Author : ZAINAB IDRIS MAKAWA Category : KDP NOVELS
yau
din nan da za ayi kamunta din.
Wajen yasha decoretion gwanin shawa Auwal ne ya kawomu donshi na kira ya zo ya dauke mu zuwa
wajen nasha kallo sosai dolene ni kaina nasan na tashi ga sanin da sukai min a baya ina Aeesha lokacin.
Gashi tayi gaiyan yan classmate din mu sunzo bukin dan ganin kwam da masu aure da ire iren mu duk
an hallara wajen ana kashe kwarkwatan idanu.
Haka taso ta raina min wayau a cikin mutane na nuna mata bata isa a gaban kowa na juya Allah yasa
babanta na wajen yana kai da komo shiya ban hakkuri na tsaya nida Asmau da maryam har Auwal ya
juyo ya dawo daukan mu.
Muna gefe na fada maku irin wanan sha,anin yana hawa min kai ban faye son shiga taro ba don haka
nake komawa baya in tsaya.
Amma haka yan mate din mu idan suyi gulman su sai suzo wajena don kawai suga abinda ake fada din
na canzawa na din da suke fadin nayi.
Dogon rigan abaya daine na saka sai takalma da bag daya dan rataya nina koma abin kallo zakice nice
amaryan abinda Aimana bata so ke nan kuma ya faru.
Tun ba,a tashi ba Asmau ta nemo muna ita na mika mata dubu hamsin nace mun tafi kaina na ciwo
sanyi nake ji.
Ko ganin kudin ne yasa ta dan sake tana fadin zazzabin nan dai bai sakekiba kila sai kin hada da asibiti
nace dole.
Gobe dai zaki shigo ai balle gobene yace muna zaizo da abokanshi nace wake nan tace angonta nace sai
yadda hali yayi in dai naji sauki insha Allahu zan shigo.
Dama Auwal yana nan bai tafi ba muna hanya naji yana waya da wani yana mashi kwatancen unguwar
mu kusan tare muka iso ashe bakaniken motane ya dauki motana ya tafi da ita.
Ni banji komai ba har kasan zuciyana amma Asmau sai fada takeyi wai haka kawai inbada mota a tafi da
ita niko nasan don nace sai anwa motar tawa service ce zan fara shiga yasa yazo ya dauki tawa.
Saidai su sun dauka wani abune ya faru yasa aka dauki motan daga gidan mu sam hakan bai dameni ba
koda Abbu ya tambaya na fada masa za,a duba tane kafin na fara amfani da ita.
A zuwa lokacin munyi waya da Aimana yakai karo na uku tana tambayana abinda ya dace ma,ana dai
da alaman ta huce hushin da takeyi dani din.
Hakan da nagani yasa zan daure inkoma inbashi ba nayi alkawari a raina har a gama bukin ba zan kara
taka gidansu ba.
Magani nasha na kwanta don in huta sai kuma na dauki wayata na bude ina duba sakonnin dake ciki
yanzu kan na sheda numbershi da ba kowane ya santa ba sai wanda yaso ya sani din.
Ya jikin naki ya rubuta daidai ina hawa ya turo sakon na mayar mai da sauki cikin mamaki don ya fara
ban tsoro ni dai a sanina ai yan gidan mune suka san banda lafiya kadai.
Are you sure ya rubuta nace yeh i am ok insha Allahu na lumshe idona zuwa yanzu kan na fara jin wani
yanayi game dashi kuma abubuwan da suka faru tsakanin mune a baya suke dawo min a rai .
Yawan gargadin da yake min akan na natsu kada in tsaya kula samarin jami,a masu batawa mutum
lokacin da bata suna da tarbiya na rike tarbiya da nazo dashi.
Zama popular bashine cigaba ga dalibi mutukar ba studies dinka bane ya fitar maka da suna a cikin
makaranta ba zakice wani babana ne ko yayana da muke ciki daya dashi yadda yakan tsare gida yana
min fada kan karatuna.
Alhamdullahi wanan huduban ko ince nasihan nasa na kama ya kasance ban yarda nayi saurayi ko daya
ba a cikin makaranta duk ko da irin barazan nan da nake fuskanta a wajen wasu ban kula hakan aboki na
shine classrep din mu sai wasu course mate da wani lokaci zamu hadu muna tattaunawa akan abinda ya
daure muna kai ga karatun mu.
A hankali nabi filon da nasa kaina ina sauke ajiyan zuciya bawan Allah nan ya fitar dani kangin
wullakancin dake bibiyan rayuwata a baya gaskiya.
Ta yadda ya daukaka darajana mafi girma a yanzun cikin al,umma meye daukaka a yanzu gun mutane
shine su ganka cikin rigar arziki ba a wullakance ba sai kiga an mata da wani nasaban kai ba kowa bane a
idanuwansu.
To Alhamdullahi sutura gwargwado akwaishi gareni duk daga bawan Allah nan Bash haka kuma motan
shiga ta motace ta masu dan hali duk daba motan karya bace balle ina nasa a raina zan taba mallakan ko
keke balle mota din a yanzu.
Sakon S matazun na bude yake fada min in two weeks zai shigo yana son ayi magana akan zancen mu
akai ga matsaya Allah ya kaimu na bashi amsa dashi don bai online a lokacin.
Sai yazid dake fada min Abba ya sayowa kowansu Laptop saura mota yace sai kuma ya koma fadin
gidan ya koma shiru yanzu sunyi missing dina a gidan Abba ya tambayeni sun fada mai na koma gida.
Haka dai nayi tabin sakonsu ina karantawa ina bada amsa don ba ko yaushe nake samun shiga
whatsapp ba sai lokaci lokaci irin dare haka idan zan kwanta wata rana.
Sako na sake gani daga man din na bude yana fada min da safe Auwal zai kawo min motarshi daya bari
nan nayi amfani dashi kafin a duba min nawa .
Cikin mamaki nace motarka kuma sir ya rubuto min da yes ko tayi maki karamane da shiga yanzu ?
Haba dai sir motarka ai tayi min girma gaskiya zan dai jira a gyara min tawa ba wace kika sani da ita
bace ki bari a kawo din ki gani ya rufe da tambayan bukin wacece kukeyi.
Wata yar uwarmu ce na rubuta da farko saina tunada hatsabibancinshi yanzu haka yasan ko yaya muke
da Aimana din don waya fada mai ma muna bukine wai na tambayi kaina.
Gaskiya abin ya fara yawa ni dai karda duk sirin cikin gidan mu yana a idon bawan Allah nan ne ba dama
nayi ko tari sai a kunnuwanshi ?
Gashi na kasa gane hatsabibin dake bibiyata yana fada mashi komai daya shafi rayuwata dana duk
wanda yake a kusa dani wai ace har abuja danaje ban huta ba ?
Aimanace we are so closed with each other tare muka taso da ita a wancan unguwar da muka fara
zama da farko kafin mu dawo wanan gidan nan dai nayi masa bayani yadda zai gane.
Bai ban amsa ba jna ganin ya sauka har barci ya daukeni washegari masu fita karatu suka fita gidan ya
koma tsit dagani sai anty Safiya sai Ammah da Abbu a gidan.
Ammah ce naji tana kwala min kira na amsa na fito tana zaune saman kujera dan tsuguno na zaman
tsakar gida na sameta.
Ta juyo tana fadin kina son hora kanki da yunwa yar nan gari ya waye baki fitowa ki nemi abunda zakici
sai ki shige daki ki kwanta.
Allah ya wadata mu da abinci da kika kawo muna ga taliya ga doya ga wake ga mai ga kuma shinkafa to
mutum ya zauna haka da yunwa a daki tun safe.
Fito ki dora abinda kike so kici wa ranki mana tundai ina saka maki ido har nakai ga maganan abin haba
Aeeaha sai kace wata bakuwa kuma yanzu ?
Ammah banjin yunwane ai anjima kadan zan samu abinda naci idan naci yanzu zai ban wahala ta
kalloni tana fadin tauuu wata sabuwa ba daiyi dariya nace Abbu yana barcine tace abinci yake ci idonsa
biyu.
Ta sake fadin ko sauran ba zakici ba ke nan na girgiza kai nace Ammah sai anjima dai ni a ban idan ba
zataci ba anty safiya ta fada daga bayan mu.
Tunda kece mara kunya ba dole ai in baki kina daki kin zube muna diya ga wahalalu kin samu ko jeki ta
kwanciya kici kwancin isan shi zai fiddake kunya.
Na kula dadi yayi maki yawa a kwanakin nan abuncine ba sai kin nema ba gashi ki girka kawai wai don
samun waje ba zaki iya tashi ki girka ba malam na fadan gaskiya ana ganin laifinsa ?
Daki na koma ban tsaya saurarensu ba wanka nashiga nayi har lokacin ina jin muryan Ammah bayan na
shirya zan fitone naji anty safiya din na kwala min kira wai ana min sallama a waje.
Dana fito na samu anty safiya din ta dora wutan abincin rana taji fadan da Ammah din tayi mata ke nan
a lokacin nace ku daiji dashi.
Nina sani don Asmau ta fada ranan tace laifin babansu kawai ake gani bakin cikin uwarsu ma zaisa ya
gudu irin dabi,an banzan nan takeyi ace ba a girka abinci a gida saidai abawa yaro kudin da uban ya dan
bayar ya sawo dan wani abu yaci shi zancen sanwa babu shi.
Sallama aka karayi daga kofan gida na amsa don na kusa isa nakuma sheda muryan Auwalne yake
sallaman lokacin.
Auwal kaine tafe ashe yace nine wallahi rankishi dade ina naga zama tunda safe yallabai yace naje na
wanke mota suka bata min lokaci yanzu kuma ya kira nace ban samu kawo maki ba.
Ya falfaleni aiba shiri na taso a guje gata nan dai a waje a bude get na shigo da ita sai in shiga inga baba
ya ban sako wajensa.
Au har an gyaramotar ke nan na tambaya yace a,a bai maki bayani bane tasa motan yace nakawo maki
ai kai na kada ina fadin Auwal.
Wana boss din naku saiku Auwal ni kamar aljan nake ganinsa wani lokacin ya kwashe da dariya kafin
yace kinsan fa shi especial force ne kuma na inter national .
Saidai idan baiso sanin komai akan mutum ba yanzune za a binciko masa komai na mutum kuma ba
kowa yasan da yana wanan aikin ba donsu boyayyune a cikin mutane.
Haba nikan abin yana ban mamaki Auwal komai ace mutum yasani game dakai kamar aljanni ni har ya
fara ban tsoro wallahi.
Ba wani dogon hira nake dashi ba mai tsayi duk da mun shaku kuwa don gogan tun farkon hadamu yai
min warning akan hakan baisom yaji ina dogon hurda da Auwal din badon komai ya daukeshi ba don aiki
kawai.
Kofan na bude mashi gudun kar dan leken asirinsa ya fada mai kuma mun kebe da Auwal ai na tsawom
lokaci.
Saida ya shigo da motar gabana har faduwa ya dinga yi ganin motar tare da tsoro ya gyara mata zama
ya fito ya shiga yaga Abbu din sun dan jima kafin ya fito yai muna sallama ya tafi.
Abune yasa min kira nazo na zauna a gefe daya kokarin bude takardan kilishi yakeyi sai kuma ya fasa ya
dauko wani leda ya mika min yana fadin sakon da yaron nan ya kawo min ne yanzu ki bude ki gani saiki
raba biyu ki saka min a bankina.
Saura kuma ko ki boye a wajen ki koki aje min nan karkashin katifana duk da har nan din ana zaran min
kudin wani lokaci.
Har yanzu ana wanan dabi,an yace kedai bari yar nan ai zanyi maganinsune Allah dai ya ban lafiya nana
kiga ikon Allah kaf zan kwashesu in mayarwa ubansu da abinsa.
Abbu kayi hakkuri anty safiya bata da lissafi idan abinta ya tashi niko meke damunta ban sani ba ?
Yace jahilci kada ki kara ga wanan ba komai bane sai jahilci da hauka ai yar uwarta kin gani ita dayan yar
taki ba haka take ba tunda ita malamace sosao bata yarda ta rasa daya ba.
Tana zaune tana zubawa uwar plan din data hada tun bata dauka ba har yakai uwar ta dauki zancen da
muhinmanci a take kamar yadda yar ta tsara tasa a kira mata imamu ya dauka suka gaisa.
Take fadin kayan nan da Ahmad ya dawo dasu nake son ka kawo min nan yanzun nan zan tura a auna
minsu a gani ?
Ina hjy kaya ai sun zama kudi ina jiran na kamalane na zo ai na sameki don maimartaba ya bada bakin a
sayar dasu gudun kaddara tunda yanzu kowa yasan suna hannuna .
Bata san lokacin data karbe waya hannun uwar ba tace wani munafunci yakai har baba yaji wanan
zancen kuma ana abu tsakanin mu iya mu yan dakin nan.
Au dama nasan kina kusa mara kunyar tsiya ke ai duk wanda yasa maki kuran nan da yana raye dana
masa kari akan hakan don sunan ya dace dake KURANYA .
To kaya kan sun zama kudi a yanzu don niba Ahmad bane imamu nake ba zan saka kaya haka ina kallo
ba.
Ai wallahi baka isa ba inma har sayarwa za ayi ai a gaban kowa ya kamata ayisa ba a dunkule ba .
Ko yanzu bai baci ba don kinsan wanda ya saya ba kuma kowa bane yaron nan Bashir ne dan wajen
Ahmad idan na kawo kudin basuyi maki ba saiki kirashi ki fada masa kin tayar da ciniki tunda nakine
dama ?
Tana jin ya kashe waya taji kamar ta dora hannu akai watau su imamu zai rainawa wayau dama plan ne
abin don an mayar dasu mata shine za a yaudaresu a fito masu ta wanan tsigar.
Yayin da dattijuwar kuma take cikin wani hali jin zance yakai inda bata son ya kai shine damuwanta ita
kuma ?
Kura don Allah ki rabani da zancen nan ki barni inji da abunda halinki yaja min a yanzu dutsen nan dole
maimartaba ya tambaya inda ta samoshi ?
Kallon uwar tayi cikin mamaki tace kwarai kina mamaki ne don na fadi hakan nasan dolene ya zargeni
ba kuma kowa yaja min hakan ba saike kura saboda irin bakin cikin ki da hassada.
Ni kuma ina biye maki ga duk abinda kike so tunda kikaji fitsararen yaron nan ya sayi abin nan to akwai
wata a kasa ke nan yasa tun lokacin na mikawa Ahmad shi ya sayar acan kasan ba tare da kowa yasan da
hakan ba .
Amma kika dinga tsegumin da har yaji duk abunda kike fada akansa ya kasa kawar da dutsen nan tun
lokacin nagaji da wanan zubar da mutuncin da kike min wallahi nagaji.
Hjy yanzu ba zancen fada bane ai yadda za a karbo dutsen gwal din nan daga hannun Bashir shi zamuyi
tunane tunda nakine kowa yasani.
Kallon baki da wayau tayi mata kafin tace da ita tashi ki koma gidan ki ni zan shiga daga ciki sai jikin hjy
kura din ya fara sanyi .
Don ta fahunci uwar ta shiga wani hali a lokacin halin da ita kadai tasan meke faruwa da hakan don har
wani zazzabi taji yana neman rufe ta a lokacin.
Yadda ta umurce hakan ya faru tasan dole akwai dai don sanin halin mahaifiyar tasu da tayi kamar
yunwar cikinta kusan ma,ace ita din ta kwaso saidai a yanzu tasan ta dara mahaifiyar nasu ga komai ta
damata ta shayen.
Program akeyi kamar yadda aka tsara za,ayi amarya Aimana taci kwaliya sai ido ke binta wasu na
sha,awa wasu kuma da abinda ke zuciyarsu kan auren .
Ganin yadda take nuna ko in kula ga kuma rawan kai duk da bata san angon ba shima bai santa ba sai
kudi da yake turowa uwar ta raba gida uku ta dauki kashi biyu ta mika masu kashi daya ta bisu da dadin
zance na bakinta.
Abin duniya baya boyuwa yanzu duk yadda kake gani ka gina rami ka rufe a yanzu sai wani yaji zance
suna ganin mutane basu san yadda kan auren yake ba .
Su kuma mutanen unguwa suna kallonsu kar don sunsan gaskiya ga zance anata masa kwaskwarima da
kanikanci kowa da abinda yake fada kan da hjy din.
Amma baban Aimana yace indai yana sallah komai zasu fada suyi ta fada din shi ba ruwansa tunda
yaga yarsa yace yana so.
Mukan sai yamma lis muka samu hallaran wajen taron kauyawa day din da akeyi daga nisa na packer
mota muka fita bayan na kullene muka fara gaisawa da idon sanin cikin unguwa.
Ga gaiya harna tsiya da tayo don son a sani ace bukinta yakai buki idan an tambaya ance ai kasan
wajene miji yake ita zata cabe tace Canada gaba da America yake zaune.
Muna gefe daya muna kallon didima a wajen sai al,amari akeyi wai ana koyon yan kauye wani abin ma
ko a kauye yanzu da aka waye saidai tarihi ya basu labari.
Ana ci ana sha dan gudun mawan da take samu shi take faman kashewa don tafita kunya tunda ango
bai iso ba har lokacin.
Sai cewa take yace sun kusa isowa Nageria ai ko kuma tace wai jitgine ya samu matsala suna kasa kaza
da nice ita ba zanyi komai din nan ba sai angon nan sun iso su fitar suyi yadda al,adan yake a hausance.
Koda aka tashi ba gida muka nufa ba muka kwasa zuwa gidansu na samu Ammah ta dade da komawa
gida saboda nisa a gidan nasu mukai sallah magariba da isha,i ina ganin karfe tara yayi nace zamu tafi.
Aimanan ce tazo ta kirani muka shiga dakin mamanta don ba mutane a lokacin kowa ya watse dama
gaiyan na ranan don ace ango zai iso a ranan ne yan ganin kwam suka taru don sheda kuma basu iso ba.
Muna shiga ta zauna saman gado tana fadin Aeesha kinga mutumin nan baizo bafa nina fara gajiya da
wanan karyan nasu shida mamashi.
Yau in munje tace muna kaza gobema da abinda zata fada muna idan munje nifa na fara shakku a kansu
wallahi ga mama sai faman kuka takeyi wai munki jin maganan ta tun farko nida daddy.
Haba dai saboda nisan wajene fa canada aiba lagos bane ko enugu kasan wajene fa kin daiji abinda
Addah ta fada ai tace akwai nisa sosai wallahi.
Tace nima in na tuna hakan sai na danji ban damu ba haba dai zasuzo mana yaya za,ayi aure ba ango
kusa kuma ba wanda fa ya taba ganinsa ko yanzu bananan ne na tambayeta hakan ?
Tace haba dai zaizo ban fada maki ba Aeesha aiko a waya zan kiraki ku gaisa kada ki damu da mutane ki
sake kawai ki sha,aninki ina ruwanki da wasu can.
Ban yarda na fadi wani abin sukan zancen ba tace saboda hassada ai nace kaza son haka hakkuri kurum
na bata na kwantar mata da hankali tsakani da Allah kuma.
Karshe dai tare muka wuce zuwa