Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
Abbu ya zata
don dawowanane saida yaje yake jin labarin yasha bambam da abinda ya zata din.
Don haka ya dawo gida yana fada muna zamu tafi ai muna passport don Abba yace umura zai tafi
damu bana jin hakan yasa Ammah dan sakewa ta sauko da fushin da takeyi dasu din.
Don da a jirace take waninsu ya tunkareta da zancen dawo dani gida da tayi suji a ranan sai gashi ko
tashin zancen ba wanda yai wanan maganan cikinsu.
Koda na dawo saida nayi kusan kwana uku su maryam suka san na dawo sai gasu mun dade muna hira
kafin yamma yayi na rakasu suka tafi.
A nan tsakar gida na zauna inda naga Ammah na gyaran wani sarka muna hira da ita Asmau duk basu
dawo ba suna school a lokacin.
Yanzu ke don Allah da kika matsa ki dawo nan zama hakan yafi maki can a cikin daula da kikeyi
Aeesha ?
Ammah ba hakana bane dangin mijin ummu basu son zamana a gidansu kuma ni gaskiya nan din dai
yafi min dadin zama dace .
Nan na soma bata labarin abubuwan daya faru har ciwon hindu da irin kokarin da nasha akanta amma
haka yan uwansu zasuzo suyi ta sakin magana a kaina.
Ran Ammah din bayi dadi ba take fadin ai saisuyi da wani basai kin kara zuwa zama ba iyakarki dasu
zuwa ki gaidasu ki juyo kamar kowa.
Yana zaune daga gefe daya yana duban wasu takardu a hannusa yayin da iyayyen nasu suke hira irin ta
manya yaji daddy yana tambayan .
Na daina ganin wanan yar ma gidan nan yanzu wace ya ke nan sai kuma ya tuna yace au Ayshaa kake
nufi ?
Ta koma gidansu hannun marikanta abinda yasa ya dago ke nan ya dan kallesu takoma gida wani abune
ya faru kuma ?
Ba abinda ya faru Ahmed tana matukar kafa zucin iyayyen rikon natane kawai ita kuma nan hjy ta kasa
natsuwa ta fahinci hakan.
Yadda take son yarinyar ta kasance mata na fahinci yarinyar na farko bata da saurin sabo haka kuma
bawai yawan dai hayaniya ke gareta ba za ace.
Allah ya kyauta ita hindun ai ta samu sauki sosai ba samu mahaukaciyan nan itama tana fada wai ka
dauko diya ka dunkuleta a gida ko gaishesu bata zuwa yi.
Naji mama na fada da ita tana fadin ita haka bai mata dadi bane yadda gaba daya hindun ta sauya
lokaci guda ,.
Abinda nakewa kaunar zaman ta da yarinyar na ke ta dinga gani kyawawan dabi,unta don yarinyar ta
yarbiyantu sosai wallahi.
Zata daina ai insha Allahu don gaskiya akwai alaman natsuwa sosai gareta yanzu so idan aka kara
hakkuri insha Allahu zata dawo.
Wayanshi dake gefenshi ta mika hannu ya dauka shiru yayi kamar mai nazari a cikin kwalkwalansa sai
kuma ya fasa kiran kasancewar iyayyen nasa suna falon zaune.
Yarinyar nan tana da hankali kuwa yake tambayan kansa tare da mamakin yadda ta iya tsalake gidan
nan ta koma wancan gida ?
Saida dare bayan ya koma gida ina shirin kwanciya naji wayata na ringing alaman kira na shigo min.
Ina dagawa sunan da naganu saida ya ban mamaki don yaushe rabonsa daya kira layi na da sunan kira.
Haka na daure na daga a cikin sallama ya amsa min tare da fadin yaushe kika koma gidane yau na
shigo ban sameki ba naji baffa na fadin kin koma gidan ku.
A takaice na bashi amsa da fadin kwanaki why Ayshaa baki mutanen nan ba zasuji dadin hakan da kike
masu ba ?
Banyi masu komai ba kawai nafi jin dadin nan gidan mune da can sai naji yayi murmushi kadan yace.
Keda aka kaiki don koyon wasu abubuwan zaki kama hanya ki dawo gida meyasa ko wani lokaci bakiwa
kanki adalcine Aysha ?
Kada kuga laifina nan din yafi min sauki zamane fiye da can din kumani ba wanda yai min bayanin
koyon wani abu ai.
Haka dai hiran namu kamar kullum yake tafiya fada fada nasiha nasiha yake fadin na dinga zuwa nace
ai zan diga zuwa duba su.
Mun dan dauki lokaci kafin muyi sallama tunane na fara a lokacun bayan mun gama wayan dashi irin
yadda gidan nasu ummu komai a sarautance akeyinsa.
Ba laifi don dan zama nan na koyi abubuwa na rayuwa da dama a tsanake koda na dawo na kasa yin
wani hayaniya yanzu duk da dama ba yinsa nakeyi ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[11/10, 9:43 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,
8️⃣8️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6
Haka rayuwa take manya sunce watarana kasha madaci wataran kasha zuma wanan duk mai rayuwa a
doron kasa sai ya dandana rayuwa biyu wata rana.
Irin hakan na kasance a ranan da sakon Abba yazo muna na zancen zuwa yin umuran mu don naga ga
masu salo da yangan cewa sunfi kowa nasaba .
Amma Allah da ikonsa nice a cikin zan fara zuwa umar nayi sunna wani hikima sai ubangiji Allah mai
girma da daukaka.
Su Abbu sun tafi har gida sunwa Abba godiyan hakan bayan komai ya kammala suka fara shirye
shiryen tafiya nidai nawa kawai ance in tasone muje shine nawa don kowa ban fadawa zamu tafi ba.
Yan gida kuma da suka sani Abbu ya gargadesu da inyaji zancen a waje sune zai dauki mataki kan
hakan .
Wanan yasa sukaja bakinsu sukai shiru har saida abin ya tabbata akaji a bakinsu da suke sallaman
mutane don tafiya kana suke hadawa da sunana kan tafiyan.
Nan su maryam sukaji nasha korafi a wajen su ta nan kano muka tashi zuwa saudiya inda amanan
gidan Abba ya zauna akan Samira don itace babba da za a bari a gida.
Saboda zancen tafiya dasu anty safiya sai daga baya lately ya tashi abin kudi nan da nan suka samu
visan su ya fito.
Can gidan su ummu kuma su yaran Anty baraka da yan aiki zasu kula masu da gida tare da sauran yan
uwansu dake gari komai an tsara yadda zai kasance a lokacin.
Tashin dare mukayi muka isa can da sanyin safiya sai da tafiyan yazone na fahinci akwai mutane da
dama a wanan tafiyan namu irin yan royal family daddy su Man bash daddy imamu baba dalhatu Ciroma
da dai sauransu.
Fanin mata kuma su dana lissafa da matayensu idan biyune ko daya sunzo dasu donshi daddy imamu
matansa biyu dukka yazo dasu wanan tafiyan hjy Nasare da maigidanta har da yaron ta namiji.
Akwai hindu da hadiya yar aikin nan nasu sai yaran ummu kaf dinsu duk tare mukazo dasu sai dai an
dan samu bambamcin jirgi don wasu sun rigamu isa kasan a lokacin.
Mun ga mamaki sai faman tunane nake a kasan raina yanzu a wanan kasan mai albarka aka haifeni
amma kuma na koma abin kyama ga mutanen da nake rayuwa a cikinsu.
Ina tare da Ammah da su anty baraka duk da anty safiya tafiyan mu kusan dai tana tare da ummu ko
wani lokaci ita da hadiya mai aikinta.
Abbu kan baiyi sakaci da tunatar damu kasan da mukazo ba don haka muka bada himma sosai wajen
bautawa Allah tare da godema da irin baiwan da yai muna lokaci guda a rayuwa.
Muna tare dashi ko yaushe ina kuma kula dasu har muka bar madina garin dadi zuwa makka akwai
matukar nisa sosai tafiyan don sai yamma muka isa tun abin safe.
Na dauka kamar daka danyi tafiya sai garin ashe abin ba haka bane tafiya mai nisane a tsakani cikin
daren nan kuma muka nufi yin dawafi .
Har wanan abin dake tarin zuciyana dai gudane shine wai anan dai aka haifeni Abbu bai bari mun dawo
gida ba saida safe don nan ba irin madina bace da ake gargada mutane a rufe kofofinta.
A washegarin Ummu ta shigo dakin mu don su gaisa da yan uwanta don gaskiya Abba yayi kokari
mukan a ganin mu don kusan mu goma mukazo daga bangaren ummu.
Don har da wasu yan uwansu maza mutum ukku da suke uba daya yayyenta mata kuma su ukku mukai
wanan tafiyan dasu din.
Ammah kunci kaji ko ta fada tana zama saman gadon dakin sai Ammah din ta dago tana fadin ina zanci
kaza Asiya gani da budurwa a gabana.
Aeesha muke son mu hada kudi mu sayawa yar babban sarka ta aure kinga wanan damane ubangiji ya
bamu ba zataje a haka ba ai.
Wace sarka kuma Ammah me Aeesha zatayi da sarkan gwal kuma wace zata iya sayan shagwan gwal
daya a nan idan taso.
Kallon da taga matan wajen suna mata don daga ciki har da dangin mijinta a dakin yasa ta gyara tana
fadin .
Sana,an ubanta ke nan fa Ammah akallah kada inyi karya suna da shaguna a cikin garin nan banda na
Dubai da zasu kai goma ko fiye da hakan ma dai .
Don sana,ansu ke nan tun fil azal su harkan gwala gwalai danye da wanda aka sarrafa din nan haba dai
kici dadi iya dadi yadda kike iyawa don Allah.
Ammah tace to ai bamu ga ubanba balle ace tana dashi din ba gara dai mu aje iya karfin mu ba tun
yanzu koba gaskiya ba tana cewa hjy babban nan nasu da muke daki daya.
Tace to aini kinga na daskare a waje daya wanan zance nata ya kashe min jiki ke gaki komai kuka gani
kuce Aeeshan zaku saiwa.
Bayan uwar yarinyar nan na fada maku kullum yarinyar nan yar gatace haka dai Allah yayi zata rayu
daku tun farko nata kaddaran ke nan yazo a hakan.
Ita bata rayuwa da iyayyenta a cikin daulan da Allah yai masu ba ya jefota hannun ku don wani nufi da
yabarwa kansa wanan .
Tunda kikaji ta fada haka din ne saidai muyi fatan zuwanshi lafiya da kuma nasara kada a samu
muhawaran amsanta din.
Wasu a dakin shirme suke ganin zancen ummu din da karya a cikinsa tun yaushe suka dawo suke fadin
mahaifina zai baiya har ranan ba wanda yaji duriyansa kuma.
Hakan ya kawo dan tsegume acikin tawagan suna zunden ummu da sakin habaici a kanmu kan inma
karyane dai mutum kansa yaiwa ai don ba,a karyan arziki ga bawa uba kuma ba wasa bane nemansa ai.
Kawai a tsaya a yadda nake ta samoni a yawon banzata datayi a nan cikin larabawa yafi wanan karyan
da take shatawa mutane ko yaushe tunda kowa yasan gaskiya a yanzu.
Ita hjy babbace ke tseguntawa Ammah abinda yan uwansu ke fada a kan zancen da Ammah tayi a
masaukin mu tana mamamin yadda wata ta fitar da zancen cikin dan lokaci haka ?
Itama Ammah ta hau nata bakin a cikin mota tana sakin magana sukai tsit don sunsan duk yadda akayi
zance ya koma masu suma kamar yadda yazo masu.
A gaskiya zangayen nan yau banjin zanyisa Aeesha jeki kuda keda sauran karfi ku zagayo in an jima
rana yai sanyi sai mu tashi nida hjy mu zagayo.
Ammah ce ke fadan min hakan don ko yaushe ina lake dasu ita da hjy ban damu da bin yan matan dana
hango daukan kai da izza a wajensu ba mu yan mata cikin tafiya mu kai biyar.
Sai naga tun a madina suna nuna irin su wasunefa suna abu izza izza da isa yasa na daina kula harkansu
haka kuma Abba da ummu duk inda suke suna makalene da yaransu .
Hakan yasa sai yan tsofin da nake dawainiya dasu su biyu hjy babban da Ammah ke nan ko ina dasu
zaki ganni ko tare dasu anty safiya wani lokacin.
Mikewa nayi ina gyara hijjab dina tare da fadin hjy bari na samo maku abinci kafin na tafi hakan yasa
hjy babba miko min kudi tana fadin yar nan kamar kinsan abinda zan fada ke nan .
Imamu yace muci kaji muci sai mun koshi mu bar kimshe kudi a jikin mu shi nake son nace ki karbo
muna dan dankalin nan da kaza mu tausa kafin ku shige ciki.
Hjy bari na sayo maku na cikin shagon nan mai dadi zaifi Ammah ta miko min kudinta itama na tunkari
katon shagon mai abin mamaki shago mai tambari agogo a tsakiyan makka shagon daya kumshi
abubuwan mamaki a cikinsa ga wani babban hotel hawa na takwas da sai ka isa zaka sauka a cikinsa kai
shagon dai sai wanda yaje ya ganowa idonsa karyan arzikin dake cikinsa Bin dawood ke nan.
Sashen abinci na nufa amma saina tsaya shiga bayinsu don freene shiganda ga kuma tsabta shima
wajen kaji kamar kada ka fito.
Na shiga nayi wanka na kara gyara jikina tsab na fito ina wuce shagonan kayan karau da sai inda idonka
ya tsaya da kallo a cikin wajen.
Ina gab da kawai wajen sayar da abincinsu nayi karo da wasu mata da miji da yaransu biyu suna rigima
wai sai uban ya daukesu a kafada ga kuma matar nasa makale a hannusu ta nuna bata damu ba.
Sun dauke min hankali ina tafe ina waigensu har naje nayi karo da mutum ban sani ba na juyo da sauri
don ganin waye na bashi hakkuri tunda nasan laifina ne .
Balarabe da shigan haraminsa yayi lage yadda maza keyi yayin bautar ubangiji sai wasu na tare dashi
sunkai goma a bayansa .
Sorry please na fada da kawar da kaina na nufi wajen duk da naso na karasa ganin draman da nake
kallo a wajen.
Saidai abinda zuciyana ta nasa min cikin second yasa na juyo da kaina da sauri ina sake kallon
balaraben shima tsayawa yayi yana bina da kallo kamar yadda mutanensa suka jabaya sukai cirko cirko a
wajen.
Fafafafafa naji gabana ya soma faduwa idan ba karya nakeyi ba wanan mutumin searching dina ya bani
jikin photonsa dana shiga Internet nayi saidai kuma wani lokacin kama garesu suma sai kaga kamar
wanda ka baro a bayane kagani kuma again.
Kafata naja da sauri na isa shagon abincin a nan na hadu dasu hindu suna saye suma muka fara magana
a tsakanin mu sama sama dai har lokacin wani irin faduwa gabana yake min.
Nagerian balaraben ya fada a bayan mu sai suke fadan yeh yeh na sheda fuskan mutumin shike kusa
da wanda nagani din a lokacin .
Sukan sunga balarabe sai sallo sukeyi suna watsa masa turanci a wajen shan jinin jikina nayi ana miko
min abincin dana bada kudi donsu sun tsaya a hada masu ice cream mai chuculet da sugar a cikinsa.
Ina juyowa shine a tsaye bayana ya furta Aysha ?
Na,am na amsa masu zuwa lokacin nagama karaya da komai da zai iya afkuwa a lokacin Allah yasa a
gaban yan uwana wanan abin zai faru dani.
Sunana Umar bin sultan Abdulrashid daga Ouman mazauni Dubai da fatan kin shedani yake fada sai
hankalin su hindu dasu Amira ya dawo kanmu lokaci guda.
Na shedaka kai mahaifinane da ban taba ganinka ba a rayuwata sai a wanan wajen mai tsarki Allah ya
nufi haduwana dakai cikin yardansa.
Kin sansane Aeesha husna kanwar Man take jefo min tambayan a gagauce na juyo a hankali nace da ita
mahaifinane Husnah.
Isowan matan royal family din nan a cikin su harda mami sayan abinci Allah ya nufa za ai komai a
gabansu saidai ba iyayyena ko daya a kusa lokacin.
Har yanzun wai baku karbi abincin bane suka fada sai kuma suka mayar da hankalinsu kan abinda yake
faruwa hindu ke fadin wallahi mahaifinta tagani a nan yanzu.
Mahaifin ta tasan shine balle taga wani balarabe ta lake mai kuna kiransa da mahaifinta matar daddy
imamu ke fadan hakan tana turesu tare da matsowa wajen tana fadin tsaya dai mugani .
Tsaya mummy shine mafa ya shedata hindu ta fada ai basai an fada ba don ga zahiri nan sak wallahi ya
akai hakan ya faru mami ta fada.
Naji dai uwargidan daddy imamu na waya da ummu hjy Asiya kuzo fa gamu nan wajen sayen abinci
mun gamu da wani balarabe ya tsayar da yarinyar nan ta wajenki wai yarsace.
To gamu dai ciki dasu a tsaye cirko cirko ta kara fada don banji me aka fada a cikin wayarba lokacin .
Yayin da shi kuma yana tsaye kusa dani yana waya yana kwantacen inda suke tsaye a lokacin .
Don haka nayi kokarin fita daga wajen wani a cikinsune ya tareni yana watso min larabci daga bakinsa.
Matsa min na wuce gun iyayyena na bashi amsa a cikin larabci dayasa gaba dayansu wajen suna
kallona cikin mamaki jin ina iya harsen larabawan a fatar bakina.
Isowan su ummu ya dakatar da binda suke min a baya aka tsaya ana kallon kallo a tsakaninsu kafin
Abba ya tari shi mai bina din da tambaya.
Don da farko baiga shi Bin Sultan din ba saida wanan din ya nuna masa shi ya nufi wajensa cikin
mamaki suka tsaya suna gaisawa.
Zuwa lokacin na nufisu Ammah cikin kuka na mika masu abincin ban tsaya ba nashiga yin dawafi suna
nema ina cikin wajen bautar Allah tare da godiya ga ubangijina.
Ashe bayana Abba din ya tabbatar masu da wanan shine mahaifin Aeesha kuma ubangidansane wajen
sana,ansa .
Yayi masu bayanin ko waye shi tare da fada masu duk shagon da zakuga an rubuta Bin sultan nasu su
suke dashi da yan uwansa.
Haka abin Allah ubangiji ya kawosa a saukake garemu ya gabatar mai da Abbu da Ammah a matsayin
marikana su suka tayar dani kuma har yanzu a hannusu nake rayuwa.
Ban fito ba saida nayi zagayena sau bakwai lokacin sallah la,asar yayi nabi jam,i akai sallah damu a
massalacin harami muka samu fitowa don nasan zan samu su Ammah a inda muke zama dasu.
Saidai ban samesu a wajen dana barsu ba din mamakine ya rufeni a zuciyana ina tsaye ina dan dube
dubene na ga wasu larabawa a cikin jallabiyan dake kamar uniform a ga mazansu tare da dora dan jan
kyale akai sun nufoni .
Nayi saurin fahintar hakan na shige cikin mutane don tun a cikin wajen sallah na kula dasu gashi naji
ance a