Chapter 35 Reading Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA HN Novels

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka by ZAINAB IDRIS MAKAWA

Author :  ZAINAB IDRIS MAKAWA Category :  KDP NOVELS

Chapter   35 / 109

102K to 105K   out of 326.5K words

Transforming your body




Kece Aisa mahmud ta fada na amsa da ehh sannu da zuwa zaki dawo nan da aiki damu a karkashin
wanan division da fatan zakiji dadin aiki damu nan cikin kwarewanki.

Kai na gyada mata a hankali ina sauke wani siririn ajinya zuciya a boye ta mike tare da fadin muje kiga
wajen zaman ki.

Na bi bayanta har zuwa inda suka nuna min kowa na kan aikinsa ya kurawa computer ido suna bincike
sannu nakai zaune ina ajiyan zuciya karo na barkatai a tare dani.

Yanzu kuma Allah ina ka kawoni na fada bayan nabi kowa da kallo nagansu murda murda ba annuri a
fuskan kowa a lokacin duk da safiyace kusan kowa yana na wajen nake gani.

Idona na mayar kan computer din dake gabana a kunne ina karata abinda yake halbowa min lokacin
signal din na kurawa ido na dan lokacin.

Inter na shiga sun turo mjn password da sauran bayanai ina bi daga can kuma suna kallon ashe ta cikin
computer nasu suna bincike a kaina da yadda nake gudanar da aikina.

Ance himma bata ga rago ganin ga abin sarrafawa gabana yasa na shagala da aiki da computer din ina
shiga ko ina da nake son bayanansa .

Saida lokacin break yayine naga su fita guda guda hakan yasa na duba naga lokaci yayi mema zanci
yanzu idan na fita na tambayi kaina ?

Dadin kano ke nan ga abubuwan filawa nan na gargajiya da zakaci ya kosar da mutum amma nan sai
shegen kayan karya marasa dadi da suke sayarwa kawai sai tsada ba dadi a baki.

Zama na gyara ina lumshe ido don tunawa da gurasan filawa da mukayi a bayan marfin sanfara a ci da
kuli kuli da ganyen kabeji ko salad bayan an yanka albasa da ata ko tattasai .

Nakanso shi sosai don nakan masa zaman kansa inci in koshi in yini ina shan ruwa sam baki ganin
wanan cimar a garin Abuja.

Fantan gora mai sanyi tare da vegetables eggs rolls dake nade kamar an nade tabarma ko kafet guda
biyu aka dora min saman table din nawa.

Jin an aje abu yasa na bude idanuna nabi abin dake cikin leda da kallo kafin na daga kai na kallo maishi
dake tsaye yana murmushi yace .
Gani nayi baki da niyar fita nayo oda dake ko zaki karya dashi sai dai don Allah nayo maki fa kada ki
dauka wani abune yasa na kawo maki sunana Isma,il ni aiki ya kawoni nan.

Nagode na fada karki damu mu din yan uwane tunda mune musulmai a nan ya tafi nace ni Aeesha
wanan farin jinine ko wani taimako daga Allah.

Ido na sauke kan kayan daya aje min din da akalla ya kashi kudi mai yawa wajen sayesa don nasan
yadda kayansu yake tsada a wajen.

Na jima kafin nakai hannu tare da bissimillah na dan guntura kadan naji dandanon abin gashi nan dai
shiba ganye ba ba kuma nama ba.

Ganyen cabej ne da carot sai kifi da kwai aka nadesu ina jin waje daya haka ya dan bada ma,ana ake
sayarwa mutane ba laifi hadin yayi dadi na gama na dan sha ruwan fantan na kora saina jini normal dani.

Sun dawo munci gaba da aiki yanzu kan na gane me mukeyi a wajen shiga na,aurace ta bincike akan
wani takardan da aka bamu tare da wasu sunaye don haka na mayyar da hankali sosai ga aikin.

Sallah kawai ke tayar damu lokacin har ban kullah ba wayana na samu miscalled kusan hudu a lokacin
daga unknown number na tattara kayana na fito .

Muka hade da Enkeci nan take ban labari abinda ogansu yace wai an dauke ni daga wajensu an mayar
dani office din manya don yar masu kudi.

Dariya kawai nayi tare muka jera da ita muka tsalaka muka tare taxi zuwa gida kodana koma kusan
magariba na shiga gidan a gurguje .

Nasamu yan gidan sun dawo tsatsaye na gaidasu na shiga ciki babu dakin kam baida matsala na debe
kayan jikina na sauya da wanda nake zaman gida dashi.

Na tsaya na nunke kayan na fito don inyi alwala saboda idan kana ciki baka sanin lokaci sallah yayi
saidai kayi amfani da lokaci kawai.

Hakan nayi lokacin ai da sauri na jawo baya don bayin baya shiguwa saboda wari daki na koma kamar
zanyi kuka ga lokacin sallah na shigewa don har duhu ya baiyana ko ina.

Hakan yasa na dauki goran ruwan da na dawo dashi na fito lokacin na samu basira din zaune suna ta
zuba yare da yan uwarta zan fita take fadin ina zuwa Aisha ?

Alwala zanyi a kasa don bayin baya shiguwa anty i dont now mutum zai kewaya ga ruwa ga Izzal kayi
lalura ba zaka tsaya ja gyara waje ba for god sake tunda muna shiga muna ibada a ciki ?

Yare naji tanayi ban gane komai bani banda ighole da naji kamar tana fada a yaren nasu nidai nafice
Amira ta biyuni zuwa kasan nan nayi alwala muka hawo saman na samu ansa wanan yarinyar da muke
kwana daki daya da ita wanke bayin tana kuka tana maganganu a cikin yaresu kamar fada.
Wallahi banda abin nan da abin nan da dan office din mu ya bani nayi break banci komai ba haka na
kwanta har lokacin.

Wayata dake kara na daga na dauka number dazun ne dana gani ina dauka naji ana fadi a cikin hausa
mum ta dauka fa .

Sallaman naji na amsa sai naji tana fadin haba yata ina nan nadamu da zancen ki ke kuma kinki daga
waya tun dazun hankalin mu wallahi ya tashi.

Ko kin dauka mu din zamu ha,incekine yasa kikaki daga wayan mu wai sai lokacin nagane wanan matar
ce data rage min hanya da safe.

Subbanallah sorry mah wallahi wayarce take silent a cikin jakka yasa ban daga ba kuyi hakkuri don
Allah mama na fada a karshe.

Nikan na damu wallahi zancen ki ya tsaya min a rai tun safe wallahi yanzu yaya kina gidan ko kin bar
gidan nace ina nan mama to kinci abinci ?

Murmushi na danyi nace a,a ban sayo ba na manta in sayo da zan dawo you see hafsat mena fada
maku dama wallahi hankalina ya ban irin wanan rayuwan yana da wuyan sha,ani wallahi.

Ta tsaya tana magana dana kusa da ita kafin tace kina jina yanzu gasu nan zuwa su kawo maki abinci ki
dan fito don su ganki don Allah .

Ina jin bata kashe waya ba taci gaba da maganan dasu ta bangareta tana fadin wallahi ai kinsan halina
mama haka kawai fa ni da kaina nace mu tsaya mu taimaka mata.

Yaya za ace mutum ya kwanta baici abinci ba don Allah ya kwana hakana suna ta zance akaina dai haka
da kuma kan karatu yana sa mutun ya koyi darasin rayuwa da yawa a cikin rayuwa.

Shiryawa nayi na fito a don dole tunda bata jira cewana ba ta naji ta fita zancena tanawa wata bayani
lokacin hakan yasa na sauko na kira serah nace tazo ta rakani kasa don Allah in karbo abu.

Muna saukowa motansu na zuwa a slow suna duban ta inda zan fito a cikin gidaje wajen don kowa
yana cikin gidansa lokacin sai yan tsirarune a waje suna harkan gabansu.

Sun shedani tun daga nisa hakan yasa Yazid din yayi min horn yana sake min dim light suka karaso
muka gaisa dasu na tambayesu mama sukace tace a gaida ke.

Saida ta fito ta miko min abincin nayi godiya yazid yace anty hafsat ke nan yayatace ita amma ban
yarda ba don nine babba yanzu .

Bata da jiki sosai tace kyaleshi sister kinji mum ta dawo dazun tana min hira sai banji dadin hakan ba
wallahi naji na matsu da inzo na gan ki wallahi .

Ga wanan yana taban labarin waike kamar fulanice kuma dai ya rasa ya zai fada min ke mum tace mu
fada maki da safe idan kin shiya ki jirasu a inda suka daukeki jiya.
Kai Allah ya kyauta zance gun wasu ba sai an saba ba da juna ko sun san mutum ba ashe haka nake jin
zancensu a raina har muka rabu.

Bayan sun wuce na juya zan koma naji serah ta ya futoni na waigo tsiyan abin bata iya turanci ba sai
sharbe take sarawa yasa ni ban ma hira da ita wani lokaci saina kurame a tsakanin mu kuma.

Ta nunani tace Ungo na Lucas do am for you dan murmushi nayi nace ke don Allah zo muje ni kan ban
gane ba wallahi tayi ta kokarin min kwatace nace ban gane ba.

Ta karbi leda a hannuna ta hau sama don cikin wasu take away masu kyau aka zubo min abincin basu
sa a kayansu ba.

Ta rigani shiga daki da kayan don yar uwar nasu bata falon muna shiga ta nuna min akwatina tana
fadin cikin gwalanci yadda zan gane tana kiran sunan Lucas din a lokacin.

Yasa nagane abinda take nufi cewa lucas din yayi kokarin balla min jakkata ranan wanan babban suke
kira da lukas gashi da wani kai ya tara suma sai yawan son zama da dan pant wai wando ko yaushe gashi
da kayon jiki fuska kamar alade.

Ni kaina wani lokaci wallahi nakan yi sabo idan na dubi basira na kance ko me yaya ya gani a wanan
matar ya tsallake matan kano oho ?

Banda farin fata bata da kyau yau balle nagobe saidai hasken fatan da take dashi kawai shine dai ga
kiba ga kazanta a nan ya yanke tushe wajenta.

Shiko gashi dan gaye dashi fes fes idan ka ganshi waje sai kazo gidansa ka raina masa da wayau kilama
hakan yasa bai zama gida ko yaushe .

Sai dare yake dawowa da safe kuma in ya fita sai dare koda weekend ne kuwa rayuwansu dai gaskiya ba
abin koyo a cikinsa saidai ki.

Abincine lafiyayye suka sako muna na danci kadan na ajewa Serah sauran idan ta shigo ta lebe taci don
zance duk wani aiki itace meyinsa itako dayan sai zama yin cards da maza shine aikinta.

Tausayi serah din ke ban wallahi ina ko jin ta cikin dare data shigo ta samu a inda na aje mata ta dan
tadani daga barcin take tambayana wai taci nace ehh.

A take ta zauna tayiwa abincin nan tas tare da sauran ruwan dana aje din danasha ta kwanta ina
kallonta cikin duhu ta ban tausayi.

Washegari na shirya ban tsaya yin komai ba tunda ko anyi sai su bata illa bayi dana gyara nayi wanka a
gurguje nafito na kitsa na fita.

Ina isa suna isowa da mota suka daukeni kusan kwana uku jere a hakan tare dasu nake zuwa wajen
gwajina da yanzu nake jin dadinsa har nake ji kamar aikin a jikina.
Ranan thursday ranan sa kayan gidane da kuma tashi da wuri wajen aiki don haka ranan nayi kwaliya a
cikin atamfan da akaiwa dinkin buje da riga na fito dagwas dani.

Komai nawa na asali kuma ya baiyana a yau fili ranan kuma hjyn nan likita da Allah ya hadamu ta fara
ganina da kyau ranan ita kadaice tazo ita ke driving din kanta tace Yazid mashirirci ne yanzu ya tashi
barci zaisa ta makara.

Ta saukeni tare da mata alkawarin a ranan zan zo gidansu da karfe hudu tace idan mun tashi in kira
yazid yazo ya daukeni.

Akwai aiki sosai a office din mu hakan yasa ban fito da wuri ba sai after five muka fito banyi sanyi a
gwiwa ba na kira lamban Yazid din yace min sun kira ance busy yasa shi kuma ya wuce wurin kwallo.

Amma zai buga hafsat tazo ta daukeni donshine hafsat din tazo daukana ina tsaye kafin ta iso wanan
meenat din ta fito sai motar ta ya tsaya kusa da inda nake .

Saida ta fito na gane ma itace don ba motan da take shiga bace ta shigo ranan tayi tayi motar ta tashi ta
ki tashi.

Hakan yasa na dan matsa ina fadin da matsalace sister saida ta dan ja tsuki tayi min kallon banza kafin
tace wallahi ta tsayane haka kawai .

Oh kin gwada kuma baiyi ba tace wallahi banki din mu gani na fada tayi min wani kallon banza kamar
ke din sai kuma ko me ta tuna ta miko min kamar naki karba saidai na karba din.

Na shiga na gwada dabarata tayarwa daya motar ta bada kara ta juyo da mamaki tana kallona nikan na
fito na mika mata key din .

Amma da mamaki wallahi na dauka sai kuma tayi shiru tana zama tace amma dai kinsan kanta dama
nace eeh irin mota ta dace nasan matsalan ta lokacin da ita na koyi mota .

Fuska ta sake a daidai hafsat din tazo taga kuma motar datafi nata din still quality tazo dashi mukaiwa
juna saida safe muka kama hanya.

Unguwar yadda nake zato da dan nisa damu duk da kamar waje dayane saidai su suna tsalake gaba
kadan da yan nervy dake wajen.

Gidane mai kyau na fada a gani din nan wajen mai babban get dagani dai gidan wanine ko wata kusa
mai gidan muka shiga daga uwar har dan dana sani basa gida lokacin.

Saidai ashe suna zaune tare da kakan su data haifi maman da kuma wata yar uwar mahaifisu dake
zama dasu itama haka muka gaisa .

Take masu bayani da cewa inna sabuwar yar mum da take baku labarin sun hadu a hanya da itace ai
wanan din ta fada cikin hausansu na yan bauchi .
Kafin wani lokaci an cika min gaba da kayan motsa baki da komai har da tambayana dayan matar yar
uwar mahaifisu tayi wai ko zan watsa ruwane in shiga dakin hafsa in watsa nace a,a .

Sai after six mama din ta dawo gida bayan har munyi sallah magariba muna ta hira dasu hiran dai sama
sama ne don basu barni nayi bakunci ba .

Saiga mama din ta dawo daga wajen aiki tana shigowa hafsa din ta makaketa tana zuba shagwaba a
raina nace ehh yi abinki ke dai Allah ne ya baki.

Ni ba marainiya ba amma wani marayen yafini jin dadin rashin iyayye a kusa da da ban girma ba Abbu
nakanwa hakan inji dadi amma tunda na fara girma idan ya dawo na lake mai Ammah takan fatatake har
nazo na daina karan kaina.

Gashi ita ba irin hakan a tsakanin mu ina naga fuskan hakan gunta wai hakan yana shagwaba yaro a
cewanta ni dai gani nan dai Abbune kawai gatana sai Allah.

Don shine ban wasa nima da lamarin Abbu din don yayi min komai a rayuwata da nake fatan Allah yaja
nisan kwana in rama mashi halarcin da yayi min kullum addua na ke nan.

Bayan sun gama da diyar naga ta nufi wajen mahaifiyat nata dake zaune saman sallaya tana jan tasbaha
a lokacin tayi mata irin wanan gaisuwan na ruguma tare da dukawa gabab uwar ta dafa kanta tana fadin
sam barka usei usei.

Naga ta juya gurin wanan matar tace Addah barka da gida sukai wana gaisuwa na mubayi da ita kafin
tayo kaina tana fadin ohh my daughter sannu da zuwa.

Ashe kin samu zuwa din wallahi aiki ya tsayar dani nakai war hakan ban dawo ba sannu kinji can kuma
tace ina fatan kunyi sallah dai ?

Mum ai da alama bakuwan diyar taki irin kice don ina daukota saida tayi sallah haka kuma ana
magariba ta rigayi kowa tashi zuwa sallah.

Masha Allah kin gani ko hafsat ina fada maki abinda na hango akan yarinyar nan Addah na kama maki
yanzu gashi kin fada da bakinki ai .

Ta mike tana fadin bari nayi sallah ina da alwalana hanya sallah ya riskeni ban samu yi ba ta mike zuwa
wajen da uwar take ta tayar da sallah.

Allah sister mum duk abinda nayi ita dai ba daidai ba na rasa me zanyiwa mum in burgeta duniya
murmushi na sauke a fuskana tare da fadin one day zata fada har a gaban ki.

Addah din tace masha Allah kinji ko yau dai ga wanan bata san da ina fadan hakan gareki ba itama ta
fadi nan suke dan labarin halin matar nake fahintar komai a gareta.

Bayan kowa yayi sallaj isha,i kuma again aka kara gaisawa da juna lokacin na mike zubur ina fadin zan
tafi mama dare ya soma yi.
A,a a yata ko gaisawa bamu samu yi ba fa duka duka karfe nawa yanzu after eight yanzu fa cikin dan
nauyi da kunya nace ban taba kaiwa wanan lokacin a waje ba haka kada hankalinsu ya tashi.

Sam da hankalisu zai tashi aida yanzu sun kiraki suji kina ina da sun damu dake mama din ta fada sai
nayi murmushi kawai ina dan daukar jakata .

Ba zan hanaki ba ai hakan yana da kyau koba mafadi a kusa kai kayiwa kanka fada dan tarbiya shike
nuna kansa duk inda ya samu kansa dama.

Amma dai weeken zakizo muna nan mu gaisa da kyau don yazid yace min baki taso aikima da wuri ba
yau hakan yasa ya tura hafsat ta daukoki ?

Allah ya kaimu mama saiga Yazid din yashigo da kayan yan ball a jikinsa yadda uwar ta gaisa da kowa
hakan shima ya gaisa da iyayyen sai yar uwar yabawa hannu suka gaisa kafin ya ce min sallam na amsa
da wa,allakas sallam gareshi.

Badai tafiya zatayi ba mum aikuwa shi zatayi dare yayi kada hankalin mutanen gidansu ya tashi ok ya
fada yace hafsat bari na fito mu sauke tako ?

Wallahi kaman kasan nasan ni mum zatacewa na sauketa yanzu Allah kuma na gaji yau test mukayiwa
fa mum ta fada a dan shagwabe.

Ni dai ina kallon rayuwa a wanan gidan dama ance tafiya ganin gari ga wanda yaje gashi ko na ga
abubuwa a wana tafiyan.

Ya fito cikin jallabiya naji uwar tace dashi mr man i hope dai kayi sallah ya dan tabe fuska yace haba
mun tun dazun ai masalacin mlm khalid nake sallah kin sani tun seven da wani abu mukai sallah.

To Aisha kiyi hakkuri ko zama bamu samu yi ba saidai jibi din indan kin shigo in Allah ya kaimu ranan
ina gida ina up ba inda zanje insha Allahu sai mu zauna dake kinji.

Har kofan gida suka ajemu wai sai baya mun fitane suka miko min leda da bansan lokacin da aka saka
muna shiba a motar wai inji

35 / 109