Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
suka gudu dashi wata
kasa yayiwa mutane karyan ya mutu annaminiya kawai ?
Haba mama ki bari agama saurarenta mana ai yanzu ta fara labari take bamu a yanzu labari kuma shine
toshen abinda muka zauna nan saboda shi.
Imamu ke wanan maganan da mahaifiyarsu data hau fada ya kalli mai maganan yace muna saurarenki
ta danyi murmushi tana fadin afuwan rakishidade ba abinda kike nufi a raina tun a wacan lokacin.
Iya dai muna zaune da uwar dakin mu da dadi ba dadi muna hakkuri don mu cin ma burin mu na
samun guzuri a wajen aikin da mukeyi din.
Wanan yasa muke kafa kafa da komai don kada mu samu akasi duk da uwar dakin namu tana da wani
hali na banza na kazanta.
Amma haka muke daurewa mu gyara komai har dadin hakan yasa ta sake jikinta damu wata rana na
kawowa bakinta abinci a falonsu na samu wanan hjy suna hira ganina baisa sun fasa hiransu ba ina yan
aiyukana ina saurarensu .
Nan nake jin abinda suke kullawa yakai tsawon sati daya suna wanan shirin na yadda zasu kashe
mazajesu su mallaki dukiyarsu ya koma nasu.
Salati falon ya dauka hjy mama ta hayayyokota tana fadin dashi kika yaudaresa ashe mai martaba
wanan yai mata tsawan da kowa ya kadu ashe tsohon da dan sauran kwarinsa.
Itako Asiya din tace gata ai a gabanku idan kazafi nake mata kada na tsayar daku saida nagama bibiyan
su tsab naji duk irin plan dinsu don har ta riga da tafara poisining dinsa a cikin turare tace.
Hankalina ya daga ban fadawa ko abokiyar tafiyana ba hajja laure dan itace kamar uwar dakina ga
tafiyan.
Ranan dana tabbatar zasu kashe bawan Allah nan duk da iyakata dashi hange daga nisa idan nafito yin
wani abu nakan hangonsa idan yana kasan.
Yasa na samu lokaci na fita na sameshi na sanar mai da komai da farko bai yarda ba sai na fada masa ya
kula da jakar tafiyansa da kuma motarsa don plan biyu sukayi a kansa dama.
Idan har ya samu kyatare na farko to tabbas ba zai ketare na bayan ba danta da wasu suka tura cikin
dare ya bata burkin motarsa duk a gabana dana hana idona barci naga hakan sai kuma .
Idan ya tsira daga hakan to an zuba masa kwayoyi da yana shiga wanan landarin aka kamashi dasu
sunansa matace a can din.
Nasan hankalinsane ya kasa kwanciya da abinda na fada mai don ban taba ganin macen da bata kaunar
mijinta ba irin wanan ko yaushe ta shigo gidan namu tun kafin hakan bata da aiki sai aibanta mijin nata
da munanan gurika a gareshi tun lokacin nasan zata iya komai a kansa saiga wanan shawaran nasu yazo
na kuma ji komai a kunnena lokacin.
Bayan kwana daya ga yadda tace zatayi tafiyan sai ya dage tafiyan nasa bansan ya akayi ba ya samu
ganina ni dai ina kwance a dakina naga uwar dakin mu tashigo ta kirani inje ina da bako a waje.
Shine dana fito cikin mamaki nasamu shine ke nemana saida muka dan taka dashi yake fada min yaga
komai kamar yadda na fada yanzu yaya za ayi don dabara ya bace masa yanayinsa kawai ma zaka kalla
kasan hakan ko bai fada ba din.
Nice na tsara masa akan ya shiga motar yayi tafiyan da ita sai yabar gidan a canza masa mota nan yace
ai tare dani zaiyi tafiyan don ba zai barni nan ba su gane su halakani daga baya.
Hakan yasa naji tsoro na yarda na bishi ba tare da kowa yasan da hakan ba don bayan nadawo gida a
ranan na samu uwar dakin nawa na fadin abinda shi gawane ya more rayuwansa iya na yau kawaine ai .
Don su sun dauka da harkan banzane yazo nemana duk da akwai aminci a tsakaninsu kawar nata kuma
ta yarda ta hadashi dani.
Washe gari tunda asuba na sulele zuwa inda mukayi dasu zamu hadu a can na tsaya suka daukeni
saidai ganin su subiyu ya ban mamaki wai ashe yaronsane ta hada dashi ya kaisa inda zai shiga jirgi don
akwai nisa da wanan gari shi aka bari da motar bamu san yaya ya karsaba dasu.
Allah ya taimaka muka ketara lafiya saidai muna isa can kuma maganin da akai poisining dinsa tun a
gida yaci karfin sa haka nayi faman jinyarsa har Allah ya bashi lafiya.
Sai muka kara gaba daga nan don bansan inda ya samu labarin cewa a gida an aika ya mutu har
matarsa ta tattara tabar kasan ta koma gida da komai nasa wanan zaman jinyar da yayi akaji shiru aka
dauka hakan gaskiyane.
Iya abinda zan iya fada ke nan sai kuma ta danyi murmushi a bayane ta dora da fadin sai bayan
shekaru ukku ne yazo min da zancen aure a tsakanin mu.
Naso na bijirewa hakan ya lurar dani zama haka ba zai yuyu ga ko wanen mu ba wanan yasa na duba
na yarda da bukatanshi na aure ashe kuma rabon yaran nan ke tare damu bayan hakan iya abinda na
dan sani ke nan.
Tir da Allah waddai ke tashi akan kura falon wace keta kuka tun soma zancen ita Asiya din saidai idan
ta fadi wani zance wani lokacin takan dago kai kamar zatayi magana sai kuma ta fasa idan tayi tunane.
Don ko imamu ya isheta wirun wanda keta faman jamata Allah ya isa ta wullakanta masu daki da
mugun nufinta.
Ni dai ina kwancene bayan nayi wanka Asmau tashigo min da ruwan zafi tana fasin mummy tashi kisha
shayi din Allah ko hanjinki zai walwale sin ban iya ganin ki haka ?
Kallonta nayi na dan saki murmushi na mike ina karban shayin nace nagode ma,una haba dai wai ance a
kyaleki ko yunwa ya isheki ki fito ai inji su mama.
A,a mama tana can ta kwashi zuga sun fita tare da bakuwa cikin wata dirkekiyar mota kinga mama fa a
gaba ta hakince anga wajen lasan maiko.
Asmau baki da gankali anty nawa kikewa sheri ai gara ta lasa kada banza ya wuceta ita da ta lashi nasu
a baya fa ?
Mummy ai bata lasa a banza ba tunda gaki sanadin ki suna cin alherinta kuma kinga ba ayi a banza ba
ai.
Kingani ko mau ta saba da yawo ni sai ince ma kila ba aure takeyi ba fa tunda sun iya bat da sau kamar
me ?
Don Allah mummy kice Allah kin tuba ga yara sunyi kama da ubansu sosai dan haskenta dai suka kwaso
kawai za,ace.
Ni wallahi shawa take ban idan tana magana sai kace larabci takeyi wai kuma ba a saudiya suke ba tace
wani gari naji ta fada dai haka.
Oho dai koma ina suke ita ta sani yanzu ai na fada ina kurban shayin mai zafi a bakina don naji dadin
shansa lokacin.
Mummy ai laifinkine dakin sake tun jiya da kinji komai a bakinta don naji suna dan hiran bayan
tafiyanta da Ammah da Abbu dazun.
Asmau wai Abbu fushi yakeyi dani fa yau har ya fita bamuga juna ba sai ta danyi murmushi tana fadin
aiba baban kano kadai ke fushi dake ba mummy kowa yana fushi da abinda kikayi mata din.
Mummy mahaifiyace fa yau ko gidan karuwai take zaune ko kuma a tsakar juji dole ki nemi albarka a
wajenta mummy ki bar fushin nan din Allah ki dan sake hakana.
Kafin nayi magana su maryam sukai sallama suka shigo gidan yasa muka bar zancen muna jin suna
gaisawa da Ammah kafin su shigo Asmaun tace don Allah mummy kada ki nuna masu komai ta mike
tafita daga dakin.
Na bita da kallo cikin mamaki ni idan suna Abbu mamaki suke bani wani lokaci don sai suyi abu kamar
wasu uwayen mata wallahi.
Mun gaisa bayan sun zauna farida ta kalleni tace wai ashe mumcy ta zo jiya muna gida aka shigo ana
fada muna na danyi dariyan yake nace wallahi sai gata kwatsam kamar daga sama.
Wai baki da lafiyane besty naganki wani iri mana maryam ke tambayana haka kafin nayi magana farida
tace keko dai ai dole ina ganin fa basu taba haduwa ba sai wanan karon.
A,a dama da zazzabi na dawo daga Abuja ina kwance sai gasu kwatsam haka dai suka sameni tace
nikan dai nagani don fuskanki ya nuna bakijin dadi.
Umm yanzuma shayi Asmau ta kawo min indan sha shina gama sha kuka shigo ina mumcy din take mu
gaida ita ?
Anya kamar Asmau tace min sun fita da anty safiya ina nan daki kwance tun dazun ni yanzu na tashi na
fada masu hakan.
Wai ko yaya akayi ta gane gida har sukazo dama tasan da gidan mana tunda tanayo muna sako a kai
akai dole zata samu wanda yasan gidan ya kawota.
A raina kuwa cewa nayi kai dan Adam da tambayan kwakwam yake komai saiya sani dalla dalla ya
gamsu yara ke nan yan mata da wanan tambaya inaga uwayensu.
Da komai zasuso suji su fayece shi ga wasu suma tunda suna yan gida banga laifinsu ba don suna son
jin karya da gaskiyan zancen ne suma tunda ana tare su karas a wani wajen.
Wai ashe aure takeyi a can din ance mijinta dan garin nan ne har da yaransu ko har hudu haka su
mama suke fada .
Koma meye dai ai yanzu tazo duk wani tsegumi sai yakare dama mutane mune da gajin hakkuri komai
sai yan bani na iya sun saka masa aya akai.
Ko yadda baban gidan nan ke faman fada cewa aure takeyi a can din ai ya isa a yarda amma sai akama
mayar dashi makaryaci kai bari wallahi naji dadi kamar nice wallahi danaji wanan labarin besty maryam
ke fadan hakan.
Nagode besty amma ai dadina ragagene tunda abinda akewa tsegumin kansa bai baiyana ba .
Wa wai kina nufin mahaifinki shima insha Allahu ai zai bayana din tunda aka fara hakan yanzuma kila
ita tasan inda yake dolema zata sani insha Allah.
Murmushi kawai nayi banyi magana ba naji farida na fadin kamar ko kin sani Aeesha shine ai maman
gidan akwai naji tace a sannu dai komai zai walwale insha Allahu.
Yanzu dai koma meye suyi ta fada ai ya rage a garesu ko hakan tagode ai da ace babu kowa naka ba
asan inda suka shiga ba kuma dukkansu ai shine tashin hankali dama.
Muryan Abbu na fara ji kafin na anty safiya nan nake fadin ina ganin sun dawo don naji muryan anty
safiya tare suka fita dama .
Asheko sun dawo din a falo muka sameta zaune sai da gabana ya fadi don hamshakiya nagani a lokacin
tare da yaranta duka da suka biyota.
Ummu ga yan uwana yan gidan baba akwai sunzo gaidake na fada yasa ta juyo tana masu murmushi
don da ummu naji yaron dazun ya kirata haka shina man din naji ya fada jiyan .
Cikin haba haba ta taresu suka gaisa tare da tambayan sunayesu suka fada tana ta faman fadin masha
Allah masha Allah.
Turanci nayiwa wanda karamin kebiwa ina tambayan sunan sa sai ido ya kura min dan larabcin dana
koya na buga masa don malam ya fayece muna larabcin ma nau,i nau,ine ba komai wasu ke ganewa ba.
Ya amsa min da Abubakar na tambayeshi sunan yan uwan nasa ya amsa da fadan hanza umar Aliyu na
fada min cikin sakewa.
Daga inda take zaune ta zubo min ido tana sararenmu cikin mamaki nayi kamar ban ganta ba nima naci
gaba da dan larabcin dana koya da yaron.
Wai tsaya don Allah me naji kinayi dasu kamar larabcin kema Aeesha anty safiyace ke min wanan
tambaya ?
Nace shine mana anty saidai na fahinci nasu akwai sarkewa a cikinsa ba komai suke fahinta ba wanan
yar dama ashe kina jin larabci ke nan kadan ba anty tunda na daina zuwa makaranta yanzu.
Ina laifin wanan dun mu da mun iyane aida mun masu tun jiya haka muke zaune dasu har suka koma
gida.
Sai kuma tashiga basu maryam labari a cikin mamaki tace yau naga karyan arziki maryam kinji wai gidan
mama Asiyane haka ?
Kada in maku karya gidan yakai daga gidan nan zuwa gidan baba raba kaya inma ban rage ba na kalleta
cikin takaici na dago daga bayan kujera inda nake kife zan koma daki naji muryan ummu din na fadi cikin
larabci.
Kija yan uwanki zuwa dakin naki su zauna ko zasu sake jiki a can a gaskiya ba duka na gane meta fada
ba saidai kallomin dana hada yasa na fahinci me take nufi.
Hakan yasa na juyo a daure na kalli yaran ina fadin suzo muje dakin nawa mu zauna dasu sai ko naga
sun taso sun biyo ni.
Dama ance tsakanin da da mahaifi ko miji da mata sai Allah hakane da yaran nan da suke matsayin
kanne a gareni ta fara soma cin galaba a kaina.
Yana zaune da wasu takardu a hannunsa mami din ta shigo part din zama tayi kafin ta soma magana
shine ya dago ya fara gaida ita yana fadin.
Yanzu na kammala bayan nan na baffa ina son in mika masasu ina batun in fito mu gaisa sai gaki mami
wasu bayane kuma ta dago tana kallonsa akan kaddaransa daya barine don yana son ya sallami mummy.
Wace mummy din kuma ta tambaya a gagauce yace mummy kura ma mami me zai sa ya zauna da
matar data tashi halakashi banda Allah yasa yana da sauran kwana a gaba.
Magaji don Allah ka rufa min asiri ka rufawa kanka zancen nan kada wani yaji da hannunka a ciki ina ka
fito da wanan zance don Allah ?
Mami ban mata kazafi ba haka zancen yake Allah ya taimaka wanan matar nasa itace ta cecesa a
lokacin dalilin aurensu ma ke nan don ba karamin wahala yasha ba a lokacin.
Yau zasuyita su kare ai tunda suna can an kirasu gaban maimartaba za a fadi komai don ita hjy da bata
da aiki sai mara mata baya ta fara nuna masa bai isa yaiwa yarta wullakanci ba .
To zataji abinda zai gurgizata kuwa yau don ba karamar criminal bace abinda taso tayi min ke nan da
yarta yasa kuke ganin ban daga mata kafa don nasan nufinta.
Shiru tayi ta kasa magana sai fadi take anty kura dai anty kura taso kashe yaya sayadi wai da gaskene
wanan magana magani ko wasa ?
Mami ban wasa dake ko ita da zan fadi hakan akanta gaskiyan zancen ke nan wallahi she attend to
murder him kan dukiyan da bai kai ko kwatan na yanzu da yake dashi ba ta kasa hakkuri da hakan.
Ba shege kamar manir dinta ai dan har dashi cikin case din ya sani shima da hannunsa a lokacin
innalillahi uwar ke iya fada a bakinta kawai lokacin.
Tace ashe zancen family din waziri ya zamo gaskiya a kanta amma ko anty kura ta cuci mu wallahi don
ta batawa hjy mama sunan zurian ta har abada.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[10/17, 7 AM] Zainab Idris Makawa Writer: [9/14, 8:52 Safiya] Seenabu Makawa:
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
7️⃣2️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105
ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH
YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
https://chat.whatsapp.com/C2uMqqgfoJ89mPvNpGTgi6
Maimartaba baba wani irin laifi na aikatawa kura haka data cuceni yau ba laifin kura nake gani cikin
wanan zancen don tayi yunkurin kashe ba ?
A,a sai halaka min da tayi ta hada kai dashi ya kashe mahaifinsa shine abinda ya tsaya min a raina ke
nan har yau na kasa fahintar meyasa tayi wanan gangancin saka manir a cikin plan dinsu ?
Ai duka abun mamakine saka maniru kuma wajibine wata rana sai ya dawo ya kasheta itama da
hannunsa wanan haka zancen yake.
Imamu ya fada a hasale yana kallonta cikin bacin rai nan hjy mama tace dashi imamu yar uwarka
kakewa wanan fatan haka ?
Koma me tayi dai yar uwarkace kai baka da yukan kankareta a jikin ka don haka ka iya bakin ka cikin
zancen nan .
Ballema ban hada baki dashi manir ba inma haka kake tunane koda wanan makiran taganshi a lokacin
da wanda yai aikin shi baisan ainihin abinda za,ayi ba a ranan.
Makira kuma ta wuceki kura keda kikai makircin rashin imani ai abinki yayi muni kura wanan zancen
kawai sayadi ya barki da Allah ya saka masa yafi sauki.
Baba ciroman su ke fadan hakan shima a hasale ya cigaba da fadin kura kin bamu kunya watau duk
abinda sayadi ya fada ko kunyan idon mu bakiji ba kin amsa laifin ki haka din ne.
Ke kuma hjy da kike fadan imamu ba zai debeta a jininsa ko bai debe ba aita debo don ba imamu ba
duk macen data iya haka ga mijinta ko ke da kika haifata zata iya kashewa saboda abin duniya.
Kwarai kuwa ko yanzu meya rage ta aikata na kasheta nasan komai ido kawai nasawa kowan ku
godiyana ga Allah sauran tsarkaken zuciya ke garesu maimartaba ya fada .
Ya sake nuna kura yace wanan ina son ku sheda ko mutuwa nayi ban yafe kura taci gadona ba kunji na
fada maku.
Ya yunkura kamar zai tashi ya kuma koma ya zauna ya kallosu yana fadin aure dai a tsakanin Sayadi da
Amina kunsan ya haramta dama dai tayi masa takaba ku shedane duk nan.
Da ita da diyanta sunci gadinsu tun yana raye haka amina ta rufe ido ta wullakanta dukiyan bawan
Allah nan tana takama itace da azaba ran gobe kiyama.
A dai sasauta mata iya ya fada yayi mai wani irin kallo yaja bakinshi yai shiru kafin ya ballo wani aiki wa
kansa kuma don yasan shima mai laifine a wanan maganan.
Aikuwa bai gama rufe baki ba yaji mai,martaba na fadin a sasauta maku dai tunda tare dakai akaci
kudin don kai ka daure mata gindi ta handame komai a lokacin.
Ya dukar da kai yana fadin tuba bake rankashidade bansan haka zancen yake ba na tsaya mata a
lokacin.
Falon yai shiru