Chapter 4 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   4 / 109

9K to 12K   out of 326.5K words

kasance mace da bata da son hayaniya dama.

Dan dagowa tayi tana kallonsa tace ba komai sannu da zuwa ya amsa yana kallon inda yaran nasa suke
zaune.

Kafin ya shige daki juyawa tayi itama ta shiga dakin ta sameshi kaya yake kokarin sauyawa a lokacin
saboda dare da yayi yake fadin kince ba komai kuma naji kina jawa aimana kunne ai ?

Bata jine nayi warning dinta kan matan dake zuwa gidan nan kitso tabar shiga lamarinsu amma batajin
hakan idan suna zancensu wani lokacin zakaji ta tsoma baki ita karama da ita ina ita ina shiga zancen
manya don Allah ?
Yace hakan ba kyau gaskiya ki dinga tsawata mata tundai irin matan nan da yanzu suka gane zuwa
gidan nan ko ba a fada ba yan duniyane nima nayi tsoron hakan gaskiya.

Amma da nayi tunanen halinki sai naga in dai kece ba za a samu matsalan komai ba kuma Allah ya kara
karewa din ku dai bi komai a sannu.

Tunda baku san inda suke fitowa ba haka kada azo watarana ace ai gidan nan wani jidali ya faru a
dalilin zuwa kitso nan kinga sai anbi a sannu komai.

Ya gama shirinsa ya fito waje inda tayi masa shimfida ya zauna yana magana da yaransa dake gefensa a
zaune kafin ya mayar da hankalinsa kan yaran abincinsa.

Yana budewa yaga tuwon shimkafa tayi lafiyayyen miya ya dago ya dan dubeta yana fadin yau ciniki
yayi kyau ke nan haka banga abinda na kawo anyisa ba ?

Nasan zakayi magana ai tukwicin kitso aka kawo min yakai kwano shida ko bakwai koma yafi hakan har
da kudin kayan miya ta hada min wata hjy ce dattijuwa haka nayiwa kitson kullum tanawa Aimana ba,a
tana kiranta da sarakuwar ta.

To Allah ya saka mata da alherinsa shimkafa haka mai uban yawa har kwano shidda mama Aimana
zatayi magana taji yaran sun kaure da fada a tsakaninsu.

Wanan yasa ta dakatar da zancen dataso ta furta ta mike zuwa wajen yaran dake fada kan kashi tana
raba masu gardama a lokacin.

Ba komai sukewa fada ba dan kashin miyan data saka masune bakai nasu hudu ba wajen ta rabo shine
dalilin wanan fada ta juya zuwa wajen telen miya ta dauko mai dan girma ta mikawa Aimana din da
bataba da farko.

Mijin na zaune yanaci gaba da cin abincinsa saidai hankalinsa na wajensu har lokacin kafin matar nasa
ta dawo inda yake tana fadin.

Naso in dan debawa Ammah koda kwano dayane daga cikin shikafan nan akai masu suma su dan sa
albarka yace hakan yana da kyau shine zama tare ai.

Ya fada yana taunan kashi don yasan koda matarshi taba aminiyar nata kuma uwar dakinta dan abinda
ta samu batayi aikin banza ba.

Don Ammah mutumiyar kirkice a wajensu dan zaman su tare zakace yar uwarsuce ta jini don abinsu a
yanzu ya koma kamar zumunci a tsakaninsu.

Don ko haihuwa tayi Ammah na tsaye da ita sai tayi arba,in zata zauna gidanta taga ta samu lafiya da
karfi hankalin Ammah ke kwanciya hakan yasa itama Rakiya din ta dauki Ammah din tankar yar uwarta
na jini a cikin unguwa duk kuma sanadiyar zaman unguwane kawai ya hadasu.

Zan iya cewa dasu kawai suka yarda suke hurda na cancan a tsakaninsu har suna iya fadawa juna
damuwansu wani lokacin wanan ke nan.
Aeeshace take sauri don aiken da Ammah din tayi mata tana saurine don gudun fadan mahaifiyar nata
don tasan aiken yana da muhinmanci.

Duk kayan data jawo bai fita gareta don zama tsuman da kayan sukayi ko kuma suyi mata kadan sub
dage mata a yanzu sakamakon girman da jikinta ya kara a yanzu.

Sai wani bakin rigane wanda Ammah din tayi ta faman boyo shekara da shekaru sai yanzu kuma ta
mannawa Aeesha din a yanzu don takai munzalin amfani da rigab a yanzu.

Saidai tana jawoshi ta tsaya ta kurawa rigan ido na dan lokaci kamar tana tunane akai kafin zuciyarta ya
bata amsa da kwarai tabbas sune din.

Rigace wanda taga matar da Abbu ya ambata da nana kuma wai itace mahaifiyarta wace ta kawota
duniya ta watsar da ita ta bata a cikin tsana da kyama a yanzu.

Zakice matarce tsaye a gabanta a lokacin takewa kallon tsana da bakin ciki a zuciyarta lokacin wani
hanzari tayi tana wurgar da rigan dake hannunta din tana cika tana batsewa tare da jera tunane a
zuciyarta.

Juyawa tayi bayan ta dauki rigan ta nufi kofan fita daga dakinta a lokacin saidai tana fitowa daga dakin
tana jin muryan Aimana dake sallama tana shigowa gidan nasu a lokacin.

Wanan yasa ta dagata daga yunkurin zuwa dakin mahaifiyar nata ja tayi ta tsaya dole tana amsa
sallaman duk da zuciyarta ba dadi a lokacin tana fadin Anty Aimana kece.

Ehh Aeesha ina Ammah tana dakinta ta fada sanin su ba bakin gidan nasu bane sun saba shiga dakunan
nasu yasa ta fada masu haka kai tsaye.

Tana tsaye da wanan rigan a hannnunta har lokacin bata koma dakinta ba taji Ammah na fadin Aeesha
ina kikene wai dauko min kwano daga nan waje.

Hakan yasa ta yada rigan a kofanta ta nufi inda roban yake ta dauka tana nufar dakin mahaifiyar nata a
lokacin.

Tana shiga dakin idonta ya sauka saman shikafan gwaunatin dake cikin roban da sukazo dashi din
mikawa Ammah roban tayi ta karba ta juya ta fita daga dakin ba tare data tsaya nuna wani damuwa da
abindake wakana a dakin ba.

Miskilanci da izza da isa irin na Aeesha yana damun amma sin yarinyar duk yadda tayi ta rage wanan
halin sai ya zamanto kamar tana kara ingizatane a lokacin yadda take haka ta saka hijjab dinta saman
kayan ta fita zuwa aiken nata a lokacin.

Sai bayan tafiyan yaran Ammah ta fito rakasu ta dawo ta hango wanan rigar da Aeesha din ta jefar a
wajen cikin mamaki Ammah ta karasa wajen rigar tana dauka.
Bin rigan tayi tana tuno da abubuwa da dama dasuka faru a sanadiyar wanan rigar da yar nata ta yasar
a kasa a yanzu rigace mai dibin tarihi a wajen su don ya zamo rigace dake tuna masu da abubuwa da
dama dasuka faru a baya.

Da wanan rigan yar uwarsu ta baiyana a garesu cikin kunci da bacin rai rugume da kaddaran rayuwanta
Aeesha da suke kyautata zaton da yau ba Aeesha a raye da yanzu suna rayuwa da yar uwarsu a cikin
sallama.

A hankali ta duka tana daukan riga a kasa tare da furta kayya wanan yar da ace kinsan mahinmancin
wanan rigan a gareki Aeesha ba zaki taba gangancin yada rigan nan a kasa ba a yanzu.

Bayan daukan rigan a cikin karfin hali sannu a hankali takai rigan a hancinta tana sunsuna don tabbatar
da shakan abinda take sonji a hancinta lokacin.

Kamar ta kadu don yadda tayi saurin cire rigan a hancinta cikin sauri bayan shakarsa da tayi na dan
lokaci.

Ba komai yasata hakan ba saijin har wanan tsawon lokacin wanan rigan yana kamshin yar uwarta da ta
bata tsawon shekaru da dama.

Wanan kamshin Nana ta dawo masu dashi tanayi wanan kamshin ita kanta yarta keyi wanda kamshine
na daban wanan turare yakeyi kamshine da banda wajen yar uwar nasu a lokacin basu taba jin wanan
kamshin ba sai kanta.

Hawayene suka taru mata a idanunta lokaci guda don tuno da yar uwar nata tare kuma da irin bakin
ciki da takaicin da dawowanta garesu ya kumsa masu a zuciya wanda har yau ya kasance tana girbansa
ita a zuciyarta

[7/30, 11:00 PM] Zainab Idris Makawa Writer: ELSUTRA HOME OF FASHION & BEAUTY ACCESSORIES
AND BEYOND

MAMAN BIBO KAYAN MATA

08068871330 KOKO ROAD SOKOTO




JA YA FADO,,,,,,,,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
00️⃣55️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,



YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,




HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,




Murmushin takaici ta sauke ta kara kame rigan a jikinta kamar hakan zaisa ta jin saukin abinda ke kunar
zjciyar ta tunane ta fada na dan lokaci akan hakan.

Lokacin nashigo da sallamata idonane ya sauka akan rigan dake rike a hannunta rugume kamar mai
tunane a lokacin.

Cikin karfin hali idona akanta nake fadin Ammah na dawo tace ingaidake ta gode kaita dago ta sauke
min kallo da idanunta da suka kada sukai ja a lokaci guda ba yadda na barta ba da zan fita.

Na juya zan shiga daki naji muryanta tana fadin Aeesha yaki zo nan hakan yasa na juyo na dawo inda
take rigan dake hannunta ta jefo min kafin na karaso gareta tana fadin.

Kinsan daraja da muhinmancin wanan rigan a wajen mu kuwa da kika watsar dashi a nan wajen kanki
daya kuwa idan baki sani ba yau ki sani wanan riga da kike gani darajarta tana da yawa a garemu.

Saidana dan kara kallon rigan da take kokarin miko min na mika hannu na karba a hannunta makin na
nufi dakina dashi saina nufi dakinta dashi a lokacin.

Bina Ammah din tayi da kallo cikin mamaki tana fadin ina zaki dashi cikin sanyin jiki na juyo ina fadin
dakin ki zan mayat don ni ban komai da kayanta.

Galala tayi tana kallona a cikin mamaki kafin tace itawa ke nan banyi magana ba kawai nasa kai na fada
dakin na aje rigan na fito.
Har lokacin sai faman kallon mamaki take min don yadda na daure fuskana akan zance ba kuma iya
fuska ba gaba daya raina a bace yake don zancen rigan nan data dauko min din a lokacin.

Hijjab na dora saman kofa ban shiga daki ba na nufi wirin girkin mu mamaki ya hanata wani kyakyawan
motsi a lokacin don na barta da fargaba da tsoro dayasa take zargin duk yadda akayi na dan san wani
abu a yanzu kan yar uwarta ke nan.

Wata zuciya ta keabeta da fadin ina zataji halin dan yaune kawai da bakin wayau irin nasu nufi nakeyi
da bansa kayan da wani yai amfani dashi kila don tasan halina da tsandan tsiya.

Aikina nakeyi cikin lumana yayin da har na kai ga hasa wuta ita kuma tana zaune kamar an shukata
cikin tunane sai muryanane ya dawo da ita da nake fadin.

Ammah akwai sauran gari ko nake tambayarta don tun lokacin nan da sukai tafiya ya kasance gari bai
katse muna a gidan har sai mun tsaya jiran Abbu ya dawo daga kasuwa don muna dan ragewa a yanzu
din sai hakan yake muna amfani wani lokacin kafin ya kawo din munyi amfani da dan wanda ke nan
kuma ya ishemu a gida.

Saida ta dan dauki lokaci kamar ba zatayi magana ba kafin naji ta sauke ajiyan zuciya da dan karfi tana
fadin wanan shimkafan da maman Aimana ta aiko dashi nake son a dan sulala da wake mu dan canza
abincin yau tunda Allah ya kawomunashi.

Dakin na nufa don nasan inda kayan suke wake na dauko don in gyara can daga gefe daya na koma na
fara gyaran waken nima dai zuwa lokacin a cunkushe zuciyana yake.

Don tun sanda nasan da zancen mahaifiyana nake faman dakon bakin cikin daya yafi na baya a zuciyana
sanin koni waye a yanzu yafi tayar min da hankalina.

Don zuciyana tana min wasi wasin akoda yaushe akan koni yar halakce kamar yadda nana din ta fadawa
yan uwanta saidai ni zuciyana yafi karkata da cewa ni din ba yar sunna bace gaskiya.

Duk da hankalina a lokacin ba zai iya hango min gaskiyar zancen da Abbu ya fada min sai nafi hasashen
Abbu din ya saya min zancen nasane don in yarda dasu din.

Wai baki sauri Aeesha ki daga kanki ki dubi gabas tab yake da dari daya hadu yana shirin game gari kin
zauna kina tunane haka .

Hakan yasa na mayar da hankalina ga abinda nakeyi a lokacin bani kadai ba har ita Ammah ina kule da
jikinta a mace yake har lokacin nasan kuma sanadin rigar nan dana fito dashi daga wajena nayasar a
wajene yasata shiga wanan tunanen haka.

A raina nace lalai Ammah da nana din nan da Abbu yace itace mahaifiyata akwai wani abu mai karfi a
tsakaninsu don yadda Ammah din take shiga cikin damuwa haka.

Zuciyanace ta bata amsa da fadin gaki kuwa baidai wuce matsalanki Aeesha don rikon dan da baka san
asalinsa ba yanada wahala.
A take naji idanuwana sun ciko da ruwa a lokaci guda tausayin kanmune ya mamaye zuciyana a wajen
don nasan nikan a yanzu mara gatace duk da kokarin gatan da Abbu da Ammah ke nuna min sai wanan
lokacin nake jin hakan bai wadatar dani ba a gaskiya.

Ba malam bahaushe ba ko wani kabila nason ace yau ga asalinsa nikan a yanzu nagama sanin banda
wani asali ko gata a duniyan nan kuma.

Tunda ba wanda yau zan nuna ace dan uwan mahaifinane mace kona miji ina wanan tunanen ni
dakaina naba kaina amsa da fadin No wander yan uwan Abbu suke min abu issa issa idan nashiga cikin
su.

Daga yara kuma har manya haka zasuyi ta hattarana kamar ba yan uwana ba har yakai idan munje wani
taro nasu na daina nisa da Ammah duk inda take anan zaka sameni .

Sai ya kasance yanzuma dana girma bani sha,awan bin Ammah zuwa sha,aninsu saidai taje ita kadai ta
dawo na dauki shekaru a yanzu ban zuwa sha,anin su.

Kauye kuma da take zuwa tun ina saka rai har na fahinci bata son zuwa danine kauye sai nafi daukan
zancenta a lokacin da tace dani don mayu sunyi yawa a garin nasu yasa bata son zuwa dani wanan yasa
na debe rai a lokacin.

Amma yanzu da naji tarihina a wajen Abbu na gane kuma na fahinci abinda yasa Ammah din take min
hakan don haka ya zamo wajibi in debe raina a dukka bangarensu biyun ga baki daya.

Ba kuma don komai saboda in tsirar da mutuncina gare don daga yara har manya duk sun san asalina
nake gani akan me zan matsawa kaina yanzu shigarsu bayan nasan asalina a yanzu cikin al,umma.

Asalin Abbu dan cikin kanone dama nomane ya mayar da iyayyensu kauyen su Ammah har suka zama
yan gari amma kowa nasu yana a cikin kano har kuma wasu daga cikin yan uwansa mata sunyi aure a
kauye don can mahaifinsu ya maida rayuwansa a lokacin.

Ko a bakinsu zasu iya jin tarihina a lokacin sai a yanzu da wayau yazo min kuma nasan asalin nawa
wanan tunanen yake zo min a raina don haka a yanzu gaba daya saina share wanan gabaki daya a raina.

Ina fada maki hakane mai karatu don jin da nayi da Abbu ya dawo yana fadawa Ammah zancen bukin
wani dan uwasa da zai ma dansa aure.

Gashi kuma idan ana bukin a can Ammah take kwanaki kusan biyu ko ukku saboda tazaran dake akwai a
tsakanin mu don Abbu bai yarda ya sai gida ako kusa da unguwarsu ba a lokacin.

Can yaje nesa sosai dasu yasai wanan gidan da muke ciki don rikona da ya dawo wajensu yayo kaura a
kauye zuwa nan kano don rayuwana ya inganta ba tsamgwama .

Saidai duk da hakan ba a tsira ba don anyo gudun garane aka fada zago saboda kallo daya zakiyi min
dani da iyayyen nawa babu wani kamanceceni da nayi dasu don haka ba sai an tsaya bata bakin fadin su
din ba iyayyena bane na asali.
Don haka tunda wanan zance yazo kunnena na yankewa kaina shawaran ba zanbi Ammah zuwa bukin
nan duk yadda ta taya min zuwa saboda yadda a yanzu na tsani shiga cikin mutane saboda haka nake
daukan kaina kamar wata muji a gaban mutane idan na shiga waje.

Daga inda nake jin Ammah na yanka fadan rashin fada masu bukin da wuri da ba,ayi ba don gashi
jibinr ita ko wani shirin kirki bata dashi a yanzu don haka an mata girshi a bukin.

Dariya yaso kamani nake fadi a raina su Ammah ho wanan wajen ko kinje da shirinki na gaske wa
zaisan ma kinzo mutanen da suka goge suka waye idonsu na a bude.

Karshema su ke zama yan aiki don angansu na kauye a wajen duk da gaskiya kira da tsarin su Ammah
ba abin kushewa a cikinsa don mutanene tsayayyu ga diri da ake bukata a wajen mace Allah ya hore
masu.

Irin wanan kamar itama nana din nan tana da wanan halittan nasu a yadda naga zubinta a cikin hoton
don ba inda ta rago Ammah din wajen kama saima ince kamar ta fisu cikar halitta ko don ita ta wayene
fiye dasu yasa hakan oho bandai san komai a game da rayuwanta ba har lokacin.

Aiko ban kai ga karshen tunane ba naji bayan Abbu ya fita Ammah din tana kwala min kira hakan yasa
na amsa kamar a tsorace na fito lokaci guda daga dakin.

Ashema har Abbu ya fita ban farga ita kadai na samu a zaune a tsakar gida take fadin abinci fa nace
yanzu zanci Ammah.

Na juya zuwa inda abincin yake na dan debo kadan gefenta na dawo in zauna ina shirin zaman naji tana
fadin kinji min mutanen Aeesha ?

Don rainin wayau da an mayar damu tallaka wai sai yau din nan ake sanar da malam zancen bukin dan
gidan Alh sale don kawai sun raina mutane inbashi ba iyayye uwa daya uba daya ace sai yau din nan
malam zaiji wanan zancen don Allah ?

Mafarin in ba ajeba suce an ki zuwa ni yanzu na rasa data ina zan fara ma tunda nasan zuwa dole tunda
banji yace dani komai ba.

Shirun da taji nayine tana magana yasa ta dago ta dan dubeni tana fadin bakiji mena fada bane wai ina
magana kinyi shiru haka ?

Idonta data sauke ga abincin nawa yasa kuma ta canza akalan zancen bukin da fadin wai meke
damunkine yanzu Aeesha ?

Ina kule dake fa a yan kwanakin nan da kamar akwai abindake damun zuciyarki ace wai wanan dan
abincin kamarki zataci kamar za abawa jariri dan watanni haka ?

Dan murmushi nayi ina fadin amma malamin mu yace yawan cin tuwo haka da yawa yana sa mutum
kiba lokaci guda ni kuma banson kiba wallahi

4 / 109