Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
bari taje baraka ta illantata a ciki ita da hadiyace suka shiga saita nufo dakin tazo
ta samu muna zaunar da ita na juya zan dauko abincin a zuba mata saiga ta.
Sannu da fitowa ummu na fada hankalin ummu din ya kasu gida biyu ta kalleni ta kalli Hindu din da duk
ta fada na mika mata plate din dana dan zuba mata abincin .
Kin falka ashe ummu ta fada ta dan daga mata kai umma ta sake fadan to yaya jikin naki tace da sauki
cikin yar siririyar murya.
Kici abincin sai ki kwanta ummu ta fada bari in dan zauna tace tana diban abincin aka turo kofa
mahaifinsu ne yashigo kallo daya zakai mai ka fahinci damuwa karara a fuskanshi .
Duban mu yayi yana fadin yaya akayi nan ummu ke fadin yanzu nima nashigo na samesu da ita ashe ta
falka daga barcin .
Ya dan dubeta yana fadin yaya jikin naki tace da sauki Abba cikin yar murya dake nuna jikinta ya tabu a
lokacin.
Meke damunki yanzu sai kuma ya dubi abincin dake hannunta yace kici abincin mana kada yai sanyi.
Fuska ta bata alaman bata son abincin nace anty ko a hado maki ruwan zafi kila zaifi dadin sha gareki
yanzu sai ta gyada min kai alaman eeh.
Na juya zan tafi naji Abban na fadin kinga ranan dan uwa ke nan sai hadiya ke fadin wallahi itace tazo
ta kirani mukai mata wanka ta gyara dakin ai dan uwa akwai dadi wallahi.
Allah ya sauwaka Abban yace ya juya ya fita daga dakin ya barsu da ummu dake dan mata nasiha tare
da fadin da kinji zai motsa maki kiyi magana kinji kisha magani.
Haka dai mukai ta fama da ita na mayar da hankalina ina bata kula sosai duk da ba wai ta sake bane
fuskanta a daure yake tamau .
Ban bi ta nata ba tunda nayi alkawarin taimaka mata ko bata son abu zan matsa ta tashi tayisa irinsu
sallah wanka cin abinci da sauransu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[11/7, 7:18 AM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
8️⃣6️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6
https://sitrix.africa/signup.php?ref=foleesco
Sannu sannu dai har na saba da hakan zan lekata da safe nagaida ita haka kuma idan na koma barcin
safe na tashi nayi wanka zan kara lekata indan jima a dakin.
Tun ina daukan hakan a matsayin ramuwar alherina ga Abba har yazo ya zame min jiki shiga gaida ita in
bata dan kulawan daya dace a taimaka mata dashi.
Tun tana shareni tana bina da harara idan nashiga itama tagaji ta sauko dole nike taimaka mata da
wasu abubuwa don jikin kamar yai mata nauyine nake gani.
Ya Allah ka raba dukkan musulmi da fadawa cikin wanan rayuwan na shaye,shaye ka kare zurian kowa
da ganin wanan bala,in amin.
Don gaskiya raba mutum da shaye shaye ashe ba karamin fitina bane hakan don ko nagani ga boyar
Allah nan yadda tasha wahala sosai.
Yauma kamar kullum hakan ya kasance bayan na tashi nayi wanka na karya na nufi dakin nata a zaune
na sameta tayi shiru tana tunane.
Tunda nayi sallama ta dago kai ta dubeni ta kawar da idanunta a kaina niko nace a,a yau anty zaune
ake ?
Tunda jiki yayi sauki bari mu tsefe kan nan naki don Allah ko kalabane nayi maki manya yafi ki zauna
dashi hakan .
Zanso hakan nima don kan yana damuna da kaikayi saidai banson abinda zai taba min kan a yanzu don
wani irin abu nake ji a cikin kan wani lokaci.
A hankali zan tsefe maki ai sai a kwashe koda kalabane yafi na juya na fita na dauko cumb da tsinke na
bayan kan zama tayi kada ina bakin gado na fara tsefe mata kan a hankali.
Sai ajiyan zuciyan nan nata da takeyi ko a lokacin shi take faman sakewa lokaci lokaci muna gab da
gamawane iyayyensu maza suka shigo dubata don abinda na kula shine.
Iya sune yan dakin hjy mai babban daki ke faman sintiri dubata bayan su ba wani bare dake zuwa
dubata.
Gaidasu mukayi nikan gaisuwana har kasane dama don saida na zamo saman gadon na gaidasu din.
Yayin da ita kuma hindun daga yadda take zaune ta gaidasu daddy man ke tambayan yaya jikin nata ?
Shi kuma daddy imamu yana fadin sakariya wanan data gaidamu cikin mutunci tafiki ne a wajen mu ?
Matsalan ke nan ai Kura ta gama lalata yaran nan ga baki daya kowa basu ganin girmansa a idonsu ai .
Har suka juya suka fita daddy imamu yana kan mata fada shi kuma dayan daddy yana cewa zata daina
ai tunda tana ganin anayi yanzu nan inda take.
Shikuma Abba naji yace kadama ta daina da sannu zan shiga rigan arzikinta gidan nan idan bata bar
wanan halaiyan banza ba.
Koda suka fita dakin yayi shiru na dan lokaci dagani har ita ba wanda ya iya magana a cikin mu jin
shirun yai yawa nake fadin .
Gashi har yanzu ba akira ba zaman jitansu nakeyi a nan da sun kira zan wuce service ina fatan su kaini
inda na rubuta don ina son in kara aiki a inda na taba koyon aikina Abuja.
Wai kina nufin kun kare nace mu muka gama wanan shekaran ai ku kuna gaban mune sosai aida
gamawa ina ji.
Sai naji tace ba haka bane kunyi sa,aku mu har yanzu ai bamu karasa ba da saura ni yanzuma gaba
daya na daina zuwa fa.
Sallaman da akayine ya hana fadan wani abu ko yanzu din iyayyenta matane nake ganin sunzo dubata.
A,a masha Allah jiki yayi sauki mami ta fada yau har da tsifan kai haka hindatu ?
Hjy ko tazo a sa,a yau ga fuskanki nan shar dashi wallahi gaskiya jiki kan yayi sauki wallahi saiga su suna
shigowa sunkai su biyar dakin.
Ban daki na shiga don in wanke hannuna kafin mu gaisa nake jin wata daga cikinsu na fadin kina da
hankali kika ba wanan yar kanki tana maki tsifa ?
Yar kishiyace fa ba abin yarda bane irin su ana neman lafiyaki zaki sake harda bata kai ta tsefe maki ?.
Bayan hakan ma a zatona kamar Sayadi da wata manufa ya zaunar daku gidan nan tare kada dai tayi
saurin sakin jiki dasu haka gaskiya .
Karan budan kofan nafito daga bayi ina yarfe hannuna yasa suka juyo wai ashe a zatonsu fita nayi waje
suke wanan maganan dama .
Gaidasu nayi zan fita naji mami na fadin Ayshaa kike ko gasu hjy da sister dinta ku gaisa ta nuna min
tsofin biyu dake hakince saman kujera zaune.
Juyawa nayi zuwa inda suken na kara gayar dasu naji basarakan tace au itace wanan yar tana mai kura
min idanu na dan lokaci.
Fita nayi na basu waje sam banji dadin zargin da sukewa mahaifiyata ba saidai banda hirumin da zance
wani abu wanan yakin natane a yanzu.
Falon babu kowa don haka na nufi wajen anty baraka a zuwa lokacin Allah ya gani zaman wanan gida
nikan ya fita min rai zan iya cewa run zuwan hindu komai ya jagule kuma.
In ma donta natane da sauki ai amma irin maganganun dake fitowa bakin matan nan gaskiya ya fara
damu na.
Ban jima ba saiga ummu a dakin take fadin au kina nan ashe na dauka kina dakin ne ai har yanzu nace
zuwan matan nan na fito.
Matar maigarice fa mahifiyarsu yaya imamu da Ahmed tare da yar uwar haihuwanta kakan mam bashir
ke nan ai ta uwa don abu daya suke akace.
Kinga ko dole suzo dubiya tunda itace ta haifi uwar hindu din kinsan nan dai tashiga min bayani akansu
nasan ashe ba karamin halaka bane a tsakaninsu.
Sun tafi ai tun dazun nasan ba zan taba fari a gurinta ba shiyasa ban ma wahal da kaina binsu ba don
gani suke kamar nice nayiwa yar tasu asiri wanan matsalan ya sameta.
Bamu da gadon hakan komai namu ga Allah muke barinsa anty barakace naji tana fadan hakan cikin
tare ummu data dauko zancen.
Aisu basu gane hakan tunda kamar kishiya nake a wajensu suna dauka saboda nice Sheck ya rabu da
yarsu .
Sam basu ganin girman laifin data shuka akansa ko kadan sai kokari suke su dora min laifin ko ina asiri
me zai kaini yiwa dan kishiya hakan ?
Sam sam ban son zance saidai ba yadda zanyi sai naji ko banso tunda uwata zancen ya shafa kuma ina
gidan a lokacin.
Ban koma dakin hindu ba saida ta aiko hadiya cewa nazo na kama mata kan yasa na koma ina gama
mata kuma na kakabe jikina na fito na bar dakin.
Gyara shine mace akace don ko wanan kitson ya fito da fuskanta daya sauya abaya saidai nayi
mamakin jin kalman godiya a bakin ta lokacin dana gama zan fito daga dakin.
Kwana biyu dai na fara jayewa daga shishigin dolen da nakewa hindu dama ban iya ba na dolene don
in gyarawa mahaifiyata zuciya da zamanta.
Sai gashi naga ana son kawo min cikas a cikin lamarin a lakaka muna abinda bamu taba tunanen yinsa
ba a rayuwa.
Ga kewan iyayyena dana sa a rainadon har yau da nake da sati ukku da zama wanan gidan babu kowa
da yazo dubana ko wani abu a gidan nan.
Har anty safiya saidai kullum mu gaisa a waya dasu ko inji ummu na waya dasu tana fadin muna nan
kalau ba wani matsala.
Ai yanzu na sake tankar bani ba hakan naji tana fada ko ranan wanan yasa nashiga damuwa donko
gaskiya gida kawai nake son zuwa a lokaci.
Abin mamaki har dasu maryam ba wanda ya tako kafansa ya biyoni nasan ko dokan Abbu ne wanan a
kaina.
Balle yadda ya rufe ido ya hana Asmau biyoni a lokacin yaci mata mutunci yana har yana ikirarin idan
bata zama ta koma gidan ubanta .
Murmushi nayi dana tuna wanan ashe don akawoni nan in zauna da ummu aka shirya hakan ?
Ta kula kwana biyun nasakawa raina damuwa hakan yasa ta sameni daki da yamma ina kwance ni
kadai a dakin ba komai nakeyi ba a dakin koda tashigo.
Ganinta yasa na mike zaune ina gaida ita ta amsa tana bina da kallo kafin ta samu bakin gadon tayiwa
kanta wajen zama a nan.
Dan shirune ya biyo baya kafin naji tace Ayshaa meke damun ki a yan kwanakin nan kika zabi zaman
daki haka ke kadai ?
Ba komai ummu na tari numfashi ta kafin ta dora ba komai kike shiga daki tun safe ki zauna farki kina
zuwa wajen baraka kuna hira yanzu duk kin daina.
Wajen hindun ma da kike zuwa har sheck najin dadin hakan gaba daya kwanakin nan kin daina why me
yake damun ki kike boye min ?
Ba komai ummu kawai dai gida nake son zuwa ummu ina son inje inga iyayyena don Allah ?
Amma dai kinsan suna lafiya tunda a kullum kuna waya dasu har kin gaji da zama damu ke nan ko ?
Ba haka bane ban saba zama ban gansu bane haka don Allah ummu kicewa Abba ina son in koma gida
hakana.
Sai naga tayi shiru na dan lokaci kafin kuma tayi murmushi kadan tana fadin saidai kije ki fada mashi
da kanki don bansan yadda zance kince kina son komawa gida ba a yanzu.
Sai naga ta mike tsaye tana fadin idan zaki saki zuciyar ki garama ki sake don banjin zaki koma gida
yanzu kuma .
Gabanane ya fadi don jin hakan na dan dago ina kallonta takai kofa koda take fadin hakan kamar insa
kuka sai naga ta fita.
Shiru nayi ina tunanen hanyar da zanbi a cikin sauki in koma gidan mu din wajen iyayyena dana saba
dasu ko yaushe na leko waje zanyi tozali da dayansu .
Sabanin nan da sai in ta fito ko tana bukatan wani abu zan ganta muyi magana akai balle mijinta da
wani lokacin sai wajen cin abinci kawai muke haduwa da juna.
Banga amfanin kuka ba don hakama kukan baizo min ba a lokacin haka na daure ina ta faman sake
sake a raina.
Haka kuma banyiwa Abbu zancen ba ko a cikin waya na share kowa ina yan harkokina a gidan kamar
na sake zuciyana ba komai.
A wani gida dake cikin unguwar masu karfi dake tsakiyan Dubai tsohon ne tare da yayansa maza su
hudu zauna .
A wani katafaren falo cikin suna tataunawa da tsohon dake sauraren su kowa yayi tsit saishi babban
dan nasa dake magana.
A hankali tsohon da ya ke rike da babban photon a hannusa sako da lungu na jikin yarinyar dake jikin
photon yake bi da kallo kadin ya dago kai yana jijiga kansa ya dago yace.
Hakkun yarinyar nan indai itace jikina ya ban jinin muce ita tun ban ganta ba don wanan digon dake
gefen fuskanta mafi yawan mata daga cikin mu suna dashi haka.
Haka kuma idon ta sak na gidan mu ta dauko har hancinta da mutane ke muna kirari akansa namu ne.
Abdulrashid ya ambata yana dago kai yana kallon yayan nasa dake zaune suna kallonsa cikin mamaki.
Don basu taba zato ko tsamanin samun saukin kai haka daga mahaifin nasu ba don sanin halinsa da
sukayi shi irin mutanen nan ne dake tsaye akan zuriansu ko yaushe .
Wanda aka kira din ya dago kansa yana kallon mahaifin nasu don yaji abinda zaice a lokacin duk da
alamun yadda yake kallon photon yana nuna masa gamsuwa a yanayinsa .
Wani shiri kake dashi kan zuwa dauko yarinyar nan ina son in ganta in kara tantance hakan a fili ?
Don yarinyar gaba daya yanayin family din mu ta debo wanan da ganinta ba tantama jinin muce ita
indai har hakan take ?
Baba a yadda na shirya nan da karshen shekaran nan zamu isa kasan mu gana da iyayyenta na can kan
zancen zuwanta nan din.
Don bamu san da wace irin tarbo zamu samu a wajensu ba idan munje don shine nake son mu kira
abokan hurdan mu na can kasan suyi muna bincike aka al,adan kasan idan haka ya kasance.
Anya kuwa hakan daka tsara baiyi tsawo ba ku dai sake shiri kayi abindaya dace don a kullum alhakin
yarinyar nan yana bin dan uwankune.
Bama shi kadai ba har mu nan duk da bamu sani ba amma muna da kamishon hakan a wajen Allah don
na tabbatar ko a gidan saraura take halinda take ciki na rashin uba yana sakata kuka.
Basai ka tsaya kiran wani ba yanzu haka wanda ke auren mahaifiyarta muna bussiness dashi tsawon
shekara ashirin da wani abu amma ban san shike auren uwarta ba sai yanzu.
Nan yake basu labarin yadda ya ganosu dan zuwa gidan nasu da sukayi har yaga ummu din ikon Allah
tsohon ya fada a karshe.
Nan dai suka tsayar da zancen akan tafiyan don haka tsohon shiyasa su ware kudi daga asusunsu don
wanan tafiyan da zasuyi din idan sun kirashi wanda zai masu jagoran suji.
Zasu dawo suyiwa tsohon bayani akan yadda suka tatauna da mutumin a hakan suka aje zancen nasu
sukayi sallama dashi .
Anya hjy yayasayadi ba wani shiri yakeyi akan yaran nan ba don a yadda matarsa take fada min shiya
matsa kan yarta ta dawo nan wajensu da zama.
Gashi kuma ya mayar da hindu gidansa cikin kulawansa ni sai zuciyana ke ban cewa kamar yana da
wani manufa akan hakan ?
Kura dake zaune shiru ta gama jin halin da aka gano yarta ciki na sauki saidai zuciyarta bai yadda cewa
wai don shaye shayen da aka hanata yi yanzu da karfi da yaji bane ta samu wanan matsalan kamar me
tabin hankali.
Saukin abin wanan labarin da yau Nasare tazo dashi na cewa ta samu hindu din da yan gidan a garden
suna shan iska.
Kasa hakkuri tayi ta dago kai tana katse hjy Nasare dake wanan bayanin da cewa Nasare kin fada mata
ta daina yarda dasu hakan da takeyi.
Akan me zan fada mata mutanen da suke sakata nishadi ana ganin sauki yaya zan koma kuma ince
kada ta yarda dasu ?
Wanan ai sai su daukeni munafuka su kuma daga zuwana sunga sauyin fuska ga yarinya nikan gaskiya
ban fada ba .
Waiko yaya kinga yadda hindu ta koma yanzu kuwa naso ki daure muje gidan dake ki ganewa idon ki
yadda ta murje tayi kyau sosai wallahi.
Mahaifiyar tasu ta katse masu zance da fadin ke dake zuwa bai wadatar ba sai ita taje taje ganin takaici
ko daukarwa zuciya magana ?
Koni kaina ranan na dawo da mamakin Sayadi a raina haka kuma na kula da wani abu ashe gaskiya
manya keyi hada maraye cikin zurian ka yana dakushe maka hasken diyan ka.
Da a karshe sai dai subi bayan shi na tabbatar da wanan abin a ranan kan Sayadi duk addu,an da nake
kwana da wuni akan yaron nan ashe yake fadawa.
Haba mama don Allah ai suma nakin suna da nasu daidai gwargwadon da Allah ya basu tayi tsuki tana
kawar da kai gefe daya alaman ke yarinyace Nasare.
Falon ya dauki shiru na dan lokaci kafin ta juyo tana fadin Nasare ki duba ko dakin da yarinyar nan ke
rayuwa kawai a cikinsa don Allah yadda aka tsarashi da kayan alatu ?
Mama ni banga wani anbin damuwa ba a nan tunda yaya Sayadi kowa yasan tun farko yana da zafin
nemawa kanshi don anga wanan aiba abin mamaki bane yanzu.
Kaiya ta fada taja tsuki bata kara furta komai a bakinta ba saidai zancen ta ya saka kura dogon tunane
na dan lokaci don taji tana son ganewa idon abinda ke cikin gidan tunda har hjynsu tayi wanan magana.
Tasan abin bana wasa bane abinda idonta ya gano mata don haka ko yayane zatayi amfani da wanan
daman tasan yadda ta shiga gidan ta gani.
Kafin ta dawo ta soma shirin dake ranta dama zanga zanga don ba tajin