganan banza haka ?

Macen ma ba wata macen arziki ba mara asali da galihu irin wanan har meya rudekane haka da
yarinyar nan wai yarinyar da akace bata da asali.

Yaya Kurafa ta tura an mata bincike mai kyau kan yarinyar nan uwarta har yau tana cikin duniya tunda
tayi abin kunyar nan ba,a san inda take ba .

Salman yai min daidai dayayi hakan tunda yanzu ta kama kanta ai dakai kallon da yakewa uwar yasa
mamaki ya hanata cigaba da magana itama ido ta tsura mai da kallo.

Mami shi salman ya fada maki duk wanan ko hjy kura au Bashir yau gwaggon naka kake kira haka da
sunanta gatsau ba sayawa kan mace.

Nifa ka fara ban tsoro wallahi da wanan halin daka dauko yanzu in wani yace min zakayi hakan zan
karyata maishi gaskiya.

Salman kai ka tabbatar da abin da mami ke fada gaskiya ne har cikin ranka bada wani manufa kajewa
yarinyar nan ba ?

Manufar me kake zatonshi dashi akan waan yar mara asali wai shi irin kane da bai son ciwon kansa har
ya zauna yana jayayya akan wanan banzan.

Mami ki tambayesa idan ba yaje bane da niyar batani gunta don daga baya ya koma sonta ?

Da sauri salman din ya dago kansa cikin mamaki irin hatsabibancin dan uwan nasa cikin karfin hali yace
No ba haka bane Man ka saurareni.

Wai akan mace mace fa har zaku yarda ajiku haka imagine kai yanzu magaji bakaji kunyar hakan ba
tsakanin ku don Allah ?

Wallahi mami nasan da farko naso yarinyar nan harga Allah kamar inyi hauka amma kuma irin yadda
naga tafi maida hankalinta ga mam bashir sai na taushi zuciyana ga hakan sai,,,,,

Wani kallo ya jefowa salma din dake bayani a lokacin na ka kama kanka dan iska idanuwansa suka
kada sukai ja yace kinji dan iska ko ?

Mena fada maki mami yanzu ma a gaba yake fadin yaso yarinyar wai lokaci guda ya juya a fusace ya
nufi hanyar dakinshi.

Munaga rasulu kai muna agaji ya Allah yanzu a kan mace yau kuke hakan a gabana don Allah ku rasa
yar da zaku tsayawa fitina sai yar shegiya ?

Kai mami nifa ban dauka yarinyar nan shegiya bace fa Allah husnah ba inda tayi kama da yan iska
gaskiya ga yarinya da mutunci da kunya da kamun kai mami nata kiranta da shegiya haka ?
Nadiya da suke labe ita da husna suna sauraren abinda ke faruwa tsakanin yayyun nasu take fadan
hakana ga yar uwar nata da abin duniya yayi mata yawa a zuciya kan masoyinta salman.

Don Allah matsa can ki ban wuri da shirmen ki abinda ake nufi shine Aeesha din nan fa bata da baba
bada aure aka haifeta ba .

Ta waro ido tace wa yar uwar da zina aka haifeta duk wanan kyau nata ba yar sunna bace haba haba
iyayyenta basu kyauta mata ba wallahi.

Nadiya ni shirmenki ya isheni don Allah ki barni inji da abinda ya dameni yanzu shi yaya salman duk
son da nake nuna masa amma ya koma son budurwan yaya Man kuma don Allah don yaga baya kasan
wanan ai cin amanane Nadiya ?

Baifi minti ashirin ba ya fito ya samu mami zaune ita kadai yake fadin ni zan koma ke nan dama
maimartaba ya kirani kuma nagansa zan koma wajen aikina ke nan .

Don an fadama gaskiya akan abinda ba zai yuyu ba ka dauki zafi Allah ya kaika lafiya mami don Allah
abar zancen nan please .

Idan kana son mu bar zancen nan ka shirya da dan uwanka don ba zanso Adda umma taji wanan
zancen daya faru tsakani ku ba ranta ba zaiyi dadi ba dajin hakan ga salman.

A fada mai ya je ya gyara inda ya batani don ban taba abinda zai zubar da mutuncin ahalina ko na
zauren mu ba balle yanzu in soma nasan abinda nakeyi.

Ya riko hannun uwar ya sunbata alaman tasa masa albarka ta lumshe idanuwanta a hankali alama
shaukin uwa da danta yana shiganta a lokacin.

Da fada mrs zebeth ta tareni ranan kan ban tsaya ba duk kokarin da nayi naki zuwa taron da akayi din
na bata hakkuri na shiga ciki.

Bincikena na ranan dana soma hakan ya gagareni yasa naja tsuki na lumshe idona barci na dinga ji na
dan lokaci yasa na kifa kaina da alaman gajiya.

Zubur nayi na mike da irin firgitan nan da mai dan barcin da baiyi nisa ba yake fisgar mutum a hakan na
dan zabura nima lokacin.

Dan dube dube na farayi kamar ina neman wani abu a wajen kafin na kusa dani ya juyo yana fadin any
problem ?

Nothing na bashi amsa ina gyara kaina inda na kara shiga computer din shiga na fita can na fada
account din wani scarmer kuma nan na zakulo wani mai datsan kudin manya da sauri na tsurawa
account din ido.

Gybrain na fada ya juyo da sauri computer daya na tsurawa ido yasa ya taso daga wajen zaman shi
yazo daga bayana yana duban abinda na binciko.
Jesus ya fada a dan tsorace hakan yasa hankalin mutane ya dawo kan mu daya bayan daya suketa
zuwa duban me muke kallo da har hakan ya jawo hankalin madam din mu.

Ta taso da dan bujenta fingili tana zuwa ta duka itama tana duba chineke god wooo da sauri naga ta
juya zuwa sit din ta ta danna signal ba afi yan mintuna ba saiga su MD IG din wajen sun shigo.

This is miracle tun wajen eight month ke nan muke neman wanan abin amma sai yau ya fito how
comes aka samu shi a yanzu.

Edward ya bar searching din a system din nan kafin ya bar office din nan yanzu kuma wanan yar ta
tonoshi ta bude ya fito da komai.

Tana masu bayani nayi kasa da kaina don idanuwansu dake kaina a lokacin cikin mamaki sun dade
wajen ana abinda ya shafesu a kira wanan akira wancan suna daukan bayanai.

Ni kaina na tsargu da irin kallon da duk wanda ya shigo yake min yasa naji gaba daya na tsani wanan
aikin ma don kada ya jawo min matsala wajen .

Hakan yasa nayiwa kaina alkawarin ban kara binciken account din kowa har nabar wajen lokacin tashi
yayi na fito zuwa gida.

Yazid ya daukoni ina zaune nayi shiru can na lumshe idona nace ka duba motan nan tunda muka fito
nake ganin kamar yana bin bayan mune.

Ke jami,a kamar wasu masu laifi wa zaibi bayan mu muda bamu da komai kuma ba masu laifi muke ba
balle a bimu a baya.

Kila dai tafiya mu kusan gudane amma bari in tabbatar da hakan ko zarginki zai zamo gaskiya sai naga
ya dauki hanyar wani lungu da sauri shima mai motan ya dauka .

Hakan ya tabbatar muna damu yake bi a baya ashe din burki yaja a wani waje hakan yasa mai motan d
alokacin yake gab damu yazo ya shigemu kamar bamu yake biba a baya.

Shiga wanan layin fita sai gamu a kofan gidansu ya danna horn maigadi ya bude muna yasa kai da sauri
zuwa cikin gidan.

Juyowa yayi ya kalleni yace waye wanan din nima shi nake tunane a raina amma abinda mamaki
gaskiya duk da dai ya nuna bamu yake bi a karshe koma waye aniyarsa ya bishi ko inji mata.

Na bude mota zan fita naji ya kira mama yana fada mata ban tsaya naji amsanta ba na fara tafiya ban
daiga ya kara fita ba kuma zuwa dauko

42 / 109