Chapter 95 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   95 / 109

282K to 285K   out of 326.5K words

da basu tsayawa a kullum su dage suna inganta
ilimin kasan kamar na sauran kasashen duniya.

Sai kiga dan baiwa ya kare da iliminsa a titi wajen neman matsuguni ya rasa sai diyan manya da basu
dage wajen daukan ilimin ba sune a karshe suke cin gajiyan abinsu.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[11/26, 9:51 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:




JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

9️⃣6️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6




Yanzu Abby kana nufin yarinyar nan itace ta fidda wanan bayanin da aka kasa fitar maka duk dadewan
nan ?

A hankali ya motsa kujeran da yake zaune inda ya kunna masu cctv din dake office din suka bi da kallo
tun shigowana har abinda ya faru.

Allahu akbar, Abdulradeed bin sultan ya fada shikuma dayan na fadan Ikon Allah , ashe mun tauye
yaran nan matane da muka hanasu ilimi suma mata suna da amfanin su.

Mahaifina dake zaune yana nazari a zuciuarsa yana kuma jin duk abinda kowa ke fada a lokacin saida
ya kasa furta komai a fili zaune yake kawai ya zuba masu ido.

Yana fadi a zuciyarshi lalai Ubangiji mai hikima da basirane buwayi gagara musali mai yin yadda yaso da
bawa mai bayarwa sanda yaso ya kuma amshe a lokacin dayaga daman hakan.

Shi addu,ansa tun yana yaro diyansa su kasance maza bai kaunar diya mace don yadda yake ganin ake
masu sam basu da yancin kansu cikin al,umma.

Mussanman a yankunan su da mata suke cikin bauta a gidajen auren su har tsufansu wanan yasa
lokacin da Asiya ta haifo yar nan mace yaga gara kawai ya barta da yar yai tafiyanshi don ko ya karbeta
bata da wani amfani a garesa.

Ashe abin ba haka yake ba itama ya mace kamar da namiji take wani lokaci ya duba yara nawa suka
tura karatu sun kumayi karatun fiye da wanan yar amma basu da wanan fasahan nata.

Yau gashi yar da ya guda a baya da yake tunanen baiyanata ga a halinsa a lokacin tankar daukan
yukane yayi kirari ya daba wa cikinsa cikin alu,ummanshi.

Sai gashi Allah ya jarabeshi ita dince dai rabonsa a duniya da Allah ya azurtashi da ita don bayan ita
baida wani dan ko bari ba a taba yi a gidansa ba.
Yau gashi kwatsam yar ta dawo cikin rayuwansa har takai ga bada gagarumin nasaran da basu taba
tunanen samu ba haka lokaci guda.

Lalai wanan wani hikima ubangiji yake son tunartar dasu da hakan ace yar da ta taso kasa irin Nageria
tai karatu a can zata samu wanan hikimar haka ina ga da namiji dan Nageria ke nan ?

Dama yana jin kirarinsu cewa idan da za ace Allah mutum ne da sai ace a cikin bakaken fata Allah yake
bakin fatan kuma dan Nageria haka yaji turawa nawa yan Nageria kirari da jahilcinsu.

Don shi dan Nageria yana da naci kan abinda yasawa gaba gasu da hikima da wayau da sanin kan komai
illansu dayace shine yaudara.

Ko hakan ba dukka suka taru suka zamo daya ba don akwai nagari a cikinsu yasha gwadawa yana ganin
hakan akwai masu yaudaran akwai kuma na Allah .

Dafashin da dan uwansa yayi yana fadin me kake tunane haka Omar Abbi na magana dakai bakaji ba ?

Ajiyan zuciya ya sauke mai karfi yana lumshe idanuwanshi kafin yace ina tunane akan hikimar ubagiji
nane baba Allah shine mai yin yadda yaso ga bayinsa.

Na dauka yar nan a yanzu bata da wani amfani a wajena saina tabi sunana ko na ahalina sai gashi ashe
abin ba haka yake ba gun ubangiji.

Ita din mace ce mai kamar maza Allah ya halittota da wani baiwa da basira a tare da ita abinda nake
hangowa ke nan yanzu a zuciyana.

Murmushi mahaifin yayi yana fadin na rigaka wanan tunanen tun jiya wanan abin ya tsaya min a zuciya
har nake jin ba zan taba bari tayi nisa damu ba a yanzu.

Don Allah ya jefota cikin mune a daidai lokacin dayaga dacewan hakan a garemu ita din mace ce amma
tankaraza goma .

Yarinyar da zata iya kwato muna baiyanan dukiyan mu dake shirin salwanta cikin yan mintuna kalilan ta
fitar muna da bayanin komai ai kasan ba karamin baiwa Allah ya aje anan ba.

Yanzu haka ina tunanen abinda yafi dacewa nayi akan yar nan kada hankalin ta ya koma gida saidai
hanya daya nake ganin zan bi shi na aurar da ita a nan ta zauna a tare damu sai lokaci lokaci zata dinga
ziyaran can din a sannu har hankalinta ya dauku saidai su biyota nan din.

Kwarai kuwa Abby wanan tunanen yayi gaskiya haka kawai za ayi yarinyar nan ta zauna a nan tare
damu.

Kai ya fara girgizawa yana kallonsu suma din shi suke kallo a cikin mamaki ya fara fadin kada muyi mata
haka abby ?

Idan muyiwa yarinyar nan haka bamuyi mata adalci ba bamu kuma cika alkawarin da muka daukarwa
iyayyenta na can ba.
Mahaifinane yayi namijin kokari fadan hakan ga mahaifinsu da yan uwanshi inda yaci gaba da fadin
tana da iliminta tayi girman da zamu bata zabi da yancin kanta a yanzu.

Duk da hakan ba laifi bane amma cika alkawari kuma abune mai muhinmanci a rayuwa munyi alkawari
zata koma garesu idan tazo taga waje.

Yanzu kuma muna da bukatanta a nan sai mu jata a cikin hikima da basira ta yadda zata yarda ta zauna
din ba a cikin tursasawan mu ba.

Kuna da fahinta tsakanin kai da ita Abbi ta hakan zaka nuna mata irin muhinmancin da zamanta wajen
mu zai muna haka muma diyanka din zamuna nuna mata so da kauna fiye da irin da can Nageria suka
nuna mata din take kaunansu.

Idan haka kake gani sai mu gwada amma idan wanan baiyi ba ka sani ba zan taba bari wanan yar ta
koma hannu mutanen can ba gaskiya.

Abu daya zan mata shine ko yaushe taji tana son ganin su zan iya turata ta dibosu ko kuma su suzo nan
su ganta shine abinda zan iya .

Hakan ma yayi a cikon hikima da dabara sai a dauke mata hankali da can din saidai na fahinci dukiya ko
wani abu haka kamar baya gababta fa Abbi ?

Duba ga yadda nasha mata tayin abubuwa ko tana da buka amma sam taki sai tace min tana dashi ko
bata amfani da irinsa.

Daga yadda akai mata tarbiyane hakan nima na nazarci wanan tun muna makka yarinyar bata da irin
rigima haka gaskiya Abbi ya fada.

Amma nayi mamakin hakan ban zaci za a samu wanda ya taso daga Africa da wanan halin ba a yadda
nake ganin rayuwansa wani iri a nan.

Allah yana tare damu ba zai yarda mu haifo abinda zai zamo yafi karfin mu ba a yanzu zaku iya tafiya
tafiya wajem harkokinku dama don wanan na neme ku.

Saidai idan naga shawaran nan baiyi ba zan zartan da nawa da nake ganin shine mafita a kan yarinyar
nan haka zamuyi mata mu nuna mata gata cikin ahalin nan namu a yanzu.

Mu aurar da ita a gidan mutunci cikin daraja kamar yadda mukaiwa sauran yan uwata a baya shine
magana ta kuna iya tafiya.

Ganin sun kasa motsawa su tashi yasa ya sake kallosu na ukkun shine ya dan nuna yana da magana don
haka tsohon ya kalloshi yana fadin Haroon kana da magana ke nan ?

Yace eh Abbi kamar yadda Omar ya fada nima haka tunanena yake don yarinyar nan tana da bambanci
dasu Salma tana da ilimi haka kuma al,adan data taso cikinsa daban ne ita .
Idan an hadata da wani hakan ya zama kamar tauye hakkine a gareta zataga bamu kyauta mata ba
duba ga wayewa irin nata a yanzu Abbi ?

Shine nake ganin me zai hana a bata dama aji ra,ayinta a akwai dayawa cikin kasan nan da suka nuna
ra,ayi a kanta.

Zasu kuma baiyano zuwa gareta har in mun bata daman hakan ta hanyar sakar mata wani bussiness da
zata gudanar a nan hakan kuma zai dauke mata hankali da can Nageria.

Abinda naso fada ke nan tun farko a fara fito da baiwanta yadda duniya zasu santa haka kuma
hankalita zai dauku a wanan harkan da za a dorata akai.

Kafin wani lokaci insha Allahu zata kara daga darajan wajen sosai donshi nake ganin kamar zatafi
dacewa da wajen harkan sayar da na,ura ko harkan gwal.

A hankali Abbina ya lumshe idanuwasa don jin yadda yan uwan nasa suke na,am da yarsa cikin so da
kauna a garesu.

Duk da hakan ba abin mamaki bane ko wani sabon abu duba ga irin yadda yai dawainiya da fama da
nasu yayan ga baki dayansu a baya.

Don sun masa haka ga nasa wanan ba wani abin mamaki ba duk da irin tashin hankali da fitinan da
matarsa keyi akan hakan bai sa ya fasa daukosu ya masu abinda ya dace ba a matsayinsa na wanda yafi
ubansu karfi da fada aji a cikin gwaunatin kasan.

Zan iya cewa kusan shine nabiyo wajen hazaka da baiwa don shima duk abinda ya saka ransa Allah na
basa ikon cinma wanan abin cikin yardan ubangiji.

Zaman kadaici da kewan gida sune a yanzu suka taru sukai min katutu saboda zama waje daya gashi
banda wani labarin yan gida da zanji ko kewansu zai ragu a zuciyata.

Daga kwancen da bara ya fado min in gwada duba daya daga cikin mutanene ko Allah yasa watansu ta
samu waya da zamu iya charting da ita na dai san kodana bar gida babu mai wayan kwarai a cikinsu.

Abin mamaki kuwa ina shiga online na samu sakon samira dana Asmau harma da farida a take nayi
reply din sallamansu tare da aje masu voice massage don basu online dukkan su a lokacin.

Amma sai naji kamar suna online ne a lokacin hakan ya saukar min da farin ciki lokaci guda namike na
fito daga dakin a cikin walwala.

Don damuwana ya gushe a lokacin ina jin kaina tankar munyi waya dasune a ranan .

Dolene kadaici ya dameni don ba kawa ko abokin fada ko wani wanda zan zaune dashi muyi hira watau
komai da mutum ya gani a duniya yazo mai hakan damane daga ubangiji.

A gida sai inga ai sun dameni da hayaniya ko yawo sai gashi a nan ina neman hakan ban samu ba don
ba wanda nake wani hurda dashi ko nasansa balle inje gurinsa.
Firowana yayi daidai da zuwan wanan Faisal din muka gaisa yake fada min kana yana nemana a
falonshi shidasu Abbi.

Tare muka jera zuwan falon dashidon amsa kiran ina ganinsu sai naji gabana ya fadi tunda nasan wani
zance mai muhinmancine a kaina ganinsu hakan gaba dayansu.

Irin gaisuwan mu na hausawa nayi masu Lah lah lah haram haram kakana ya fada daga inda yake hakan
yakan fada duk lokacin dana manta nayi wanan gaisuwan na duki dana saba dashi a gida.

Murmushi na dan sake kafin na juya zuwa nasu kalan gaisuwan ya nuna min waje in zauna na kai
zaune din a takure ina saurarensu.

Tambayana suka soma da sabon yanayi na amsa da alhamdullahi yace masha Allah sun kiranine don su
fada min hukuncin da suka yanke a kaina.

Jin hakan yasa gabana faduwa lokaci guda da har na dago kai ina satan kallon yanayin kowansu a
hankali saidai ban fahinci komai a fuskan su ba da zance ga abinda ke shirin faruwa dani din lokaci

Dan shiru ne ya biyo baya kafin kakana din ya soma magana cikin wayewa da gogewa da duniya yana
fadin naga yartawa zaman kadaici yai mata yawa a yanzu don shine muka yanke shawara.

Zaki fara bussines damu a nan mu doraki a hanya kasancewa mahaidinki baida wasu diya da yawa da
zasu tayashi harkokinsa.

Duba da irin baiwa da ilimin da kike dashi duk da bamu taba barin wata ya mace ta shiga harkan
kasuwancin mu ba tare da aure ba.

Jin hakan yasa na dan dago nayi mai kallon ido da ido na dan lokaci yace kwarai yayan mu a nan muna
masu auren wurine da sun tasa shekara sha biyar zamu aurar dasu.

Amma duba gake ba al,ada guda ya tarbiyartan dake ba da namu yayan na nan koda munyi hakan a
yanzu hakan ba zai zamo wani abin tsegumi ba tunda kinzo muna da ilimin ki ba zamuso mu tauyeki ba
mu hanaki cika burin ki na rayuwa.

Munsan mutum yana ilimine don cinma wata manufa a rayuwansa donshine ba zamu tauyeki ba a
yanzu don alkawari mukaiwa iyayyenki da hakan .

Saidai ni a gaskiya naso na aurar dake a nan koda zaki koma da aurenki da mijinki amma iyayyen ki gasu
nan suce dani a,a mu barki kiyi irin na al,adanku nacan da kika taso a cikinsa.

Wani kallo nayi mai yasashi fadin kwarai shawaran da nayi ke nan a farko amma sun hana hakan a
gareki ya fada yana kallona.

Murmushi na dan sake a fuskana mai baiyana jin dadin hakan a gareni yake fadin da naso aurar dake
ga daya daga cikin basaraken kasan mu don kije can ki koyi al,adunmu na gargajiya sosai.
A,a abi a barta ta zaba dai a nan yayan mahaifina ya sake fada tare da fadin ko ba haka ba yata da fatan
zaki zabo muna dan mutunci da kimar kamar yadda kike mai mutunci din nan.

Haka dai suka soma barkwanci kafin inji maihaifina yayi magana a karo na farko tun zamana wajen naji
yana fadin zuwa monday in Allah ya kaimu zaki fara fita office dan uwanki na nan zai nuna maki yadda
abubuwan suke tafiya a wajen.

Naji dadin hakan sosai kuma banyi tunanen komai a kaiba lokacin jin zanyi aiki in huta zaman banza ko
wani wahalan tsayawa neman aiki din irin yadda naga mutane da yawa nayi a Nageria.

Ka kare karatu ka koma kuma zaune don gwauni bata san yadda zatayi da yan bokon nata ba a can haka
kuma babu wasu kamfuna masu yawa da zasu iya tsayawa su dibi ma aikata a wajen ko za a rage yawan
masu zaman banza.

Koda na bar wajen Allah Allah nake in samu wani na gida da zanwa wanan albishir mai dadi ya tayani
farin ciki saida ban samu kowa ba hakan yasa na hakkura ina murna ni kadai a raina.

Ina kuma fatan monday din tayi in soma fita kamar yadda suka umurceni da yi din a wajen kakana nake
jin cewa mahaifina ya saya min mota da zanyi amfani dashi nan din.

Ranan jumma,a bayan nagama komai ne nace bari dai in bude data in shiga online hakan nayi ina
budewa naga samira online itama.

Sallama nayi mata saida aka dauki lokaci naga tana ban amsa nan muka fara hiran yaushe rabo take
fada min irin kewata da sukayi.

Har take tambayana yaushe zan dawo nace ba lokaci don ma aiki zan soma zuwa a nan company
mahaifina .

Mummy kardai ance kin tafi ke nan nace haba dai me zai hana in dawo samira zan dawo ai idan na
gama ganin gida.

Karshe dai na gwada kiranta video call ya shiga nan naga kowa da nayi missing a gida har Abbu ya karbi
waya mun gaisa dashi a ranan.

Barci nayi sosai ina mai farin ciki a zuciyana kamar in bude ido in ganni a gida amma ina a yanzu dole
inyi hakkuri a wajen iyayyena maza kamar yadda nayi a can baya.

Dama ba haushe yace da gidan ubansa akan sanshi don haka zama ya zama min dole sai washegari na
samu man da murta nake sanar dashi abin alherin daya sameni.

Amsan daya bani shiya kashe min jiki dayace I know GF kin tafi ke nan ba zasu taba bari ki dawo
Nageria ba kuma rayuwan ki gaba a yanzu zai koma can ne.

Kamar yaya na tambayeshi yake fadin aida zaran kin fara aikin nan kuma shike nan mu da ganin ki
kuma sai wani ikon Allah kuma.
Dan murmushi na sake ina fadin saboda aiki zanki zuwa gida ba saboda aiki ba saboda abubuwa da
dama da zasu taso maki yanzu ai.

Haka dai ya shashantar da zance yadda ba zan gane nufinsa ba mukai sallama sai daga baya na soma
tunane saidai zuciyana taki yarda da cewa hakan zai iya hanani komawa gida din a lokacin.

Don ganin irin cigaban da rayuwana ya samu ga aiki a hannu ba ko a Nageria ba abinda yasha fada min
ya zama gaskiya dakewa da karatuna zai zamo min alheri a rayuwana nan gaba gashi ko nagani din a
yanzu.

Yau da ace banda ilimi ko wani wayewan kai duk yadda sukasoni ragagene tunda yanzu na kula din
karatunane ya saka sukai wanan tunanen a kaina.

Tsab na shirya monday din zuwa company mahaifina kamar yadda naji sun fada a wajen shi zanyi aiki
da zan soma din.

Wurime daya karba sunan waje zakice da glass zalla aka kera wajen don tundaga waje har ciki abin
kallone a yadda wanan Faisal din ke fada min wajen sabone ba,a dade da budeshi ba.

Matar mahaifina taso Autansu ya zauna wajen amma Abbi yaki yarda da hakan donshi kansa ya gina
wajen hakan gar ya jawo masu sabani a tsakani su.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

[11/28, 9:59 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:




JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

9️⃣7️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6




Kallo daya naiwa company na dukar da kaina don zuciyana da nake jin yana min soya kan zancen da
muka gama da Faisal a ciki

95 / 109