Chapter 81 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   81 / 109

240K to 243K   out of 326.5K words

kokarin sabawa shari,a zata tsawata maka.

Na kula da hakanne daga yan aikinta da yaran anty baraka kuma don sallah akan lokaci suke samun
matsala nikan bata taba tunatar dani yin sallah ba tunda nazo gidansu.

Ya kasance safiyace don haka bani saurin fitowa saina kwatanci maigidan ya gama da iyalinsa ya fita
nakan dan fito nayi breakfast .

Balle wanan rana ta hutawa don asabarce ranan hutune don karshen mako kowa na hutawa lokacin
na gyara kwanciyana ina rufa.

Ban ko kula da karfe nawa ba don dadin barcin da naji lokacin saboda mun raba dare muna hira nida
kanne na a falo muna kallon wani film.

Ummu kuma tashige dakin mijinta ta barmu dasu anty baraka nan muka shagala saida muka kai
karshen film din kowa ya nemi wajen kwanciya.
Kinga ko dole inyi barcin safe a lokacin har na dan samu na koma barcin naji motsin bude dakin muryan
ummu naji ta shigo tana fadin .

Wai har yanzu a kwance kike ki tashi kije Abban ku yana magana dake falo .

Da sauri na dan yaye bargon ina fasin ni ummu tace zan maki wasane na dago na fara sabule rigan
barcin dake jikina na mayar da wanda na wuni dashi a jiya don baiyi datti ba bandama kamshin dake
tashi jikinsa.

Suna zaune duk da yaran a falon wajen cin abinci na danyi sallama ya juyo yana amsawa tare da fadin
yata nace a kira min ke mu karya mu kuma yi hira don yau ba fita zanyi da wuri ba saboda ke.

Don tunda kikazo bamu samu zama dake munyi hira saboda zirga zirgan da yai min yawa a kwanakin
nan bissimillah taso ga waje ki zaune ya fada.

Ba daman musu cikin jin kunya dole na mike zuwa saman kujeran daya nuna min din wanda kamar a
ajere suke gefen dama ummu ce a zaune saini sai barin hangunsa Hamzane sai Abubakar umar da Aliyu
suna tsakiyan mu.

Ina zama ummu ke fadin yau zakici girkin larabawan kyauye donshi muka girka salsal ne sai al,jar da
ganyen carbejen nasan zakiji dadinsa ai.

Na dai kalli abincin da aka zuba min yana turiri ko bakaci ba yadda akayisa kasan abin dadi aka hada a
wajen hadinsa.

Sun fara ci bayan suna ta ambatan bissimillah daga baku nan su na dauki folk da spoon nayi bissimillah
nima na fara yanko abincin a hankali na dan kai bakina .

Da tafarnuwa na fara karo yana min sallamu alaikum a cikin girkin kamar in dawo dashi ta dago kai ta
kalleni na samu na hade da kyar ina fadin tafarnuwa a hankali.

Rike take da spoon din ta kasa kai bakinta tana kallon yadda na debi ruwa na bidashi da sauri naji tana
fadin akwai aiki kuwa gareki babba.

Mijin ya dago kai yana fadin lafiya dai ko abincin bai mata bane tace wai dan tafarnuwan nan da aka
zuba takewa wanan borin haka ?

Allahu akbar naji ya ambata yana aje cokalin hannunsa yace bata son tafarnuwane basaci a gidansu
donshine bata saba dashi ba haka .

Zakiko koya don a kasan ku ake shukata fiye da ko ina a duniyan nan duk ranan da kikaje gida dashi ko
wani gida zasu tarbeki.

Nima hakan nake da ai dana je arab da farko nashe wuya a can wallahi gashi uwar rikon nawa ba
tausayine gareta ba haka zata tsutsiyeni dole sai naji saidai idan nagama naje na amayeshi.
Har nazo na saba a karshe yanzu gashi na iya wanan ai ba a cika tafarnuwa ba don nayi masu magana
tunda nasan bakyaso tun zuwana gidan ku na kula da hakan.

Ko yayane ki koyi cinsa koda kadanne don gaskiya larabawa da tafarnuwa aka sansu wanan zai iya ja
maki matsala su zargeki akansa kadai don komai da zakici can indai ba nasha bane zakiji dandanonsa a
cikinsa.

Kaina dan gyada alaman na gamsu a dadafe na samu yakai cibi biyar na mikedon barin wajen naji
ummu tace dani har kinyi me ?

Na koshi na fada ina kokarin ficewa tsakiyan kujeran dakin na nufa da sauri ranan bakina yasha brush
da kurkura don warin ya fita amma duk na hade miyau ina jin dandanonsa daram a harshena.

Wanka nayi na shirya cikin wasu atamfa dinkin dogon rigace ta sauka min har kasa hannu iya gwiwan
hannnu ya tsaya min saidai yasha kwaliya da hannun da kasan rigar zuwa wuya.

Na daura dan kwali daram ya kafu sosai saman kaina sai gyalen kayan dana dauko na yafa a jikina don
Abba da naji yace yau yana gida a tare damu.

Plat shoes na saka a kafana na fito suna falo gaba dayan su zaune tare da yayansu don haka sai na
tsargu na nufi part din da anty baraka suke ciki.

Don wanan da muke part din masu gidan ne nima aka ban daki a cikinsa inda zan zauna kwana biyu
ma,ana ba,a dai wareni ba ke nan acikinsu.

Saidai rashin sabo dasu ya hanani sakin jiki dasu yadda suke son na kasan ce wanda hakan yake kara
nuna natsuwa ga Abba din.

Ina kuma zaki haka Ayshaa ?

Muryan ummune ya shiga kunnena take tambayana tare da bina da kallo cikin mamaki na juyo ina
fadin gun anty baraka zanje mu gaisa in dawo.

Kuje da kannen ki su gaida ita ku dawo tare ga Abban ku zaune yana jiran ku wanka nake son shiga
nima .

Na amsa da to ummu na dan tsaya yaran sukazo suka sameni muka nufi part din dasu don gaida yayan
tamu dake can.

Abba ya dago ya kalli ummu bayan mun shige yana fadin yarinyar ta samu tarbiya fiye da zato wallahi
sam ban ganin wani nakasu a halayenta .

Haka ake son ya mace ta kasance mai tarbiya da alkunya a waje sam ba yadda kuke dauka bane abin
tsarin yadda aka tarbiyartan da itane hakan.

Ki kara janta a jikinki kema kin sani yana da wuya tunda bata saba dake ba tayi saurin sakin jiki yadda
kike so.
Ki godewa Allah da wa yan nan bayin Allah da kika barwa amana suka tsaya tsayin daki tsakani da Allah
suka kula maki da tarbiyanta haka.

A yadda nake ganintan nan kamar ko sauyi ko irin kawaye haka bata kulawa kinga hakan aiba karamin
sa,a kiyi ba Asiya.

Ta dago ta kalleshi don jin ya baci sunanta na yanka yace kwarai a gaban ki yar nan hindu ke shigowa
gidan nan kina ganin yadda nake takai da ita tarbiyanta gaba daya ya lalace fiye da zatonki wallahi.

Wai kuma a hamnun uwarta data haifeta ta barta ta koma haka balle wanan da kamun kai zalla ne kike
gani a gareta dolene ba zai yuyu ga dan adam ya kasance daidai ba sai andan samu akasin wani sauyi a
wajensa.

Nata ba illa bane ko rashin kunya yanayin natane yake haka don haka gidiya yakamata kiyiwa ubsngiji
don yanzu ni na rasa ta inda zam fara akan yaran nan .

Wanan yasa nayi amfani da daman zuwan Ayshaa gidan nan nake son aron rigar arzikinta na dan
hadasu zama da hindu a nan na dan lokaci .

Don taga yadda tarbiya ke tafiya ga ya mace cikin natsu don haka ina son kiyi hakkuri kikai zuciyarki nisa
keda kowa naki a gidan don kinsan ba kunya ne da ita ba.

Kana nufin hindatun zata dawo nan ke nan itama da zama yace ehh saidai ban tsanmanin zaman zai
dauki lokaci ina son yin amfani da wanan daman in gwada sa,ata ga hindu ko Allah zaiyi sanadin da zata
natsu.

Ita kadaice ya mace a wajena a yanzu banjin dadin yadda rayuwanta ya kasance a haka Asiya yadda naji
har shaye shaye takeyi da sauran munanan Abbu da Allah ya hana.

Allah ya kyauta yasa hakan ya zamo sillan shiryuwanta Amin ummu ta fada a fili saidai gabanta na
faduwa can ciki dajin abinda ya fada game da yar tasa.

Dole tace iya hakan tunda shi bai kyamaci yarta ba babu dalilin da zata fito masa fili tace zata kyamaci
nasa yar a yanzu a gabanshi.

Kamar ya karanci zuciyar ta taji yana fadan da fatan ba zaki dauki hakan takura ba a wajen ku
kwadayin tarbiyar yarkice yasa na yanke wanan hukuncin.

Kada ka damu ubangiji Allah ya shirya muna su a baki daya abinda ya samu hindu ai ya samemu muna
tunda an zamo daya yanzu.

Allah yai maki albarka Asiya ina alfahari dake a kullum kan zamowa mata tagari a gareni sallaman hjy
Nasare da hindun a bayanta da suke shigowa yasa sukai shiru a lokacin.

Muna can part din wajen anty baraka da ake buga hausa ita da yaran yayin dana dan kishingida saman
gadon tare da wayana naraba hankalina biyu ina saurarensu ina kuma duban sakon wayana lokacin.
Duk da uwar na koya masu hausa suna fada amma ba daidai ba sai zuwa nan yasa suka sare saboda
duk wanda yazo hausane sai suke ganin nasu ba daidai bane.

Har muka taso muka fito ana gardama fadan lafazi hakan yasa nake fada masu a cikin larabci suyi
yadda suka iya ana fahitar mai suke nufi da abinda suka fada din.

Dago kan da zanyine mukai tozali da su hindun dake zaune sun zobo min ido suna kallon mu haka
muka karaso wajen na sheda hjyn da suke tare wanan matar da sukaci min fuska ne ranan da naje gaida
man da baida lafiya.

Duk dadai ita bata fadi wani mugun kalami a kaina ba bayan tambayan da tayi da cewa nidin balarabace
ko wani kabila sai yar uwartace ta sake min magana har takeyi min kashedi a kan dansu .

Dace na kama gabana don man yafi karfina irin mune shegun diya tsaraban saudiya da ake zuwa nan a
yadda mu muna galafiri mu addabi mutane a gari.

Cin mutunci tayi min ranan da ba zan taba mantawa da hakan ba sai gashi yau mun hade dasu a gun da
bamu zata ba dukkan mu.

Matar na kalla ina gaida ita da kwana don taji darajan haihuwa a idona dana ummu dake tare da dan
uwansu na gaida ita tare da juyawa zan bar wajen.

Naji muryan Abban yana kiran sunana da Ayshaa yaki zo nan gareni ki zauna magana zanyi daku duka a
cikin harshen larabci hakan yasa na dawo na zauna a kasa kasancewar duk su duka manyane a gareni.

Nan naji Abban yace kingani ba hjy Nasare abinda nake son fada ke nan sai gashi a fili ya baiyana yanzu
don Allah ya dace muna zaune haka da yar nan ?

Ya nuna hindatu din da hannu ta dago ta kallo uban tare da kallona da nake kasa zaune cikin ladabi
yana fadin kin gani the difference is clear akwai banbamcin tarbiya sosai a nan.

Aiba za a hadaba ma yaya don yar nan nasan tana da tarbiya sosai don ba yau na fara ganin hakan
gareta ba gaskiya.

Saboda mun taba haduwa gidan yaya Ahmed da ita alokacin mun dauka cewa mam bashir magaji shike
nemanta sai mukaga sabanin hakan kuma yanzu.

Don kasan magaji da batar da sawu ya batar damu sosai kan halakar dake tsakaninshi da yar nan don
kowa ya dauka soyayya sukeyi da ita a lokacin.

Don an fadi kalaman da basu dace ba a kanta gaskiya lokacin sai yaya Ahmed daya nuna muna bacin
ransa a lokacin yasa hjy ta kyaleta muka tafi.

Yanzu haka tun ranan da nasan halakarku da yarinyar nan yaya kunyan abinda ya faru nake ji wallahi
don Allah hjy Asiya ki,,,,,
Haba haba dai hjy Nasare Ayshaa ai yarkice koda banda halaka da dan uwanki tunda kin haifi sa,anta ai
ta zama yarki.

A Cikin kunya ta amsa da gaskiyane wanan zance kin dai izza min nauyina kan hakan yata ki yafe min
ance matar na tuba bata laifi inji yan iya magana.

Allah ya kyauta dama na kirakune saboda ina son hundu zata zauna damu nan kwana biyu yanzun zaki
tafi ki barta nan a guna alabashin idan naga kamun ludayinta na gamsu dashi zakiji abinda zai biyo baya.

Ba hindun da aikawa haka ba har ni dake zaune saida na dago kai na kallin Abban cikin mamaki don jin
irin hukuncin daya yanke kan yarsa .

Kafin na dan saci kallon hindun din naga duk ta lalace man bleaching duk yai mata illa a fuskanta.

Haka kuma gashi ta fada don ta rame tayi wani irin baki ta koma wata irin jagwal da ita da gani akwai
abinda ke damunta.

Ma,ana dai ruwa ya karewa dan kada,,,,,,,,,,

Abban yace wanan yasa nace ki zo min da ita gidan nan ba tare da kowa yasan tsarin dake a zuciyana
ba .

Don dama haka nake son in gishirta ba tare dayiwa zuwan nata wani shiri ba kana ya juya wajen ummu
yana fadin.

Hjy Asiya da fatan zaki saka min ido akan motsinsu dukkansu biyun daga ita har yar uwarta Ayshaa ki
saka masu duk wani motsi nasu ido a gidan nan.

Duk da yake yau yaya babba zata iso gidan nan itama don ,,,,,,

Hjy Nasarece ta katse shi da fadin yaya babba dai yaya babban yace kwarai itace zata zo nan ta kwana
biyu damu komai akan tsarinta za,a bishi.

Shima wacan na tura a nemo minshi ance kwanaki an gasa ghana yanzu dai ko ina yake na tura za a
dawo min dashi gida insha Allahu indai yana raye.

In Allah yaso ma yana raye yaya kurciyane dai da rashin sanin ciwon kai da sakaci Nasare har yaushe
yaro kamar wanan za a sakar mai dukiya irin haka da sunan kasuwanci a wani kasa.

Hauka irin ta uwarsu ni ban taba jinsa a rayuna ba Nasare kamar munir ne zata tura zuwa wani kasa ya
zauna shi kadai wai yana kasuwanci ?

Ita da take son kudin meyasa bataje ta zauna ba sai shi zata tura saboda rashin sanin ciwon kai da
hauka.
A daiyi hamkuri a daina tuna abin yaya kada rai yai ta baci a banza don Allah kayi hakkuri ta juya ta kalli
yar tasu tana fadin hindu kinji abinda mahaifinki yace don haka ni zan koma gida ke nan inwa su hjy
bayani kina nan gidan mahaifinku ya rikeki.

Da fatan zaki mata bayanin waye yaya babba don ta kama kanta kafin ta iso ta dan murmusa tana fadin
aita santa yaya ko bata santa ba tana da labarinta ai ban dakine kawai yaya babba bata bin mutum taga
yanayin da yake ciki idan yana karkashin ikonta.

Wata yaya babba kuma ni meye hadina da wata yaya babbansu can tunda ban hada komai da ita ba ?

Mikewa hjy Nasare din yasa na dan dago tana fadin yaya ni zan tafi dama ina shirin zuwa dubiyane
gidan kanwar Alh data samu hatsarin mota hanyar jimeta Allah dai ya gyara abin da sauki ba wanda ya
mutu motar daice akace ta nakasa.

Subbahanallah Allah ya tsayar nan ya maida sabon rabo ummu ke fadan hakan da tun farko itama
nasan tunanen zuci takeyi a lokacin.

Amma mummy da an barni na koma na kimtsa sai in dawo daga baya saidai kuma ai kinji abinda
mahaifinki ya fada yanzu a gabanki ?

Ke ki kama min baki a wajen nan ko yanzu kisan halina kin dauka kowa irin kine mara tarbiya halan ?

Kin kai yar uwarkice dana tsayar da ita kuma ta zaunu a nan ko don ita bata da halin banzane batayi
min gardama ba ?

Watau kin mayar damu sakarkaru zaki koma ki debo min kayan mayenki kizo min dasu gida kishiga
hankalinki kada ki dauka bansan abinda kike aikatawa ba garin nan ?

Bayan haka kuma duk wata kawarki data kuskura tazo gidan nan tuni na fadawa masu gadi su kama
maishi a daure min ita sai ranan dana waiwaiyeta.

Zaune yake saman kujera a falonshi jikinshi yana saye da kayan motsa jikinsa daya saka tun safe da zai
fita jugging .

Har lokacin mamakin daya kwana dashine ke damunsa a zuciyarsa duk da yasan hakan ba wani abu
bane amma kuma yana da mamakin maganan daya tsunta a bakin baffan nasa dake mata murna akan
jerabawanta.

Yasani bai nunawa yarinyar wani abinda zai nuna yana sonta ko yana jinta a zuciyarsa ba asali kuma
tun farko haka abin yake bai taba mata kallo da wanan tsigar ba gaskiya.

Kallon karamar kanwarsa yake mata a da saidai a yanzu zuciyarsa dake masa barazana akan hakan inba
karya fadi karya ba zai iyacewa a takaice ya fada soyayyan yarinyar nan yanzu .

Saboda ba mintu biyu cikaku kome yakeyi sai yarinyar ta fado masa a zuciyarsa da farko ya rasa
ma,anan wanan bakon yanayin da yake ji amma yanzu ya fahinci sone zallah hakan ke nufi .
Shigowan salman dakin ya katse masa tunane ya shigo yana fadin Man ashe kana gari yanzun nan naga
daki a bude na gane kana ciki.

Jiya na dawo da safe ban kuma zauna ba muka tafi unguwa da baffa akan zancen filinsa da yake son ya
karba saidai maishi ya tsaya muna dan tauri kai da farko amma yanzu komai ya daidaita tunda yaga zaiyi
biyu babu baiga kudinsa baiga fili.

Don Alkali yace a dauresa shi din barawone ta yaya zai sayi abu a hannun mace kasan halin baffa da
sanyi yasa a sakesa a basa kudinsa da mummy ta sayar masa har ya dora masa dan riba a sama kuma.

Allah sarki ina jin ana ta yabonsa ai a gari wai ashe shike da company HAAU a garin nan aketa cewa na
wani balarabene can ?

Nasane mana sunan yaransa ne yai amfani dashi yanzu kuma wanan filin da muka karba duk wani gina
da aka dora wajen za murjesa a gina katafaren plaza amma wanan din ba nasa bane mahaifin Ayshaa ke
son dora wanan wajen suyi shagunan su saura kuma abada hayansa ga masu bukata .

Ni har yanzu ina mamakin wanan lamarin watau dai da gaskiyane mahaifin yarinyar nan yana raye
dama ya barta a nan ?

Idan kana shakkun hakan ne kana iya,,,, wallahi ban shakka akai kawai dai abin ne yake ban mamaki
matuka wallahi.

Ranan nake ji da sunanta ashe cikin wa yanda suka lashe jerabawan su wanan malamin nasu na office
din mu nagani da list din yake fada min.

Ashe zakaje kai mata murna ke nan sai yayi murmushi saboda yasan gatse yake masa yacewa dan
uwansa din ai naje na bata hakkuri lokacin har gidansu.

Ta kuma nuna min

81 / 109